Showing 66001 words to 69000 words out of 237425 words
wace kalma ta ta sai ya tsinci kansa a kogin tausayinta, yes she's right da ace yar mas
u hannu da shuni ce da Doc Asim be yarda ko yatsanta ya taba ba balle har ya cire kodar mahaifiyarta, and secondly na ji zafin hawayen da ta zubar da cewar da tai Mama Fulani ta mareta, yasan Halin Mama Fulani daman ba jutuwa take da yan aiki ba, shiyasa d
uk wacce aka kawo da taje ganin gida bata dawowa, a dayan bangaren kuma yana jin haushin yadda Muhseen yake masa. Iya kokarin da yai ta isa gida ba tare da Rahma ta gane yana cikin damuwa ba, ko da ya isa ya sameta a falo dinning mai dafa musu abinci namij
i yana serving dinta, yana daya daga cikin dalilin daya saka take son zama a Abuja a nn ko kofi bata kawarwa mai musu aiki ne namijin dan kabilar igbo yake mata komai ciki kuwa har da dafa abincin da gyara duka dakunan. Juyowa tai ta kalleshi da far'a da a
lama tana cikin farinciki.
“Dear welcome”
Karasawa yai kusa da ita ya kai bakinsa ya sumbanci gefen kumatunta sannan yaja kujera a kusa da ita ya zauna.
“Na yi waya da Doc Perry gobe zan je na ganshi”
Shiru nai na wani dan lokaci sannan ha ka
lleta.
“Why ba zaki bari sai nan da kwana biyu ba idan kin huta”
“Ba wani zancen hutu, tunda yanzu na samu lafiya ai zan iya komai, kara kawai na maida hankali gurin neman haihuwar”
Ya gyada mata yana mikewa tsaye kamar be jidadin. A daren da tun
ani biyu ya kwana a ransa, na ganin Doc Perry da Rahma ta ce za tai da kuma na Ataa wanda be san dalilin na damuwar kansa da tunaninta ba. Ko da suka tashi da safe mai dafa musu abinci ya gabatar da komai a beburin karyawa, a tare ya karya da matarsa sanna
n na ya shiga dakinsa ya shirya cikin shiga ta manyan kaya ya fito yai mata sallama ya kama hanyar kamfaninsa.
A kamfanin ya wuni duk wani abun da akai baya nan sai da aka gabatar masa da shi ya ganshi kuma ya duba yadda komai yake tafiya kowa ya san d
a cewar oga ya dawo sannan suka shiga meeting, bayan sun fito ne yake labartawa Nasir zancen ganin Doc Perry da Rahma zata je yi.
“Then why da ba zaka fada mata gaskiya ba? For how long za kai ta aje wannan sirrin ne Aliyu?”
“Ban sani ba, iyakar abu
nda na sani zan iya ajiyarsa har karshen rayuwata, kawai kasa a nemo min Doc Perry ina son magana da shi”
“Haka zaka daukarwa kanka a duk lokacin da zata je ganin wani likita sai ka samu kudi ka bashi a rufe maganar? Anya hakan zai haifar maka da da mai
ido Aliyu? Idan ma kai baka son ganin iyalinka ai familynka suna so, muma kuma muna so”
“Matata tana da muhimmanci a gareni Nasir, idan ta san gaskiya ni ne zan fi shiga damuwa domin zata saka kanta a damuwa ne, kuma duk abunda nai mata zata ga na mata
ba daidai ba, and kasan Mama Fulani ma zata fara damunta just like Momy daman can ba jutuwa suke da Momy ba”
“Amman wannan kawai ya isa ka kasa kanka a wannan matsalar? Kana ganin idan kai ne Rahma zata zauna da kai? No ina da Tabbacin duk yadda take s
on ka ba zata zauna da kai ba, shekarar ku takwas da aure Aliyu idan baka fara tunanin samun haihuwa a yanzu ba, zuwa yaushe zaka fara? Lokaci yana tafiya, a yanzu nan gaba kadan karfin ragowa zai yi ba karuwa ba, ya kamata kai tunani”
Aliyu ya tsaya ci
kawa bakinsa iska a lokacin daya riga Nasir shiga office din.
