Showing 201001 words to 204000 words out of 237425 words

Chapter 68 - ZAKI COMPLETE

taba yin fushi da ni ba sai amman yadda na ga ya hade rai na san ba lafiya ba. Kallon jikina nai duk da nasan ba a jikina ba ne matsalar domin ni kadai ce a falon ba tare da kowa ba balle har ya ce wani ya ganni babu Hijab.

“Wani

abun nai ba daidai ba?”

Na tambaya ina turo baki kamar nima din wani abun akai min.

“Yanzu ba dan neman magana ba, miye na wani daukar tsintsiya ki yi shara daga nan sai kice mopping za ki yi ki yi wankewanke da wasu abubuwa ko? Na san halinki ai,

kuma can da da kike ke kadai ba ki yi ba sai yanzu da kuka zama ku biyu?”

“Ina yi ai ko lokacin?”

“A gidan Momy ko? Tun da aka miki aure kin taba shara? Sai yanzu za ki tsiro saboda neman magana kuma idan na ce ki daina ki fara min gardama?”

Na je

far da tsintsiyar.

“Na daina, naga gidan yayi datti ne kuma babu mai sharewa”

“Da muka dawo haka kika ganshi? Kin san lokacin da ake shigowa a share ko a goge ne?”

Na rausayarda kai.

“Wuce ki yi wanka za mu je mu yi ma Mama barka da tashi, ku

ma za mu koma asibitin gurin likitan”

“Mi zai min?”

“Zan siyo magani a can kuma ina bukatar ganinsa dan ya fada miki irin abubuwan da zaki rika ci da yi da kunnenki kiji domin ni kin raina ni idan na ce ki daina sai kokarin yi za ki yi”

“Aa ban fa

raina ka ba”

“Zamu gani”

Ya fada yana jam kumatuna ba tare da ya mim murmushi ba, a dole na koma ciki nai wanka na shirya kamar yadda ya bukata, a tare muka fito da shi yana kallon yadda yake kallon tafiyata wata kila so yake yai sauri ko na taka ba

daidai ba yace da gangan na ke yi saboda ina da ciki. Shi ya bude min motar na shiga sannan shi ma ya shiga ya zauna, sai ya kai hannunsa a bakinsa yana karanta abunda ban san ko minene ba sannan ya saka dayan hannunsa ya daga Hijab dina ya bude rigar zan

en da ke jikina ya shafa min addu'ar a ciki. Sannan yai ma motar key daman tuni mai gadin ya bude mana gate, a hankali ya fara tukin har muka fito daga cikin gidan.

Na yi zaton gidan za mu fara zuwa sannan mu wuce asibitin sai ya fara zuwa asibitin sai d

ai ba wacan ba ce domin wannan katuwa ce sosai ga ma'aikata ta ko'ina gwanin ban sha'awa. File aka fara bude min sannan ya sake tambaya ko ina jin sani abun bayan abunda na fada mishi jiya.

“Bana jin komai”

A nan ya sake rubuta wani abun a farar taka

dar ya mikawa Aliyu.

“Ka kara mata da wannan, wannan kuma results dinku ne na jiya congratulations”

Aliyu yayi murmushi yana kallona, kunya ce ta rufe ni nai kasa da kaina ina watsa da yan yatsuna cikin Hijab.

“Doc ka fada mata abunda ya kamata t

ai da wanda be kamata ba da abubuwan da zata ci”

Aliyu ne ya bukata da kansa, a take likita ya fara lissafa min irin abubuwan da zan rika ci da kuma aikin da zan yi wanda ba mai wahalarwa ba.

“Aa no doctor ni fa ko bokitin ruwa ba zata dauka ba, bal

le wani shara da wanke wanke”

“No ai aikin yana da kyau amman kar ayi na kashe kai”

“Ko na raya kai ba za ayi ba, balle na kashe kai, ina ciki fa aka ce Alhaji”

Aliyu ya fada yana nanatawa, shi kuwa likitan sai dariya yake, ni dai gaba daya kunya

ta gama kamani har bana iya daga kaina.

“Ta so muje”

Tashi nai ina tafiyar cike da kunya shi kan tuni ya kai kofa har ya bude min kofa yana jira na fito, sai na fita sannan ya fito, ba ko kunya ya kama hannuna zuwa gurin motarsa da kansa ya bude min

sai da na shiga na zauna sannan ya rufe ya zagoyo gefensa ya zauna, tukin mota yake amman gaba daya hankalinsa da tunaninsa na kaina, minti biyu uku sai ya kalli inda na ke.

“Kina son wani abu? Kina jin wani abu?”

Yayi min irin wannan tambayar ta ka

i sau takwas kamin mu isa family house na su, a harabar gidan ya faka motarsa har na kai hannu zan bude sai ya danna dan wani abu dake gefen motarsa motar ta rufe, kallonsa nai sai ya fara min magana a natse.

