Showing 105001 words to 108000 words out of 237425 words

Chapter 36 - ZAKI COMPLETE

daina tsifar nan karki gajiyar da kanki idan mun ci abinci zan ka

i ki saloon a gyara miki kai”

Sauka tai daga kan gadon.

“Bana son fita ko'ina yau na fadawa Mommy ta aiko da mai mata kitso ta zo ta min”

Bandaki ta nufa ta barshi a gurin zaune. Bayan ta gama abunda zata yi ta fito sannan shi ma ya shiga ya wanke

bakinsa ya fito sai ya same ta gaban madubi zaune tana kallon kanta hawaye na sauko mata.

“Wani abun ne kuma?”Juyowa tai ta kalleshi.

“Yanzu Aliyu idan na mutu ba zaka wuce wata daya ba zaka mantani ko?”

Kallonta yake ba tare da yace mata komai

ba.

“Idan na tuna ba saboda ni ka zo garin nan ba sai na ji kamar na hadiye zuciya na mutu, ban taba kawowa a raina cewar zaka taba son wata mace ba, watan ma kazama yar aikin gidanka kuma yar bara a titi”

“Taso muje mu ci abinci”

Shine abunda y

a fada yana juyawa.

“Ba ka son ayi maganarta ko? Saboda ta fini kyau ta karbu a zuciyarka, saboda kana sonta wata kila ma ka kosa na mutu ka aureta....!”

“Rahma....!”

Ya kira sunanta a tsawace da duka muryarsa, ba ita kadai ba har kujear da take z

aune a kai sai ta girgiza.

“control your tongue, Bana son nanata magana kin sani, kuma bana son bata miki rai amman kina kokarin ganin sai na bata miki rai, kin riga kin karya yarinyar kin kuma juya mata baya dan haka babu ruwanki a cikin wannan magana

r, idan wani abun ne a tsakanina da ita ne ba da ke ba, lamarinta ya daina damunki kina damuna, ki bar ni na ji da ciwonki da kuma kuskuren da na aikata”

Tunda ya soma maganar hawaye yake sauko mata har ya gama ya juya ya fice daga dakin cikin bacin rai

. Maganganun da yai mata suna ta maimaita kansu a cikin kunnenta, zata ita rantsuwa ta sake ra tsewa babu kaffara, cewar Aliyu be taba daka mata tsawa kamar haka ba, ko fada sukai ko suka samu tsabani sai dai ya kyaleta ya ki yi mata magana ya daina kulata

amman ba fada kamar haka ba.

“A a ba zaka auri wata ba Aliyu ko bana da rai balle ina raye, ba zaka so wata ba”

Ya fada tana girgiza kai sai kuma ta saka hannunta ta watse duk abunda yake kan miron ta dauki stool din ta jefi ruwan mirror da shi a t

ake ya watse ya fadi kasa tana ihu kamar wata mahaukaciya. Kuka tai sosai har sai da kanta ya soma ciwo kamar ance mata da gaske Aliyu son Ataa yake kuma aurenta zai yi, sai da idonta yai ja sosai sannan Aliyu ya shigo dakin ya daga daga kwancen da take ya

rumgume matarsa tsantsan jikinsa.Wani lokacin yana dagawa Rahma kafa saboda ciwonta yasan abu kadan zai iya sanadin tashin ciwonta ko kuma ya saka ta cikin wani hali, idan ma ta yi kishi ai saboda shi tai kuma saboda tana son sa, sai dai hakan ba zai saka

ya biye mata ba ta yarda cewar ita kadai zata zauna a gidansa ko a zuciyarsa duk kuwa da ba shi da muradin auren mace sama da daya. Kara fashewa tai da kuka tana jimkeshi da hannayenta. Sun dauki lokaci a haka kamin ya dagota ba tare da ya ce mata komai b

a ya saketa ya shiga bandaki yai wanka tana zaune a gurim har ya fito ya shirya a gabanta ya saka agogon hannunsa da atm dinsa da wallet sannan ya kalleta.