“Kamin na ga wasu yayan Rahma na fara gani, be kamata ace wani abun ya shiga tsakaninmu ba”
“Haihuwa ita ce shiga tsakani? Kai ba haihuwar ka akai ba?”
“Yes i mean kasan yanzu idan kow
a ya gane gaskiyar Rahma zata shiga matsala ta shiga damuwa, kuma muna son junanmu ni da ita, be kamata abunda be riga ya zo ba ya saka mu damuwa”
“Ina da tabbacin da akanka ne Wallahu Rahma ba zata zauna da kai ba, zata fi son ganin gudan jininta fiye
da kai, ballantana tana ganin cewar tana yar nai nera zata iya samun wani mai nera ta aura”
“Baka san yadda Rahma take so ba ne Nasir baka san so ba ne”
“Fine, idan kana son ka gane gaskiya ka daina cewa kai da ita ba ku da matsala, ka fada mata cewa
r kai ne mai matsalar wannan karon idan kunje tare ka biya Doc Perry ko nawa yake so ya fada mata haka, na tabbatar zaka ba ni wani labarin dabam”
Aliyu yai shiru yana nazarin kalaman Nasir. Ta wani bangaren yana ganin kamar be dace ya gwada Rahma kamar
haka ba, wani bangaren na zuciyarsa kuma yana ta zugashi akan ya gwada din. Har ya bar office din be samu matsaya daya akan gwadarwa ko kin gwadarwa ba, ya sa dole zata kira shi tace mishi tana asibiti ya sameta a can a gwada lafiyarsu ta bangaren haihuwa
kamar yadda ake musu a ko da yaushe, sai dai ba shi tabbaci ko Doc Perry zai yarda da hakan ba har ya aikata domin shi babban likita da kowa ya san da zamansa cikin garin Abuja, matukar kana amsa sunan mai nera to ka san Doc Perry, likita daya kware akan
aikinsa kuma yake fadin gaakiya a ko da yaushe, ba iya nan kawai yake duba mutane ba har kasar waje an san da zamansa, sai dai Rahma bata taba damuwa da su je gurinsa ba, sai a yanzu da haihuwar ta fara damunta. A hanya yai sallah la'asar sannan ya isa fam
ily house gurin wato gidan Alhaji Hamza. A harabar gidan yai parking amman be fito cikin motarba ya tsaya dannen dannensa har ya hango Ataa ta fito daga Garden daga ita sai daura gaba, kirjinta a cike ga farin daya bayyana kansa a jikinta, gashin kanta a j
ike da alama wanka tai ko kuma ruwa ta fada, amman idan ruwa ta fada ai dole har tufafin jikinta zai jike, be taba kula da surar mace karamar yarinya kamar yadda ya kula da ta Ataa yau ba, karamar yarinya ce amman tana da abunda yake kauna a jikin mace wat
o breast ga yawan gashin kai, wanda ko Rahma da take babbar mace bata kaita breast ba, ga gashin kai kamar wacce akai wa dashe ya kwanta har gaban goshinta gwanin sha'awa, and every takunta jikinta motsawa yake fatarta na sheki kamar mai shafa wani kasaita
ccen mai. Kasa dauke idonsa yai daga kanta har ta shige garejen ba tare da ta kula da shi ba.
“Miyasa tai wanka a Garden?”
