Showing 27001 words to 30000 words out of 237425 words
wannan sherin”
Cewar Doc Asim cike da gadara. Ni ko ina jin haka sai tsoro ya kamani take na saka kuka, ni ce da gaskiyata amman na risina har kasa ina rokon Doc Asim yafiya, sai ya fisge kafarsa
ya daka min hannu har sai da dan yatsana ya fashe saboda zafin takalmin kafarsa. Haka suka rika ni saboda tsabar zalince suka saka ni a cell din mata ina ta kuka kamar raina zai fita.
Daga cikin matan da ke cell din ta daka min tsawa wai na yi musu sh
iru na cika musu kunne da hayaniya, a haka nai shiru na samu guri na rabe a cikin dakin mai cike da sauro da duhu sai wari yake.
Ba a bari ka fito ko da sallah za kai, fitsari ma sai dai kai a cikin cell din gaban kowa da kowa. Dukan tunani sai ya kar
karta gurin Nana ban san halin da take ciki ba, ban san iya tsawon lokacin da zan dauka a nan ba.
Da dare yai sai naga ana fita da mata masu kyau, can da asuba kuma aka kawo su, ni dai ina zaune jigum har safe ban saka komai a bakina ba, sai can da azaha
r wani dan sanda ya bude min yace na fito a nan na samu damar yin alwala na raba gafen masallacin mazan nai rama sallah da akd bina sannan na gabatar da azahar, a lokacin ne dan sanda ya kawo min abincin shimkafa da miya har da kabeji da nama, kadan na ci
saboda cikina ya daure sosai bayan na gama ya bani ruwa mai sanyi na sha.
“Idan an jima da dare zan zo na dauke ki, sai mu fita mu sha iska, idan mun dawo zan yi belinki da safe kin ji”
Na gyada masa kai cike da fahimtar inda manufarsa ta dosa, ba s
ai ya fada min na fahimci dan iska ne, ashe abunda suke da matan da suke fita dasu da dare kenan.
Yadda ya fada haka ya nufoto ni da dare guraren karfe goma sha biyu ya bude cell din wai na fito, ni ko na ki yarda na fito din, da ya shigo ya jani da ka
rfi sai na fasa masa kuka ina ta masa ihu kamar zai sace ni a dole ta saka ya kyaleni yai tafiyarsa.
A haka na kwana hudu a cikin cell babu wanda ya zo belina, abinci kuwa sai idan polisawan sun ci sun rage su ba ni raguwar ko kuma mutane za da ke cell
din idan an kawo musu sun ci sun koshi sai su ba ni ragowar. A cikin kwana biyu Allah ya hada jinina da daya daga cikin yan matan cell din, na dauke ta kamar yaya ita kuma ta rike ni tamkar kanwarta kasancewar ta girme ni nesa ba kusa ba. Bata fada min da
lilinta na zuwa cell din ba amman na fahimci kamar shaye-shaye take har aka kawo ta nan, da fira tai mana dadi take tambayata dalilin zuwana gurin na fada mata sai ta tausaya min sosai. Ita ce ta taimaka min ta fitar da ni daga cell a lokacin da aka zo bel
inta sai akai belinmu mu biyu ni da ita.
Ranar da na fito daga cell din har iskar sai na ji ta badan ina ra jina kamar mai hanci, abu ga marasa shi, daga station din zuwa uduth akwai dan karen nisa amman haka na taka da kafa idan na gaji sai na tsaya n
a hutu har na isa cikin asibitin, ban san time din da na isa ba, sai dai da naje sai suka hanani shiga, a gurin na zauna har hudu tai sannan na shiga ciki, gurin da na san na bar Nana na nufa sai na samu babu ita a gurin gadon ma har an dora wata, ban tamb
ayi kowa ina take ba na juyo na kamo hanyar Clapperto ina kuka. A iya tunani Nana ta rasu, idan ma ta rasu ina suka kai gawarta? Kangon gidan na nufo sai na tarar an saka kwano an zagaye shi an rufe ruf ba ta inda mutum zai iya shiga, a gurin na zauna nai
ta rare kukana sai da nai mai isata, ban dauki wannan abun komai ba, face kaddara da kuma jarabawar rayuwa wacce ko waji dan adam yake fuskanta sai dai kowa da irin tasa, amman a iya ganina da jina ban tana ganin wanda ya shiga matsanaiciyar rayuwar da na
shiga ba, kullum abun gaba yake ba baya ba, idan na natsu ina tunani sai na ga ban kashe kowa ba, ban hada Allah da wani ba, amman abubuwan da suke faruwa da ni kamar na kauce hanya ne, wata kila akwai wani abun da na ke ba daidai shiyasa Allah yake jarrab
ani, kuka nai mai isa ta sannan na tashi na doshi gidansu kawata Farida. Ina shiga ta yo kaina da gudu ta dafani.