“Kin dai ga cikin mutane ne, bana son ki je

ki ci wani abun da zai lalata miki ciki ko ki ci da yawa, kuma ki ci yaji ko ki zauna da yunwa, da ama ace Mama ce kadai ko Ammy zan iya yi miki magana a ganbansu amman Mama (Nana) ba zan iya miki magana a gabanta ba, pls ki kula da kanki”

“Tau”

“I

love you”

Ya fada sannan ya cire abun ni kuma na bude motar na fita ta nufi bangaren Ammy, sai na ji ya kira ni.

“Babyna, za mu fara zuwa mu gaishe da Mama”

Juyowa nai na karaso inda yake tsaye ba tare da na ce masa komai ba, a tare muka jera mun

a tafiya zuwa part din Mama Fulani, yana ta kallon yanayin tafiya kamar mai kirga yadda na ke takawan. A falo muka samu Mama Fulani zaune kanta sanye da hular wanka hannunta kuma rike da brush an zuba masa mai daurin kirji ne a jikinta sai kuma wani karami

n tawul da ta rufa a saman jikinta, Rukaiyah ya mata kafafuwanta. Zaunawa yai kusa da ita, ni kuma na zauna a dayar kujerar sai kallona take kamar bata taba ganina ba, gaba daya ta wani yi sakuku kamar ba ita ba, ni ban taba ganinta a cikin yanayin tausayi

ba sai a yau.

“Mama yanzu kika tashi?”

“Eh Aliyu”

Ta amsa tana aje numfashi.

“Na'am, amman Mama ba ki jindadi ko?”

Ya tambaya cikin yanayin da ke nuna tsantsar kulawarsa a gareta.

“Muhseen ya duba ni ai, kuma yanzu idan nai wanka na kar

ya zan sha maganai”

“Mama ina kwana”

Na fada ina dan risino kaina alamar girmamawa, sai ta kalleni kawai ta kasa amsawa kamar mai jin nauyi ko kunya, mikewa tai tsaye ba tare da ta amsa min ba ta nufi hanyar dakinta sai da tai rabin stairs sannan ta

juyo ta kalleni sai kuma ta dauke kai ta shige dakin.

“Ku baku iya gaisuwa ba ne?”

Maganar Aliyu ta saka na maida duba a gurin Maryam da ke gyaran cucumber da kuma Rukaiyah wacce ta gama matsawa Mama Fulani kafafuwanta.

“Ina kwana ya Aliyu?”

Har sauri suke gurin gaishe shi suna hada baki.

“Ba ni ba ita, matata ce yadda kuka respecting dina haka ita ma za ku mata”

Ya fada babu alamar wasa a tare da shi, a tsakanin Rukaya da Maryam ban san wa yafi wani nauyin baki gurin gaishe ni ba, ni k

an wani irin kunya da girma ne ya rufe ni a lokacin ba dan na san sai ya cilasta ni amsawa ba da ba zan amsa ba, sosai na ji daraja ta ta dagu, ba kuma dan sun san wacece ni a yanzu ba, sai dan auren dan'uwansu da ke wanda ya zama dole su girmamani ko da k

uwa sun haife ni.

“Ta so muje bangaren Ammy mu gaishe su”

Ba musu na mike tsaye, ina gaba yana bayana har muka fito daga part din Mama Fulani muka nufi bangaren Ammy.

“Ba dan Mama tana jin kunyarki da nauyinki ba da yanzu ta rumgume ki tana nuna

miki jindadinta da farincikinta aka my samun cikinki”

Ban ce masa komai ba, muka cigaba da tafiya, fuskarsa ba yabo ba fallasa muka nufo bangaren Ammy sai dai muna shiga falon ganin Muhseen zaune yasa ya dan canja fuska kamar be ji dadiba, ni kan har na

yi farat zan fara masa magana sai na tuna cewar ina da aure a yanzu kuma ina tare da Aliyu. A saman kujera yake zaune Kamar yadda Ammy da Nana ma suke zaune a saman kujera, tun da nai sallama ya dago kansa ya kalleni sai ya maida idonsa gurin wayar be sak

e dagowa ba, har na zauna ina gaisawa da Ammy da Nana, Aliyu ma ya gaisa da ita, sai Muhseen ya mike tsaye ya face daga falon idonsa akan wayarsa ni kuma na bi shi da ido ina juyowa Aliyu ya watsa min harara a cikin sigar da babu wanda zai gani ya fahimta

sai ni da akai wa.

Mikewa yai ya fice daga bangaren Ammy ya bar a nan, ni kuwa na tashi na koma kusa da Nana na zauna a kasa na dora kaina saman kafafuwanta, sai ta fara shafa kaina tana murmushi.