Ya tambaya kansa cike da mamaki kamin ya tuna da cewar ai babu bandaki a garejin. Then miyasa ba a aje ta BQ ba? Ya sake tambay
ar kansa sai dai wannan karon a zuci yai tambayar kamin ya hade yawun bakinsa ya bude motar ya fito ya nufi part din Ammy sai da ya fara gaisawa da ita kamin ya shiga part din Mama Fulani. A falo ya samu kowa ban da Muhseen, Maryam da Rukaiya na ganinshi s
uka natsu sosai ko motsi kirki basa yi, cikin mutumci suka gaishe shi ya amsa musu kamar yadda ya ba fuska a daure sannan ya gaishe da Mama Fulani ita kan fuska a sake. Be yi zaman mintuna biyar ba Ataa ta shigo falon sanye da wani milk lace wanda ya kara
fito da kyau sosai sam ba zaka ganta a hanya ka za ci yar talaka ce ba, lace din ya kara fito da kyauta da jan fatarta sosai ta yi mugun kyau duk da kasancewar bata shafa mai ba balle ma hoda haka ta fito naturally beautiful. Kasa dauke ido daga kanta Aliy
u yai yana ta kallonta kamar yau ya fara ganin mace mai kyau, yanayin tausayin da ke fuskarsa yasa shi jin tausayinta ba tare da wani dalili ba, q nan ya lura da tabon bulalar da ke fuskarta da kuma kumburar da fuskar tai da idonta, tafiya take kamar zata
fadi saboda rashin karfi na yunwar da take ji. Tana karasowa gaban Mama Fulani ta zube tana mika mata ragowar sabulun da ke hannunta.
“Gashi na gama wankin na wanke dika”
Ta fada cikin wata sautin murya daya saka tsigar Aliyu tashi.
“Je kitchen
ki aje”
A nan Ataa ya hade hannayenta ta kama kafafun Mama Fulani ta rike ta fashe da kuka.
“Ki taimaka min dan girman Allah ki ba ni abinci yunwa na ke ji kamar na mutu....”
“Bata ci abinci ba?”
Aliyu ya tambaya yana kallon yadda hawaye suke
sauko a idonta kamar ba gobe.
“Ai tun jiya da tai maka rashin kunyar nan ban bata abinci ba, kuma na fadawa Ammy karka bata, na sa Maryam ta zane mata jiki, kuma yau na hada ta wankinsu tun safe sai yanzu ta gama, haka zan rika mata tun da ta zabi yi m
a mutane rashin kunya”
Wani irin abu yaji na rashin jindadi yana ratsa zuciyarsa a take tausayinta ya rufe shi, how old she's da za a ace tai wanki tun safe har la'asar and an a hana mata abinci kuma a saka Maryam ta dake ta duka saboda shi, a tunanin M
ama Fulani rashin kunya tai masa shiyasa ta yanke mata wannan hukuncin.
“Ke zubo mata abinci”
Ya fada yana kallon Rukaiya, da sauri ta tashi ta nufi kitchen din ta zubo mata abincin a plate ta kawo sai ta tsaya gabanta.
“Tara dankwalinki a zuba
miki ko kuma ki je ki dauko plate dinki”
“Bata da darajar da zata ci abinci a plate din ne? Give it to her....!”
Ya dakawa Rukaiya tsawa, da sauri ta mikawa Ataa plate din, cikin wani irin rawar jiki Ataa ta karbi plate din ta aje a gabanta ta saka h
annu biyu tana cin abincin da su bata iya hakurin har ta cinye da dama ta sake debowa saboda azabar yunwar da take ji, sai dai idan ta ci da dama ta ci da hagu bata ma tsayawa tauna abincin sai dai kawai ta hade, jikinta na ta rawa sosai. Wani irin tausayi
nta ne ya rufe shi, ko ba komai saboda abunda akaiwa mahaifiyarta take aiki a gidan saboda ta sama mata magani kamar yadda ta fada masa, kuma sune silar ciwon mahaifiyar kusan shine silar komai ma, domin ko dukan da Mama Fulani ta saka Maryam tai mata ai s
aboda shi ne, iya kar abunda yake jin zai iya yi a yanzu na taimakonta ne ta samu saukin rayuwa a gidan kamin ya karkato da hankalinta har ta yarda ya taimaki mahaifiyarta ya nema mata magani.
