Showing 231001 words to 234000 words out of 237425 words

Chapter 78 - ZAKI COMPLETE

wane saboda ina jin nauyin fadin sunansu hakan nan kawa

i wasu su kira na da yata kasancewar ina da sunan yarsu wasu kuma su ce min kanwata.

Daga lokacin na fara fa'idantuwa da wayar da Hamma ya siyo min, domin ta nan nake chat dasu idan sun ga wani abun mai amfani sai min sharing su tambayi tafiya da ta miji

, masu grps suka saka ni wata babban a cikin mu kuma ta bude mana wani grp na koyon girkin d muke, wai ko da akwai abunda Malama tai jawabi wanda mutum be gane ba sai yai tambaya a fada masa ko a kara wayar masa da kai. Na kara ilmi ba kadan ba, domin a ci

kin groups din da nake ana yawan turo abubuwna da suka shafi matana aure na inganta zamansu yadda za a iya kula da miji yan'uwan miji da sauransu, a cikinsu akwai wani wai shi Women Diaries na wata marubuciya, ina karuwa da grp din sosai abunda ban fahimta

ba kuma sai nai tambaya a take za a fayyace min komai.

   Daga ranar da akai wacab case din ba ba su sae kira ba, har na sawon wata daya, sai da suka kara bincikensu suka tattara dukan hujojinsu suka tabbatar da abunda ake zargin Doc Asim da shi bayan s

un tsananta bincike sannan suka mika shi kotu. Wani abun mamaki Doc Asim har da daukar lauya mai kare shi, ni da Mama ma lauya ne yake tsaya mana duk wani abincike ko gabatar da shaida shi yake yi. Hakan ya saka wani lokacin ba da ni ake zuwa kotun ba domi

n cikin nawa wani lokacin sai ya taso min da zazzabi wani lokacin kuma kamar ba ni ba. A cikin wannan halin Hamma ya dauke ni muka koma Abuja daman wani lokacin  yana tafiya yana dawowa saboda aikinsa, ni kuma baya son tafiya da ni saboda koyon girkin da n

ake. Yanzu kuma na kamalla daman ajin akwai na wata daya akwai na wata biyu uku hudu biyar har shakera uku ma ya danganta da wanda ka zaba. Ni kuma ya biya min na wata biyu ne kawai kuma babu laifi na iya abubuwa da dama na zamani da kuma irin na da da ake

saffarawa a girka tun daga kan na sha wato home drink's har abincin. Wani abun kuma ina ra'ayi zan leka YouTube na duba na fada masa ya siya min kaza da kaza idan babu ina son na hada.

Muna saura kwana biyu muje Abuja Hamma yake fada min zancen baikon d

a za ayi ma Amina, na yi murna sosai ina jin na taka wani da za a kira matar yaya kuma a fada min wani abun na kanen mijina idan za ayi. Sosai na so mu fasa zuwan har sai an yi baiko amman Momy ta hana saboda tana son na walkilce a gidan Mama Fulani na kai

lefen Muhseen da za'ayi wanda ba zata samu zuwa ba saboda baikon Amina ita ma Mama Fulani ba zata samu zuwa ba saboda kai lefen.

  A ranar da muka sauka Abuja a gidan Mama Fulani muka sauka kamar yadda Hamma ya saba idan yayi tafiya zai sauka a gidan Ma

ma Fulani idan a sokoto ne kuma zai sauka a gurin Momy. na yi mamakin yadda muka samu Mama Fulani ta murje ido kamar ba ita ba, sai marhabun take mana da far'a da komai irin yadda take tarbar Hamma, tana ta nuna kulawarta akaina ni dai ban sake jikina sosa

i ba sai dai na lura hakan ba karamin dadi yai ma Hamma ba, ba ita kadai ba har su Maryam da Rukaiya sun murje ido suna sakewa da ni kamar komai be faru ba, ni kuma na kasa mantawa a duk lokacin da na kalle su ko kuma suka min wani abun na karramawa ko kul

awa sai na tuna da baya. Suna ta shirye shiryen kai lefen Muhseen da za'ayi kamar yadda Momy ta fada.

Sai da muka huta a gidan sannan muka doshi gidanmu da ke can Abujar, an gyara ko'ina na gidan kamar muna ciki muna rayuwa.

“Na yi mamakin ganin gida

n nan a haka, haka wacan zuwan na tararda gidan wanke fes”

“Gyarawa ake”

“Wa ke gyarawa?”

