Showing 138001 words to 141000 words out of 237425 words

Chapter 47 - ZAKI COMPLETE

ne ai ban yi illa ba”

Tasowa Aliyu yai daga saman kujerar da yake zaune yana fadin.

“Ataa ba ki da hankali kuma kur

ciya na damunki, Momy kina ganin abunda na ke fada miki ko? Ya ganta tana wanka ta na canja tufafi kuma shi ne yanzu a tsaye a gabanki har kina amsa dariya? Wallahi baki san ciwon kanki sam”

Muhseen yayi murmushi har zai yi magana sai muka hi Aliyu ya k

yalkyale da dariya mai karfi wacce ban taba zaton bakinsa na iya irin wannan dariyar ba.

“Magana ta fito Muhseen kana son Ataa saboda ka ganta a sirara, Wallahi wannan nuna mata rashin daraja ne da raina mata hankali, what a shame lallai kai yaro ne kum

a wawan duniya tun da har tsiraicin yake maka sha'awar kallo what a sad”

Yana fadar hakan ya fice yana dariya dariya irin sosai din nan kamar ba ta hankali ba.ALIYU POV.

Duk wata dariya da yake na fuska ne kawai amman ransa cike ya ke da bacin rai d

a bakin cikin jin cewar Muhseen ya taba ganin Ataa tsirara wani abun yaji marar misaltuwa har yana jin kamar kirjinsa zai rabe biyu, sai kuma ya ji kamar ya danne Muhseen ya cire masa idanuwa. Be san abunda ya kawo shi yau ba ma, gashi yana cewa ba za a ta

fi da Ataa abuja ba saboda shi da Kamal shi kuma yazo yanzu.

Yana faka motarsa harabar gidan sako na shigowa wayarsa, ganin sunan Rahma yasa shi budewa domin baya cikin mood din saurare kowa a yanzu.

_I'm sorry akan abunda ya faru, Mommy ta yi fushi n

e sosai shiyasa amman dan Allah ka yi hakuri, kuma ina neman izininka zan tafi Dubai jibi_

“Really?”

Ya furta bayan ya gama karanta sakon.

“You will regret this Rahma ke da iyayenki”

Ya fada sannan ya bude motar ya fita zuwa cikin gidansa, haka

ya kwana a gidan cikin wani irin yanayi na bacin rai tsakanin wanda Rahma tai masa da abunda Muhseen ya fada sai ya rasa wanne ya fi masa zafi. Ko da ya tashi da safe kansa kamar zai tsage sabar bacin ran daya kwana da shi jiya, he feel unsafe sai da yai

wanka ya shirya cikin wasu tufafin ya dauki hanyar arkilla tun da farar safiya haske ma be gama bayyana ba. Ko da ya shiga falon babu kowa sai ac da wutar da aka kunna, but he got lucky yau Momy a part din ta tai sallah asuba after Daddy ya tafi masallaci

ita kuma ta dawo part dinta tai sallah, daman ta kan yi haka wani lokaci wani lokacin kuma acan take yin sallah ta. Tura kofar dakinta yai ya shiga ba dan ya tabbatar tana ciki ba, idan ma bata ciki shi zai kwanta a nan ne for a while hankali zai fi kwanci

ya ace yana gidan fiye da yana can dabam. Zaune ya same ta saman carpet karbin a hannunta tana ja. Ita kanta ta yi mamakin ganinsa da safen nan.

“Lafiya dai?”

“Lafiya kalau Momy ina kwana”

“Lafiya Kalau, amman ba lafiya na ka zo da safen nan”

Ya yi shiru na wani lokaci sannan ya ce.

“Momy wai Rahma ta turo min sako zata je Dubai”

Da mugun mamaki Momy ta kalleshi.

“Dubai? Da izinin wa?”

