Showing 144001 words to 147000 words out of 237425 words
mai girma ne shiyasa bata son fada bata ma tana min zancen family ta ba, kuma bata taba cewa zata tafi g
anin su ba ko kuma ma ta koma gida gaba daya duk kuwa da irin halin rayuwar da muke ciki.
A cikin wannan tunanin ne motar Aliyu ta kunna kai cikin gidan, kawar da fuskata nai dan kar ya ga hawayena na noce kana kasa sai dai hakan be hana daya fito daga
motar ya doso inda na ke ba.
ALIYU POV.
“Mi akai miki?”
Ya tambaya fuskarsa ba yabo ba fallasa, sai ta kara yin kasa da kanta kamar tana kokarin boye kukanta. Rainawa yai daidai ita yana leken fuskarta.
“Waya taba ki?”
Banza ta masa ta k
awar da fuskarta sai ya mike tsaye ya nufi cikin gidan ya barta da kanshin turarensa. Tun daga shigowarsa falon ya ga tv a kashe babu kowa a ciki ya san ba lafiya ba, domin sun saba kunna tv ko ba sa kallo su barshi a haka, kitchen ya fara lekawa domin ya
fi tararda Momy a can ganin bata nan yasa ya wuce dakinta sai ya same ta zaune saman gadonta da magani a hannunta tana sha, yana ganin yanayinta gabansa ya fadi, da sauri ya karasa kusa da ita ya zauna bakin gadon.
“Momy lafiya?”
Momy bata iya ce ma
sa komai ba sai Husna da ke tsaye ce ta labarta masa abunda ya faru. Cikin wani irin bacin rai Aliyu ya mike tsaye da zimmar fita sai Momy ta kirashi.
“Ina za ka je?”
“Momy ba a haifi dan da zai fada miki magana na kyale shi ba, idan ba shi da hanka
li to yau zan amsa shi”
“Ban yarda ka ce masa komai ba, ban yarda wata magana marar dadi ta fitowa daga bakinka zuwa kunnen Muhseen, ban yarda ba”
Dawowa yai ta zauna babu wani abu a duniyar da ya wuce bin umarni uwa ko da ko ba shi da dadi.Zaman sa
da minti biyu zuwa uku Daddy ya shigo shi ma hankalinsa a tashe, domin ko kadan baya son tashin hankalin matarsa kamar yadda ita ma take gudun na shi.
“Kin yi kuskuren aikata abunda kika aikata Hajiya, ba lallai ne Muhseen ya fahimce ki ba, kuma tabbas
zai dauka kin yi hakan ne saboda ki hana shi ita ki aurawa Aliyu ita”
Dagowa Momy tai ta kalli Daddy.
“Ban san na yi kuskure ba sai a yanzu, kuma ta hanya daya ce na ke ganin zam iya gyarawa”
Aliyu ya yi saurin kallonta.
“Wace hanya?.... Mom
y karki ce dai za ki aurawa Muhseen ita? ”
“Ta hanyar bata dama ta zabi wanda ta ke so tsakanin kai da Muhseen ko kuma wani ma dabam, idan kuma bata son auren zai tai ta karatu har lokacim da zata ji karatun ya gundireta”
“Momy karki bata damar za bi
Wallahi Ataa bata san wanda take so ba”
“Aliyu.... ”
Daddy ya kira sunansa yana kallona ya kada masa kai.
“Tashi ka fita”
Mikewa Aliyu yai ya fice yana jin cewar abunda Momy take son ta aikata be masa dadi ba.
“Ta wannan hanyar ce kawai n
a ke jin cewar zan yi ma Ataa da mahaifiyarta adalci kuma na wanke kaina a gurin Muhseen, so babu abunda ba ya sakawa, idonsa ne ya rufe har ya iya fada min ba dadi kuma ya aikata abunda ya aikata, amman ba halinsa ba ne”
“Amman ko ma minene ai be dace
yai miki abunda yai ba, tun da ba karamin yaro ba ne shi”
Husna ta fada, sai Momy ta kalli Daddy da idonta dake cike da kwallah ta ce.
“Ina son ka min izini, na tafi Abuja gobe kamar yadda muka tsara, idan ma babu jirgi zan iya zaman mota”
“Zuwan
ki Abuja yanzu ba shi da fa'ida, zai kara lalata abun ne kawai”
“Murna kawai zan tafi saboda na fadawa Fulani zan zo gobe nai mata murna”
Daddy be ce komai ba ya juya ya fice daga dakin.Daddy na fita Aliyu ya dawo dakin ya xauna a inda ya zauna dazu
n.