“Ataa ina kika shiga? Mi ya same ki wannan irin ramar fa? Duk kin yi baki kamar ba ke ba”
Kasa amsa mata nai sai kawai na fashe da kuka
.
“Ataa ina kika shiga? Hankali Nana duk ya tashi kullum zancen ki take”
“Nana tana nan?”
“Gata a can”
Ta nuna min wani tsohon kitchen dinsu, da gudu na nufi kitchen din ina shiga na samu Nana kwance sai kawai na fada jikinta na fashe da sabon
kuka na rumgumeta kankan ina jin kamar wani zai rabani da ita. Ita kukan take ni da ita sai aka rasa mai rarrashi wani, Farida ma da ke tsaye jikin kofa tana kallon mu kuka take.
“Haba Ataa ke kuka ita kuka sai ki saka zuciyarta rauni ai”
Maganar F
arida ce tasa na tsagaita kukana na share hawayena ita na saka hannuna na share mata hawayenta. Ta rame sosai wata kila ko abinci bata samu sosai ya akai ma ta bar asibitin ta dawo nan?
Ganin na daina kukan yasa Farida ta fita ta bar ni daga ni sai Nana
.
“Nana ina Lukman?”
“Yana gidansa na gaskiya, sai idan Allah ya hada mu”
Wani sabon kuka na ji na cika min ido, sai tausayinta da shakuwarta da Lukman ta rufe ni, daman daga ni sai ita sai Lukman muka rage, yanzu kuma ya tafi ya bar mu mu biyu k
awai.
“Ina kika je Ataa”
“Karar wannan likitan na kai gurin yan sanda akan rashin kula da ke da yai da kyau, sai ya juyar da abun a kaina suka rufe a cell sai da wata mata ta fitar da ni”
“Ranar da kika bar ni ban iya kwana cikin asibitin nan ba,
sai na saci kafa da suna zuwa bandaki na gudo na dawo gida, a nan na tararda gawar dana, na nemi taimakon mutane akai masa wanka aka siya masa likkafai akai masa sallah aka je makabarta aka binnesa, a ranar mai gidan nan ya turo aka kore mu, da safe ana k
ewaye masa gurinsa dan kar mu sake zama, Farida ce tasa muka dawo nan ta ba ni kitchen dinsu na zauna a nan nake ta rayuwa da tunaninki, na dauka ma ke ma kin mutu kin bar ni ni kadai”
Na kama hannunta hawaye na min zuba kamar yadda ita suke mata zuba.
“Ban mutu ba Nana, kuma ba zan tafi na barki ba, kuma In-Sha-Allah za ki samu lafiya sosai, zan nema miki magani In-Sha-Allahu”
“Aa ba sai kin nema min magani ba, dawainiyar da kikai da ni ma Allah ya miki albarka, da kuciyarki kin fada cikin wata r
ayuwa mai tsananin wahala da sarkakiya, kina fuskantar kalubale kala kala na rayuwa”
“Idan ban nema miki lafiya Nana wa zan nemawa? Ba ni da wani wanda ya fiki a gurina, ganinki kawai yana sani kwanciyar hankali”
Dan murmushi tai sai ta koma ta kishi
ngida da alama har yanzu lafiyar bata wadace ba, taya ma zata wadace bayan ba a nema mata magani ba, ba a mata maganin daya dace ta sha ba. Babu abunda ke zuciyata sai Allah ya isa da na ke yi ma azzalumi likitan marar imani da tausayi.
A gurin muka kwa
na ni da ita cikin matsuwa domin ba kitchen mai fadi ba, gashi duk ya kone saboda girkin da akai cikinsa can baya kamin su daina girki ciki, da dare Farida ta kawo mana abinci da alama ma tuwonta ne wanda zata ci ta kawo mana, dan nasan mahaifiyarta ba zat
a taba dauka tuwo ta ba mu ba, balle yadda ake fama da tsadar rayuwar nan.
Bayan mun gama sallah asuba, Nana ta koma bachi, ni kuma na daddaka gawayin da na shafa a fuskata, na yafa hijabina na fito ba tare da sanin kowa ba, da kafa na taka har unguwar
Nasarawa, babban unguwa ce ta manyan masu kudi da yan siyasa gida gida na soma shiga ina tambayar aiki, a ganina samun aikin zai fi min bara, domin bana sha'awar baran tun da na rasa dan'uwana Lukman, amman aikin zan iya samun abinci har na kawo wa Nana.