ALIYU POV.

Sam be jidadin ganin Muhseen ba ba

kuma dan komai ba sai dan yana tare da Ataa, idan ya tuna cewar Muhseen ya taba son Ataa abun tana taba shi kuma yana jin babu dadi, duk kuwa da kasancewar ya aureta amman wannan kishin yana nan cikin ransa. Ko da ya shigo bangaren Mama Fulani yayi zaton z

ai samu Muhseen a falo ko dakin Mama Fulani amman sai ya samu akasin haka, domin kuwa Mama Fulani ce kadai a dakin zaune rike da brush din dazun tana kallon wani gurin kamar mai tunanin domin shigowarsa kadai har da zabura tai.

“Mama har yanzu laifina

kike gani?”

Bata ce masa komai ba sai lasa lips dinta da tai cikin yanayin damuwa.

“Wallahi Mama Nasir ne ya kawo min wannan shawarar amman ba wai dan wata manufar nai ba”

“Ina maka murna Aliyu wannan babban abun farinciki ne da jindadi, ba zan i

ya fada maka ko misalta maka yadda na ke ji a yanzu ba, sai dai abun bakinciki na zan iya nuna ba”

“Saboda mi Mama”

“Kai ma ai ka sani Aliyu duk wani abun da zan musu a yanzu ko na nuna farincikina ba yarda za su yi da ni ba, kuma har abada Ataa ba x

ata daina ganin cewar bana sonta balle kuma abunda yake cikinta. Aliyu kunyar kaina na ke ji, kunyar kaina na ke ji sosai”

Ta fada idonta cike ta kwalla har ya fara sauko mata, murmushi Aliyu yai yana kokarin nuna mata shi be ga wani abun damuwa ba.

“A rashin sani kika aikata Mama, kuma ni danki ne, Ayusher ta sani dole ki so abunda yake cikina tunda har kina so na, na fada mata bani da kamar ke da Momy a duniyar nan, ni yanzu abunda na ke so ma idan kin yi wamka kin shirya kije ki roka min Mamanta t

a bar min matata ni ba sai ta je d ita can nijar ba”

“Nijar za su tafi?”

Ta tambaya tana share hawayenta.

“Eh ta fada min tun shekaranjiya cewar Mamanta tace za su tafi ta ga dangi tare da Sarkin Agadaz za su tafi idan zai wuce, da na yi nijar bi

n ta muje tare, yanzu kuma na canja sha'awara gaskiya idan tai tafiya mai nisa da wani ganin dangi jagalgala cikin za ayi, kara dai tai hakuri sai idan ya girma sai mu tafi tare ko kuma idan ta haihu”

“Gaskiya ni ma ban bada goyon bayan ta tafi yanzu b

a, taya zata fara yawo da karamin ciki ma?”

“That's why I love you Mama, kina da mugun fahimta, yanzu dai ki yi wanka sai ki je ki yi magana da Mamanta ki roka min ita”

“Aa ba zan iya ba”

“Zaki iya”

“No-no Aliyu i can't ai da kunya nai maganar

a yanzu ma, duk abunda zan yi kar suke kallona, jiya mahaifiyarta ta kasa sakewa da ni, itam Ataa ba so zata tai b Wallahi balle har tai tunanin abun kwarai zan mata”

“Mama pls for me? Ai za ki iya min komai ko?”

Ta gyada kai cikin damuwa.

“To pl

s ki yi magana da ita as my mother kuma saboda grandchild dinki ba wai as abunda kika aikata cikin rashin sani ba”

Yawun bakinta ta hadeye ta tashi ta nufi bandaki cikin yanayin damuwa.

*Manage pls*

“Ina ganin zai fi kyau idan ka hakuri ka bi m

atarka Aliyu, ko kuma ka kira Momy ko Ammy ka rikesu su yi ma mahaifiyarta magana idan zata yarda ta barta na wani lokacin idan cikin yayi kwari”

Tana zaune bakin gado take fadin wannan maganar bayan ta fito daga wanka, Aliyu ya dago kansa daga kan waya

rsa ya kalleta.

