Showing 12001 words to 15000 words out of 237425 words

Chapter 5 - ZAKI COMPLETE

wani ya cire ba, domin ba kowa zai yarda ya bada kodarsa ba”

Aliyu yai shiru kamar mai nazari can kuma ya kalli Mommy ya ce.

“Ba lallai ya zama haka ba, kin san Nigeria ce, akwai talakawan da ba su san darajar

kansu ba, za su iya siyarwa saboda kudi”

“Amman ko talaka sai wanda talaucinsa ya kai makura gaskiya, ai sai da lafiyar ake neman kudi”

Momy ta fada with doubt. Aliyu yai murmushin kasaita.

“Momy kenan ba ki san talaka ba, na san Doc Asim zai iya

siye zuciyar talaka da kudi ya samu abunda ya ke so, domin ya san shi ma zai fanshi fiye da haka a garemu, shi fa talaka wawan mutum ne, indai za ka nuna masa kudi to zai maka komai na duniyar nan”

“Wato ďan wajen Fulani kai da Maman ka Fulani ban san

wanda ya fi wani kyamar talaka ba, su ma fa mutane kamar mu duka daya muke a gurin Allah”

Ya kalli Momy cike da mamakin yadda take hakikancewa idan ana maganar talaka.

“Momy kenan, ai Mama Fulani gaskiya ta ke fada, tsakanin mu da talaka sai dai akw

ai mu amfana da shi shi ma kuma ya amfana da mu ta hanyar biyansa hakkinsa, amman ni ko abota bana fatar ta hada ni da talaka”

Daddy yai murmushi yana dafa kafardar Aliyu ya mike tsaye.

“Sai ka yi hanzarin samun Doc Asim ku tattauna, kasan matsalar

matarka ita dayar kodar na daf da daina aiki”

“Yeah haka za ayi, san same shi mu tattauna, Thank you Dad”

“Your Welcome”

Daddy ya fada yana nufar hanyar da zata sadashi da part dinsa. Momy kuma ta mike tsaye tana fadin.

“Talaka ba shi da kima a

idonka kai da uwarka Fulani”

“To ai ba shi da kimar ne Momy ki ce kin ki gane sai hada shi kike da mu, bayan kuma ba daya ba ne, as long as ba da ganganci Doc Asim ya cire kidney din nan ba babu abunda zai dame ni, ni zalince ne kawai ba na so, indai n

a san na biya ka to dole ka min aiki ba wani uzuri da zan dauka, so indai siyenta Doc Asim yai ni ya kyauta min wlh kuma zan bashi fiye da abunda zai tambaya”

Ya fada yana mikewa tsaye ya nufi dinning area, wani kebantaccen guri ne da ya kusan ayi babba

n falo da shi amman ba a zuba komai a gurin ba sai kato dinning table da freezer, daya daga cikin kujerun dinning din yadi aja ya zauna yana kallon Momy wacce ta taso ta nufo shi tana fadin.

“Ba ka ci abinci ba ka fito? Matar ta ka har yau ba ta iya gi

rkawa ta baka ba?”

“Momy kin san lafiya be isheta ba, kodar ďaya da ke jikinta ma ance ta fara lalacewa, so ba komai na ke bari tai ba, and Momy kin san wahala ai sai talaka”

“Au ni da nake shiryawa Daddynku fa?”

Murmushi yai kadan yana dora duka

hannayensa saman dinning din.

“Ai ke Momy saboda kin kwana biyu ne, ke da kina da kurciya ai Daddy ba zai bari ki yi girki ba, i rather na yi oder a restaurant da nai forcing dinta ta girka min, besides ba komai ta iya girkawa ba ita a gidansu ba aiki

take ba”

Momy ta tabe baki tana saka masa sikari kwaya biyu a kofin tea. Bayan ya gama karyawa ya sauko daga dan stairs din dinning din yana taba wayarsa ya nufi kofar fita kanensa na mika masa gaisuwa. Kai kawai ya daga musu ba tare da ya amsa musu ba

sai kara hade fuska yake kar su ga damarsa.

Fitowa yai harabar gidan yana amsa kiran Rahma, da yai picking shiru yai har sai da ta fara magana cikin yanayin damuwa duk da irin faduwar da gabansa yai jin muryarta kamar tana cikin damuwa.

“Dear ina dri

ving na kade wani”

“Hope babu abunda ya faru?”

“Ya ji mu a kafa da kai”

“Lafiyarki na ke tambaya”

Ya tambaya kamar maganar bata son fitowa daga bakinsa, sai dai tashin hankalin da ke zuciyarsa da burin jin lafiyar matarsa ya saka shi fidda numf

ashi kadan-kadan.

