Showing 90001 words to 93000 words out of 237425 words

Chapter 31 - ZAKI COMPLETE

gashi yanzu ina zaune gabanta ina kula da ita. Farida ce ta shigo dakin ta tsaya daga jikin kofa tana kallona.

“Bayan tafiyarki abun yai tsamari bata iya tashi komai a inda take take yinsa, na iya

kokarina na kula da ita, daga baya Mama ta hanani, wacan kitchen din da ke cikin gida ya lalace shiyasa Baba ya buga mata kwano ya dawo da ita”

Hannu na saka na share hawayen idonta.

“Kin san ba zaki iya kula min davita yadda ya kamata ba, miyasa k

ika ce za ki yi? Miyasa kika bari na tafi? Aminta ba ta ce haka ba Farida yanzu da mahaifiyarki ce kina tunanin zan iya barinta a haka? Wallahi ba zan iya ba”

“Na yi iya kokarina Ataa Wallahi dawainiya da Ataa ba abu ne mai sauki ba”

“Eh na sani ai,

ba abu ne mai sauki kula da Nana ba, ba abu ne mai sauki kula da uwar da ba taka ba, amman kin san ba dan dole ba babu yadda za ayi na tafi na barta, idan kika duba dalilin tafiyata kadai ya isa ya saka ki tausaya min ki tausaya mata ki kula da ita”

Ta

yi shiru bata ce komai ba, ni kuma na mike tsaye na fito waje nai alwala nai sallah na cire Hijab din na aje na rafka uban tagumi ina kallonta, ta ina zan samu mafita? Duniyar nan ta juya min ko ina na raba ba dadi, duk inda na saka gaba da zimmar cimma bu

rina sai wani abun ya shiga gabana ya tare, sai yanzu na gane kwata kwata bana da sa'ar rayuwa kuma bana da nasara a rayuwata sai dai hakan ba zai saka na kyale rayuwar Nana a haka ba, ko da ko raina zan ransa. Ta ina zan fara baran zan koma? Ko kuwa sata

zan yi? Wani zai kaiwa koke na ko kuwa mutuncina zan siyar? Duka ban gan mafita a wannan ba. Da tunanin inda zan samu taimako na kwana na a raina.

ALIYU POV.

Bayan sun shiga cikin gidan ne Rahma na dakinta na wuce dakinsa yai wanka ya fita

masallacin unguwar yai sallah la'asar sannan ya dawo cikin gidan ya shiga dakin Rahma, zaune ya same ta saman sallaya da alama ita ta gama sallah ne a yanzu. Kasa ya zauna kusa da ita yana kallon fuskarta dake dauke da damuwa, har ya bude baki yai mata mag

ana sai wayarsa dake aljihu tai vibration alamar kira, ciro wayar yai ganin number Mama Fulani be tsaya bata lokaci ba ya daga.

“Aliyu kana ina?”

“Gida”

“Zo ina son magana da kai?”

“Lafiya dai?”

“Lafiya akan matsalar haihuwarka ne, Rahma ta

fada mana gaskiya ai”

“Gaskiya kuma? Wani abun ne?”

Mama Fulani bata sake ce masa komai ba ta kashe wayar. Sai ya kalli Rahma

“Wani abun kika fada wa Mama?”

“Ban yi magana da Mama ba, amman na yi da Momy shi ma kuma ban san cewa ba su sani ba



Wani kallo ha aika mata irin kallon nan na me kika fada musu.

“Na fada mata cewar matsalar haihuwar daga kai ne”

“For what?”

