Showing 213001 words to 216000 words out of 237425 words
na gari, Mai Martaba ba aikata laifi ba, kuma be yi hakan dan ya jefa rayuwata a matsala ko damuwa ba, yayi hakan ne saboda al'adar gidan nan ce, ni kuma sai na bijire na gudu na bar muku abun
kunya da magana a gari, soyayya da kurciya a wacan lokaci ta debi da yawa har na kasa gane cewar abunda na ke kokarin aikatawa babban abu ne kuma be dace na aikata hakan ba, a lokacin dana farga daga abunda na aikata kuma sai na ga lokaci ya kure min ba z
an iya gyara komai ba, amman na gode Allah daya ba ni ikon neman yafiyarku a lokacin da na ke da rai kuma kuke raye, Wallahi ba zan iya kwatanta irin farincikin da jindadin da na ke ciki ba a tsakanin lokacin da nai arba da mai martaba da kuma ganin ki a y
au”
Mama ta fada tana hawaye. Sun dade suna tataunar magana tun tana a tsaye har ta kai g zaunawa, tana sako labarin Babana wai ai ga fuskarsa nan a fuskata, a lokacin da Mama ta bata labarin cewar tana da wani dan bayan ni wanda ya rasu sai da Kakar ta
wa tai kuka, sai dai Mama bata sako mata labarin ciwon kodarta ba a cikin labarin da ta bata. Ban bar dakin sai da na fara jin bachi kusan ma a cinyar Mama na fara shi sai da ta tashi ta ce na koma wai na baro mijina can shi kadai. Sannan na tashi idona da
kufan bachi na dawo inda aka sauke mu kamin na iso har na gaji domin akwai tazara sosai a tsakanin bangaren matan sarki da kuma inda aka sauke mu. Ban yi mamakin samun Aliyu a farke ba, daman ban kawowa raina cewar zai iya kwantawa ba tare da ya gan ni na
dawo ya tabbatar ni na fara yin bachin ba, hakan kuma ba karamin dadi yake min ba. Na yi zaton ko zai yi magana ya ce yaje na zauna na barshi a gurin, sai na ji shiru be ce komai ba kamar ma hankalinsa yana wani gurin. Bandakin na shiga nai fitsari na fit
o ina hamma har da hawayen bachi na cika min ido na ce.
“Baka kwanta ba?”
“Ba zan iya bachi ba sai na tabbatar ke kika fara yi”
Hawa saman gadon nai ba tare da na ce da shi komai ba.
“Ba za ki canja tufafin jikinki ba?”
“Bachi na ke ji sos
ai”
“Na canja miki?”
“A a ka bar su hakan nan”
Tashi yai yaje ya rufe kofar falon sanna ya dawo ya tura ta dakin sai kuma ya kashe wutar ya bata bayana ya rumgume hannunsa a kan ruwan cikina.
“Babyna gobe zan koma”
Ya fada min kamar mai rad
a bakinsa daidai kunne na.
“Miyasa baka son zaman nan ne?”
“Ina son na ga yan'uwanki su san ni na sansu, amman tafiyar ta dole ce”
“Miya faru?”
“Rahma bata da lafiya, ina bukatar na je na dubata”
A take bachin da nake ji ya wartsake wani ab
un na ji ya soke ni a cikin zuciyata wanda ban taba jin irinsa ba.
“Ko kadai kana neman wani uzurin ne daman?”
“Ko kusa, tafiyar ta zame min dole ne tun da ciwo ne ke damunta, ya kamata na je na dubata”
Shiru nai ban ce masa komai ba, sai dai ban
jidadin ko sunanta daya ambata ba balle kuma zancen dubata, wata kila shi ya kitsa haka saboda na bishi mu koma ni kuma bana jin zan yi haka, ko kuma yayi hakan ne domin ya koma wata kila kuma ita ce ta tsara hakan saboda ta samu damar da zai dawo ya baro
nan ko kuma ta hargitsa mana tafiya ko wani abun da dabam da ban san ma'anarsa ba. Ni kan har na manta da yana wata mata wai Rahma ashe fa Aliyun ta ne nake aure, ko tana ina ma iho ban sani ba, kuma ban ji zan iya tambayarsa ba domin bana son ji wani abu
n daya shafi sunanta ma balle kuma ita din da kanta.