“Momy kar ki yi haka dan Allah, Wallahi Ataa ba zata taba ce miki tana so na ba”
“Ba kai na ke son ta ce tana so ba, wanda duk zuciyarta ta natsu da shi na ke son tace tana so, idan kana da dama gobe zamu je Abuja tare da kai, Husna ki kaiwa Dadd
ynku abinci”
Tana fadar hakan ta kwantan saman gadon saboda zazzabin da take jin yana taso mata.
ATAA POV.
Bayan ya wuce na tashi na shiga ciki na cire kayan jikina na saka uniform din islamiyar da hijab din na fadawa Nana cewar zan tafi makar
anta sannan na fito sanye da takalmina na nufi gate na fice abuna, domin an san hanyar da ya bi da ni lokacin da zai kai ni dan haka zan iya kai kaina a kafa ma domin na saba tafiyar kafa.
Ban ankara ba na ga an faka mota gabana tare da bude min ganbun
motar.
“Shigo”
Yau ya furta ba kamar ranar da ya kasa ce min na shiga ba, ba musu na shiga na rufe motar sai na dan kalleshi kadan na dauke kai, yanayinsa na canja fuskarsa da bawa mutane tsoro da yi musu barazana ta koma kalar tausayi da damuwa. S
ai da ya fara tuka motar sannan kalleni a raunane ya ce.
“Momy zata ba ki zabin wanda kike so”
A tsakanin tambaya da labari sai na rasa wanne yake ba ni daga ciki, tambaya yake za ta ba ni zabin? Ko kuwa fada min yake.
“Ban sani ba wata kila yau
ko gobe ko jibi ko anjima”
Sai kuma yai shiru ya cigaba da tukinsa, ni kuwa ina ta karantar abunda yake kokarin sanar min.
“Ba za ki za be ni ba saboda ba ki so na, ba za ki za bi Muhseen saboda ya bata miki rai, Kamal za ki zaba saboda kina jin ce
war shine kawai mutumen da be taba yi miki komai ba”
Shiru ya kara yi kamar dai dazun ba sake cewa komai ba har muka isa islamiyar, waya yai ya sanarwa da malamin zuwana sannan ya fita daga motar ya zagayo gefena ya bude min na fito, sai ya tsaya yana k
allona har na shige cikin makarantar.Kamin na karasa cikin makarantar malamin jiya nan ya fito ya tarbe ni, wani ajin ya kai wanda ni kadai ce a ciki sai kuma shi da ya dawo dauke da tarin littafai ya miko min. Tambaya ya soma min inda na tsaya a karatuna
abunda na ke iyawa da wanda bana iyawa, sai ya fada min cewar zai mayarda ni alifun ba'un ta yadda zai zama ina iya hada harafi da kai na karanta abu, har yana fada min wai sai na yi hakuri domin zan ga a cikin sa'anina ni kadai ce na ke wannan karatun, sa
m hakan be dame ni ba, domin neman ilmi ne, ilmin ma wanda zai amfane ni duniya da lahira, ban taba jin cewar na girmi karatu ko kuma karatu ya girme ni ba, a kullum fata na bayan samun lafiyar Nana na samu na yai ilmi ko da kadan ne. Bayan ya gama mim gwa
je gwajen da zai min ya mayarda da ni wani dakin mai cike da dalibai wasu sa'ana wasu na girme su wansu kuma sun girme me sai dai dukansu suna da karatu gwanin sha'awa abun ke nuna cewar makaranta ba a wasa da karatu.
Karfe shi da daidai aka tashe baya
n an saka wata Rukaiyah ta yi mana addu'ar rufewa, haka muka jero muka fitowa daga makarantar wasu na tafe suna fira da abokan tafiyarsu wasu kuma sun koma can wani bangare suna siyen wasu abubuwan na kwalan da makulashe, sosai da sosai na jidadin zuwana m
akarantar sai ya tuna min da lokacin da na ke karama ina zuwa wacan ilamiyar ta Clapperto ta Khalifa. A inda na bar motar Aliyu fake da zan shiga a gurin na same ta sai dai yana cikin motar zaune kuma da alama ni yake jira. Karasa nai ina kallonsa ta cikin
gilashin motar wanda ya kasance fari ba kamar na dayar motarsa ba wanda ya kasance baki, ya kwantar da kujerar motar ya kwanta jikinta ya rumgume hannayensa a kirji ya lumshe ido.Ina kwankwasa kofar motar sai yai saurin bude idonsa ya kalleni tare da miko
hannunsa ya bude min motar na shigo, hannuna na kai na rufo motar sannan na maida hankalina gurin littafan da ke hannuna. Shi kuma yai ma motar key mu ka kama hanyar gida.