“Na dauka sun sani”

“Ko sun sani be kamata ki yi wannan maganar da su Rahma”

“Abun ne ya fara damuna yanzu, ku

ma a da suna ta ganin laifina amman yanzu za su fahimci ba daga ni ba ne wata kila za su daga min kafa”

“Amman idan matsalar daga ni ne be zama damuwarki ba? Kina kokarin chanjawa daga yadda na sanki Rahma”

“Ba canja nake ba Aliyu, damuwar ka damuwa

ta ce, sai dai a yanzu matsalar nan ni ta fi shafuwa fiye da kai, a baki rame na ke zan iya mutuwa a ko da yaushe, ba tare da na bar abunda za a tuna da ni ba, amman kai kana nan raye har na tsawon lokaci”

Be sake ce mata komai ba ya mike tsaye yana sak

a wayar ajihunsa ya fice daga dakin. Cikin bacin rai ya isa gidan sam be jidadin abunda Rahma tai masa ba, domin be fadawa kowa ba kuma be za ci zata iya fadawa wasu ba, wasun ma kuma iyayensa. Ko da ya shiga falon Kanensa na ciki suna ta fira da dariya,

be kula su ba ya haye sama zuwa dakin Mama Fulani sai ya samu Momy da Abbah a ciki suna fira shiga dakin da murmushinsa ya zauna saman kujerar da Abbah yake zaune yana gaisawa da shi.

“Abbah dawowan rana kai?”

“Eh Wallahi Hajiya Fulani ta fada min n

a ce bari na samu na zo mu gaisa da ita”

“Gaskiya kam ko mu da muke cikin gida muna wahalar ganawa da kai balle ba ko”

“To ya za ayi aikin ne a haka sai hakuri”

Mama Fulani ce ta shigo dakin ta tsaya jikin kofa tana kiran Aliyu.

“Aliyu magana

nake son yin da kai fa”

Tashi Aliyu yai ya bi bayanta suka nufi dakin Baby a ciki suka zauna. Ta kalle irin duban bana wasa ba ta ce.

“Rahma ta ce matsalar daga gareka ne?”

“Matsalar me ba?”

Yayi kamar be fahimci abunda take magana akai ba.

“Ba mu da matsayin da zaka fada mana matsalar ka ne Aliyu? Ko kuma ka boye mana gaskiya ne saboda ka kare matar ka?”

“Ba ko daya, na san idan na fada muku za ku damu, ni kuma ba haka na ke so ba, kuma ko da matsalar daga ni ne idan Allah ya rubuta zan

haihu zan haihu”

“Da gaske ne kenan?”

“Gaskiya ne Mama”

Mama Fulani ta rufe baki idonta cike da kwalla.

“Aliyu da gaske fa ka ce”

Na gyada mata kai.

“Gaskiya ne Mama, sun ce kwayoyin halittafa ba su da karfin da za su rayu a mahaifar R

ahma”

“Kuma babu wani abun da za a iya yi? Babu wata mafita”

Ta tambaya cikinnmuryar kuka domin har ga Allah bata son abunda ya taba Aliyu, balle kuma haihuwa da take babbar abu.

“Mafita kawai addu'a kuma zan cigaba da neman magani ko Allah zai sa

ka a dace”

Dafe kai tai cike da tausayinsa. Tashi Aliyu yai ya koma kusa da ita ya zauna.

“Mama ki daina damuwa ba komai”

“Akwai komai Aliyu, haihuwa tana da muhimmanci sosai za mu so muga jikokinka, kuma ba zan so wata macen ta ki ka saboda rash

in haihuwa ba”

“Miya kawo wannan maganar kuma?”

“Kana tunanin Rahma zata zauna da kai a haka? Gashi ta fara korafi tun yanzu, shiyasa na so ka kara auren tun tuni amman ka ki”

“Babu zance aure a gabana Mama, ni bana iya zama da mace sama da daya b

ana iya rayuwa da mata biyu”

“Ba ni kadai ba Aliyu Momynka ma ta damu kuma duk wanda yake kaunar ka idan yaji wannan maganar dole zai damu da matsalarka”

“Ko wane bawa da akwai abunda ake kaddara masa Mama wata kila ni irin jarrabata kenan”

“Haka

ne”

Ta fada tana share hawayenta sannan ta ce.

“Kuma ina son na fada maka karka taba yarda ko tunanin daukar kodarka ka ce zaka bawa Rahma dan na san halinka”

Murmushi yai mai sauti.