“Wai izini take nema”

“Uhmm Wallahi Rahma nan ta maida wani sholobiyo, daman tun farko kai ka

nuna mata fita ba da zininka ba ai, yanzu kuma ganshi ba nan, maganinta kamin ta dawo ka auri wata Wallahi”

“Yes nima abunda na kwana da shi a raina kenan”

“Haka ma za a mata, kuma idan zaka bi nawa Ataa na ke son ka aura wacce ta raina take ganin b

a komai ba ce”

Kamar saukar Aradu haka Aliyu ya ji maganar Momy, Ataaa Ataaa Ataaa Ataaa sunanta na ta maimaita kansa a kunnensa, da sauri ya kalli Momy.

“Momy Ataa?”

“Yes”

“Amman..... ”

Sai kuma ya mike tsaye ya saka hannayensa aljihu ya d

aga kansa sama yana shakar iska kamin ya sauke ya juyo ya kalli Momy.

“Momy seriously?”

“Yes don't you like her?”

“I do, but.....”

Sai murmushi ya subuce masa ya shafa kansa.

“Momy ke kike fada min wannan da kanki? I can't believe this”

Murmushi Momy ta yi.

“Do you love her?”

Shiru yai na wani lokaci yana sauraren yadda zuciyarsa ke mugun bugawa with full farincikin da be daga ina yake sauko masa ba.

“Momy wasa dai kike min?”

“Indai tana son ka da gaske na ke yi”

“Zata so

ni mana Momy ai ita bata san so ba, zan koya mata komai Momy trust me”

Ya fada yana dukawa ya kama hannayenta duka biyu ya rike, shi kanshi sai yanzu yake jin cewar son Ataa yake yi, duk wani abun da ya dade yana jinsa akanta sai yanzu kullin ya watse

a jikinsa da zuciyarsa, domin tun da ta zo duniyarsa sai yake jin kullum kamar a takure yake.

ZAKI

By Khadeeja Candy

39...

Kamar an diga man kuli a cikin ruwa mai mugun sanyi haka Aliyu yaji jinin zuciyarsa ya taso yayi tsama saboda kalaman Muhse

en.

“Kai Pretty wai kin duba madubi yau ko? Gaskiya Allah ya iya hallita”

Cewar Muhseen yana kara kallon yadda uniform din yai mata mugun kyau kasancewarsa Maroon color, ga gashin kanta data sakawa ribbon ya sauko har bayanta gwanin sha'awa. Ko wace

kalma ta Muhseen Aliyu hade ta yake da yawun bakinsa, ba kuma iya yawun ne kawai yake hadewa ba har da abunda yake ji yana taso masa yake dannewa, shi kanshi ya san yayi abunda ba zai iya ba, yana tsaye wani na yaba kyau matarsa.

“A a ba mu da madubi

ai”

Ataa ta fada tana murmushi.

“Zo na nuna miki kanki a wayana”

Ya zauna a kujerar da ke kusa da shi yana ciro wayar daga aljihunsa na gaba, bata zauna din ba ta juyo ta kalli Aliyu wanda idonsa ke kan wayarsa tunawa da yace ta daina sakewa Muhs

een.

“a a bari na je na duba a Mota”

Ya fada sannan ta fara takawa zata wuce Muhseen ya bi bayanta da kallo komai na jikinta motsi yake a cikin uniform din kasancewarta mai tubultubul kuma uniform din ya dan kama jikinta din jiki ga shi bata da koma

i a ciki, da gangan yai hanzarin kai hannunsa ya kama gashin kanta ya juyo da ita ta rika yatsun hannunta.

“Pretty ina zoben da na baki...?”

Bata amsa shi ba tai saurin fisge hannunta tana kallon Aliyu hankalinta a tashe kamar wacce za ayi ma wani a

bu.

“Muhseen....!”

Aliyu ya daka masa tsawa a cikin muryar da shi kan shi be san da zamanta ba.

“Karka sake kuskuren yabon kyau Ataa balle ka ce zaka kai dan iskan hannunta ka taba ta, wannan ya zama na karshe ina nufi na karshe....”