“Mama pls karki sake horata da yunwa”
Ya fada cikin taus
hin murya kamin ya kalli Maryam yana mai jin haushi na rashin dalili cikin kakkausar muryar ya ce.
“Karki sake dukanta, tun da ba yar ki ba ce”
“To Ya Aliyu”
Ta amsa da sauri sannan ita da Mama Fulani sukai kallon kallo, mamaki ya gama cika su ga
ba dayansu. Wani bakin haushi da bacin ran abunda akai ma Ataa ya rufe shi, ga kuma tausayinta a bangare daya, yana ta kallon yadda take auna abincin a bakinta kamar wacce bata taba cinsa ba sai yau. Tsarkiwa tai ta fara tari tana ta wani abu kamar za tai
amai saboda cikinta daya kulle.
“Kawo mata ruwa”
Ya fada yana kallon Maryam da mamaki ya kusa kashe a inda take zaune. Tashi tai taje ta debo mata ruwan na fonfo ta kawo mata Ataa ta saka hannu biyu ta karba.
“Na gode”
Ataa ta fada sai ta kaf
a bakinta ta shaye ruwan gaba daya. Tana dire kofin Sulaiman Mai ban ruwan fulawoyin gidan ya shigo da sallamarsa, aka rasa mai amsa sai Aliyu saboda kasaita kowa ganin yake ba zai iya amsa sallamar wanda yake kasa da su ba.
“Wai Kamal ya ce yana salla
ma da Aisha”
Aliyu ya kalleshi Mama Fulani da sai yanzu ta samu damar magana ta ce
“Aisha ko Maryam dai?”
“Aisha dai ya ce”
“Ba mu da Aisha a nan gidan”
“To”
Ya tashi da sauri ya fice, sai kuma ga shi ya dawo ya sake zubewa kasa kamar daz
un.
“Ya ce wai Aisha mai aikin a nan gidan Ataa”
Mama Fulani ta kalli Ataa da bata san wainar da ake toyawa ba sai aikin aika abincin take a bakinta sannan ta kalli Sulaiman ta ce.
“Wane Kamal din wai?”
“Kamal dai soja wannan makocin mu”
“
Ya ce yana kiran wannan yarinyar”
Mama Fulani ta fada tana nuna Ataa da tsananin mamaki.
“Haka dai ya ce”
“Tashi ka yi tafiyarka”
Aliyu ya fada masa sannan ya mike tsaye ya bi bayansa yana wani irin taku na kasaita da isa. Mama Fulani ta kalli
Maryam.
“Wai ko dai manta sunanki yai?”
“Hmmm Wallahi ba wani mantawa kyau ne yake rudarsu, ba ki ganin wannan yarinyar kamar aljana”
Rukaiya ta fada tana kallonta, sai Mama Fulani ta kirata dan kara tantancewa.
“Ke”
Ataa ta dago ta kalle
ta.
“Na'am”
Mama Fulani ta kura mata ido tana ta kallonta kamin ta gyada kai.
“Eh lallai ko ba shakka”
Maryam taja tsaki.
“Shegiya mai kama da mayu, duk sai na yanke gashin kan nan”
Ataa dai bata ce musu komai ba, da ta gaji da yadda su
ke ta hantararta sai ta tashi ta fice daga falo dauke da plate din da cofin ruwan domin ta san Mama Fulani ba zata taba son kayan ba tun da ta yi amfani da su.
*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence
via 08036126660*
ZAKI
By Khadeeja Candy
22...
Ya Muhseen ya gyara tsayuwarsa yana kallon da mugun mamaki.
“Me kake nufi? Dan iska ne ni?”
