Showing 153001 words to 156000 words out of 237425 words
na fada masa kai tsaye cewar mahaifinki ne so, a lokacin ne mai martaba ya cilasta ni kula dan aminsa, mahaifinki kuma aka koreshi daga masarautar
, babu yadda mahaifiyata ba tai ba dan ta fahimtar ta shi amman ya ki fahimta, aka cilasta min komawa makaranta a cikin wannan yanayin, na shiga damuwa matuka ina jin cewar da zarar na sakw dawowa a garin mai martaba zai aura min wani ne dabam na ummaruje
ba, daga makarantar na dawo nijar ba tare da sanin mai martaba ba, na sauka a wani hotel na chanja shigata nai shigar da ba za a taba iya gane ni ba, na je da kaina har cikin gidan su Ummaruje, tsoro sai ya kama mahaifiyarsa da mahaifinsa da dukan yan gida
n kasacewar gidan yawa ne, suna ganin cewar idan mai martaba ya san na zo nan zai iya fusace yai musu wani abun, ni na fada masa durina na guduwa, kuma ya yarda saboda so na sosai daga Agadez muka yi doso gurin wasu yan'uwansa, suma suna ya jin tsoro daker
muka samu suka yarda aka daura mana aure a sirrance, sai labarin neman Ummaruje ya fara karade nijar, muka sake guduwa da dan abunda yake hannuna muka dawo kamba, da kudin hannuna muka kama haya, mahaifinki kuma hai shago kofar gida, kuma sai Allah yasa a
lbarka abun ya karbu, sai da na shekara biyar a kamba sannan na haife ki, daga nan sai mutane suka fara tambayar dangina, ganin kowa be zo sunanki ba daga dangin mijina har nawa, daga haka muka fara jin mutane umguwa na zancen wai ni yar sarki ce, sai zama
n ya gagare mu a nan saboda tsoro da fargaban abunda zai biyo baya, muna ta ganin kamar Mai martaba zai iya aikowa nemana ko kuma ya saka a kama Ummaruje, ya siyarda komai nasa kudin hayar mu kuma muka barsu nan muka koma argungu, zaman a can be karbe mu b
a saboda sanar'a shagon da mahaifinki ya fara yi sai ta soma komawa shiririta, sai muka bar yankin gaba daya muka shiga bodinga, a lokacin ne mahaifinki ya fara sana'ar tura ruwa yana siyarwa, sai dai zaman kaune babu dadi saboda ban saba ba, tun ina jin k
unyar na je na yi itace shi kuma ya fita siyar da ruwa har ya zame min jiki, sai na kwana biyu uku ban yi wanka ba, wasa wasa har nai sati kuma babu wanda ya kula ko ya damu da hakan, a hakan ma har na ke ganin na fi wasu tsafta, daga bodinga mahaifina ya
rika shigowa cikin sokoto yana haduwa da wasu fulani da kuma buzaye, idan ya dawo sai ya rika ba ni labarin sokoto ita dai kamar kamba tana da tarin yan nijar da yawa a ciki, ya fada min cewar akwai da yawa a cikin fulani da buzaye da suke rabawa a irin gi
dajen da ba a gama gina ba su zauna, sai nai sha'awar mu yi haka saboda ina son na dawo sokoto da zama daga haka muka tattara muka dawo sokoto, a talatar mafara muka fara sauka, a nan muka fara fakewa a wani tsohon gidan da ba a kare ba, ya cigaba sana'ar
siyarda ruwansa, ni kuma ina kulla gida ina siyarwa, kwata kwata na koma kamar ba yar saurata ba, kalar fatata ta canja wahala ta rufe ni ga kuma cikin Lukman da na samu a wannan lokacin, ya sani laulayi har na haife shi, mijina yana nuna min kauna sosai y
ana kula da ni iya gwargwado, bama cikin matsalar komai domin yana kokarin kawo wa mu ci, har kuka girma ya sakaki a makaranta sai dai yana rasuwa komai ya canja mana Ataa kin sani.... ”
Kuka take kamar yadda nima na ke kukan, hakika na sani na san loka
cin lokacin da mahaifina yai bankwana da duniya ba tare da ciwon komai ba a cikin gida muna fira da shi sai kawai muka ji yayi shiru ya risina daga zaunen da yake muka jijjiga shi shiru Nana ta kira sunanshi ta zuba masa ruwa amman shikenan mai kasacewa ta
kasance, bayan mutuwarsa muka muka siyar da baronsa da duk wani abu na sa muka bar unguwarsa zuwa gidadawa a nan muka kafa bukkarmu kamar yadda muka ga Baba yayi, muka zauna a gurin har zuwa lokacin da masu gidan suka bukaci abunsu, muka sake tashi, da ha
ka mukai ta yawo zama guri guri Nana kuma na fita tai mana bara ta kawo kudin mu siya abinci, har muka fara zuwa tare da ita da muka tara mai yawa sai ta saka ni a makarantar Yakubu mu'azu ni na fara zuwa lukman kuma ya hakura sai gaba, kudin tsintsiya da
kudin pta suka hana ni komawa makarantar sai na cigaba da ya islamiyar ita ma ina haruffa na daina zuwa saboda baran ya shiga kaina na, kuma wani lokacin da yunwa na ke zuwa na dawo, karatun ma sai ya daina zama a kana ya zama bana gane komai, Nana kuma ba
ta damu ba saboda bara kawai ta saka a gaba.
