Showing 69001 words to 72000 words out of 237425 words

Chapter 24 - ZAKI COMPLETE

babu wanda ya zo har dare yai, ban fita karbar abinci a part din Mama Fulani ba, sai na je part din Ammy a can na ci abincin dare na sannan

na dawo garejin na kwanta abuna na kwana har safe. Kamar yadda na saba da wuri na farka ina gama sallah na shiga na gyara falon Mama Fulani sannan na je part din Ammy na gyara kamar yadda na saba, bayan na gama Mama Fulani ta ce na dauko gurina aka zuba m

in abincina, har zan fito sai ya Muhseen ya kirani ya kara min da na shi na fito ina ta murna, a garden na zauna na cinye abuna sannan na dauki plate din naje na wanke na kawo gareji na aje. After like one hour Rukaiyah ta shigo garejin tana rike da makull

in mota.

“Ke ta so muje ki riko min kaya”

Da sauri na taso na biyo bayanta a zato daga mota zan riko mata su ko kuma a cikin gida zan dauko na saka mata a mota sai na ji ta ce.

“Ki shiga gidan baya”

Juyawa nai da zimmar komawa gareji na dauko

Hijab dina sai ta daka min tsawa.

“Ke ina za ki je?”

“Hijab dina zan dauko”

“Ba Hijab ba ubanki shiga mota muje”

Da sauri na nufi motar na bude na shiga daga ni sai lace dina na jiya da sai dankwali, sai da na rufe motar sannan ta shiga mazau

nin direba ta tashi motar muka fice, ni dai ina zaune a baya ina ta kalle-kalle har muka isa wani katafaren shago irin wanda na ke gani a tv nan, wanda komai da komai ana saida a ciki kuma komai bangaren dabam, ni kallo ya hanani rufe motar har sai da naji

an dangware ni da karfi.

“Bakauyar banza rufe min mota”

Sai na saka hannu biyu na rufe. Na bi bayanta muna ta taka dan karamin matakalin har muka isa gaban babbar kofar wacce wasu masu uniform suke budewa mutum idan zai shiga, wani dan kwando taja

ta mika min shi.

“Ja wannan mu tafi duk abunda na nuna miki ki dauka”

Na saka hannu na karba ina turawa, wai ita ala dole sai ta nuna ni din yar aikin gidansu ce ta sha wani bakin gilashi a fuska tana sanye da yadi babu mayafi a jikinta, ni kuwa duk

sai naji na takura da rashin mayafin duk kuwa da na lura kusan rabin matan da suke shigowa shopping din basa da mayafi kuma kowa be kula ba, duk inda muka bi kallona ake nasan wannan baya rasa nasaba da gashin kaina da nai masa tsoro daya na ya sauko har

gurin mazaunaina, da kuma haskena ga kyau kamar wata balaraba. Turin kwandon be dame ni ba dan ji nake kamar ina tuka mota duk inda na ga dama juyashi na ke ina jindadi. Dauko wannan dauko wancan haka take bani umarni ina bi kamar bawa da uban gidansa, mun

a isa sashen kayan dadi ta umarce ni na dauko madara ina kai hannuna sai na ji an rike hannun, da sauri na kalli gafena.

“Na kama ki”

Kamal ne sanye da kananan kaya fuskarsa da murmushi kamar kullum ni ma Murmushin nai sai kuma nai saurin kallon Ruka

iya wacce ita ma murmushin take sakar masa.

“Rukaiya shopping kuka zo”

“Eh Wallahi har ma mun kare daman ba da yawa zan yi ba ya aikin?”

“Lafiya kalau, sai ki ba ni aron Mamanar tawa ta raka ni shopping tun da kun kare, kadan na gama sai mu koma

gida tare”

Sakin baki tai kamar zata ce masa ba mu kare ba, sai kuma ta ga kamar be dace tai karya ba, dan haka tai murmushin yake.

“Ba matsala”

24

“Thank you, idan kin je gida ki fadawa Mama Fulani ni na areta kuma zan kawo ta nan ba da jimaw

a ba”

“Okay ayi shopping lafiya”

Taja kwandon daga hannuna tai gaba a abunta kamar tana jin haushi. Sai da ta wuce sannan ya dawo da dubansa gurina ya ce.

“Shiga ciki na turaki”

Ba shiri na bude baki.

“Aa mutane suna kallon mu, kuma mutane

ba sa shiga cikin kwadon zuba kaya ai, za su mana fada”

“Ko?”

Ya fada yana murmushin kan na sake cewa wani abu ya dauke ni ya zuba a cikin kwandon yana dariya, ina kokarin fitowa ya girgiza min kai.