“Mi ya kawo wannan maganar kuma Mama? Idan na na bata ai Ra

hma matata ce”

“Eh matarka ce amman mu iyayenka ba ku yarda ka bata ba, kar ma ka taba wannan tunanin a rayuwarka, sai dai a nema mata magani ko kuma a samu wata dabam a siya mata amman ba taka ba sam ba mu aminta ba...”

Mama Fulani bata kare gama ru

fe bakinta ba, Rukaiya ta shigo dakin da sallama tana fadin

“Mama Abbah na kiranki”

Mama Fulani ta mike tsaye ta fice tana nanatawa Aliyu zancenta, har Rukaiya ta juya zata fita Aliyu ya kirata ta juyo.

“Kamal ya kawo Ataa?”

“Eh amman be shigo

ba ita kadai ta zo kuma Mama ta bata kudin mota ta maida ta gida”

Mikewa yai tsaye da sauri.

“What? Miyasa?”

“Daman ai Mama ta ce ba zata kwana a gidan nan ba”

Rukaiya ta bashi amsa tana kallon yadda hankalinsa ya tashi. Fita yai daga dakin ya

nufi dakin Mama Fulani sai ya same ta ciki tana magana da Momy.

“Mama miyasa kika kori Ataa?”

Tsayawa tai kallonsa kamar yadda Momy ma take kallonsa.

“Why Mama why”

Ya tambaya kamar ya fasa kuka.

“Aliyu wai miye alakarka da yarinyar nan ne

? Ina ce a nan gidan ka santa kuka aiki kawai ta zo amman kun bi ku fitini kanku da ita”

Cewar Mama Fulani Momy ta kalleta ta ce

“Yanzu Fulani sai da kika sallami yarinyar nan? Ba asibiti Kamal ya kai ta ba?”

“Ya dawo da ita ai na bawa Zaharadeen

kudin motar ta na ce ya dora ta a mota, ni ba zan zauna da ita a gidan nan ba”

“Baki kyauta min ba Mama, ba ki san kudiri akan yarinyar nan ba”

Cewar Aliyu cikin rashin jindadi.

“Kudirinka kamar ya?”

Be bata amsa ba ya aika mata da wata tambay

ar.

“Wace tashar kika ce ya kai?”

“Ko kaje yanzu ba zaka same ta ba, and bari na fada maka indai na isa da kai karka bi bayan yarinyar nan”

Mama Fulani ta fada tana nuna shi da yatsa. Sa ya zauna a saman kujerar dakin ya dafe kansa, ji yai babu d

adi gaba daya ranar ba tai masa dadi ba, an kori Ataa Mama Fulani ta hana ya bi bayanta and ga abunda Rahma tai masa.

“Daga zuwan yarinya ku dauki wani buri ku dora akanta yar talakawa? Abun kunya ma aiki take a gidan nan fa haba Aliyu ko kowa zai ce y

a so ta ai ba da kai ba”

Dagowa yai ya kalli Mama Fulani.

“Ba son ta na ke ba Mama, taimakon zan yi saboda halin da muka saka ta”

“Wane hali? Halin me kuka saka ta? Ina ma kasanta idan ba nan gidan ba? Ko kuwa dan fadan da nai mata da be taka kara

ya karya ba shine wani hali”

“Ba shi nake nufi ba, kodar mahaifiyar yarinyar nan aka cire aka sakawa Rahma ba da amincewar su ba, aikin da take a nan saboda ta samawa mahaifiyarta magani take”

Momy ta zaro ido tana rufe baki.

“Daman yarinyar nan

ce? Ta ina ka sani?”

“Ta mana aiki ai Momy ko kin manta?”

Ya fada yana kallonta da damuwa a fuskarta.

“Kasan da ita ce ka kyaleta tana ta shan wahala? Ka kasa taimakonta? Anya kana da imani kuwa? Wace irin zuciya ce a kirjinka? Wane irin rayuwa

ce wannan?”