“Ki min alkawarin kula da kan ki pls”
Ya fada yana sumbatar saman kaina, sannan ya juyo da ni ya shiga aikawa ko wane bangare na jikina da sako. Mun farka da wuri sakamakon kiran sallah asuba da y
a tashe mu wanda ake yi aciki masarautar, sai da ko wannen mu yai wanka sannan mukai alwala shi ya fita zuwa inda yake jin karar loudspeaker masallacin na fito ni kuma nai tawa sallah a cikin dakin, ina ta tunani ta inda ya ji cewar Rahama bata da lafiya b
ayan ma layin Nigeria ba yayi a wata kasar kamar yadda ya fada min, kwata kwata zancen tafiyar nan be min dadi ba, wata kila saboda na saba da shi ne ko kuma saboda Rahma zai je gani yasa na ke jin ba dadi oho ba dai zan iya fadar dalili ba.
Bayan an g
ama sallah da kamar minti talatin sannan ya shigo inda na ke.
“Good Morning”
Ya gaishe ni tun kamin na mika masa tawa gaisuwar, nikan kasa amsawa nai sai kawai na gaishe shi da halshen hausa sai ya amsa min yana kissing goshina.
“Lafiya kalau, k
in tashi lafiya?”
“Lafiya kalau”
Hannunsa ya miko ya kama nawa.
“Ta so mu kwanta ina son kiji dumi jikina kamin anjima”
“Da rana zaka tafi?”
“Ban sani sai an bincika min idan akwai jirgi”
“Wa zai bincika maka? Taya ina ma ka ji bata da l
afiya?”
“Na kira wayarta ne, sai Yayarta ta dauka ta fada min”
“Amman ka ce layin Nigeria ba yayi a wata kasar”
“Yeah ban da Airtel na can yana yi a nan, har daga saudiya ma ina kira da Airtel, na saka Nasir ya bincika min, ke kuma yanzu ina son k
i fada musu zancen tafiyar idan mun shiga gaishe su”
Na gyada masa kai kawai ba tare da na ce komai ba. Kamar yadda ya fada na ji dumi jikinsa sosai ta a kuma wanin abun mukai ba bayan dogon bachin safe normal sleep, sai dai yadda ya shigar da ni jikins
a ya rumgume ya saka na jidadi kuma na ji dumi da yake fada.
Misalin tara aka kawo mana abincin karyawa tun daga kan shigar masu kawo abinci za ka tabbatar da cewar bayin gidan ne, domin sukansu suna sanye ne da tufafi kala daya sun jero kamar tururuwa
. Duk yadda ya so na ci abinci sosai sai na kasa, sakamakon dadin da raina baya min kan tafiyar da zai yi.
Sai dai na yi kokarin boyewa domin ni ma ban ga abun damuwar akan zai tafi gurin matarsa ba. Daya daga cikin yan matan gidan aka aiko wai na shirya
na fito ni da mijina za mu je mu gaishe da Mai martaba da matan gida. Ni ce kawai nai wanka na shirya shi Kan Aliyu tun kamin mu fara karyawar yai wanka ya shirya.
Rana ta fito sosai ko da muka shiga bangaren Mai Martaba tare da mai mana iso, na yi za
ton wani gurin dabam za a kai mu inda Mai Martabar yake kebe sai ga mu a fadarsa ta jiya duka iyalansa da hakimansa suna ciki ban da shi. Muna shiga sai idon kowa ya dawo kan mu
“Zo nan ki zauna”
Wani Dattijo ya fada yana nuna min inda zan zauna din
a kusa da shi. Ni da Aliyu muka zauna a kasa sai ya fara nuna waenda zan gaida sune iyayena da kuma abokiyar zaman kakata, da kuma sauran da suke yan'uwana wasu dai ban ga fuskokinsu a jiya ba, sai yau ina kyautata zaton zuwa su kai a yau, sai haba haba
suke da ni da kuma Mama. Duka zuri'ar Sarkin farare tas wasu ma har sun fini fari da jar fata, ga kyau kamar larabawa daga mayan har yara da matashi farare ne, sai dai wani ya fi wani farin, a cikin hakimansa kuma akwai fafaren da bakeke, matanyen na sanye
da shadda ga wani uban ginari a hannu da wuya ko wacce ta saka gwanin sha'awa.
A lokacin da sarkin ya shigo sai da kowa ya mike tsaye masu kirari ta bude rigunansu suna tare masa gaba da baya suka fara wasu kuma na fita da katon mafecinsu. Yadda ake ma
sarkin sai da abun ya burgeni kuma ya kara min jindadi. Sai daya zauna sannan kowa ya zauna, da dai daya masu rawanin suka fara zuwa suna mika masa gaisuwa baya amsawa sai dai badawansa su amsa a madadinsa har suka gama gaisuwar.