“I'm fine amman shi mutumen ya ji ciwo”

“As long as be mutu ba, ba wata damuwa ba ce, turo min address din inda kike yanzu”

Be jira abunda zata ce ba yai hanging, he don't mind ya tambayi inda zata je ko abunda ta je yi, saboda

ya yarda da matarsa ko kasar zata bari bata fada masa ba ba damuwarsa ba ce indai zata je kalau ta dawo kalau. In few minutes ta turo masa sakon inda take sai ya forward massage din to the one of his bodyguard.

_Ka samu Madam a wannan address din, ka b

iya wanda ta kade ko dubu nawa ya ke so, and make sure matata ta isa gida lafiya_

Yana tura masa sakon ya mayarda wayarsa aljihu ya nufi motarsa yana wani shan kamshi.

ATAA POV.

Hankalina ya tashi sosai lokacin da na ga yamma ta gabato mahaifiy

ata bata ko matsa ba balle ta bude ido, ban san kan aikin asibiti ba, amman a yadda na ke jin ana cewa ko tiyata akai wa mutum indai ya kwana ya wuni yana farkowa sai dai tawa uwar shiru. Ina ji ina gani yunwa ta saka ni a gaba tana ta cina ni kuma na gaga

ra kai ko da ruwa a bakina na natsu ina ta sauraren kukan da cikina ya ke min. Shiru shiru babu wanda ya sake leko dakin likitan be dawo ba, sai da yasa an aiko mana da abinci dare, a nan Lukman kawai ya ci ni kasa ko da kallon abincin balle na kai hannu n

a ci.

   Bayan na gama sallah isha'i ina ta kaiwa Allah kukana, sai na hango Nana na motsa har tana yawo da kanta, da sauri na mike na tsaye na rika gadonta ina kiranta cike da jindadi.

“Nana Nana Nana”

Shiru bata amsa min ba sai juya kan take yan

a dantsar baki kamar bata cikim hayyacinta, ban yi dabarar na je kiran nurse ba balle kuma likita sai kawai na daga zanen da aka rufa mata na ga inda aka mata dinki yana fitar da jini kadan-kadan  ganin hakan yasa na fita daga dakin da sauri na nufi wani d

an guri mai kamar reception inda nurses da yawa maza da mata suke tsaye wasu kuma a zauna.

“Mama ta ta motsa amman bata magana kuma na ga jini gurin da aka mata aiki”

Na fada cike da damuwa, sai duk suka tsaya suna min wani kallo kamar na kyama, a n

an na kalli tufafin jikina hakika na yi dauda sosai tufafin da ke jikina wadanda na saba sakawa ne kullum, kuma ba damuwa nai da na wanke ba, gashi dazu na ji girki da kara sun kara datti, sai dai ba da dauda na ke a yanzu ba ta lafiyar Nana na ke. Daya da

ga cikinsu taja tsaki kamin ta aje biron da ke hannunta ta nufo ni tana fadin.

“Ni Wallahi ba son irin kazaman patient din nan na ke ba, idan kuma ba ka kula su ba ace ba ka yi aikin ka ba”

Sai sauran suka saka dariya, sai duk na ji na muzanta na ji

babu dadi amman hakan be hana ni binta a baya ba ita kuma tana gaba har muka shiga dakin.

https://chat.whatsapp.com/HlKVwXU1HwlIrs8jJeHHqZ

*Z A K I*

By Khadeeja Candy

6





ALIYU POV.

Kamar kullum idan zai kwanta sai ya tsaya ya du

ba wasu abubuwan a laptop dinsa haka ma idan ya tashi da safe musamman abubuwan kamfaninsu na samar da gas wato Sky Global Resources, babban kamfani ne da babu irinsa a nigeria wanda ke samar da gas da man fetur da ma hako wasu ma'adanai na kasa da saffara

su, kuma shi yake wakiltar babban reshensu da ke Abuja inda ake tura komai, hakan yasa dole komai rashin lokacinsa dole ya matse a haka ya kula da wasu abubuwan.

A dakinsa ya ke amman ko'ina n dakin kanshin expensive perfume din Rahma yake, yana daf

da rufe laptop din Rahma ta turo kofar dakinsa ta shigo hannunta rike da mug, bakinta ya sha janbaki har kyali yake, wata rigar bachi ce a jikinta mai kamar rariya, komai na jikinta a bayyane yake kamar ma bata saka ba komai ba. Dagowa yai yana kallon yadd

a ta nufo shi tana wani irin taku kamar kwararriyar karuwa, da fuskarka ta miskilanci, a lokacin da ta karaso kusa da shi sai ta kurba ginger tea dake cikin mug din a bakinta ta saka dayan hannunta ta dauke laptop din dake jikinsa ta aje gefen gadon da yak

e zaune ta raba kafafunta biyu ta hau saman cinyoyinsa ta juye masa tea a bakin. Murmushi yai bayan ya hade tea ta karbi mug din hannunta ya aje kan bedside drawer ya wutsilo da ita saman gadon ya zama na shi ne a samanta yana ta kallon bakinta wanda ya sh

a janbaki.

