Showing 135001 words to 138000 words out of 237425 words
karko zai yi ba”
“Idan tana son sa fa?”
“Bata san sa bata san wanda take s
o ba, ita kanta bata san waye ita ba balle kuma ta san wa take so a haka da take, kuma Muhseen ba dan Allah yake son ta ba, kyauta ne kawai yake rudarsa kuma kin sani Mama Fulani ba zata bari ya aureta ba, lalata mata rayuwa kawai zai yi”
“Samun wanda z
ai auri Ataa a yanzu saboda Allah yana da Wahala ai, yarinyar da ba a san waye nata ba? Yar talakawa kamar yadda Rahma da iyayenta suka fada, kara ma Muhseen din dan kyauta kawai yake sonta wani ma neman fasikanci zai yi da ita ai kara a aurarda ita tun ka
min wani ya lalata mata rayuwa domin ba wani wayo da ita ba”
“Momy wai mahaifiyarta tace miki tana son aurarda ita? Ki bar yarinyar nan ta fahimci miye duniya tukuna, dan Allah mu bar maganar nan, kuma karki da ita Abujar nan dan girman Allah Momy”
Y
a karasa rai a bace gaba daya ransa ya gama baci, maganar Ataa na zuwa ganin Kamal da kuma zancen Momy ga kuma wannan maganar da wani Muhseen. Kasa cin komai ya yi a dinning din sai kallon kanensa da ke cin abincin yake domin Momy tuni ta tafi bangaren Dad
dy dan kai masa na shi breakfast din. Tashi yai ya fice daga falon ya dawo cikin motarsa ya zauna sannan ya kira Nasir ya labarta masa abunda ya faru. Dariya Nasir ya saka masa kamar wani mahaukaci.
“To kai yanzu miye matsalar da soyayyarta ta Muhseen?”
“Nasir ba san yadda na ke ji ba na, yarinyar nan bata sam ciwon kanta ba ba ta ma san waye ita ba, karatu ne abunda na ke son yarinyar ta samu a yanzu, that's why na kira ka samo wani mai koyarwa ya rika zuwa gida yana koya mata boko idan ta fara fahim
tar komai yadda ya dace sai na kaita makaranta, islamiya kuma zan saka ta ta su Siyama”
Har yanzu Nasir dariyar Aliyu yake, ya san son Ataa yake shiyasa yake kishinta amman jin kai da kasaita ta hana shi fahimtar hakan, wata kila kuma ya fahimta kawai d
ai baya son nuna ne dan kar a masa dariya, irin yadda ya tsari talaka ace ta kai har ya fara son wata yar talaka.“Za a nemo wani malamin, amman ka san shekaranjiya ma Kamal din yake tambayata ta whatsapp wai ina yarinyar abokina”
“Ka rantse”
“Wallahi
, har yake cewa ya san abunda yai be kyauta ba, amman wai ransa ne ya bace kuma abunda Mama Fulani tai bata kyauta ba”
“Sakaren banza har yana da baki yanzu stupid”
Nasir yayi dariya.
“Shi ma ai yana son ta ne kamar”
Tsaki Aliyu ya ja ya katse
kiran yana rika sitarin motar, sannan ya lalubo number wani abokinsa wanda ya san yana fannin makaranta ya kira shi ya fada masa cewar yana son a sama masa wanda zai rika koyar da wata karatu a gida, domin ganin yake Nasir be dauki abun serious ba, and id
an ba karatun ya sakawa gaba ba yana ganin kamar Momy zata iya daukarta ta bawa Muhseen amman idan ta fara karatu dole zata kyaleta.
ATAA POV.
lokacin da na bar falon da kuka na fito zuciyarta cike da jin haushi Aliyu da nasan cewar hana tafiyar
zai yi da tun farko ban fada masa ba. Gurin Nana na dawo lokacin tana balcony zaune ni kuma na wuce dakin na hau kan katifa na kwanta ina ta kukana a hankali dan bana son Nana ta ji. Ina jin lokacin da Momy da kanta ta kawo mana abun karya har ta zauna kus
a da Nana tana tambayar ina na ne.
“Ya sega ciki dazun ya shiga ta kwanta”
“Ko ta yi fushi ne saboda na ce ba a a Abuja da ita ba?”
“Abuja?”
“Murna za muje yi to tace zata bi mu amman yanzu Yayansu ya zo ya ce ba za a je da ita ba, wai ba zata
je ta barki haka ba”
“Ataa haka yake ai wani lokacin da haurin hutsi amman nan da nan ka sauka”
Ban san abunda ya bawa Momy dariya ba har sai da tai magana bayan gama dariya.