“Karki fito basa fada”

“Ni kunya na ke ji”

“Nan Abuja ce ba ruwa kowa da kowa”

Tura ni ya fara yi yana tafiya yana dauko duk abunda yake so yana sakawa a gwandon.

“Fada min abunda kike son na siya miki”

“Bana son komai”

“Kina son abun goge baki? Ko kadar mata ko turare?”

Na yi shi

ru ban ce komai ba sai yai murmushi ya fiddo wayarsa ya dauki ni hoto.

“Bari na taimaka miki na saka ki a status dina ko wani zai gani ya zo kawata”

“Kawarka? Mace?”

“Eh mana”

Saurin sauka nai daga cikin kwandon duk na san wasu sun gama gani n

a domin ya zaga wani bangare na shopping din da ni a ciki har wasu na kallona. Da kanshi ya koma yana tura kwadon duk wani abun kwadayi daya gani sai ya dauko guda biyu ya fasa ya ci ya bani rabi sai kuma ya saka rabi a cikin shopping basket din. A haka ya

daukar min kadar mata da turare da man goge baki sannan muka zo gurin biya ya ciro kudi mai yawa ya bada sai suka saka masa kayan a leda wani daga cikin yaransu suka zo suka dauka suka kai masa a mota. A tare muka fito daga shopping din yana cin chocolate

.

“Na jidadin zuwa shopping din nan kin ga na hadu da ke, jiya na aika kiranki waya hana ki fito?”

Nan ma shiru nai masa ban ce masa komai ba, sai ya bude min gidan gaba yana fadin.

“Shiga muje yau dai sai kin ba ni labarin abunda ya kawo ki gari

n Abuja”

Sai da na fara taka wani abu dake gefen murfin motar sannan na shiga cikin katuwar motar mai tuli sosai, sai shi ma ya zagoyo ta mazaunin direba ya zauna ya rufe motar yana kunna ac motar tare da kai hannu ya rage karar sautin da ke tashi sanna

n yaja motar muka hau babban titi yana ta kallona kamar ba driving yake ba.

ZAKI

By Khadeeja Candy

23...

Kamal na tsaye yana lasar wayarsa yana jiran fitowar Ataa sai ga Aliyu ya fito yana wani shan kanshi, bayansa Kamal ya rika kallon a zatonsa

ko tana bayansa ne amman sai yaja gate din rufe bata fito ba.

“Kai kake kiran Ataa ne?”

“Eh nine Aliyu ya aiki, ashe ka dawo”

Kamal ya fada yana mika masa hannu.

“Yes, wani abun ta maka ne?”

Da mamaki Kamal ya sake kallon Aliyu sai kuma y

ai murmushi.

“Mi zata min bata min komai ba”

“Miyasa kake kiranta?”

“Mun saba gaisawa da ita ne kwana biyu, yau kuma ban ganta ba, shiyasa na aika a kira min ita, da wata matsalar ne?”

Aliyu ya tsaya kallonsa kamar ba zai yi magana ba can kuma

ya ce.

“Babu, idan gaisuwa ne, ba sai ka kara aikawa nemanta ba aiki take, aikin da aka kawota dan shi”

Aliyu na fada masa haka be tsaya jiran abunda zai kara cewa ba ya juyo ya dawo cikin gidan, cikin wani irin jin haushi da be san dalilinsa, a da

yan bangaren kuma yana jin idan har ya kyale rayuwar Ataa zata iya shiga wani hali domin kyanta zai rudi samarin su fara jan ra'ayinta ga wata hanyar da dabam wacce bata dace ba. Cikin falon ya dawo ya zauna sa dai be samu Ataa a falon ba sai Mama Fulani d

a Maryam da Rukaiya suna wata magana ganinsa sukai shiru.

“Lafiya yake nemanta?”

“Lafiya kalau, wai zuwa yai su gaisa”

“Su gaisa?”

Mama Fulani ta tambaya da mugun mamaki.

“Shi Kamal din? Kuma ya tsaya a waje?”

“Ai ba zai shigo ba dan kar

mu dauka gurin Maryam ya zo tunda gurinta ya saba zuwa shiyasa ya aiko a kira masa wannan kazamar”

Rukaiya ta fada tana yatsina fuska, Mama Fulani ta ce.

“Ni fa tun ranar na ke ta mamakin ganinsa har cikin falon nan, domin abu ne mai wahala ya shig

o cikin gidan nan idan ba Aliyu ya zo nema ba, sai kuma Maryam wani lokacin idan yana son su gaisa”

Aliyu ya kalleta kamar ya ce wani abu sai kuma yai shiru ya maida hankalinsa gurin tv. Rukaiya da Maryam kuma suna ta kallon juna alamar gulma na cikin c

ikinsu tana cin su. Wayarsa yai jit alamar kira sai ya cirota daga aljihunsa ya duba number Rahma ce, hakan yasa shi picking ba tare da bata lokaci ba.

