Showing 33001 words to 36000 words out of 237425 words

Chapter 12 - ZAKI COMPLETE

su Farida na gais

he ta ita da mijinta shi ya amsa da far'a sabanin ita da ko kallon kirki bata min ba, wata kila tana ganin kamar mun takura tane mun zauna mata a gida mun hana ta wali a yadda a gidanta.

Yau ma achaba na hau na fada masa inda zai kai ni, ba aje ni ko'ina

ba sai bakin gate din gidan na mika masa kudinsa na sauka, ina kokarin yin knocked gate din sai na ga an bude shi gaba daya, ashe mai gidan ne zai fita sa na raba gefe sai da ya fice sannan na shiga ina mikawa mai gadin gaisuwa bayan ya amsa min na nufi k

ofar gidan wato kofar babban falon da zai sada ka da cikin gidan gaba daya. Da nai knocked din kofar sai na zauna kusa da kofar dan nasan ba yanzu zata bude min ba, haka nai ta zama

a gurin har mai gidan ya dawo ya faka motarsa inda sauran motocin suke ya

fito fuskarsa da Annuri da haifa ya nufo kofar ya saka keys din hannunsa ya bude.

“Ina kwana?”

Be amsa min ba, sai kallon fuskata yake ta yi wata kila yana mamakin yadda yau ban saka nikab dinba na sake shafa bakin gawayi, ni dai ban kalleshi ba dom

in matarsa ta fada min mijinta baya son kallo. Shi ya fara shiga sannan na bi bayansa na shiga kai tsaye na nufi gurin jiya na dauko tsintsiyar da mopper na fara gyara falon sannan na shiga kitchen na gyara, ban san a wane dakin ta ke kwance bana son na sh

iga ta ce na mata ba dai-dai. Sai kawai na nemi gefen kujera na zauna, ina ta jiran fitowarta shiru har bachi ya dauke ni a gurin ban sani ba. Can cikin bachin nawa na ji an watso min ruwa mai dumi hakan yasa ni farkawa a firgice, ashe ruwan tea da ke hann

unta ta watsa min.

“Ina kwana”

Na mika mata gaisuwa kamar a rikice.

“Ba ki yi bachi a can gidanku ba ne da za ki zo nan kina mana bachi? Ba aiki aka dauke ki ba?”

“Na gyara nan na gyara kitchen ina jiran ki fito sai na gyada dakunan”

“Miye

a fuskarki kuma?”

Na yi shiru ban ce mata komai ba sai kawai ta tabe baki ta zauna a kan kujerar.

“Shiga ki gyara min bedrooms dina”

“To”

Na amsa a ladafce sannan na dauki tsitsiyar na nufi dakunan na gyara na na dawo na dauki mopping na goge

ko'ina na wanke bandakunan sannan na sauko.

“Na kare”

Na fada mata bayan na maida kayan inda na daukosu. A gurin ta bar ni tsaye bata ce na tafi ba, ba ta ce na tsaya ba, har jikinta sauko hannunsa rike da agogon hannu yana kokarin sakawa.

“Kin t

abbatar za ki iya driving da kanki? Idan ba za ki iya ba don't stress yourself zan turo direba ya kai ki”

Shine abunda ya fada mata, ita kuma ta girgiza masa kai.

“Aa zan iya, wannan yarinyar za ta rika min kayan”

A gabana ya kai bakinsa a goshin

ta ya sumbace ta babu ko kunya, shi da kiss ni da jin kunya har na ji kamar kasa ta nutse da ni da kunya. Be yi

minti talatin da fita ba ta hau sama ta bar a gurin a tsaye ina ta jiran saukowarta, sai da tai wanka ta shirya cikin wani lace mai kyau da tsad

a sannan ta sauko idonta sanye da katon bakin gilashi nan na mata.

“Shiga dakina ki dauko min ledodi ki saka mota”

Abun ka da mai jiran umarni sai nai hanzari cira kafa na taka har dakin na dauko na kai gurin motar da ta bude na zuba su a baya, sai

kuma nai tsaye ina jiran abunda za ta ce min. Bayan boot din taje ta dauko wani tawul ta miko min.

“Shimfida wannan a baya sannan ki zauna karki shafa min dattin jikinki a mota”

Na saka hannu na karba cike da jin zafin furucinta, na shimfida kamar y

adda ta fada sannan na zauna ita kuma ta shiga mazaunin direba tai ma motar keys, muka fita ba tare ni na san inda za mu je ba, nawa ido ne kawai ina ta kallon titi har muka isa wata kyakkyawar unguwa mai manyan gidaje, gida hudu muka wuce sannan ta danna

horn mai gadin ya bude mata gate, a inda sauran motocin suke ta faka motarta ta fito sannan tace da ni na fito ya dauko mata ledodin, tana gaba ina bayanta har muka shiga cikin gidan. Alhajin nan mai kangon gidan da ya kore mu na hango zaune kan kujera yan

a dariya an zagaye shi suna ta hayaniya da alama wata wainar ake toyawa.