“Ataa.. Idan Momy ta ce ki fadi wanda kike so ki ce ni kinji....?”
Yayi maga
nar ba tare da ya kalleni ba maganar ma sai rabewa take kamar an tausar numfashinsa, ban yi mamaki abunda ya fito daga bakinsa ba domin na san Aliyu yana son Momy zai iya komai dan ya faranta mata ya saka ta farinki, Saboda ya cikawa Momy burinta, Saboda y
a faranta mata rai ko da baya so na zai iya rokon nai haka domin ya san a yanzu ba zai iya cilasta ni na yi dole ba. Kamar ya san abunda na ke sakawa a rai sai naga ya faka motarsa gefen titi ya kalleni ido cikin ido ya ce.
“Saboda Ina son ki....!”
Waigawa nai na ga ko wata aljana ce a baya da yake gani ba ni ba, sai na ga babu kowa, to ko dai shi ma ya sha wani abun ne kamar Muhseen? Anya ma dai Aliyun ne ko waninsa.
“Ni ce Ataa ce”
Na fada dan na tunatar da shi idan na manya wata kila ya dauk
a wata ce dabam ba ni ba ko kuma Rahma. Idonsa na raurau ya ce.
“Ki zargi duk abunda za ki zagar Ataa, ki fada min kalamai masu zafi da da ci irin kalaman da kika san za su taba kwakwalwata, ki tsane ni adadin tsanar da kike tunanin na cancanci samu da
ga gareki, amman karki zabi wani bokin rayuwa bayan ni”
Da gaske kalaman nan daga bakin Aliyu suke fitowa, mutumen da baya kaunar talaka da talauci shi ne ya zaunar da ni gaban motarsa yana fada min irin maganganun nan, sam ban yarda a gaske ne ba wata
kila wata gadar zanen yake kulla min idan na aureshi ya rika cin ubana kullum ko kuma wani abun ne dabam, amnan idan ba shi ba taya ma Aliyu zai ce yana so na? Taya ma zai so ni da gaske? Ina da kyau ai wata kila shiyasa na canja ra'ayi ya ji yana so na.“B
an taba jin ina son ki dan wani abu na jikinki ba”
Ya fada yana girgiza min kai, ashe a fili nai maganar ban sani ba.
“Suna nan da yawa wadanda suka fiki kyau da komai a duniya, amman da ke Allah ya jarrabe ni, a tsakanin jiya da shekaranjiya da yau
na kasa tantance irin kaunar da na ke miki, da gaske son ki na ke Ataa amman ban sani ba sai da Momy ta dora ni a hanya, sai na gane son ki ne yake ta wahalar da ni ya hana ni sukini, ban taba jin abunda na ke aji a yanzu ba, ban taba jin cewar idan wata
ta zabi wani ba ni ba zan iya shiga matsala sai a kanki Ataa, ban taba jin kishin mace ba sai a kanki Ataa, ki yarda da ni ki bani dama na bude miki duniyarki, na maye miki gurbin Abubuwan da kika rasa, zan inganta rayuwarki Ataa zan nuna miki ko wanene Al
iyu, ta aurenki ne kawai zan nunawa mahaifiyarki da ke kanki wanene ni, yanzu haka bana son na hada ido da Mahaifiyarki, ki taimaka min Ataa idan Momy ta tambaye ki kira sunana, ko da ba zaki so ni ba ki taimaka min ki aureni, Wallahi ina son ki Ataa... ”
Saurin bude motar nai na fita sam ban yarda Aliyu bane, idan kuma shi din ne to ba kalau yake ba, da kafa na karasa gidan na bar a gurin cikin mota zaune. Gaba daya rikewa nai tunanin ma na rasa ta ina zan fara, sai nuna kai na ke ni kadai ina tambayar
kaina.
“Wai ni ni fa”
Nana ma ta lura da hakan har ta tambaye ni abunda yake damuna, ban boye mata komai ba domin a halin da nake ciki a yanzu ina bokatar abokin da zan fadawa damuwata.
“Wanene Kamal?”