Sai da yao gyaran murya
sannan yai dan jawabi akan dawowa Mama da kuma zancen yafiyar da yai mata, sannan ya sallami wadanda ba familynsa ba ya bar iyalan gidansa kawai ya sake gabatar musu da jawabi tare da nasiha da kuma jan kunne akan al'amurran rayuwa, fada musu abubuwan da
ya samu Mama na bijire musu da tai a ciki har da zancen cire mata koda wanda kowa be san da maganar sai a yau. Babu wanda be girgiza ba da jin lamarin kuma aka tausayawa Mama, duk na san ba za a rasa wadanda a zuciyarsu za su ce Allah ya kara ba domin ita
ta jawa kanta. Hankalin kakarmu ya tashi sosai jin cewar an cirewa Mama koda sai dai Mai Martaba ya shaida mata ya jaddada mata kuma ya tabbatar mata da cewar za a kwato mata hakkinta domin tuni elya mika abun ga kungiyar likitocin kasar, ko zuwan nan da z
ai yi sai da ya roke su akan su daga mana kafa ta samu zuwa ganin danginta kamin su gama tattara bayanai.
Yayi takaici kuma ya nuna bakincikin akan abunda ya faru da kuma gina mana rayuwa da tai ba tare da yan'uwanta ba. Sai dai abun jindadi kuma mai
muhimmanci dawowarta a yanzu wanda hakan zai ba ni damar sanin yan'uwanta da kuma yan'uwan mahaifina kamar yadda sarkin ya fada.
Bayan ya gama jawabinsa ne aka sallami kowa, ni kuma sai na raba kusa da Mama na fada mata cewar Aliyu yana son na koma yau
saboda Rahma bata da lafiya, ita kuma ta fadawa yayanta yayanta kuma ya samu Mai Martaba ya fada masa a take, Mai Martaba ya sa a bincika masa idan za'a samu jirgi da a yau, aka tabbatar masa da babu sai dai gobe, saboda haka dole Aliyu ya aje tafiyar har
gobe.
A ranar aka kai ni gurin kakannina na bangaren uba, ganin cewar Aliyu zai tafi ba masanar ko ya dawo yanzu ko kuma sai nan da kwana biyu ko wani lokacin, su kansu ba za su jidadi ace ya tafi ba tare da sun ganshi ba, kuma za su iya daukar cewar
saboda su suna takalawa ne, tare da Mama muka tafi da kuma wasu daga cikin yan gida, akwai tafiya mai nisa sosai tsakanin unguwar da Sarkin yake da kuma inda su suke. Ko da muka isa rana ta bude sosai a unguwar su har sun sauke sallah azahar. A hanyar mu t
a zuwa ne na ke labartawa Aliyu jawabin da sarkin yai abubuwan daya fada, domin duka maganganun da yai da yaren buzanci yai shi wanda kuma Aliyu ba ji yake ba.
Sai da aka fadawan ta Mai Martaba ya hado mu da su suka shiga aka sanar sannan mu ka bi baya.
Gidan kasa ne gaba daya gidan, sai dai irin ginin nan ne na mutanen da wanda ake na iyali da yawa, wanda zaka samu wani lokacin har da jikoki ma a gidan. A gidan muka wuni ni da Aliyu suna ta kiran mutane a zo a ganmu wai yar Ummaruje ce kamar yadda take f
ada, tsohuwar ko gani bata yi sosai Nene na ke jin suna kiranta, ta yi farinciki sosai da ganin mu kuma ta yi kuka ita da duka yan gidan jin cewar Baba ya rasu, ba su kadai ba ni kaina sai da nai kukan tunawa mutuwar tasa, yau ga ji a gaban iyayensa amman
babu shi. Sai da dare muka baro gidan a can muka ci abincin rana da dare da za mu dawo aka tasa min nonon rakuma saboda an bani na sha na jidadi har na roka. Kallo daya za ka ma fuskokinsu ka fahimcin cewar suna cikin farinciki da jindadi ganinmu, ban yi z
aton Aliyu zai sake jiki kamar yadda yai a yau ba, fuskarsa na nan a yadda take babu wani walwala sosai Murmushin ma ba komai yake ba, amman ya sake jiki ta hanyar cin abincin da aka kawo mana da har ma da Nonon ragumin wanda ya fada ai yana shansa a gidan
Mama Fulani wani lokacin tana siye ta aje. Duk kuwa da kasancewar an aiko mana abincin daga masarautar suna ganin kamar ba za mu iya cin wannan ba, wani abincin ma na san saboda Aliyu aka girka shi irin tuwon shimkafa miyar Allayahu da akai da man shanu g
a naman kaji da garo a ciki.