Da haka har karatun ya gagareni na daina zuwa gaba daya, sai Lukman da ke zuwa shi ma jefe jefi.
Mahaifina yana son mu daga ni har Lukman da kuma Nana, na sani a dan zaman da nai da shi na rayuwar da na sam
u tare da shi ya nuna mana kauna, a kullum burinsa ya zai inganta rayuwarmu da ta Nana, yana yawan fada min cewar dadi na nan zuwa ko ba shi da rai za mu jidadi ni da Nana da Lukman, shi ya tafi Lukman ma ya tafi ni da Nana kawai muka rage.
Gaba daya j
in nai kaina yayi nauyi kuma yana ciwo, saboda tunawa da baya da kuma jin labarin Nana, sai dai bana ganin hakan a matsayin laifin da mahaifinta zai iya cewa ba zai yafe ba, wata kila yana raye ko kuma ya mutu Allah nasani, sosai zuciyata ta cika da kaunar
Aliyu domin shine mutumen da ya fara maida ni mutum ya sa na maye gurbin duk wani abu da na rasa kuma yarda ya so ni yadda na ke, ba dan kyau na ko wani abu nawa ba, tsabanin duk wanda zai kalle ni ya so dan kyauna, Momy kuma ta biyo a sahu na biyu a kaun
ar da ta nuna min na son danta ya aureni saboda ya inganta rayuwarta kuma Rahma ta daina min kallon banza, yana da wahala a zamanin nan ace wani wanda baka sani ba kamar Momy da Aliyu su soka tsakani da Allah. Sai a yanzu na ke gane wasu abubuwan da Nana t
ake hango min.
Hakika zabuwa da iyaye akwai ciwo da damuwa, ni kaina da Nana ta kamu da ciwon nan ina ta tsoro da zullumin rabuwa da ita, ni kenan da ke tare da albarkata ina ga ita da guduwa tai ta bar iyayen? Sai yanzu na gano dalilin cewar da take tan
a son ta san hannun da zan fada kamin ta bar duniya, tana kuma tsoron gaba saboda tana tunanin ba iyakar kaddararta kenan ba, lallai ko kadan ta ga na kuma abu ya zo da sauki da ya zama kodarta kawai aka cire kuma har ta samu tattafin Aliyu ya nema mata ma
gani ta warke. A yanzu kam na yarda da zancenta cewar kaddarar Aliyu ce ta zo a hannunta kamar yadda tata kaddarar ta zo a hannun Babana.
Labarin Nana be kara min komai ba sai tausayi da jinka da kuma ganin darajar zabin iyaye ko da kuwa mai cutarwa
ne, matukar ka bata musu rai dole ne sai wani abun ya same ka ko da ko kadan ne, kaunarta na ji ta karu a raina da kuma son zama kusa da ita, domin a yanzu ni kadai ce wacce take da, kuma ita kadai ce wacce na ke gani na ji sanyi a raina wato uwata.
D
aga har ita cikin damuwa da tunani muka kwana, washe gari bayan mun yi sallah na zauna nai yi ma Babana addu'a sosai daman na saba masa a sujida sai dai wannan ta musammance, domin na san a yanzu babu abunda ya ke bukata a tare da ni kamar Addu'a ta. Misal
in takwas da rabi na shiga part din Momy na share komai kamar yadda na sabawa kaina Amina da Husna kuma suka shirya abun karyawa suka ba ni nawa ni da Nana.
Na koma na kai mata, ruwan shayin kawai ta sha ta kasa cin komai fuskarta gaba daya ta kumbura, k
ana gani ka san a daren jiya ta kwana tunani kuma ta sha kuka.