“Ta so muje ki karya”

Kamar mai jira sai ta mike tsaye ta sauri ta bi bayansa domin shi tuni

yayi gaba, kamar masu rigengen saukowa daga stairs din haka suka sauko, ita tana sauri ta cin masa su sauko tare shi kuma yana ta lafiya abunsa ba tare daya jira ta ba. Ya riga isa dinning sai yaja mata kujera ta zauna sannan ya shiga zuba mata abincin bay

an ya gama shi ma ya zauna kusa da ita ya zauna yana ta lasa wayarsa kamar be san da zamanta a gurin ba.

“Ba zaka ci abincin ba?”

“Na ci”

Ya fada ba tare daya kalleta ba, ba dan kuma ya ci abincin ba. Sai da ta ci ta koshi sannan ya tashi ya koma

sama sai ta bishi a ciki ko da ta shiga ta samu yana hada maganinta gurin daya, sannan ya shiga bathroom ya debo mata ruwan tab ya mika mata maganin ta karba ta sha. Sai ya sumbaci goshinta kamar yadda ya saba mata.

“Zan fita amman ba zan dade ba zan

dawo yanzu”

Da kallo ta bishi har ya fice daga dakin sannan ta sauke ajiyar zuciya tana jin tashi motarsa ta dauki wayarta ta kira mahaifiyarta tana kuka.ALIYU POV.

Ko da isa gidan Momy biyu ta kusa domin rana ta bude sosai wani gurin ma har an fara

kiran sallah.

Amina ce da Momy zaune a falon Amina na kwance Momy kuma na zaune suna cin apple. Daga kwance da Amina take ta mikawa Aliyu gaisuwa sai ya watsa mata harara.

“Ni za ki gaisar a kwance”

Saurin tashi tai zaune ta sake gaisheki sai k

uma ya ji amsa mata ya kalli Momy yana mika mata gaisuwa.

“Kai komai na ka na zafi ne, shi gasar da mutun a kwance kuma laifi ne?”

“Yayanta ne ni fa Momy wannan ai rashin da a ne, je ki duba min abinci”

Ya karasa yana kallon Amina, da sauri ta ta

shi ta nufi dinning. Momy ta sake kallonsa ta ce.

“Ka je da safe ka duba mahaifiyar Ataa?”

“A a ba mu dade da tashi daga bachi ba”

“Kai da wa?”

“Rahma”

“Au iyayenta sun yarda sun baka ita? Ta dawo?”

“Daman ai ba hana min sukai ba, zuwan d

a sukai a nan ma da ban amince ba da ba zan barta ta zo ba”

“Amman dai kasan ya kamata ka je da safe ka gaisa da mahaifiyar yarinyar nan”

“Momy ban san rana yayi haka sosai ba yanzu zan je”

“Kara ka fara zuwa inyaso idan ka dawo sai ka ci abinci,

Muhseen ya zo kuma ban san halin da ake ciki ba, ni bana son zuwa yanzu ina jiran Ramatu ne ta zo muje tare dan na fada mata cewar Daddynku yana da patient a asibiti ta zo ta rika kwanar mana da ita, ka ga ita ma Ataa sai ta samu tana dan hutawa kar dawain

iyar tai mata yawa”

“Ramatu mai aikin Hajiya Baraka?”

“Eh kasan tana da kirki sosai, bana son dauko wani daga gidan dangina ne ko na Daddynku bana son maganar tai ta yawo ne, amman ka ga Hajiya Baraka aminiyatace ba kowa zata fadawa ba”

“Muhseen y

a zo kik ce Momy?”

Ya tambaya yana kallon Amina wacce ta doso inda yake rike da plate din abinci.

“Eh nan ya fara sauko kamin ya wuce asibitin”

“Ina abincin da za a kai mata?”

“Gashi can a dinning”

Ya mikawa Amina keys dinsa hannunsa.