“Daddy... Happy birthday”

Hajiyar ta fada tana nufar inda yake, ban yi mamakin wulakancinta ba indai har wacan mutumen marar ganin tausayi ne mahaifinta

*Z A K I*

By Khad

eeja Candy

1





3





A gidan ta wuni ita da mahaifinta da sauran yan'uwanta suna ta tayashi murnar birthday kowa na kalla fuskarsa dauke da farinciki,kamar wadanda aka yayewa damuwa har abada. Sai da yamma mahaifinta ya fita ya barsu a cikin gidan su

na ta shagalinsu. Duk iya shagalin da akai da ciye ciye da akai Ataa na waje zaune ita kada kamar yadda Rahma ta umarce da zama waje, sai misalin sha daya na dare ta fito cikin gidan baya ta yi waya da Aliyu ta fada masa ba zata iya driving ba ya zo ya dau

ke ta.

  Ko da ta fito Rahma na kwance a balcony, matsawa tai ya saka fada ta dan musgune ta kadan ita kuma ta farka a girgice sannan sai ta jefa mata dari biyu

“Tashi ki je gidanku”

“To”

Ta fada tare da saka hannun ta dauki kudin ta gyara Hijab

dinta ta kama hanya. A gurin Rahma tai tsaye har Aliyu ya iso da motarsa harabar gidan ya faka. Sannan na soma takawa a hankali ta karaso inda yake, fito yai

daga cikin motar ya bude mata front seat ta shiga ta zauna ya rufe ya koma cikin motar yai nata k

ey ya danna horn aka bude musu gate.

Lokacin daya hau titi ya fara tafiya sai ta kwanto jikinsa, shi kuma ya kai hannunsa yana taba kanta da yake ji da zafi.

“Kina jin rashin lafiya ne?”

“Eh”

“Since when?”

Ya faka motarsa gafen titi ya juyo y

an fuskantar da kyau.

“Dear miyasa kike wasa da lafiyarki ne? Ba ki san lafiyar ki tana da amfani a gurina ba? Tun yaushe kika so ma jin zazzabi”

“Da yamma nan, yanzu ne ya fi min sosai”

Wayarsa ya ciro ya kira Doc Asim bugu biyu ya dauka.

“Do

c same ni gida yanzu, jikin Rahma ya tashi”

Yana fadar hakan ya kashe wayar ya jana motar @360 suka iso gida, ba su yi minti ashirin da isa ba sai ga Doc Asim ya iso, tana zaunen falon kusa da Aliyu ya tambayeta abunda ta ke ji ta fada masa ya bata maga

ni, sannan Aliyu ya rika ta suka shiga bedroom ya kwantar da ita, bakin gadon ya zauna kusa da ita yana ta kallonta kamar mai auna hawa da saukar numfashinta, har bachi yai gaba da ita, sannan na taso ya fito daga dakin shi ma saboda kiran wayar da Mama Fu

lani tai masa ne, saukowa yai kasa yana amsa wayar. Yadda fuskarsa take sake duk kuwa da irin tashin hankalin da ke ransa na ciwon matarsa, amman ka ga murmushi a fuskarsa ka san mai kiran yana da muhimmanci gare shi.

“Aliyu ka yafe kowa ka kyale mu ko

?”

“Na isa Mama? Ai ko zan yafe kowa ban da uwata matukar ina neman albarka”

“To ya gida ya matar ta ka?”

“Gida kalau surukarki kuma tana nan yau jikin ya soma tashi”

“Subhanallahi fatar dai da sauki”

“Da sauki ta samu bachi ma”

“Masha-Al

lah Allah kara lafiya, zan je Dubai gobe, ba lallai idan na je can na kira ka ba, fada min abunda kake son na siyo maka da matarka”

“Ni dai perfume na ke so, ita kuma ki siyo mata duk abunda kika ga ya dace”

“To shikenan, a gaishe ta idan ta tashi”

“Zata ji thank you Mama”

“Allah maka albarka”

Daga haka tai hanging. Shi kuma ya tashi cikin rashin kuzari ya nufi kitchen, tea ya hadawa kansa ya dawo saman kujera ya zauna ya kunna tv for like ten minutes ya tashi ya koma dakin matarsa.