“Dear karfe tara za mu je mu ga Doc Perry, idan baka gida ka same ni a asibitinsa idan kuma ka dawo

da wuri sai ka same ni a can”

“Kun yi magana da shi ne?”

“Eh mun yi karka bata lokaci ka ji?”

“Na ji make sure kin ci abincin dare kamin ki tafi”

“Okay i love you”

Be amsa ta ba ganin cewar yana a gaban Mama Fulani sai kawai ya kashe wayar y

a tura mata ta sako. Ko be fada ba Mama Fulani ta san da Rahma yai waya, sai dai abunda bata gane ba ta ci abincin kafin ta tafi.

“Ina zata ta fi?”

“Zamu je mu ga Doc Perry ne”

“Ciwon ya tashi ne?”

“Aa akan matsalar haihuwa ne”

“Hmmm haka z

a ku yi ta bata lokaci da kudin a banza ba ku samu mafita ba, na sha fada maka idan ba aure ka kara ba ba zaka taba haihuwa ba”

“Ni da ita duka likitoci suna cewa ba mu da wata matsala za mu iya haihuwa a ko yaushe, wata kila lokacin ne bai yi ba”

“I

dan lokaci be yi a yanzu b yaushe zai yi? Shekara takwas fa, haba abun nan yayi yawa”

“To ya za'ayi haka Allah ya kaddara”

“Aa Wallahi ba za mu gane haka Allah ya kaddara ba, sai ka kara aure mun ga ita ma wacce ka aura bata haihu ba tukuna sai mu sa

n yin Allah ne, amman dan ance za ku iya haihuwa a ko da yaushe ai ba abun dogara ba ne”

Yai dan murmushi

“Mama Rahma fa bata son kishiya”

“Ni son kishiyar na ke da aka min ita? Ko kaunar Ammy na ke aka ce maka? Amman a haka na hakura na zauna da

ita gata nan ta zuba zuri'a arzikina ma bata haifi namiji ko daya ba, sai ita wannan dan ta auri sarkin soyayya zai ce ba zai kara aure ba dan bata so ko? To baka isa ba, ni ba zan dauka ba idan kai baka son ganin zuri'ar ka ni ina so”

Juyowa yai ya ka

lleta da kyau.

“Idan kuma na kara aure ya zama matsalar daga ni ne fa?”

“Sai mu a cigaba da neman magani, amman ai yanzu ba za a gane ba sai ka kara auren, ba fa zan yarda ayi ta tafiya a haka ba har mu zo mu mutu ba mu ga yayanka ba”

Tana kaiwa

nan ta mike tsaye ta nufi upstairs. Da kallo Aliyu ya bita har ta haye sannan ya kawar da kansa ya sauke ajiyar zuciya daman ya san Mama Fulani bata masa da sauki idan aka tabo bangaren haihuwa shiyasa ko da yaushe yake kokarin ganin ya kare Rahma, amman a

yanzu dole yai ma tufkar hancin ko dan saboda Mama Fulani a yanzu yake ganin ya dace yai amfani da shawarar Nasir na maida matsalar a kansa shi kadai, sai da ya shafa kansa sannan ya mike tsaye ya fice daga falon zuwa part din Ammy domin ya gaisa da ita.

ATAA POV.

Dana soma tsarguwa da yadda suke kallon suna aybanta ni ne yasa na tashi na tashi na bar musu falon na dawo garejin na zauna na karasa cin abincin, sai da na cinye shi tass na koma ina tsude kwanon da kuma hannuna abincin ko dadi babu dan

kawai ina jin yunwa ne domin abincin Ammy ya fi na Mama Fulani dadi, da na gama sai a dauki plate din da cup din na nufi garden na wanke tare da tara wasu ruwan na sha sannan na dawo garejin na kife su guri daya da wacan plate din da Mama Fulani ta bani d

a farko, ni ina ruwana da kymarta ai na kara samun wani plate din da cup, sai da na jerasu sannan na kwanta a gurin ina jin gajiya na sauko min. Kamshin turaren Aliyu da na ji ne yasa na dago kaina na kalli kofar shigowa garejin sai na ganshi a tsaye yana

kallona fuska a hade kamar na masa wani abun, har harara na watsa masa na turo baki kamar yadda na saba idan ina fushi na juya masa baya na kama tsorona ina ta watsa da shi.