Magana A

liyu yake ma Muhseen cikin tsawa yana nuna Muhseen da yatsansa kwayar idonsa gaba daya ta canja ta rine kamar ba shi ne da farin ido ba, shi kan shi Muhseen sai da gabashi ya fadi domin ya razana sosai da yanayin da ya ga Aliyu. Kamar kyalftawar walkiya ha

ka Ataa ta bace bat a cikin falon kamin ta isa Bq har da gudunta, ganin irin tsawar da yai ma Muhseen da yake kanensa kuma dan'uwansa to ita kan ta san nata dukanta zai yi. Da sauri Momy ta fito daga kitchen tana kallonsu, kannensa ma Amina, Siyama da Husn

a duk sai da suka fito daga dakunansu jin yadda falon gaba daya yake amsa muryar Aliyu. har be janye yatsansa daga nuna Muhseen da yake ba sai rawa yatsan yake kamar zai da ki Muhseen da hannunsa.Wani irin abu yake ji yana masa yawo cikin jini wanda be tab

a jin irinsa ba, duk wani kishin Ataa da yake a can baya na yanzu ya ninka shi ninkin ba ninkin, ya yaba kyauta ya janyo gashinta kanta ya rika yatsanta, tunawa da irin kallon da yai mata da kalamansa na jiya sai ya ji kamar an yanga tsagen jikinsa an zuba

r a kasa, har lokacin Muhseen be iya cewa komai ba banda kallon kallon da suke da juna shi da Aliyu.

“Wai miye haka ne? Shikenan idan kuma abuja hankalin Fulani ya tashi idan kuma kuna nan nawa ya tashi? Wannan wace irin rayuwarce?”

Aliyu ya juyo ya

kalli Momy.

“Ki fada masa ya daina shiga gonata”

“In daina shiga gonarka ko ka daina shiga gonata? What kind of nonsense is this, idan ina yaba kyau Ataa ko magana da ita ko taba ta miye matsalar ka da wannan?”

“Babu har sai ka sake”

Aliyu ya

fada yana daga masa gira sannan ya fice daga falon zuwa bq.

“It's because tana gidanku?”

Muhseen ya fada a fusace yana bin Aliyu da kallon haushi.

“Muhseen nan mu ba gidansu ba ne, gidanku ne”

“To idan ba shi ba Momy miye ruwansa da ni? Nag

a dai ba shi da alaka da ita kamar yadda ni ma ba ni da, kuma son Ataa na ke son ta na ke be isa ya hana hakan ba... ”

Amina ta kalli Momy Momy ma ta kalli Amina kamin ita Aminar ta juya ta koma cikin dakinta.

“Na rasa gane kan Aliyu”

Muhseen ya

sake fada.

“Ka yi hakuri Muhseen zan masa magana, ka yi hakuri dan Allah”

Maganar da Momy ta masa ce ta saka ya zauna saman kujera yana ta huci da mamakin yadda Aliyu yake son masa fin karfi.

ALIYU POV.

Tafiya yake yana kamar ba kasa yake tak

awa ba shi kan shi be taba jin kanshi a cikin irim wannan yanayin ba kamar yau. Ji yake kamar ba zai jure wani ya kara yabon kyau Ataa ba, ko da mace ce balle namiji. Yana shiga bq din Ataa ta daka tsalle tana ihu ta yi bayan Nana da ke zaune ta boye gaban

ta sai faduwa yake ta yi zaton ko dukanta Aliyu ya zo ya yi, duk da bata tsoronsa a yanzu amman tana tsoron yanayin da ta ganshi a yanzu. Yayi kokarin sauke fushinsa ya dan saki fuska sannan ya taka balcony din yana isa bakin kofar dakin da Nana take ciki

ya tsaya ya cire takalminsa sannan ya shiga, risinawa yai har kasa kamar jiya ya gaishe ta ya mata ya jiki ta amsa masa fuska a sake Ataa na bayan Nana zaune tana dan lekoshi ta kawar da kai.