“Ko ma dan ruwa ne kai ta shafa”
Aliyu ya fada mishi sannan yai min alama da na zo na wuce da id
o, komawa nai cikin na dauko mopper da tsintsinyar na fito, duk irin rashin tsoron sa da nake yanzu kan na ji tsoron yadda na ganshi na san zai iya min wani abun ko kuma wani fadan ya shiga tsakaninsa da Ya Muhseen wanda a karshe ni ce aciki domin ni za a
daka. Sai da na fice sannan ya biyo ni a baya ina ta sauri kar ya cin min har na shige part din Mama Fulani, sai gashi ya shigo cikin tsannanin bacin rai.
“Mama”
Ya kwala mata kira sai gata ta fito daga kitchen din da sauri.
“Mama kar yarinyar n
an ta sake shiga part din Muhseen da sunan gyara masa daki, idan a cikin kanennsa ba zai saka wata tai masa ba ya hakura da gyaran kawai”
“Cewa kikai ya miki wani annmimiya?”
Mama Fulani ta fada, nikan tuna har na fara kuka domin na san ni za a doraw
a laifi.
“Bata ce ba, ni dai na ke ganin rashin dacewar hakan tun da ba muharramarsa ba ce”
Da mamaki Mama Fulani ta kalleni ta kalli Aliyu sai kuma ta kalli Muhseen da ya shigo yanzu cikin bacin rai.
“Kai wani abun ka mata?”
“Ban mata komai
ba, yadda yake dan iska haka yake tunanin kowa ya ke”
“Ni ba dan iska ba ne ka fi kowa sani”
“Then why ni zan zama dan iska? Ba uwa daya ta raine mu ba? Kai baka iya kyautatawa kowa zato? A yadda kaga dama haka kake son taka mutane? Ba zai yiyu ba Wa
llahi idan zaka taka kowa yadda kake so a gidan nan ni kan ba zaka iya da ni ba, sai dai bakincikina na kashe ka”
Aliyu be sake cewa Muhseen komai ya zauna a sofar da ke kusa da kofar yana ta huci kamar wani zaki.
“Zan baka mamaki Aliyu kuma fadan y
anzu muka fara ni da kai”
Mama Fulani ta karasa fito daga kitchen din tana girgiza kai.
“Haba Muhseen? Haba Aliyu wannan wace irin rayuwa ce”
Aliyu ya dago ya kalleta.
“Mama miye laifina dan na ce kar a barshi ya kebe da wacce ba muharramarsa
ba? Yarinya mai jini a jika kamar wannan za ki turara dakinsa ace ta share?”
“Kai muharramarka ce da ka kebe da ita jiya a Gareji? Waya san abunda kai mata take kuka?”
“Muhseen....!”
Mama Fulani ta daka matsa tsawa.
“Mama ba za mu taba shirya
wa da wannan mutumen ba matukar ne dauke wannan girman kan da son milkin kowa ba, ba zai yiyi yace zai juya kowa yadda yake so ba, ba a karkashinsa na ke ba, dan haka ba zai yiyu ya ce zai juyani yadda ya ke so ba”
Mikewa Aliyu ya ya fice daga falon cik
in wano irin zafin rai marar misaltuwa. Mama Fulani ta nufo inda na ke tsaye zata dake ni.
“Zo nan bakar munafuka ai duk ke kika hada komai”
Sai Ya Muhseen yai saurin tsakaninmu ya tare ni.
“Karki da ke ta Mama, za ki dauki alhakinta ne kawai, b
a ki iya ganin laifin Aliyu sai dai wasu, bayan kuma shi ne mai laifin, kuma Wallahi sai na bashi mamaki”
Ya fada sannan ya juyo ya kalleni.
“Wuce daga nan”
Da saurina na fice daga falon har ina tuntube kamar zan fadi, abun ka da mai shegen tsoro
haka nai ta kwara ido a garejin ina ta jiran wani daga cikin yayanta ko kuma ita kanta ta zo ta dake ni amman shiru