A

TAA POV.

ban taba auna rashin imani da tausayin irin na matar nan sai yau, ta ba a gidan zan kwana ba amman ta kyale ni na zauna a waje bata ba ni abinci ba na wuni da yunwa ta bar ni a haka, yanzu kuma sha dayan dare ta ce na kama hanyar gidan, gashi

ko abun hawa babu, tsoro da fargabar abunda zai same ni, wa zai tare ji a hanya barayi ko masu cin zarafin mata duk be dame ta ba, saboda kawai ina nema a karkashinta, shi kenan dan ina talaka ba ni da gata, ni fa ya ce kamar kowa ba daga sama na fado ba,

amman saboda ba ni da shi ina talaka a yau an sake ni karfe goma sha dayan dare na kama hanyar gida. Ban samu a abun hawa ba, a kafa nai ta takawa ina ta addu'ar Allah ya kai ni gida lafiya. Ko da na isa unguwar babu mutane sosai domin daya saura na dare.

A bakin kofar gidan na tsaya nai buga kofar ba a dade ba aka bude min, babu wuta a lokacin dan haka mahaifin Farida ya haske min fuska da fitila.

“Ataa ke ce cikin daren nan? Ina kike je?”

“Gurin aikin ne, muka fita ba mu dawo ba, sai yanzu”

“Ina

kuka je?”

“Gidan iyayenta”

Sai ya bude min kofar na shigo yana ta kallona kamar be yarda da ni ba, sai da na shigo cikin gidan na hango Nana tsaye rike da bango tana kallona lokacin da na karasa kusa da ita sai na rasa me zan ce mata, na sani dole h

ankalinta ya tashi rashin ganin na dawo, gashi babu mai mata wata hidimar sai ni. Rikata nai muka koma cikin dakin sai da ta fara zama sannan na zauna kusa da ita na fada mata dalilin dadewar da nai ban dawo ba.

“Da wani abun ya same ki a hanya fa?”

“Nana matar nan da na ke yi ma aikin yar mai kangon gidancan ne wanda ya kore mu, ina ganin gaba daya danginsu basa da mutumci ko kadan”

Na fada cikin muryar da ke Nun a gajiye na ke ga kuma yunwa da na ke ji rabon da na saka wani abu a cikina tun karin

safe da na sha koko da kosai. Sama-sama mu kai fira da Nana ta nuna min rashin jindadinta na dadewar da nai a can sannan muka kwanta ni da ita.

   Yau ma kamar jiya na tashi da wuri saboda matar nan ta fada min na rika zuwa tun karfe bakwai na safe, na

san idan na tsaba lokaci wani abu zai iya biyo baya, waina na siyowa Nana ta karya sannan na fito na wanke kwanon da ta ci na maida na janyo ruwan rijiya na yi wanka na saka

doguwar rigata ta atamfata kodaddiya, ban damu da saka dankwali ba, na fita waje n

a daddaka bakin gawayin na shafa a fuskata, na saka Hijab dina na fito na leda dakin Maman su Farida na gaisheta sannan na saki labulen dakin har na kama hanyar fita sai ga Farida ta fito sanye da uniform din makaranta tana cewa na tsaya mata.

“Har kin

shirya zuwa aikin tun da safe haka?”

“Wallahi matar da na ke aiki gidan ta ne bata da mutunci ko kadan, tace na rika zuwa bakwai kin ga idan na tsaba zata iya korata gaba daya”

“Gaskiya kan bata da mutunci, tun da har zata rike ki ki kai karfe daya n

a dare sannan ki dawo, ni wallahi da za ki biye ni da kin yarda maman Salma ta sama miki aiki a Abuja, acan take samawa mutane kuma Wallahi albashi mai tsoka”

“Kai anya Farida zan iya zuwa har Abuja? Kin ga Nana ai bata da wanda zai kula da ita sai ni”

“Amman ai dan neman lafiyarta da abincin ta za ki yi, kuma idan ya wadace ku ya kamata ki dauke ta kuje har garinku ki nemi danginku, zama a nan babu kowa a tare da ku ba zai amfana muku komai ba”

“Nima ina tunanin haka, amman na fi son sai Nana ta s

amu lafiya tukuna”

“Allah ya bata lafiya, nawa ne suka dauke ki aikin?”

“8k ne”

“8k mi zai miki? Ai wannan kudin zai iya karewa a abinci kawai, gaskiya kara ma Abuja nan ance can fa irin manyan gidajen nan har 30k 50k ana bawa mutum, kin ga da kin

hada na wata uku ai ya isashe ki”

“Da gaske Farida”

Na tambaya cike da kwadayin tabbatar da zancen nata.