“Momy ta ki aminta da ni ne, a duk lokacin da nai mata maganar mahaifiyarta sai ta fada min wata maganar dabam marar dadi, ta kasa yarda cewar taimakonta zan yi, a yanzu ma ina kokarin ganin ta aminta da ni ne kuma Mama ta koreta”

“Innali

llahi wa'inna ilaihirraji'u amman wannan yarinyar tana ganin rayuwa”

Mama Fulani ta gyara tsayuwarta cikin yanayin da ke nuna bata jidadin boye mata da Aliyu yai ta ce.

“Baka taba fada min wannan maganar ba, baka taba labarta min komai ba, taimakont

a da kake son da ma gaskiyar abunda ya faru duk baka fada min ba”

“Ba abu ne mai dadi da zan rika labartawa kowa ba Mama”

“Haka ne”

Ta fada sannan ya juya ta fice daga dakin. Saukowa tai downstairs ta nufi kitchen cikin wani yanayi marar misaltuwa

, ko Muhseen da ke zaune a falon bata kula da shi ba har taje ta hada ma Abbah abinci ta fito ta fice ta kofar gaba zuwa part din Abbah, abincin ta kai masa ta zuba masa da kanta kamar yadda ta saba.

“Lafiya dai Hajiya Fulani?”

Abbah ya tambaya gani

n yanayinta.

“Lafiya Kalau”

Bata fada masa komai ba duk kuwa da kasancewar fuskarta ta nuna hakan. Sai ya gama cin abinci ya tashi a uzurce ta rako shi har gurin mota ya shiga sannan ta nufo part dinta. Lokacin da ta shigo sai ta zauna a falo tana ta

kallon su Rukaiya da Husnat dake gardama kan wani film, kallonsu kawai take amman hankalinta baya gurinsu, Aliyu ne ya sauko yana rike da wayarsa ya nufo inda Mama Fulani take zaune, sai da ya karaso daf da ita ya dan risina sannan ya ce.

“Mama ina ne

unguwar su yarinyar nan, kuma daga ina aka akawo miki ita?”

“Ban san kowa nata ba, balle na san unguwarsu”

“Amman baya kawo miki ita?”

“Wacce ta kawo min ita ma ban san inda take ba”

Tana fadar hakan ta mike tsaye ta nufi upstairs ta barshi a

gurin risine Muhseen da sauran yan'uwnas suna kallonsa domin sun ji abunda yake tambayar Mama Fulani sun kuma fahimci wacce yake tambayar, ban da Muhseen da be san abunda yake faruwa ba. Mikewa Aliyu yai tsaye ya fice daga falon, motarsa ya nufa ya shiga

ya dauki hanyar gidansa cikin damuwa. A masallacin hanya ya tsaya yai sallah magariba da isha'i sannan ya shiga gida. A falo ya fara zaunawa ya dafe kansa yana ta yawo da idonsa, har ga Allah be jidadin korar da Mama Fulani tai ma Ataa ba, all his plan yan

zu na taimakonta ne and yanzu be san ma inda zai sake samunta ba, tana kadunar kamar yadda wacan ta fada masa ko kuwa tana cikin sokoto? The way da yake ganin yanayin Mama Fulani ba lallai ta fada masa inda zai ga Ataa ba.

“Ban zata maganar zata haifar

da wata matsala ba”

Cewar Rahma tana sauko daga stairs. Kamim ta karaso Aliyu ya mike tsaye ya wuce zuwa upstairs yana fadin.

“Ba shi ya dame ni ba yanzu”

Juyowa tai tana kallonsa.

“To me ya dame ka? Wata matsalar ce?”

Be ce mata komai ba

ya shige dakinsa bakin gadonsa ya zauna yana kallon dakin kamar wani bakonsa. Rahma ce ta shigo tana tafiya a hankali ta zauna kusa da shi.

“Aliyu akwai wata matsalar ne?”