“Nana Babanki zai yafe miki matukar yana raye, shekaru da yawa ya isa ya saka zuciyarsa laushi ya fahimce ki”
“Ba zai yafe min ba, na aikata kuskure na gudu saboda biyan bukatar raina be
kamata wuya ta saka na koma ba”
“Ba saboda wuya za ki koma ba, saboda kin yi nadama kin gane kuskurenki za ki koma”
“Wata kila ma baya raye, abun kunya ne ace na haihu har dayan ya koma ga Allah mahaifina be san yayana ba, yayana kuma ba su san yan'
uwana ba, ba zan iya komawa garin nan ba har abada, na barwa iyayena da masarautar Agadez abun kunya”
Ajiyar zuciya na sauke ina sauraren motar da naji an faka harabar gidan, hayaniyar Amina da Husna ne yasa na tashi na leka window sai na hango Momy ta
fito daga motar ita kadai ba tare da Aliyu ba, wata kila ya tafi gidansa gurin matarsa ko kuma ba yau zai dawo ba.
Fitowa nai na tareta tare da rika jar jakar hannunta na bi bayanta, ita kuma tana ta min murmushi har muka shiga cikin falon, a nan ta
zauna Amina ta debo mata ruwa suna ta daukinta kamar wacce ta shekara bata gidan, ita tana marmarin gwanin sha'awa uwa mai dadi.
“Momy ya Aliyu fa?”
Husna ta tambaya.
“Ba yau ba yace zai kwana biyu kamin ya dawo”
Momy na bada amsar zuciyata t
a raya min wata kila da matarsa ya tafi shiyasa ba zai dawo yanzu ba. Ballantana na san idan Mama Fulani ta ji cewar saboda ni komai ya faru ba zata barshi ya dawo ba, a take na ji raina ya bace. Da abincin mu na rana na dawo part din mu ina jin cewar yanz
u ne ma lokacin da ya kamata na auri Aliyun ko dan Rahma da Mama Fulani sai na ga idan mutuwa za su yi, ace irin tsanar da suke nunawa talaka Aliyu ya aure ni sai ya kenan? Kuma ina tunanin ta wannan hanyar ce kawai zan yi ma Momy tukuicin abunda tai mana,
ita kadai ce hanyar da zan saka mahaifiyata cikin farinciki a yanzu na taimake ta ita ma ta sake jindadin rayuwa.
Da yamma ina cikin shirin zuwa makarantar islamiya, Momy ta aiko tana kirana Siyama ce ta shigo ta fada min gana sanye da nata uniform di
n na islamiya sai dai na ta dabam kamar yadda nawa yaks dabam kasacewar ba makarantarmu daya ba. Kamin na shiga part din Momy na hango mutumen jiya wato ustazu nan yau ma yana cikin shigarsa ta mutunci da kamala. Ina shiga Momy ta ce min.
“Wani na waje
yana sallama da ke, wai yana neman izinin mu kamin yai magana da ke, ki fadawa Nana sannan ki je”
“Momy ban iya fira ba, ko naje ban san mi zan ce masa ba”
Na bata amsa a takaice wanda har cikin zuciyarta haka ne, idan na je ban san abunda zan fada
masa ba, fira da wani a yanzu ina jin kamar ba zata min dadi ba, idan kuma na ce zan yi da gara duk mutanen da za su bude ba ki na furta kalmar so a gareni tabbas ko zai furta ko ya nuna zai zama babu kamun kai a ciki.
“To kije ku gaisa inyaso sai ki f
ada mishi an tsayar miki da miji ko kuma kina da wanda kike so”
Da wannan shawarar da ta ba ni na tashi na fita zuwa gurin mutunen, mun gaisa da shi cikin mutunci ya gabatar min da sunansa aikinsa da kuma inda ya ganni wai lokacin da na taso islamiyar n
an har ya tambaye ni gidanmu. Kai tsaye na bashi hakuri kuma na fada masa cewar akwai wanda za a tsiyar min a gida, ya nuna min rashin jindadinsa da kuma yi min fatan alheri sannan muka yi sallama. komawa nai bq na dauki littafaina na wuce islamiya zuciyat
a cike da tunanin ko zuwa yaushe Aliyu zai dawo? Mi ya tsayar da shi a abujar? Ni dai sam ban jindadin rashin dawowarsa ba, ba zan kuma kira abun da so ba, domin ba ni tabbacin ina son Aliyu ko akasin hakan, sai dai na san akwai sabo wanda ko fada kake da
mutum dole ne wani lokacin sai ka yi marmarinsa balle kuma yanzu da na fara gane amfanin abubuwan da yai min.
MOMY POV.
Bayan tafiyar Ataa islamiya Momy ta tashi ta debi yan gurin da Mama Fulani ta sako mata a kwali wato snacks da cake ta nufi b
q da su, da far'arta ta shiga bq din yana wayance wa kamar komai bw faru ba, ta karanci damuwa a fuskar Nana sai dai bata maida hankaki akan tatauna da Nana akan matsalar ba, a zatonta abunda Muhseen yai ne har yanzu yake damunta.