“Ke har yanzu hausarki bata gama fitowa ba”Sai na ji Nana ma ta yi dari
ya ta ce.
“Da san kai baka iya hausa ba, baka ji hausa ba sai faranse sai buzanci, kadan kadan ka fara jin hausa har ka ji ka sosei sosei”
“Amman kin ga Ataa ita ta iya hausa sosai sam ba zaka ce ma tana jin buzancin ba in ba dan kammani ba.”
“At
aa ya tashi cikin hausawa, tun kuna kamba kai da babanka har ka zauna argungun har ka dawo sekoto, Ataa da Lukman mai mutuws duk ka ji hausa sosei”
“Ku yan wani gari ne Nana? Na ji kin ce kun zauna kamba?”
“Daga Agadez ka gudu doso daga doso ka zo ka
mba sai ka yi argugun ka yi bodinga ka yi sokoto, kana ta yawa yawa yawa kai da mai gida na mu”
Momy ta dade tana fira da Nana a nan na ji cewar a ni a kamba aka haife ni Lukman kuma a sokoto, wanda da duk ban san da hakan ba, domin ni na yi wayo ya bud
e ido na ganni a sokoto ne kawai kuma ban taba tambayar dalilin zuwanmu ba balle inda aka haife ni.
“To amman miya kawo ku garin nan na? Miyasa kuka baro garinku Agadaz?”
Daga wannan tambayar da Momy ta yi ma Nana ban sake jin Nana ta ce koma ba har
na tsawon lokaci, can kuma na ji Nana ta ce.
“Labarinka ba se da dadi ka ji ma kunnenka, baka son kana tuna baya ba se da dadi ka ji, amman kai babban mutum ne mai kima da gima amman yanzu ba shi da amfani, ka koma kai kadai mijinka ya tafi ya barka d
an ka ya tafi ya barka yanzu ka koma kai kadan sai Ataa”
“Muna tare da ke Nana, sanin wacece ke ba shi da amfani ma yanzu kuma na jidadin da aka samu Ataa ta hanyar aure, shine babban farin cikina”
Shine abunda na ji Momy ta fada kamin Nana ta dora d
a nata tana
ɗ
a
ɗ
a hannunta.
“Ahhh Ataa yana da ubanta mai kyau kyau kyau kyau sosei, kai ne Ataa ta biyo ai, uban Ataa kana da kyau kana da fari kama da gasi kamat balaraba”
“Allah sarki Allah ya jikanshi, ashe Ataa shi ta biyo domin na lura yata ta
fiki kyau sosai, bari na leka bangaren Daddynsu na bar shi shi kadai”
Daga haka na ji ficewar Momy faga bq din ni kuma na taso na share ragowar hawaye na fito na zauna kusa da Nana na rumgumeta, cewar Ni kadai na rage sai ita ya taba min zuciya, ban tab
a tambayar dalilin zuwan mu nan ba, da kuma rashin kowa a nan ba, domin ban tana kawowa rai komai ba, kuma na lura kamar Nana bata damu da hakan ba, sai yanzu ina da bukatar ji domin na lura yan'uwa suna da rana ko da kuwa talakawa ne na tabbatar da ace wa
ni nata yana kusa da ita da bayan ni da Doc Asim be isa ya mata haka ba. Da yare buzanci ma kalleta ina murmushi na ce.
“Nana idan kin kara jin sauki sosai za mu tafi gida can Agadez gurin danginki ko?”
Sai ta girgiza min kai.
“Aa ba zan taba zu
wa ba har abada, Babana ya yi fushi da ni, na bashi kunya ba zan iya komawa garin nan ba har abada, sai dai ke kije idan na mutu”
Ban sake cewa komai ba ganin hawaye a idonta, tabbas ba dadi ne ya saka ta baro garin ba, wata kila wanin abun ta aikata ko
kuwa korarta yai oho.Da rana Amina ta kawo mana abincin rana jalof din taliya da kifi an saka mata koren wake da wasu abubuwan da na zan iya tantance su ba, sai kamshi take mai ya kwanta gwanin sha'awa. Bayan mun gama ci na shiga bandakin nai wanka daman
Nana tun da ta gama karyawa safe tai nata, ina fitowa na dauki rigar dazun na saka n zauna kaina babu dankwali daman na fi sakewa a haka. Can da la'asar sai ga Amina ta sake dawowa, wai na fito ana kirana ban saka komai ba na fito daga ni sai doguwar rigar
jikina na biyo bayanta na yi zaton Momy ce take kirana sai na ga wani mutum cikin shiga ta kamala zaune a amman wata kujera hannunsa rike da wata katuwar waya.