Saka min abincin a mota”Hannu biyu ta saka ta karbi keys din ba dan tsoronsa na sai dan Momy ta koya musu haka karbar abu da hannu biyu tun suna kanana domin yana karawa mutum kima da daraja a idon mutane.

“Da ya so mi yace? ”

“Be ce komai ba, kawai

dai yace ya dauka Ataa na nan”

Momy na fadin hakan Aliyu ya mike tsaye ya fice daga falon ba tare daya taba abincin ba. Cikin motar ya zauna har Amina ta gama saka masa abincin sannan ya yi ma motar key tun kamin ya danna horn mai gadin ya bude masa ga

te ya dauki hanyar Usmanu Danfodiyo University teaching hospital wato uduth a takaice.

Tafiyar da zata dauke shi minti ashirin da biyar ko ashirin yai ta a cikin minti goma sha sha hudu, a gurin da aka tana dan aje motoci ya aje motarsa ya fito da abin

cin dake cikin kulolin da kwadon da aka zuba plates da spoon a ciki ya aje a gurin sannan ya rufe motar. Tunanin yadda zai dauke su yake dan baya jin zai iya maya biyu yaje ya dawo dan daukar abinci kawai. Wata budurwa ya kalla ta sha kwaliyar kanti tana t

saye jikin wata farar mota sai yauki take kamar miyar kubewa da alama wasu take jira.

“Ke zo nan”

Ya fada kai tsaye kamar wacce ta sani ko kuma daya daga cikin kanensa yana kallonta fuskarsa babu alamun wasa. Kallonsa budurwar tai daga sama zuwa kasa

farar shadda ce a jikinsa ta yi mugun karbarsa kamar wani ango fuskarsa nata haske ga farinsa sai shining yake, ta kuma lura da makekeyar expensive car din da dake yake tsaye kusa da ita ta san tashi shi domin alamun naira sun nuna a jikinsa. Ta nuna kant

a tana wani lauye baki kamar wata karuwa.“Ni....”

Be ce mata komai ba sai kallonta yake, ita bata jira yace ita din ko ba ita ba sai ta karaso kusa da shi tana wani rangwada kamar zata karye.

“Dauki kulolin nan ki biyo ni”

“Okay”

Ta fada yadda

take pronouncing o din is like tana koyawa mutane karatu ne. Shi ya rika kwandon yai gaba ita kuma ta riko kulolin karama da babba ta bi bayansa zuciyarta na raya mata cewar ya kyasa da ita. Kai tsaye suka wuce ciki tana biye da shi har suka shiga dakin d

a mahaifiyar Ataa take. Inda taga ya aje kwandon ta karaso ta aje kulolin tana kallon Ataa wacce ke zaune saman gadon hawaye shar a fuskarta a zatonta ita ce bata da lafiyar.

“Sannu ya cikin”

Ta fada tana wani lankwasa harshe kamar wata bakanuwa. Ha

nnu Aliyu ya saka aljihu ya ciro wallet dinsa ya zaro dubu uku har zai dora a saman gadon asibitin ya ce ta dauka sai kuma ganin Ataa yasa ya mika mata da hannunsa.

“Aa ka barsu kawai”

“Karba mana bana maida kudi”

Hannu ya kai ta karba.

“Thank

you”

Ta furta tana juyawa ta koma tana ta sauraren ta ji Aliyu ya kirata ko ya biyo bayanta amman bata ji ba har ta fice. Ko be tambaya ba yasan an shiga tiyata ne da Mahaifiyar Ataa tunda Momy ta fada masa Muhseen ya zo kuma gashi be tarar da ita ciki

n dakin ba.

Kallon Ataa dake zaune kan hospital bed din Aliyu yai with serious face ya ce.

“Mi akai miki kike kuka?”