Ba tare muka dawo da Mama ba domin ita tana gama gaisawa da su ta dawo gida, wai bata son kowa da kowa ya zo ganta ta san ba zasu taba cire tabon abunda ta jawa musu na ja dansu su gudu ba, ballantana yanzu da ta kawo musu
labarin mutuwarsa har a bada ba za su manta da ita ba, ba kuma za su yafe mata ba, duk wani so ko nuna mata kauna da za su yi ta ciki na ciki tana ganin kamar komai lafinta, saboda ita taje ta same shi da zancen guduwar kuma ya amince.
Na dawo ima jin
kamar kar na baro na dawo nan ba, ba dan komai ba sai dan yadda tsarin gidan da kuma yadda suke haba haba da ni ya burgeni, har ta ginar gidan ana ta lekowa ana kallona, ba ma kamar lokacin da za mu tafi har da masu fitowa suna kallon motocin Mai Martaba.
A cikin unguwar na yi ta ganin zangon maza masu shan shayi da yar butarsu wasu sun yi gugun guri daya sun kuna kidan buzaye wasu kuma suna ta fira abunsu.
A lokacin da muka dawo gidan ma sai aka sake kawo mana wani abincin aka ni dai sai da na ci A
liyu ne kawai be ci ba saboda ya koshi, muna shirin kwanciya aka aiko kirana, har zan fita haka sai ya rike ni ya dauko min Hijab.
“Gidan nan har ya fi gidan mu yawan maza, bana son fitar ki haka Baby, kuma ya zama dole ki min alkawarin kula da kanki d
a jikinki da kuma babyna da yake cikin ki kamin na tafi pls”
“Taya mutum zai kula da kan shi? Da ma dai kula da wani ne ai zan iya”
Ya kama kunkuruna ya rike.
“Karki bar kanki da yunwa, ko kuma wani abun ya same ki, idan kin ji ciwo ko rashin laf
iya ki yi saurin fada, kar ki bar jikinki haka nan sake har wani ya ga kyauki ko ya yaba, ki rika rufe jikinki kina tunawa cewar ke ajiyar wani ce”
Na gyada masa, sai ya sumbance ni sannan ya sake ni na fita. Bangaren da Mama take na nufo sai dai ban sa
me ta a dakin dana same ta jiya ba sai wani dakin dabam,tana tare da mahaifiyarta da kuma wata mai kula da gidan da kuma wasu matan da aka nuna min dazun da safe aka ce matan yayyen mahaifiyata ne.
“Saboda tafiyar safe zai yi ya kamata ki fada mana abu
nda yake bukata sai saffara masa da wuri kamin ya tashi”
“Wa? Wai Aliyu? Okay bari na tambaye shi”
Duk kallona sukai har Mama dakanta kamar na yi wani sabo ko fadin maganar da ba daidai ba.
Sai Mama da sauran matan sukai murmushi.
“Ina ruwan
Ataa”
Mama ta fada.
“Mu a nan ai ba a fadar sunan miji, miji yana da girma sosai, kuma akwai kunya ka fadi sunan miji kai tsaye, ina ma laifin ki ce masa Hamma”
Cewar Mama Hajjo. Sai a lokacin na gane dalilin kallon nawa da suke, ashe dan na fadi
sunan Aliyu ne kai tsaye.
“Ga ki da sunan Maman su Mai Martaba amman ba ki iya girmama manya ba?”
Na yi kasa da kaina alamar kunya sannan na fice. Lokacin da na dawo dakin ya same shi rike da waya a hannu, ina shigowa ya dago kai yana kallona.
“
Hamma wai ance mi kake so a maka da safe kamin ka tafi?”
Na yi maganar da sigar zolaya ina dariya tare da lake kafada kamar karamar yarinya. Murmushi yai ya miko min hannunsa.
“Zo nan matar Hamma”
Sai na saka dariya na zo gunsa kamar yadda ya buk
ata. Sai ya dora ni kafafuwansa.
“Wace ki ce min Hamma”
“Cewa akai wai ba a fadar sunan miji, shine aka ce ina laifin na kiraka Hamma”
Na fada ina dariya, sai shi ma yai dariya.
“Ke kuma na rika ce miki indo”
“Eh na yarda, fada min abunda
kake so aka dafa maka da safe”
“No bana bukatar komai zan karya idan ya sauka can, akwai kayan tea a nan zan iya hadawa na sha ai”
Haka na koma na fada musu baya bukatar komai, sannan na dawo bangaren mu muka kwanta.
Washe gari.....
Ina gama
sallah asuba na kunna butar ruwan zafi na hada masa tea, ko da ya shigo ina saka masa sugar. Be sha ba sai da ya bani na fara sha sannan ya sha, sai ya tashi ya shiga wanka ya fito ya shirya nima na shiga nai wanka na shirya. Har airport