“Aljanu”

Ya fada yana kanne min ido kamin ya fada min cewar mai masa gyaran fulawoyi da gida ne yake gyarawa. Washe garin ranar da muka so ya kama Saturda

y a ranar a aka kai lefen a wata unguwar masu hannu da shuni da ke garin abuja, lefe na mai amsa sunan lefe da babban gida na masu naira irin dai wanda Mama Fulani take kwadayi kuma take so. Sun yi mana goma ta arziki bayan kayan ciye ciye har da kudi masu

yawa suka hadu mana. Ni dai ina so ganin yarinyar domin Hamma ya fada min wai ya ganta a wayar Mama Fulani tana da kyau sosai.

  Bayan mun dawo mun huta ina bangaren Ammy na shiga whatsapp dina sai ga hotonta da aka hada da na Muhseen da kuma lefen ana

tayata murna a status din Husna na gani, gaskiya kyakkyawa ce sosai fara mai jiki sai dai ba sosai ba, ban yi mamakin kyauta ba daman can irinta yake ai, wato mace mai kyau na san da hakan tun daga lokacin da aka kawo ni aiki a gidansu, kyau na cikin abund

a yake burge Muhseen, kuma ba laifi ba ne dan ya so mace mai kyau musulunci ma ya yarda a auri mace dan kyauta.

  

Daga gidan su Mama Fulani aka aiko mana da na mu kayan baikon Amina, ta bangaren Abbah da yake akai komai da shi, a lokacin da aka kawo m

ana na mu na sha dariyar Hamma saboda korafin da ya rika yi wai nawa ya fi na shi yawa, kuma haka din ne nawa dabam mai yawa na sa kuma ba mai yawa sosai ba, a waya Momy take fada min wai mai yawan shi ne nawa wata kila ina da kawaye da zan rabawa na jidad

in da Momy ta kwarrama ni ta tabbas da ace ina da kawaye a nan Abuja babu abunda zai hana ni raba musu baikon kanwar mijina. Sai dai kasancewar kawayen da nai sabo da su yan makarantar koyon girki ne kuma duk a sokoto suke babu daya a nan.

Sati daya da k

ai lafen Muhseen aka kawo baikon Rukaiya na ni kadai ba, har Hamma sai da yai mamakin jin zancen ta samu miji domin shi kansa be san wani na nemanta ba, daga ni har shi har su Momy mun ji abun ne daga sama, a ranar da Abbah ya fada masa za a kawo baikon sa

i da ya kira Mama Fulani a waya yana tambayar anya dai an yi bincike akan mutumen kuma an san waye shi? Ina jin lokacin da Mama Fulani take fadar wai ai yanzu an daina zufafa wannan binciken da ake kuma yaron dan kano ne iyayensa sun zo har da wamban kano

(Fake Name) ya fada musu shine babansa kuma sunansa yake bearing, dan haka ba sai an fadada bincike fa, aiki kuma shine manager a gidan man da ke nan Abuja. Tana ta fada masa irin kudin da ya kashewa Rukaiya daga haduwarsu zuwa yau ya kashe mata kudi masu

yawa, gashi kuma Abbah yana zancen hade yayan Ammy su uku da Muhseen ai kara a hada da Rukaiya tun da ita din ta samu kuma yace a shirye yake.

Ni kaina na yarda da zancen Mama Fulani cewar mai kudi ne tun daga kan kayan baikon da ya aiko kayana masu yawa

n da gaske irin waenda ake kaiwa a manyan gidajen, a ranar Momy ta zo har da Daddyn ma da wasu yan'uwan Mama Fulani da ke Yola.

Kamar yadda Hamma yai min alkawarin saka ni a wata makarantar be saba alkawarinsa ba, duk kuwa da kasancewar cikin nawa wata

biyar ne ya lokacin har da yan kwanaki a kai, amman a haka ya aminta ya saka ni a Royal Academy, wata makarantar kudi ce da ke nan Abuja ta masu koyon karatu da rubutu da kuma waenda ba su samu damar kare karatunsu ba kamar ssce.