Bata ce masa komai ba bayan turon karamin bakinta da tai ta saka hannayenta ta share hawayen fuskarta. Wata kila tsoron tiyatar da

aka shiga da mahaifiyarta take ko kuma wani abun akai mata, or maybe Muhseen ya fada mata wata maganar ne marar dadi.“Ga abinci”

Dauke kai tai.

“Bana ci”

A tunaninsa ko tana tsoron kar ya saka mata wani abun ne ko kuma ya cutar da ita shiyasa ba z

ata ce. Kujerar da ke gefen gadon ya janyo ya zauna ya dauki plate din ya zuba jalop din da sannan ya bude dayar kular ya zuba farfesun kazar da ke cikin ya saka spoon ya soma ci, abinci yake ci amman idonsa akan Ataa ne har ya ci rabi ya mika mata sauran.



“Karbi ki ci”

“Na ce bana ci”

“Idan na ce ayi abu yi ake ba a musa min karbi ki ci na ce”

Kallonsa tai hawaye na mata zuba.

“Ai babu wanda ya isa ya cilasata kai yi Aliyu, sai dai ka cilasta wasu, babu wanda ya isa ya taba wani naka balle

ya taba ka, yadda kaga dama haka kake haka kake juya kowa, ka taka kowa ka cilasta ka zalinci wanda ka ga dama saboda kana da kudi ni kuma kana gani na talaka”

“Ba ni na cirewa mahaifiyarki koda ba, lokacin da aka cire mata koda ina a gurin ne kin gan

ni ne?”

Ya fada yana kokarin danna fushinsa. Sai ta girgiza kai

“Baka nan, amman kudinka suna nan, ikonka yana nan, isarka tana nan waya sani ko asibitin taka ce? Kai ma baka son talaka miyasa ka sakawa matarka kodar talaka? Karyar soyayya kake mat

a tunda baka iya daukar kodarka ka saka mata ba, ba tana da iyaye ba miyasa basu bata kodar su ba? Sai ta Nana matar da ita kadai ta rage min a duniya? Kokarin kare kanka kawai kake yi ai Muhseen ya fada taya za a sakawa matarka kodar da baka san mai ita b

a? Duk wannan taimakon kana min ne saboda ka san ka zalince ni ka cutar da ni ni da mahaifiyata Aliyu kai azzalumi ne....”

Cikin wani irin fushi marar misatuwa ya jefar da plate din hannunsa ya mike tsaye yana huci kamar zai dake ta, sai kuma yai saurin

kawarda fuskarsa daga barin kallon yana kokarin saita numfashinsa. Mikewa tai tsaye wanda hakan yai daidai da shigowar Doc Bukar dakin, tana kallonsa fuskarta da hawaye ta ce.

“Na fada Aliyu ka kashe ni daman mutuwa ta fi rayuwa a yanzu, ka riga ka ga

ma da ni tun da kasa aka cire mahaifiya koda dan zalinci ka sadawa ita ta rayu mu sai mu mutu, ga mahaifiyata can ana mata aiki Muhseen ya fada min zata iya mantawa da komai ciki har da ni har da ni Aliyu, idan kuma bata rayuwa ni ce a cikin matsala saboda

zalincin da kuka mana kai da wannan likitan, har abada ba zan yafe muku ba kuma Allah ba zai bar ku ba....”

Ta fada kanta a sama tana kallonsa hawaye ke mata zuba sosai har wani dauke numfashi take kamar zata shude... Jawur idon Aliyu sukai yana kallon

Ataa take rabe masa uku ba ko biyu babu ko kyafta ido. Doc Bukar ne ya matsa kusa da su yana Kallon Aliyu sai kuma ya kalli Ataa.

“Zauna”

Ya fada sannan ya kalli Aliyu.