“Dan Allah Mama kar a sake bari Ataa ta fita tsakar gidan na

n babu mayafi a jikin, kin ga akwai aljannu masu shiga jikin mutum gidan be rufe jiki ba, ko ka rufe ma ya aka kwashe balle kuma ba a rufe din ba? Yana da ta rika rufe jikinta da gashin kanta”

“In-Sha-Allah zai rega sakawa, muna goziya jiya kaya sun zo

masu kyau Allah ya biya”

“Amin”

Yana amsawa da amin ya mike tsaye yana watsawa Ataa wata uwar harara domin mugun haushinta yake ji kamar ita tace Muhseen din ya kama hannunta ya rike, ita kuma ta murguda masa baki ta buya bayan Nana.ATAA POV.

Yan

a fita na fito daga bayan Nana na zauna daidai ina turo karamin bakina.

“Wai shi baya son ya ga wani na min far'ah ko muna wasa ko magana, ya fi son ya gan ni cikin bacin rai, idan yaga wani ya sakar min fuska ji yake kamar an masa ruwan mutuwa a zuciya



Da yaren buzanci na fada cikin mugun jin haushinsa. Dariya Nana ta yi tana kallona ta ce.

“Tunda ba ya so ai sai ki daina, namiji baya jindadi idan yana ra'ayin mace yaga wani namijin na kula ta”

“Wacan zai ra'ayina? Wallahi duk ya bi ya tsane

ni ban san abu da nai masa ba, bayan ma ni na fi dacewa na natseshi”

“Ki tsane shi aka ce mi? Ai baki da wata hujja ta tsanarsa, domin ya gama mana komai a duniyar nan”

“Haushi na yake ji kila ma dan yaga na fi shi kyau ne, sai wani ji da kan banza,

kuma sai na kula Muhseen din haka kawai sai na yi ta shiga kunci ina bakin rai kamar shi, haka jiya ya kori mai koya min karatun nan da ya zo, wai ya cika far'a ya fi son ya ga ina ta bakinciki, shi fa dariya ta bakinciki take saka shi mtchhhhhhh”

Na ka

rasa ina jan tsake har ga Allah yau kan Aliyu ya ba ni haushi, ban san abunda na tsare masa ba yake bakincikin ganin dariyata, wani lokacin ma sai yai ta abu kamar ba shi ba, dazun da naje tambayarsa ai dariya yai min, jiya yai min siyayya har ina jindadi

amman yau ya canja kamar ba shi ba.

Murmushi kawai Nana take tana kallona kamin ta koma murza yatsun hannunta.

“Yanayin yaron nan yana tuna min da mahaifinki, haka yake kishi a lokacin da yake so na, ni kuma ina kishinsa saboda kyausa, idan yayan many

an sarakai suka zo nema na ranar ba zai yi bachi ba, saboda yana jin kamar zai rasa ni”

Ta fada da yaren buzanci hawaye na sauko mata, sai na kara matsawa kusa da ita na kwantar da kaina jikinta, sai ta shafa kan nawa hawayenta na sauka a kumatuna.



Mutuwa ba tai kyau ba”

Ta fada da hausa tana son fashewa da kuka. Nima hawayen na soma yi tunawa da Baba na na san da yana raye duk wannan rayuwar ba mu shige ta ba, balle har Aliyu ya nemi takura domin Babana yana so na sosai. Ganin ina hawaye yasa tai

saurin share nata kukan tana dariya kamar ba ita ba.

“Yana can cikin rahamar Allah In-Sha-Allah”

“Eh Nana yana cikin Rahama Allah ya jikanshi”

“Amin”Sanye da uniform Siyama ta kawo mana abun karyawar mu bayan ta gaisa da Nana ta fito daga bangar

en mu ni kuma na biyota ina tambayarta ko nima zan iya zuwa makarantar.