“Idan Kamal ya sake zuwa nemanki a gidan nan sai na bata miki rai”

“To ni n

a ce ya zo nemana? Ni ina ruwana”

Yana fada a take na bashi amsa ba tare da na juyo ba, har sai da na ji kamshin turaren na shi na kara matsoni alamar ya baro gurin kofar ya nufo inda na ke kenan, sai nai saurin tashi zaune still bakina a ture ina kallo

nsa har ya karaso.

“Kar na sake ganin kin yi wanka a garden”

Ya fada yana zare min ido, ni ko kuwa be san bana jin tsoronsa ko kadan a raina ba.

“To ina kake son naje nai? Idan na yi wanka a wani gurin sai ga a ce na yi ba daidai ba dake ni ko?

Ni ba zan iya wanka a bandakin wani kato ba ace kullum zan yi wani abu sai dai na je bandakin mai gadi nai ni ba zan sake yin komai a can ba”

“Tashi ki koma bq a can za ki rika kwana”

“Ba zan koma ba, ni babu inda zan je, matar gidan a nan ta aje ni

dan haka a nan zan zauna ba zanje ko ina ba”

Na bashi amsa kai tsaye ba tare da fahimtar inda yake nufin naje ba. Matsowa yai kusa da ni ya kai hannunsa ya rika gashin kaina ya matse shi sosai ya mikar da ni tsaye da shi yana kallon idon cikin wani irin

bacin rai ya ce

“Idan ina magana kina ba ni ko wace amsa sai na ballaki”

“Ka balla ni mana, ka balla mahaifiyata ai, ka gama da ni daman, kadan ya rage kuma sai ka karasa ni a yadda kake so ai, ba zan taba tsoron ka ba Aliyu, ba zan taba kaunar ka b

a, ba kuma zan taba kyale ka ka fada min magana daya marar dadi ba, ko wace magana da zaka fada min ina da amsarta, ba zaka cutar da mahaifiyarta kuma ka sake cutar da ni ba, azzalumi kawai kai da yan'uwanka ba ku iya komai ba sai zalinci sai danne hakkin

wanda kuka fi karfinshi sai cin amana, Wallahi Allah sai ya saka min a ko wane zalinci da kuka min, kuma matarka ba a zata taba lafiya ba har abada”

Ina fada yana matse min gashi da dukan karfinsa har sai da na fashe da kuka sannan ya sake ni na fadi a

gurin na fashe da kuka.

“Mugu”

Daf da zai fice na fada masa haka sai ya juyo ya kalleni da cat eyes dinsa, sai kuma ya juya ya fice ba tare da ya sake cewa komai ba. Be yi minti biyar da fita ba sai ga Inteesar ta shigo garejin.

“Ataa wai Ya Aliyu

ya ce ki taso ki koma bq acan zaki rika kwana”

“Idan naje ai Mama Fulani fada zata min”

Na fada cikin kuka ina murja idona.

“Ba zata miki ba tun da danta ne ya saki, mi akai miki kike kuka?”

“Ba komai”

Na fada ina turo bakina tare da mikew

a tsaye nadauki jakana da plates din da tabarmar da na nade na bi bayan Inteesar, tana gaba ina biye har muka isa wani bangare na can gefen part din Ammy, an zagaye gurin da wani dan karamin gate, ciki muka shiga ni dai ina ta jin tsoro daman can gida mai

fadi sosai tsoronsa na ke ji, wasu kanann dakuna na soma hangowa gefen dakunan an kawata su da fulawoyi gwanin sha'awa, da muka isa gurin dakunan sai na tsaya na ki na karasa ciki har sai da Inteesar ta hau saman dan karamin matakalin ta tura kofar daya da

ga cikin dakunan da suke gurin.

“Ke karaso ba komai”

Nake kafada nai alamar ni ba zan zo ba, dan ina jin tsoro taya zan iya kwana a nan ni kadai. Dage labulen tai hakan yasa na karasa kusa da ita ina kallon dakin, katuwar katifa ce a kasa an lullube

ta da zanen gado mai kyau da filo har biyu a kai, a gefen dakin kuma wata kofa ce wacce nake saka ran bandaki ne a can.

“Ki shiga”

“Ni ba zan kwana a nan ba”

“Ba komai fa kuma kin ga akwai fanka da katifa”

“Ni bana so”

Ta saki kofar taja k

ofar ta juyo ni ma na juyo na biyota har sauri nake kar ta barni baya. Muna fito daga bangaren muka hango Aliyu tsaye jikin wata kyakkyawar mota yana kokarin bude ganin mu ya yasa shi tsayawa yana kallonmu.

“Ya Aliyu ta ce wai bata so ba zata zauna a c

an ba”

Kallona kawai yai ya dauke kai ya shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login