“Yarinyar da tai mana aiki wacce aka kirewa mahaifiyarta koda aka saka miki,

ta zo nan Abuja tana aiki gidan Mama Fulani and yau Mama Fulani ta koreta”

Da Mamaki Rahma ta kalleshi tasan ba mutum ne mai yawan magana ba lallai ya fada mata cewar yarinyar tana aiki a gidan Mama Fulani ba, amman bata ga abun damuwa a cikin lamarin

ba, akan mi zai damu da an koreta? A take zuciyarta ta soma raya mata son ta Aliyu yake.

“Miye abun damuwa dan Mama fulani ta koreta? Wata kila ta mata ba daidai ba ne shiyasa ta koreta”

“Ba lallai sai ta mata wani abu ba, and ba ni da wani plan a y

anzu daya wuce taimakon yarinyar saboda halin da muka saka ta”

“Ba mu saka ta cikin ko wane hali ba Aliyu, ba laifin mu ba ne, da muka ce a nemo siya mukai kuma ka biya kudi ba a hanya ka kareta ka cire mata kodar ba, ban ga dalilin damuwa ba sai idan s

on ta kake!”

Ta fada da kamar fada idonta na cika da kwalla. Aliyu ya kalleta da kyau

“So ne abunda ranki ya kawo miki? Ba ki yi tunanin ya kamata mu taimake ta ba? Ba ki duba irin zalincin da akai mata da irin rayuwar da ta shiga?”

“Ba mu muka sa

ka ta a cikin wata rayuwa ba Aliyu, idan ma zalinci ne b mu muka zalince ba”

“Amman sanadin wa? Tun farkon da aka samu kodar nan ya kamata na bincika daga gurin wa ta fito ban yi ba, gashi abunda ya faru, yanzu kuma na gane gaskiya sai na ce zan hau gad

o na kwanta nai rayuwata na kyaleta? Abunda ya faru da ke Rahma ishara ce, wata kila da ba a zalinci yarinyar nan ba da yanzu kodar da aka saka miki bata kone ba”

Hawaye ne ya sauko mata tana kallonsa.

“Mommy ta yi gaskiya, tun ba mutu ba ka fara ga

jiya da ni, da ada ne baka iya yin maganar wata mace a gabana Aliyu kuma ba za fada min wata magana da zata bata min rai ba, gaskiya ne maza ba su da tabbas, korar da akai wa wata ita ce damuwarka ba lafiyata ba? Saboda ni ina daf da mutuwa ka auro wata ko

?”

Mikewa tai tsaye ta fice daga dakin Aliyu ya bita da ido yana jin kansa kamar zai rabe biyu, gaba daya yau komai na duniyar nan ya hade masa, rumtse ido yai gam kamin ya bude ya mike tsaye ya bi bayan Rahma, yayi zaton zai same ta tana kuka sai ya sa

me tana hada wasu tufafin nata cikin akwati tana hawaye. Kusa da ita ya zauna yana kallon yanayinta ya kai hannu ya rika hannunta ya soma magana a hankali.

“Lafiyarki ta dame ni Rahma, amman hankali ya fi karkarta akan yarinyar ina zan same ta har na t

aimaka mata wata kila idan na taimaka mata Allah zai dube mu ya ba mu haihuwa kuma ya baki lafiya”

Mikewa tai tsaye ta nufi wardrobe ta rufe sannan ta juyo tana share hawayenta ta kalleta.

“Mommy ta fada min gobe da misalin Goma na safe za mu wuce,

ina son na kwanta da wuri saboda na samu bachi”

Kallon kawai yake har ta zagayo ta hau saman gadon ya lullube da bedsheet ta juya masa baya. Mikewa yai shi ma ya kashe wutar dakin ya dawo bayanta ya kwanta ya rumgumeta ta baya, lumshe ido yai ba dan bac

hi ba sai dan tausayin Ataa daya cika masa zuciya a yanzu ya fi tausayinta fiye da Rahma, sai yanzu yake ji da ma ace Kamal be dawo fa ita ba da Mama Fulani bata koreta ba, wata kila ma ba zata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login