  Karfe tara ake zuwa a

taso sha biyu ga irin mu ga yan sss2 da 3 kuma suna zuwa da safe misalin takwas su tashi biyu saura. Gaba daya makarantar da turancin ake magana tambaya da kuma bada amsa ko da kuwa tsakanin dalibi da dalibi ne, ma ji tsoro sosai ganin irin ka'idar makara

ntar sai dai hakan ya saka na kara dagewa da maida hankalin wajen ganin nima na iya turancin kamar sauran, ba musulmai kadai ba ne a makarantar akwai kistoci ma har da waenda ba hausawa ba, akwai matan aure da yan mata a ciki akwai maza akwai mata sai dai

bangaren mazan dabam matan ma bangarensu dabam, ko a cikin matan daga ni sai wata haulatu ne muke saka niqab domin ita ma ina jin mijinta irin Hamma ne mai tsananin kishi, ba niqab kadai ba har safar kafa da hannu Hamma cilasta min sakawa yai yi. A dole ku

ma mai hakan saboda ina son karatun. Shi yake kai ni ya dauko ni idan mun tashi, idan ma ba shi da time sai dai ya ce na jira shi idan ya gama ya zo ya dauke ni, wani lokacin da yar  kula ta abinci kamar wata karamar yarinyar yar makaranta ko da yake ba ni

kadai na ke zuwa da abincin ba, kuma duk wanda ya gan ni da abincin idan ya lura da yadda cikina ya fara dan tasowa zai san ai lalura ce, domin kuwa cikin nawa na kara girma cin abincin na karuwa abun har mamaki yake ba ni. Sosai na ke son zuwa Nijar guri

n Yan'uwan Mama da na Babana na ga waenda ban gani da Waenda kuma na gani na kara ganinsu, duk kuwa da kasancewar sun zo a baikon da akai ma Zainab da Batula na cousins, sai kuma na Humaira da akai kwana biyu da yin na su, aka saka lokacin auren daya da na

Muhseen kamar yadda Abbah ya fada cewar yana son ya hade su yai musu auren a tare a bar Maryam kawai ita da bata samu mijin ba.

Karatun da na ke a yanzu ya fara zame min kamar da wahala saboda na hada biyu ne, da yamma ina zuwa wata makarantar islamiya

ta matan aure wacce ake zuwa karfe uku a taso budu da rabi, a can ma na yi kawaye amman iyakana da su a makarantar wai kuma a waya da muke chatting. Ga kuma cikina da shiga wata bakwai da shi a yanzu, ba wata wahalar na ke ba bayan nauyin da cikin ke min s

ai kuma yawan zazzabin da tsandar abinci, sai dai bana nunawa a gaban Gogan nawa saboda na san halinsa yana ganin wani abun zai iya hana ni karatun ko yanzu da be ga wani abun ba yana fadar wahalar tana ma cikin yawa balle kuma ya gono ai a take zai hanani

zuwa makarantar.

  Wani iko na Allah sai na fi gane makaratun arabiya fiye da na bokon da na riga farawa kuma na dan gane wasu aabubuwan a baya domin na iya karanta hausa tun kam na shiga makarantar, bokon ma ba zan ce bana ganewa ba amman na fi gane na

arbiyan fiye da na bokon.

  

  Wata biyu da kai lefen Muhseen akai soma shirye shiryen biki, tun kan 25 Sept aka soma baki a gidan Mama Fulani ciki kuwa har da su Momy da wasu daga familynta da suka zo bikin, da mutanen yola. Abbah ya gyara ko'ina na g

idan an yi sabon fenta an sayo abubuwan tarbon baki da na hidimarsu.

A Abuja aka fara komai na bangaren Mama Fulani ta bangaren Amaryar Muhseen kuma daga Bachi aka fara sannan aka dawo Abuja aka cigaba da shagali. A cikin shagalin biki wani wani labari m

arar dadin ji ya zo mana, Waenda aka tura su je yin jere Rukaiya sun tararda da karamin gida mai ciki da falo daya da bandaki sai kitchen a tsakar gidan, ma'ana dai irin gidan nan na talakawa masu rufin asiri, yadda Mama Fulani ta sha kuka a ranar abun har

tausayi ya bani ba ita ba ba Rukaiya ba ba yan'uwanta ba, Momy ma bata jidadin hakan ba sai dai babu yadda aka iya. Ai ko a lokacin ne Hamma ya hau fada cewar daman can sai da ya ce ayi bincike Mama Fulani tace bincike ba dole ba ne kuma an san iyayensa d

a sauransu. A lokacin ne Abbah ya kiran Mahaifin yaron yana fada masa awai an je jeren dakin an tararda abunda ba a zata ba, sai Wamban kano yake fada masa cewar ai ba shi ya haife shi ba almajirin gidansa ne tun yana matashi har ya tasa ya koma Abuja yana

neman kudi, a gidan man ma shi ba manager ba ne yana cikin amsu siyar da man ne dai a tanki. A ranar Rukaiya suma ne kawai ba tai ba akan bakinciki ita da Mama Fulani. Hamma ne ya saka aka nema masa wani gidan haya mai kyau aka je can akai jeren.