“Zauna nan”
Na zauna a empty chair da Amina ta nuna min sai ta wuce ciki, ni kuma na gai
she da mutumun ya amsa min da fuskar far'a, ya soma tambaya inda na tsaya a karatuna na boko daga nan na gane cewar malamin boko ne.
“Aji hudu na tsaya a yakubu mu'azu, ban sake yi ba”
“Kin iya karanta hausa?”
“Eh na iya karanta hausa ko wace iri
, da numbobi”
“Ban iya ba”
Sai ya miko min wayar hannunsa ya ce na karanta hausa. Gata ne a rubuce a take na soma karanta ta sai dai ina yi ina gargada wani gurin kuma sai ya gyara min idan na fadi wani abun ba daidai ba sai yayi ta min dariya, bayan
na gama ya bani turanci ya ce na karanta sai na kafaranta da hausa ba tare da san ma'anarsa ko fassararsa ba, nan ma ya sha dariyata ni kaina na yi dariyar kaina domin duk turancin da ya nuna min da hausa na ke karanta shi. Muna cikin haka Aliyu ya fito t
are da Momy ashe wai yana cikin gidan ni ban ma sani ba. Mutumen ya shiga masa bayani
“Ba laifi tana da kai kuma ta yi kokari sosai, yanzu hausar ce za a dora ta akai sai kuma turancin da zamu fara daga farko domin shi tace bata iya komai a ciki ba”
“To yayi kyau”
Ya fada fuskarsa ba yabo ba fallasa, sannan ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudin da ban san ko nawa ba ne ya mikawa mutumen.
“Ga wannan ka hau mota za mu neme ka?”
Karba yai yana godiya ya karbi wayarsa da ke hanuna yai min sallam
a ni da Momy fuskarsa da murmushi ya nufi gate.
“Be yi ba ba ne?”
Bayan ya wuce Momy ta tambaya.
“No na cika sakewa bana son namiji mai sakewa da mace sosai”
Ya fada yana kallona.
“Ba na ce ki daina fitowa haka ba?”
“To ai hijab din ya
yi datti duka kayan sun yi datti”
“Je ki sako Hijab dinki”
“To ba ya wuce ba?”
Na fada ina turo baki. Harara ta yai sai Momy ta ce.
“Ataa yata idan Aliyu ya ce ki yi abu ki rika yi ki daina masa garda kin ji? Je ki saka wata kila rakiyarsa za
ki yi”
“Tau”
Tashi nai naje na saka hijab din na dawo, ko da na dawo yana cikin mota ya bude front seat da alama ni yake jira, shiga nai na zauna da gangan na ki rufe motar sai ta ya mika hannunsa ya janyo ganbun ya rufe sannan ya soka taka motar dam
an tuni aka bude masa gate.Ba mu yi wata lafiya mai nisa ba, muka iso gaban wata katuwar makarantar islamiya, wani irin dadi ne ya lullube na kalleshi da sauri.
“Saka ni za ka yi?”
Sai yai min banza kamar be san da zama a cikin motar ba, ya bude mot
ar ya nufi wani bangare na makarantar ya bar a ciki, be dade ba ya dawo ya bude min murmushi motar da kansa na fito na tsaya a kusa da shi ya wani hade rai irin kar na ga damarsa din nan, wani malamin ne ya zo ta takardu ya ya tambayi sunana da sunan Baba
lafiya ta da sauransu sai ya rubuta a form din hannunsa dabya bukaci number waya sai Aliyu ya bada tasa.
“Shikenan yanzu sai uniform za a siya mata da kuma hotonta da za a laka a jiki”
“Ana siyar da uniform din a nan”
“Akwai muma siyarwa dinkaken
ma ne”
Be tambayi nawa ba yake ba kawai ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudin masu dan dama ya mikawa mutumen.
“A bata uniform din ka rike canjin ka cire kudin form din hoto kuma za muje ayi yanzu, dan Allah ka saka ido akanta bata iya komai ba, tu
n daga farkon fari za a fara koya mata komai”
“In-Sha-Allah ba ka da matsala, ba ri a dauko mata uniform din”
Komawa yai cikin makarantar ya dauko uniform din cikin wata farar leda ya miko min na karba ina wani irin murna kamar na zuba ruwa a kasa na
sha. Sannan na koma cikin motar shi ma Aliyu ya zagayo ya shigo yayi mata key.