“Kin san lafiyar jikinki bata ishe ki ba, amman sai neman fitina, idan kuma na biye miki ciwon ki ta shi ko?”

Ya fada mata kadan kadan kamar mai rada yana ta yawo da cat eyes dinsa a fuskarta. Murmushi tai ta san halin Ali Zaki baya wasa

da wannan bangaren

komai fushin da yake ko damuwar da yake ciki, duk miskilancinsa da jin kansa indai ta wannan bangaren nan na da nan za'ayi saurin kama shi.

“Ina ta tunanin abunda zan yi na saka maka ne, Aliyu kana kokarin kawarda duk wani abu da zai

taba ni, a sadakar a lokacin da likitan nan ya fada min cewar kidney ta daya ta samu matsala, bayan kuma an cire daya, na dauka mutuwa zan yi amman gashi yanzu za amin dashen wata na samu lafiya”

“Komai zan miki Dear, na yi magana da Doc Asim dazu da ra

na har ya hada ni da likitan da za muje UK tare da shi, In-Sha-Allah within week din nan za mu gama duk wani shirye-shiyen sai muje can a saka miki, i will pay Doc Asim a huge of money saboda wannan abun da yai min, zan yi masa godiyar saving a billionaire

naira wife”

Ya fada yana kissing din wuyanta, tare da saka halshensa yana wasa da gurin.

“I promise you idan kika samu lafiya ba zan raga miki ba”

Ya fada sound so sexy kamin ya shiga aika mata da sakwanni masu zafi.......

ATAA POV.

Lokacin da nurse din ta shigo ta dubata sai ta kalle a hartsine ta ce.

“Farkawa ne za tai, kuma wannan jinin ai dole ya fito tunda jiya akai tiyatar be gama bushewa ba”

Nurse din ta fada kamin ta kalleni.

“Ga ki kyakkyawa kin maida kanki kazama”

Ko kadan ban kula wata maganarta ba, wani dadi na ji ya lullube ni jin cewar farkawa ne Nana za ta yi, sai raina ya fara fari, wani irin shauki ya kamani na ji kamar na taba ta tai magana, ina ta kallon Nana kamin na maida dubana gurin Nurse din yadda t

a saka tufafinta da yadda take aikinta sai ya burgeni daman na dade ina ganin sha'awar aikin likita ko unguwar zoma amman ba ni da wannan halin hali saboda ba ni da wannan gatan na karatu, wa na ke da shi da zai tsaya min nai karatu har na kai ga zama nurs

es ko likita? Ni da karatun secondary ma ya gagareni sai bara da aikin titi.

  Bayan ta fice na zauna a kujerar dake facing dinta Lukman kuma yai kwance kasa yana jin bachi, ido na kura mata tun ina kallonta da kyau har bachi ya soma sata na, shigowar li

kitan ce tasa na Nana tana bude idonta tana rufewa kamar bata san inda take ba. Ni nai saurin mikewa tsaye likitan kuma yai saurin karasowa kusa da ita ya shiga dubata sai na ga yana ta murmushi.

“Masha-Allah tiyata ta yi kyau, na sunanta?”

“Nana”

Na bashi amsa ina wani irin murmushi da ke bayyana irin farincikin da ke raina. Sai ya shiga kiran sunanta cikin ikon Allah da iyawarsa ta amsa muryarta can kasa kasa.

“Na'am”

“Sannu”

Ya ce da ita a lokacin da ta kalleshi. Sannan ni ma na fada.

“Sannu Nana”

Sai ta kalleni ta gyada min kai sai kuma ya dan dago kan kadan ta kalli cikinta da ke lullube da zane.

“Ina Lukman”

“Gashi yana bachi”

Na bata amsa da sauri.

“Waya kawo ni asibiti?”

“Ni na kawo ki maciji ne ya tsare ki,

shine wannan likitan ya taimaka ya miki tiyata ya cire miki dafin kuma yai miki allura ya siya miki magani”

“Allah ya saka da alheri”

Ta fada daker tana kallonsa. Sai ya cire mata wasu abubuwan da ke jikinta ya kalli Lukman.