Ta tambaye ni domin ban sakoshi a duniya
r labarin da na bata ba wacan karon a zamana Abuja. A lokacin da na gama bata kabarinta bata ce min komai ba, bata sake tambaya wani abu ba, har aka kawo mana abincin dare muka ci muka kwanta. Washe gari kamar kullum na tashi da wuri na yi sallah ni da Nan
a sannan na koma na kwanta ina ta tunanin abunda ya faru jiya sai komai ya zame min kamar mafarki kamar ba gaske ba.“Amman Nana Aliyu fa.... ”
“Aliyu ya aikata kwatankwacin abunda na aikata a lokacin da kaddara ta rubuta min haka, yana da zuciya mai kya
u Ataa tunda har iya taimaka mana ke ki samu ilmi kiji dadi rayuwa ni kuma na samu lafiya, be yi kokarin boye abun ya rufe a gidan yan sanda kamar Asim ba, mahaifiyarsa ta kyautata mana kuma ta yi fatan ki samu rayuwar jindadi shiyasa ta nemi ki auri danta
, indai har mutum mai daraja mai ji da kai da kudi kamar Aliyu zai yada kansa ya bude ba ki ya roke ki ki so shi to ko ya cancanta ki so shi Ataa, ina jin a rai shi ne mijin da nake miki rokon samu kuma nake miki fatan samu, ba zan cilasta ki ba domin ni k
aina cilastawa bata min amfani ba, ina baki shawara ne a matsayi na uwa kamar yadda nawa iyayen suka shawarce ni na ki”
Hawaye na sauko min maganganun Nana na ratsa ni, amman har gobe zuciyata Kamal take kauna.
“Karki kalli abunda Aliyu ya aikata a
matsayin cin amana, domin be zalince mu ba, fada Ataa wace ya ce zata gudu ta bar iyayenta kuma ta ce zata ga kyau? Ta yi sammani komai ya zo mata da sauki? Kaddara ce a haka na gode Allah ya abun ya zo min ta nan kawai na gode ma Allah, Ataa ina son tun i
na da rai na ki samu mijin da zai aure saboda Allah uwarsa ta dauke ki kamar yarta, domin ni na san mutuwa tana zuwa gobe ko anjima, ina son kamin na tafi na san na barki a cikin jindadi da farinciki, ina tsoron kar amin azaba biyu hakkin biyewa iyayena da
kuma hakkin kin zaba miki miji na gari, yarinya ce ke Ataa ba ki san komai a yanzu wanda yake miki dariya yana yaba ki shi kike daukar cewar yana sonki wanda kuma yake nuna miki illar abunda kike shi kike yana kokarin kare miki mutuncin ki shi kike dauka
a matsayin makiyinki, wanda kashi saba'in cikin dari na mutanen duniya haka suke, kar duniya ta rude ki kamar yadda ta yi min a lokacin da nake da kurciya, duk wanda zai so ki dan kyauki zai iya gudunki idan kyau na ki ya guje, wanda kuma ya guje ki dan ta
laucinki zai iya son ki idan arziki ya same ki kuma ya sake guje miki idan talauci ya rabe ki, amman wanda zai so ki dan ya gyara rayuwarki ba dan kyau ki ba, be kuma dubi talaucin da rashin danginki ba ya so shi ya fi cancanta ki so fiye da kowa Ataa, miy
asa Muhseen be duka ya roki ki so shi ba? Sai ya nemi tada hankalinki? Miyasa Kamal be biyo ki har nan ya nemi ba, sai ya zabi ya kyale ki yai wata rayuwar, idan kika samu wani anjima ya ba ki abinci da kudi yai miki dariyar fuska shi za ki ce kina so, Ata
a ba ki san so ba, wani be taba zowa ya ce a sallamo masa ke ba, bara kawai kike sani mu yi baran na yau da na gobe shi kawai kika sani, yadda za a baki nera ki saffarata ki ci abinci shi kawai kika sani, hakkina ne idan babanki baya raye na baki ilmi na c
iyarda na shayar da ke na nema miki magani,amman ban yi ba ban koya miki komai ba sai bara Ataa, da ban gujewa dangina ba da duk haka be faru ba, shin kin samu wanda zai fanshe ni ya baki duk wannan miyasa ba za ki karba ba?”
Da yaren buzanci ta jera mi
n komai a kwakwalwarta ta karasa tana fashewa da kuka.
“Guduwa kika yi Nana?”
“Ba shi da amfani, tun da babu komawa har a bada babu wannan zancen”
Ta fada tana share hawayenta.Ban leka sashen Momy ba sai misali goma har da rabi na safe, a lokacin
har mun karya ni da Nana sai dai daga ni har ita ba mu wani ci abincin sosai ba, na yi zaton idan na ce zan je bangaren Momy zata hana ni ne amman bata ce min komai ba har na dauki kayan da muka ci abinci na nufi part din. Amina na samu a kitchen tana kun
a gas da alama abincin rana zata dora tun yanzu maimakon Momy. Na gaishe ta cikin mutunci da girmamawa ita ma ta amsa min tana murmushi.
“Ina Momy”
“Sun tafi Abuja”
Sai na ji ba dadi da amsar da ta bani wata kila abunda ya faru ne yasa suka tafi
abuja, ita da wa ma suka tafi oho.
“Ita da yaya Aliyu”
Amina