“A a yau ba a zuwa sai da yamma, ai ita Islamiya sai assabar da lahadi kawai ake zuwa da safe”

“Na sani, amman na ga wata islamiyar idan mutum baya zuwa makarantar boko sai ya ta

fi islamiyar safe”

“Wannan ba a zuwa”

“Sai kin dawo Allah ya tsare”

Na fada ina kallonta gwanin sha'awa, sannan na juyo na dawo bq din na soma cire uniform din ina tunanin maganar Nana ta dazun wai idan yayan manyan sarakuna suka zo sai yai ta kis

hi, lallai Nana ta yi farin jini tunda har da yayan sarakuna sukai nemanta.

MUHSEEN POV.

Yana zaune a falon har Aliyu ya fito daga bq ya shiga motarsa ya dauki hanyar gida. Tunani yake ta yi yadda Aliyu ya zo rana tsaka yake son hana shi kula A

taa, idan ma wai wani sonta yake to shi mai gaba daya zai yi idan take takensa kenan shi zai fito kai tsaye ya aureta ya ga yadda zai yi. Har Momy ta gama hada breakfast din ta zubawa Siyama ta kuma zuba na su Nana ta bawa Siyama ta kai musu Muhseen na zau

ne a gurin be huce ba, a dinning ta jera sauran ta fada masa ya tashi ya karya sannan ta wuce bangare Daddy dan kai masa na shi su karya tare. Bayan ta gama da Daddy ta sallame shi ya wuce gurin aikinsa ta dawo part dinta sai ta samu Muhseen zaune a dinnin

g shi kai yana cin plantain a hankali kana ganinsa kasan hankalinsa baya jikinsa, shi kai ne a dinning din hakan na nufi Amina da Husna sun gama karya sun tafi shi kuma ko rabi be yi ba. Sai da Momy ta kai kulolin data dauko part din Daddy kitchen sannan t

a dawo dinning din ta ja kujerar da ke fuskantar ta Muhseen ta zauna.

“Ba ka ci abincin ba?”

“Momy ina tunanin ya kamata na fadawa Abbah da Daddy zancen Ataa kara su san da maganar, idan ma karatun za tai ko wani abu sai tai a gidana, ko waje ta kam

a sai a fitar da ita ai”

Momy ta dan yi shiru na waji lokaci tana sauke ajiyar zuciya. Kamin ta kalli Muhseen a natse ta fara magana.

“Shekaranjiya na tafi gidansu Rahma gurin bikonta, wai ta yi yaji ta tafi gida saboda mijinta na kula Ataa, nemawa

mahaifiyarta magani da zuwa dubata da yake sai Rahma ta dauka son ta yake, shi ne tai fushi ranar da na je bikonta ni da kawata babu kalar maganar da mahaifiyarta bata fada min ba saboda Ataa, tana kiranta da yar talakawa yar bara a titi wai yar su ba za t

a yi kishi da Ataa ba”

Tun da Momy ta soma maganar Muhseen yake kallonta dan shi be ga ta inda wannan abun ya shafe shi ba, domin ba matsalar wani ce yanzu a gabansa sai ta shi.“Gaskiya Rahma bata kyauta ba, kuma be dace tai haka ba, cewa akai Aliyun so

n ta yake ne?”

“Ni kaina ban jidadin abunda mahaifiyarta da ita Rahma kanta su kai na tun farko, kuma ina tunanin tana wannan abun ne saboda tana ganin it kadai ce a gurin mijinta, shiyasa na yanke shawarar...”

Sai ta kasa karasawa kamar mai jin nauy

i. Muhseen ya kashe kunne sosai ya maida hankali yana saurarensa, main reason din yake son ya ji domin ya fara fahimtar inda zancen Momy na dosa.

“Shawarar me?”

“Wata kila Fulani ba zata bari ka auri Ataa ba, ko kuma idan ka aureta ta gallaza mata,

ko wani abun ya samu kyauta wanda zai iya sakawa wata rana ka sabu da ita ko musguna mata, amman ina da tabbacin Aliyu ba zai iya juya mata baya ba ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login