Washe g

arin ranar da akai Walima akai Dinner, sai da kowa ya halarta sannan daga baya ni naje tare da Hamma, na sha kyau abuna ni kaina na san na yi kyau domin lace din angon blue ne mai fitar da farin mutum, ga kuma tsoraye na aka min suka sauko har bayana, kuma

nai sa'a Hamma ya bar ni na fidda abuna sai dai be barni na yafa karamin gyale kamar yadda kowa ke yafawa ba nawa babba ne amman hakan be hana ni yin kyau ba, da man kyau mace ba a fitar da surar jiki ba ne daga kyau tufafi ne da ainahin halittar da Allah

yai ma bawansa. An zubar da kudi sosai a gurin karin har nake ganin kamar hakan be dace ba, angwaye da Amare sun sha kyau sosai, duk inda Hamma yai yana rike da hannuna karin ma bayan yayi musu sai ya dawo gurina yana ta min karin ni ko har kunya na ke ji

saboda cikin jikina, ban taba daukar cewar Hamma zai iya rawa kamar haka a gaban mutane ba, ba wani rawa yai can sosai ba amman yana takawa a hankali yana wasa da hannuna. Ina tsaye da shi wata cousin sis dinsa ta zo tai masa kari ta dauki hoto da shi, na

ji zafi sosai shi kansa sai da ya lura da hakan har yai murmushi.  An yi dinner lafiya washe ya kama Assabar sai aka rabu wasu suka tafi Bachi dauren auren wasu kuma suka tsaya a nan Abuja a inda akai na su Rukaiya da Humaira da Zainab da Batula.

A da

ren ranar da aka daura auren aka tafi da su Zainab da Batula zuwa Agadez tafiyar da akai ta da ni duk kuwa da kasancewar Hamma be so haka ba, ni kuma na lake sai na tafi kuma Momy ta saka baki a dole ya kyale ni a bisa sharadin kwana biyu zan dawo saboda s

higa kotun da za ayi. A cikin garin Kaduna aka kai Humaira Rukaiya kuma a kano gidan da Hamma ya kama musu Muhseen kan a Abuja ya tare da matarsa. A gida mai kyau aka aje su su kansu sun san an musu gata, daman mai hakuri mawadaci hakurin zaman auren da Am

my tai ma jureya da tarbiyantar da yayanta da kuma cirewa rai kwadayi sai gashi Allah ya bawa yayanta inda za su huta kuma su jidadi.

  Kwana na biyu a Agadez din bayan kai su Zainab da Batula muka dawo tare da Mama da wasu da suka rakota saboda jin cewa

r zama na karshe ne za ayi, washe garin ranar da muka dawo ya muka tafi sokoto har Hamma saboda case din. Ranar da muka isa ranar aka shiga kotun wani abun da zai baka mamaki har da yan jarida abun ban san taya suka ji ba ko da yake abun duniya baya boyuwa

. Alkalin ya yanke hukunci ne akan kwararan shidu da kuma hujojin da aka gabatar a gaban Alkalin.

  Hukuncin shekara ashirin da biyar alkalin ya yanke masa daman tun da aka soma case din aka rufe asibitinsa, sai gashi kuma alkalin ya hada da asibitin cew

ar a rufe ta gaba daya. Kamar wanda akai aka yi ma albishir da mutuwa haka Doc Asim yai da fuska da ya dafe kansa. Mu kan ran mu fes domin yan yanke masa hukuncin daya dace da shi, sai dai Alkalin ya ba shi damar daukaka kara zuwa kotun Abuja idan yana ra'

ayi. Ban yi tsammanin zai yi hakan ba, sai ga shi lauyansa ya fadi cewar za su daukaka kara zuwa Abuja domin ayi musu adalci a can.

A ranar ruwa ne kawai ban zuba kasa na sha ba akan dadi da murna, amman na yi farinciki sosai kuma na yi ma Allah hamdal

la, wani abun da ya kara min jindadi da sunan Hamma be fito a ciki ba, hakan na nufin ya saba siyarda kodar kuma wai Hamma ne kawai ya siyarwa ba, domin idan har zai fadi sunan Hamma to zai fadi na sauran manyan ma da ya siyarwa.

  Cikina na cikin wata n

a tara aka fara zuwa kotun Abuja na daukaka karar da yai a wannan karon ma ba mu muke zuwa ba wani lauyan ne yake wakiltar mu.

  Asibitin da na ke awa likitar ta fada min Edd na, tun daga ranar Hamma be sake ba ri na tafi makaranta ba fita ma baya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login