“Wallahi haka Maman Salma ta ce min”

“Ai ba zuwan ba, kin ga dama ace Lukman yana da rai dazan samu sauki wanda zai kula min da Nana amma

n yanzu bata da kowa ai sai ni, ita kanta ba zata yarda na tafi ba”

“Gaskiya haka ne, amman indai ina nan ni kaina ai zan iya kula da Nana kin sani, ko da ba zan cire mata kewarki ba zan rage mata shi, ko ba zuwa aiki ba ai dole wata rana za ki yi aure

ki tafi ki barta, ko da yaki kin ki bari ma aga fuskar na ki kullum sai boyo kike”

Na yi murmushi ina kallonta a yayinda muka kawo a hanyar da za mu rabu.

“Farida kenan, ni ban taba kawo wa kaina tunanin aure ba, ban taba lissafa kaina a cikin matan

da za a iya aure ba”

“Saboda?”

Ta tambaya cike da mamaki. Sai na sake yin murmushi a karo na biyu na ce.

“Ba ni wannan lokacin da zan tsaya na yi fira da wani namiji ba, kullum tunanina ina abinci zai shigo, yanzu kuma tunani ina kudi za su shigo

na nemawa Nana lafiya, bayan haka maza basa son yarinyar da bata da arziki a gidansu, sun fi son aure yar masu kudi ko mai rufin asibiti, amman irina idan aka ce za amin aure na san daga ni sai tabarma za a kaini, wanda na san hakan zai iya janyo min wula

kanci da kankanci a gurin mijin da yan'uwansa”

Kallon hawayen da suka cika idona ta tsaya yi sai ta rumgume itama idonta cike da kwalla.

“Za ki yi aure kawata, In-Sha-Allah za ki auri mutumen da zai dauki dawainiyarki har da ta Nana ma, na saka ki g

aban mota yai ta yawo da ke a garin nan”

Na sake ta ina yar dariyar zancenta.

“Farida kenan, wa zai yi mace irina haka? Mace da batai boko ba, bata waye ba, bata iya komai ba sai bara da roko a titi? Babu wanda zai so auren makaskanciya”

“Ataa ka

rki yanke kauna daga rahamar Allah, dan jarrabe ki a haka ba shi yake nufin ba za ki samu jindadi a gaba ba”

“Na sani, kawai ina duba yanayin rayuwar ne, duniyar ta canja ba kamar da ba ne, ke dai ki tafi makaranta kar ki yi latti”

Daga haka muka rab

u ita ta wuce makaranta ni kuma na kama hanyar zuwa gurin aikina, ina ta kwadayin zuwa makaranta amman ba hali, lallai karatu da samun wanda zai tsaya maka ka yi karatun gata ne.

Ina tafe ina ta sake sake na har na isa, yau kan ni kaina na san na yi ran

a zuwa domin a kafa na zo kamar yadda a jiya din ma na dawo a kafa duk kuwa da irin tazarar da ke tsakanin unguwar mu da ta su. Sai da nai knocked gate din sau biyu sannan aka saka bude min gate din na gaishe shi kamar yadda na yi jiya sannan doshi cikin g

idan, na yi mamakin tararda kofar falon abude wata kila wani dalilin ne ya saka suka bude kofar. Ni dai na shiga da sallamata duk da nasan ba za a amsa min ba, haka kuwa akai domin mai gidan nan na hakince saman cushion amman be amsa min ba duk da idonsa n

a kaina har na karasa tsakiyar falon na gaishe shi nan ma be ce min komai ba. Ban damuwa ba, domin a tsakanin jiya da shekaranjiya kawai na fara sabawa da halinsa da dabi'unsa, matarsa ta fda min baya son yawan kallo, sai dai na lura shi din yana da kure m

utum da ido har ka soma tsarguwa sai kuma ace wai kai ba zaka kalleshi ba, lallai masu kudin nan akwai su da rashin adalci da takura rayuwa. Abu na biyu na lura baya son yawan magana kuma yana da kyama sosai fiye da matarsa, ga kamshi a duk inda ya wulga k

o ya zauna, kamshin turarensa ne ke yiwa mutum sallama tun gabanin shi yai maka, akwai kwarjini sosai idan kana kallonsa, haibarsa tana fitarta da siffar zatinsa da ainahin kyauwunsa, ban taba ganin murmushinsa ba, a tunani murmushi kamar ba zai yi ma fusk

arsa kyau ba, duk kuwa da kasancewar yana cikin sunnar Manzo na, sai dai nana jin

wannan miskilin ya ta6a ďa66aka sunnarsa ta murmushi balle kuma har ta kai shi ga yin dariya.

Gurin da na dauki tsitsiya jiya na nufa na dauka tare da mopper na nufi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login