A haka har na fada wani babban gida mai cike da fulawoyi da manyan motoci, da fari mai gadin gidan hana ni shiga yai, bayan na juyo sai kuma na ji ya kirani.
“Ke zo ana kiranki”
Da sauri na dawo na shiga cikin gidan, shi ya nuna min kofar har na
isa gaban kofar na tsaya ina ta kallon inda mutane za su fito. Zuwa can na ga wata mace ta fito wacce kudi da jindadi da rayuwar hutu suka gama bayyana kansu a jikinta. Tana kallona sai ta ya mutsa fuska.
“Me kike so?”
“Aiki”
Na Fada da sauri, sa
i ta kalli sama da kasa ta dan tabe baki ta juya cikin falon kamar tana magana da wani, bayan yan mintuna mutumen da na taba fasawa mota kuma mutumen da ya taba jefar da rigarsa saboda na taba shi ya fito cikin farar shadda riga da wando, fuskarsa kamar ta
ranar nan babu yabo ba fallasa, sai kwarjini da haifa, kallo daya nai masa na sadda kaina kasa, yau kan ban ji tsoronsa kamar yadda na saba ji ba, wata kila saboda uzurin da ke gaba ne, ko kuma dan na kawo kaina a gidansa ne.
“Look at her face, wannan
ai ta cika kazanta”
Yai magana kamar ba shi ba, ashe dai yana magana mai sauti har ta fito haka. Cikin sauri da rawar jiki na ce.
“Zan wanke wallahi zan gyara ko a nan aka ba ni ruwa wankewa zan yi”
“Nawa ake biyanki a wata?”
“Ban taba yin ai
ki ba”
“Ba ki taba ba?”
Matar ta tambaya tana kwantawa jikin mijin na ta, shi kuma ya rumgume yana mata magana kadan-kadan, ban san mi ya ce mata ba sai naga ta dago ta kalleni.
“Zan a baki dubu 8000 a wata hakan ya miki?”
“Ya min amman ina rok
on ki fara bani kudin yanzu”
“Saboda mi? Kin taba ganin inda akai haka?”
“Mahaifiyata bata da lafiya, ina son na siya mata magani da abinci, ni kuma na miki alkawarin yin aikin har wata ya kare”
“Na baki kudi ki gudu?”
“Kin fi karfin dubu takwa
s Hajiya, kuma ni miye ribata idan kin ba ni kudin na gudu? Idan ban miki aikin ba, zan biyaki kudin a lahira, mahaifiyata ce bata jindadi ki taimaka min da girman Allah”
Na fada cikin roko da neman alfarma, amman matar nan ta murje ido ta ce ita bata y
arda ba, ba za ta ba ni kudi na gudu ba.
“Ina ne gidanku ina iyayenki suke?”
Na kwatanta mata tare da fada mata cewar ba mu da gida wani guri ne mike rabe.
“Dear Za mu bata kudin, lafiya tana da muhimmanci sosai, naga hakan tun a kan ki, idan ta
gudu da kudin ta yi wa kanta”
Mijinta ne yai wannan maganar yana yana shafa bayanta, da alama yana son matarsa sosai. Ita kuma ta lake kafada wai bata yarda ba, ita ba za a bani kudin ba.
“Aa zata iya guduwa da su, baka san halin irin mabaratan nan
ba, idan kin shirya ki shigo ciki ki fara aikin”
Tana fadar hakan ta juya ya shige ciki, ni kuma na tako dan stairs din da ke gurin da zimmar shiga ciki sai kuma nai tsaye ganin yadda mijinta ya tsaya a kofar yana ta min kallon kyama.
“Ki koma gida
ki wanke wannan bakin na fuskarka ki and make sure kin canja kayanki kin yi wanka kin fito fresh sannan ki dawo aikin nan”
Ya fada yana jefo min kudin da nake saka ran sun fi dubu takwas din ya juya ya shigewarsa, ni kuma na duka da sauri na kwashi yan
dari biyar biyar din jikina har rawa yake...
*Z A K I*
By Khadeeja Candy
1
️
⃣
2
️
⃣
Kamar wacce akai wa kyauta makka yana na nufo gida farinciki ya cika min zuciya. Ina tafe fuskarta dauke da murmushi duk wanda ya kalleni ya san ina cikin farin
ciki a yau. Sallamar shiga gidansu Farida ma da karfi nai ta Mahaifiyar Farida na tsakar gida zaune tana gyara Alayyahu har kasa na risina na gaishe ta sai ta masa sama-sama sannan ta bawa banza ajiyata ni kuma na tashi na nufi kitchen da Nana take. Kwance
na same ta kamar yadda na fita na barta. Kusa da ita na zauna ina washe hakora.