“Ko na bita hankali ba zai kanwata ba Wallahi, kuma kin san ba ni wanda zau shige min gaba yai min ruwa da tsaki a wannan lamarin sai ke”

“Ba zan iya ba Aliyu, Wallahi ina tsananin jin kunyar kaina balle kuma na hada ido da Ataa ko m

ahaifiyarta, da ace komai be faru ba da yanzu ba haka ba”

“Amman Mama”

“Aliyu ba zan iya ba, dan Allah ka je ka samu Ammy ko Abbahku kai masa wannan maganar”

Ta amsa masa kai tsaye da dukannin gasjiyarta, taya ma zata iya zuwa ta ce zata roki abar

Ataa saboda cikinta? Yarinyar da ta gama wulakantawa ta aybanta. Ai wannan ya zama rashin kunya ma. Aliyu be sake cewa komai ba, ya mike tsaye ya fice, har ga Allah baya son tafiyar Ataa a garin nan yanzu ya san duk yadda zai bata kulawa a nan dole a can

sai ya daga mata kafa wani abun ma ba a gaban idonsa za tai ba, gashi tafiya ce ba nan kusa ba, waya sani ma ko ace sai taga kowa da kowa tukuna za su dawo? Ba wai baya son haduwarta da danginta ba ne, shi yadda za a jigilgila cikin ne baya so. Yana son ci

lasta Mama Fulani tai ma Nana magana ne saboda bakinta da na Nana ya hadu a wani gurin na nunawa Ataa kulawa, ko da ba zata yarda ba akalla yasan Nana zata san cewa Mama Fulani ta damu a yanzu, and hakan da za tai a yanzu matakine na murje ido ta nuna koma

i ba komai ba ne yadda za a zama abu daya, amman ya saka samun hakan daga gareta, ya sani abunda Mama Fulani ta aikata ba daidai ba ne, shi kanshi baya ganin laifinta ko ganin kuskurenta har sai yanzu da yake kokarin gyara na shi kuskuren. Cikin mota ya ko

ma ya zauna ya kira wayar Nasir tana yin ringing  yai picking kamar mai jiran kiran.

“Babban Baby gani a hanyar gidanka fa da Madam”

“Gurin me?”

“Zata zo ta ga Ataa ne kasan ba su taba haduwa ba, and tana son taya ta murna samun ciki”

Yar dari

ya Aliyu yai shi kanshi Nasir sai da yai dariya sannan aliyu ya dora da.

“Bana gida ni da ita muna nan gurin Mama, Nasir ina son magana da kai”

“Ayyah bari na sauke ta gidansu yayarta zai na same ka a can”

“Alright”

Aliyu ya kashe wayar yana t

a kallon garden gidan da ke facing din inda motarsa take fake. Fita yai daga motar ya nufi bangaren Ammy sai kuma ya samu kansa ya kasa shiga ciki sosai yake jin kunyar Nana shi kanshi har Mamakin abun yake, domin ko iyayen Rahma yana sakewa da su da su ne

kai tsaye zai iya nuna musu baya son matarsa tai nisa da shi balle kuma ace tana da ciki abunda yake kauna.

Har ya ciro wayarsa ya kira Ataa sai ya tuna da be saka mata line a ciki ba, a take ya aikama Nasir text, sannan ya juyo zai dawo part din Mama F

ulani kuma sai ya hango Muhseen ya shiga can sai kawai ya nufi gate yana ta sake sake a ransa, he can't face Nana kai tsaye ya fada mata haka and idan Mama Fulani ba zata iya zuwa tai magana da Nana ba ba zai iya rokon Ammy ba, domin a ganinsa idan har Nan

a da Mama Fulani ba su samu fahimtar juna ba shi kan shi yana cikin matsala. Bakin gate din ya fito ya tsaya yana danna wayarsa, number Rahma ya kira tai ringing har ta katse ba a daga ba, ya sake kira ba a daga ba ya san wannan baya rasa nasaba da fushin

da take da shi, sai kawai ya aika mata da sako. Jin motsin mutum da yai bayansa, zuciyarsa ta raya masa Ataa dan yasan ita kadai zata masa haka duk duniya sai kawai ya saka hannunsa ya rikota ta baya ya juyo da ita, sai ta saka dariya.

“Mi ya kawo ki n

an?”

“Naga lokacin da ka zo gurin Ammy ai sai kuma ka  koma”

Kallonta yai sai kuma ya kalli gate din gidansu Kamal a take zuciyarsa ta raya masa cewar Kamal zai iya fitowa ya ganta, and abunda ya fi tsana a yanzu wani wanda ya tana son Ataa ya ganta

ko, a duk lokacin daya tuna cewar Ataa ta furta masa cewar tana son Kamal sai ya ji ba dadi.

“Koma ciki nima Nasir na ke jira”

“To mu jira shi tare miyasa ka fasa shigowa ciki?”

“Kunyar Mama na ke ji, ke ma ki je ciki Mama Fulani na son magana da

ke”

“Ni?”

“Yes shiga gida mana”

Ya fada mata calmly yana kallon cikin kwayar idonta, wani irin kaunarta yake ji cikin ransa.

“I Love you”

Ya fada mata a hankali, sannan kama hannunta ya rika sai kuma ya saki ya tura hanninsa ya bude mota kof

ar gate din, har ta juya ta shiga Muhseen ya fado masa a rai sai yai saurin bin bayanta.

“Babyna karki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login