“Da za ka fita na wani lokaci”

Sai a lokacin Aliyu ya kalli Doc Bukar ya

sake kallon Ataa sai kuma ya nufi kofa ya fice cikin wani irin bacin rai marar misaltuwa.Ba zai iya fadar lokaci da ya kawo gurin motarsa ba wata kila ma taku biyu yai ko uku ko kuma dari ko dubu shi dai kawai ya samu kansa tsaye jikin motarsa ba tare da

ya san ya iso ba saboda tsananin bacin rai da zafin kalaman Ataa, wani irin gudu jinin zuciyarsa ke yana da tabbacin da za a bude kirjinsa a yanzu wata kila da hayaki za a gani yana tashi. Ita kadai ta kai haka duk duniyar nan ta fada masa magana irin wann

an mai zafi da daci kuma ya kyaleta ita kadai ce mutum ta farko da ta taba taba martabarsa da duk wani abun daya takama da shi tana a talakarta ta fada masa magana son ranta. Bude motarsa yai ya shiga ciki ya zauna for like 40 minutes sannan yai mata keys

ya fita daga harabar gurin. Driving kawai yake ba dan yasan inda zai je ba, gida gurin Rahma ko kuwa gurin Momy? Ko gurin wasu abokansa ko yan'uwa? Kalamanta na ta maimaita kansu a kwakwalwarsa tun yana jin zai iya jurewa har ya kai ga runtse ido yana damk

e sitiyarin motar, sam ya manta cewar tuki yake kuma babban titi yake na gawon nama, har sai da yaji ya bugi wata motar wata motar kuma ta bugu bayan tasa, da sauri ya bude ido yana kiran mafi kyawun sunan a cikin sunayen Ubangiji wato Ya Rahamanin Rahim.

Saurin tsayarda motar yai motar da ke gabansa tai gaba shi kuma ya faka tashi gefe ya fito ya nufi mai motar.

“Malam lafiya kake kuwa?”

Mutumen ya tambaya.

“I'm sorry ina cikin matsala ne”

Aliyu ya fada sannan ya bude wallet dinsa ya ciro sab

abbin kudi da zasu kai 50k ya mikawa mutumen.

“Ga wannan”

Mutumen ya kalli kudin kamar ya karba sai kuma ya dan tsaya jan aji.

“Ai ba kudi ba... ”

“Idan zaka karba ka karba kawai ba zan tsaya magana da kai ba na fada maka ina da matsala”

H

annun mutumen ya kai ya karbi kudin yana dan nuna kamar be so ba. Aliyu ya juyo ya bude motarsa ya shiga mutane sai kallonsa suke yai mata key ya sake hawa titin yana ta tasbihi saboda samun fin karfin fushinsa. Wani guri ya samu can kusa da ga ďan k'ane h

otel ya faka motarsa ya fito yana shakar iskar gurin. Har yanzu ya kasa daina jin kalaman Ataa a kunensa sai dai wannan karon a maimaikon ransa ya bace kamar dazun sai tausayinta ya soma rabar zuciyarsa fiye da da, yarinyar da ke tsoronsa da masu kudi tun

da har ta iya bude baki ta fada masa magana irin wannan tabbas tana cikin damuwa da bakinciki, ya sani ko Ataa zata fahimcin ba nan kusa ba kuma ba a yanzu ba. Yanzu ma laifin ba nata bane na Muhseen ne, for what zai fada mata cewar mahaifiyarta zata manta

da ita? For what zai mata karyar cewar da hadin kan Aliyu aka cire mata koda? Komawa yai cikin motar a fusace ya dauki hanyar gidansu Momy.

**ZAKI

By Khadeeja Candy

32...

Abinci kusan kala hudu Mama Fulani ta shirya ma bakon da zaizo, ko da

tara tai gaba dayansu sun shirya Maryam da Rukaiya sukai wanka Baby ce kawai ta wuce scul. Amman shiru bako be iso har goma da rabi. Sai misalin sha daya Abbah ya kira yace mata bakon ya sauko Nigeria gashi nan ma zai taro shi a airport.

A sannan ne Ma

ma Fulani ta saka su maryam suka kwashi kulolin abincin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login