“Nana na samo kudi har dubu takwas”
Dan dagowa tai ta kalleni cike da mamaki.
“Ina kika kudi har haka, bara ki kai?”
“A'a ai ba zan sake yin bara ba, sanadin raba
n nan aka kade Lukman, bana ma marmarin sake komawa bara, wani gida naje na ce musu zan yi musu aiki, amman sai sun fara bani kudi sannan na fara, na fada musu cewar Mahaifiyata bata da lafiya”
“Kuma suka yarda suka ba ki?”
“Matar ba ta yarda ba, mij
in ne ya ba ni”
Hannu ta shafa kaina tana murmushi.
“Allah ya miki albarka, wannan kalubale da kika fuskata tun a yanzu da kurciyarki Allah ya tallafa miki ya baki wanda zai mutunta ki ya zame miki gata”
Kasa amsawa nai a fili saboda kunya, sai a
zuciyata na amsa da Amin.
“Nana ina takardar msganin take sai naje na siyo”
“Ban zo da takardar ba, komai a can ya bar asibiti”
“Kai amman ban jidadi ba, yanzu ya zamu yi kenan?”
“Ataa ki daina dorawa kanki damuwa da wahalar da kanki a kaina”
“Idan ban miki ba wa zan yi ma, ba ni da kowa a yanzu sai ke, idan na rasa ki ban san iya halin da zan shiga ba”
Na fada idona tab da hawaye. Sai tai murmushi tana ta kallona cike da kauna.
“Ko asibintin za mu koma?”
“Asibiti babu komai sai ci
n kudi, kara ma kije gurin masu magani ki siyo abunda ya sawwaka, sauran kudin ki siyo mana abinci da su”
“Amman maganin chemist anya zai yi kuwa?Ai kara dai mu koma asibintin zai fi”
“Ataa na gaji da zaman asibitin nan, kuma wannan kudin idan ma muj
e karewa zai yi”
“Ko ya kare indai kin samu lafiya ba matsala ba ne”
“Aa kara dai mu ci abinci da su zai fi mana”
“Amman Nana rashin sha maganin zai iya janyo miki matsala fa”
“Da muje a kashe kudin ba a samu biyan bukata ba kara dai mu san mun
saka a ciki, tun da kika fita ba ki ci komai ba, ni ma da nake nan ban cin ba, magani ma ai ba yayi sai da abinci”
Gaskiya ta fada, sai dai ni na fi damuwa da ciwonta fiye da abincin, na san kudin ba zai isa maganin duka ba.
Ta shi nai na fita daga da
kin cikin rashin jindadin duk farinciki da murnar da na ke sai suka koma ciki.
Wani shagon provision na nufa na siyo mata biredi da madara da gwangwanin suga, ni kuma na siyo ma kaina gari da gida da suga sannan na dawo gidan, wannan karon Maman Farida
ba tsakar gidan, hakan yasa ni jindadin wucewa na shigewa inda Nana ta ke na mika mata ledar sannan na fito da dauki kofi biyu da ruwa na koma dakin, ita na fara hadawa da ruwan sanye sannan ni kuma na hada nawa garin na saka suga na sha, yadda take fisga
r biredin tana sai ka rantse da Allah ta shekara bata ci abinci ba. Tausayinta ne ya lullube, an cire mata koda daya dan zalinci, ga yunwa tana fama da ita babu mai bata sai Allah, dan ya tafi ya barta a garin nema yafiyarta. Tabbas ba zan taba manta Doc A
sim ba, ba kuma zan taba yafe masa ba, sanadinsa na kwana a cell, na rasa kanena, ga mahaifiyata a halin da ba zan iya juye ganinta a haka ba.
Idan zan yi tunani sai na rasa da wanne zan fara abubuwan duniya sun taru sun min tsaye a raina, har wani zafi
na ke jin kirjina yana yi idan ina tunani, na rika jin zuciyata kamar zata fasa kirjina ta fito.
Bayan mun gama na dauki kofunan na kai waje na wanke na aje mata a inda na gansu, ashe ta hangi lokacin da na aje sai ganinta nai ta fito rai a bace tana t
a masifa wai mun taba mata kofi kazamai da mu, a kan idona ta dauki kofunan ta wilgar bayan gidan, na ji zafi sosai amman ban nuna mata ba, domin fadanta akan gaskiya ne, ni na taba mata abu da ban taba ba da bata min wannan maganar ba.
Kitchen da muka