“Mun yi tafiya shekar
anjiya ban fada miki ba, tafiyar ta safe ce shiya saka”
“Babbu komi Hajjiya ya hanya?”
“Al-hamdulillah, ga wannan”
Momy ta mika mata plates din hannunta, sannan ta dora da dalilin zuwanta bq din.
“Daman Daddyn su ne yace a fada miki kuma a nemi
shawararki aji ta bakinki, wai yana son indai za ki amince sati na mai zuwa a daurawa Ataa aure da wanda take so ko waye ne, mun hanke wannan shawarar ne saboda hankalin kowa ya kwanta ita kanta hankalinta ya kwanta kin ga ko zuwa sallamar nan ba dadi ne
ba, amman idan har aka mata auren dole kowa ya kama gabansa, kuma yi mata auren ba shi yake nufin hana ta karatunta ba no zata cigaba da karatunta a gidan mijin ko kuma a nan idan zai yarda”
“Sati daya?”
Nana ta nanata.
“Nima kaina naga kamar abu
n yayi wuri, sai dai saboda kwanciyar hankali kowa ake son ayi haka, ina son ki manta da duk abunda ya faru ki tambayi Ataa wanda take so idan a kusa ne sai neme shi idan kuma nesa ne sai a san ta yi tun wuri, idan kuma kina ganin watan yayi tsawo za ki iy
a fadar lokacin da kike son a saka, nan da wata daya biyu uku ko shekara ma ko fiye da haka”
“A a hukuncin da kuka yanke ya yi, waya sani ko zan kai gobe ma balle nan da wata daya ko shekara, fatar ko wace uwa ai yarta ta samu gurin zaman da ya dace da
ita, Na gode sosai Hajiya”
“Karki jin kunya ko nauyin komai Wallahi duk wani abunda nai saboda Allah nai, dan haka karki taba kawo wani abu a ranki, ni da ke an zama yan'uwa kuma zan mata komai kamar yadda nai alkwari In-Sha-Allah, idan tarewar a nan ku
sa ne ko nesa duk daya ne a gurina”
“Allah ya saka da alheri”
Sosai Nana ta so tayi ma Momy maganar tashinta, sai kuma ta ji nauyi saboda girman Abunda Momy ta zo mata da shi, idan kuma tai mata maganar a yanzu wata kila ba zata fahimta ba, sai kawai
ta zabi aje maganar a cikin har na wani lokaci.
ALIYU POV.
be Momy sun koma tare ba saboda yana jin zaman sokoto yana gundirarsa, abunda Rahma tai masa kadai ya isa ya saka shi jin baya son zama gidan da suka kasance suna rayuwa a ciki su biyu,
ga kuma tunanin cewar Ataa ba zata zabe shi ba, so yana ganin kamar komawarsa sokoto karin bakinciki ne kawai a gurinsa bayan wanda na Mama Fulani take masa a nan. Domin Abbah ya fada mata matukar aka tambayi yarinya ta amsa musu da cewar tana sonsa za a
daura masa aure da ita sati mai zuwa.
“Wallahi Aliyu ka ma ce ka fasa idan ba haka na zan yi wa yarinyar nan raashin mutunci, sai na sa ta raina kanta sai ta gwammace a haifo ta duniya ba, ba zan taba karbarta a matsayin suruka ba, na kuma zan taba son
ta ba, kar kuma ta ce zata kira da wani sunan ko ta tako inda na ke, kuma idan aka daura auren nan sai na taka har sokoto na ciwa uwarta mutunci na ga wanda ya tsaya musu a garin sokoto, wai har da hada baki da Abbah kun ce sati daya ko? Saboda ayi saurin
yin abun ai kana jin kasan yarinyar ba yar kowa bace kuma ba neman auren suke sun ga dan arziki, wai Aliyu baka ma kunyar ace yarinyar nan ce matar ka?”
Daga ita sai shi ne a dakinta take mishi wannan fada, sai ya shafa kansa ya ce.
“Ni kaina ban t
sammaci haka ba Mama, amman ya za'ayi”
“Baka ma san abunda za'ayi ba kenan? Abunda za ayi kawai ka fasa auren yarinyar nan domin ko na aureta ba zan bari ku samu kwanciyar hankali ba, ga yan mata nan ai babban abunda za akayi ka bawa Rahma haushi a yanz
u ka auro wanda ubanta ya fi uban Rahma arziki, amman ba yar bara a titi ba, bara fa Aliyu bara”
“To zan yi tunani Momy”
Shine kawai abunda ya fada mata ya tashi ya bar mata dakin saboda Maganganunta basa masa dadi,