“Na gode na gode sosai Allah ya saka maka da alheri”
Be amsa ni ba ko inda na ke be kalla ba, ni kuma ban damu ba farincika ya gama cika zuciyata gaba daya, daga ilslami
yar ya wuce da ni gurin daukar hoto aka dauki hotona aka ba shi, fiye da kudin hoton ya bawa mutumen, abunda na lura da shi idan zai maka alheri ko ya baka hakkinka sai ya ninka maka ko kuma ya baka abunda ya fi yawan nawa, na yi zaton daga nan gidan za mu
koma sai ya nufi AGG da ni, ban taba shiga shagon ba tun da nake ganinsa sai dai kawai na bi an wuce amman har bara na yi a gurin shagon lokacin da nake tsananin bukatar kudin nan.
Yana gaba ina binsa a baya sai rabon ido nake ina kallon kayan shagon ina
ta kalle kalle da kansa yake zabon kayan ciki, yawanci gowns ne na abaya da riga da skirt na kanti, sai takalmi masu kyau ta ki hudu, sai da ya biya kudin sannan suka saka masa a mota muka fito muka shiga motar ya dauki hanyar wata plaza da ni, wannan kar
on a motar ya barni ya shiga ciki domin be bude min dan na fito kamar yadda yai min dazun ba, ni kuma na zauna a cikin motar har yayi abunda zai yi ya fito wani na riko masa manyan ledodi.A bayan mota aka saka masa musu sannan ya shigo motar yana cin wani
abu mai kamar chocolate kuma ba chocolate ba, ya ci kusan rabi sannan ya miko min sauran sai na karba na saka gefen hijab dina na goge kufan bakinsa sannan na ci, ido ya saka min yana ta min kallon rainin wayo sannan ya tashi motar muka kama hanyar gida an
a kiran sallah magariba.
A harabar gidan ya faka motarsa ya bude boot din ni kuma na bude na fito rike da uniform dina zan tafi bq sai na ji ya ce.
“Wa za ki bar wa wadannan kayan?”
Dawowa nai na dauki ledodin na yi zaton cikin falonsu za a shiga
r masa da su sai na ji ya ce.
“Leda ukun ne na ki biyu Mamanki ne”
Na zaro ido ina bude baki.
“Da gaske da gaske”
“Da karya”
Na fada ba tare da ya kalleni ba ya rufe boot din ya nufi sashen Momy, wani tsalle nai na dire rai na fes, a gaski
ya yau Aliyu ya burge ni domin na kura shi ma yana da mutunci kamar Kamal sai dai Kamal ya fishi son mutane da far'a. Nana ma ta yawa sosai da ganin kayan da kuma halin Aliyu daman tun muna asibiti take ta yabonsa tana ganin kirkisa sosai, wannan karon har
da cewat tana mamakin yadda hake ga hidima da ni haka. Bayan sallah isha'i Nana ta ce na je na masa godiya kuma na ce ita ma tana masa godiya. Rigar jikin na cire na saka daya daga cikin Egypt abaya da ya siya min na saka na yafa mayafinta sannan na nufi
part din rigar sai kyalkyali take ko'ina na jikinta.
Da sallam na tura kofar falon na shiga, sai Momy ta amsa min da far'arta Aliyu yana zaune saman cushion ya hade rai sosai kamar an masa wani abu, ina juyowa sai na Muhseen tsaye yana sakar min murmus
hi.
“Laaa Ya Muhseen”
“Pretty na”
Ya fada yana kallon yadda rigar ta karbe abun ka da farin mutum ya saka babaken kaya.“Yaushe ka zo?”
“Yanzu nan, jiya na ban ji a waya ba kuma ina da bukatar ganinki shiyasa na zo, ya kike?”
“Lafiya kalau”
Na amsa ina dariya kamar an min wani abu, ni dai har ga Allah ina son mutum mai far'a da dariya kamar Kamal da Muhseen, sai dai Kamal ya fi kwanta min sama da Muhseen din kuwa da kasancewar shi ma yana min far'a sosai, kusan sai na ce duka suna burgeni
kuma ina son su.
“Kin yi kyau pretty na rigar ya karbd ki”
Ya fada yana rika rigar nawa ya buda ta tai fadi.
“Eh dazun Aliyu ya siya min ita Nana tace na zo na masa godiya”
Yanayin fuskar Muhseen na ga ta canja sai ya dan wara ido yana zolaya
ta.
“Hop kin daina sake jikinki dai domin na lura ana sake miki da yawa”
“Sake jiki kuma?”
Momy ta tambaya sai ya kalleta
“Yes, lokacin da take Abuja a garden take wanka, a gareji take canja tufafi sai da na mata magana”
Juyowa Aliyu yai y
a kalli Muhseen yana lilo da kafarsa wacce dayar ki saman daya.
“Ka ganta kenan? Shiyasa ka ce kana son ta?”
“Idan ma haka din