“Bari a samo muku abu

nda za ku rika kwana ko, ba ki san ana dauka cuta kasa ba da za ki bar shi ya kwanta”

Na yi shiru bance komai ba, shi kuma ya juya ya fice daga dakin. Be jima ba ya dawo tare da wasu masu sharar asibitin su hudu ko wannensu dauke da abubuwan bukata, tab

arma ce da babban bargo da filo da kuma buta da carpet din sallah, dayan kuma abinci ne ya kawo mana. Wallahi sai na rasa da wanne baki zan yi ma likitan nan godiya da irin dawainiyar da yake da mu ko da shi ya haifi Nana iyaka kenan yadda yake kashe mana

kudi sai ka ce ya sanmu.

“Za a kawo muku kayan tea gobe, ai kin iya gada shayi ko? Sai ki rika hada mata tana sha da fruits”

Ya fada bayan mutanen masu shara sun fita.

“Dan Allah ya sunanka?”

Na tambaya cike da fargabar yadda zai amsa min.

“Ina son na rika saka ka a addu'a ta ne idan nai, irin alherin da kake mana yayi yawa kana ta dawainiya da mu kamar ka san inda muka fito”

Kallo yai n wasu yan mintuna kamin ya dauke kansa tare da wani guntun numfashi ya ce.

“Ba komai ba sai kin mi

n addu'a ba, Allah zai ba ni lada ai”

Yana fadar hakan ya juya ya fice, ni kuma na bishi da kallon kauna kauna irin ta wanda ya taimake ka a halin da kake da bukatar taimakon. A dare Nana ta dan ta6a fira da ni tana tambayar abubuwan da ke mana ina ta f

ada mata ita kanta tai farinciki sosai kuma tai masa addu'a sannan ta sha kankana kadan kamar yadda ya umarta, ni ko a daren sai da nai tas na ci na koshi sannan na kwanta kan shimfidar da ya kawo mana ni da Lukman, kusan sai na ce ban taba kwanciya akan w

ani abu mai dadi makamancin katifa ba irin yau.

Tun daga lokacin kullum Nana cikin kara samun lafiya take, ni da Lukman kuma ba mu kara zuwa bara ba, kudin daya bani tun a karon farko ma ban sake taba su ba domin komai na ke bukata yi mana yake babu abu

nda muke yi da kanmu tun kama daga abinci magani da duk wani abun bukata. Sai dai abu daya yake ta bani tsoro, yadda Nana ta gagara komawa daidai, motsi kadan sai ta rike kirjinsa ko gefen cikinta ta ce ciwo yake mata kuma tana yawan fadawa likitan amman s

ai ya ce ba wata matsala ba ce zata ji sauki nan gaba kadan. Mutanen da muka zaman arziki da su suna ta zuwa suna duba Nana, kusan sai na yi sati ban leka gida ba idan ma wanka zan yi sai na yi a bandakin da ke dakin, daman can kuma wanka ba damu na yai ba

, iya kar kokarin da na ke a yanzu na tsayar da sallah a kan lokacij ne ganin bana aikin komai a nan asibitin sai zama, Nana ma ina kokarin ganin na saka ta yi duk kuwa da irin kin son taba ruwa da take ko da na zafi ne yanzu sai ta ji jikinta ya kara rash

in karfi, ganin hakan yasa na samo mata kasa na koya mata taimama kamar yadda aka koyar da mu makarantar islamiya lokacin da na ke zuwa.

Kullum cikin yi ma likitan nan da ban san sunansa addu'a muke ni da Nana, yana kulawa da mu sosai, ba dan rashin laf

iyar Nana da ke cikin raina ba da Allah kadai yasan kibar da zan yi akan abubuwan dadin da muke ci, sai dai Nana kan ta kasa komawa yadda take a da, walwalarta kuzarinta da kuka sakewa ta kasa yi kusan kullum sai rama take daman can ba wani jikin ne da ita

sosai ba.

Wasa wasa muka kwashe wata daya a asibitin, har zaman ya fara gundirata ita kanta Nana da ke ciwon sai ta fara gajiya, kullum addu'ar Allah ya bata lafiya mu bar asibitin, kowa mamaki yadda dafin macijin ya zame mata haka ake yi, ko da yake l

ikitan ya fada mana cewar dafin ya warke ciwon cikin cikinta ne kawai ya rage ya warke. kusan sai na saba da nurses din da ke dan shigowa duba wani lokacin amman masu sake fuska a cikin, sauran kan sai dai su yi min kallon banza, da kuma mutanen da ke zam

waje harabar asibitin suna jinyar wasu, domin idan na gaji da zama cikin dakin da take sai na dauko tabarmar nai shimfida a waje ni da Lukman mu zauna, har ita wani lokacin Nurse Shukura tana fitowa da ita ta sha iska,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login