Showing 39001 words to 42000 words out of 237425 words

Chapter 14 - ZAKI COMPLETE

mahaifiyarsa take, yadda yake takawa sai ka rantse da Allah takun kasaita ne da nuna isa, alhalin haka tafiyarsa take, kamshin tu

rarensa na ta sanarda zuwansa tun kan ya karaso kusa da ita. Zai da ya rage sauran taku shida zuwa bakwai tsakaninsa da ita sannan ya dabbaka sunnar nan ta murmushi wacce ta kara mishi kyau da haifa.

“Na ga Daddy ya fita yanzu har mun gaisa da shi ma”

“Eh yana ta sauri za su je meeting”

Haka suka jero ita da danta suka shigo cikin falon suna wannan hirar. Saman cushion ta zauna tana nuna masa dinning.

“Ga ragowar breakfast can idan zaka ci kanenka suka raga”

Ya dan yamutsa fuska yana murmush

i dan yasan zolayarsa kawai Momy take.

“Momy kin san ai bana cin ragowar kowa ni, ina Sisters”

“Duka suna school”

Ajiyar zuciya ya sauke wanda yasa Momy sake dubansa.

“Wani abun ne?”

Ya jimm na wani lokacin sannan sannan ya kalleta a natse

ya ce.

“Momy kin san kwana ki ina ta neman mai aiki ko? Sai ga wata yarinya ta zo gidan neman aiki.... ”

Tun daga lokacin da Ataa ta zo gidan ya jera mata labarin har ya isa zangon da ya fi rikitar da shi. Da mugun mamaki Momy ta kalli.

“Kuma b

a ka ji komai a ranka ba Dan wajen Fulani? Ba zuciya da jini ne a kirjinka ba? A zalinci wata ta dalilinku har ka tsaya neman hujja?”

“Amman ni ban ce a zalince ta ba?”

“Miyasa da aka kawo maka kodar baka bincika daga inda ta fito ba? Akan me zaka zu

ba kudi mai yawa ka ce a samo maka kodar? Ba kayi tunanin ganin kudin zai iya saka Doc Asim aikata komai dan ya samu kudin ba? Ai da tun farko ka samu mai kodar ka yi magana da ita da bakinka, yanzu ga shi ka raya matarta kana cikin farinciki, ita kuma ka

jefata a damuwa da bakinciki? Ka ji tsoron addu'ar wanda aka zakinta, kuma ka ji tsoron Allah ya isa, domin idan bata bi jikinka ba, tana bin dukiya da kaddara”

Lumashe ido yai ya bude yana fusar iskar bakina a hankali.

“Ka tuna lokacin da aka ce mak

a Rahma zata iya rasa ranta idan ba mata wano dashen kodar ba? Ka tuna? Ka auna ka ji ya yarinyar nan ta ke ji? Ita da mahaifiyarta ce, kamar ni ce ko Fulani aka cirewa koda ba tare da saninka ba? Idan ka gano me zaka yi?”

“Zan yi duk abunda zan yi na k

wato muku hakkinku”

“To sai aka samu akasi ita yar talakawa ce, bata da wannan ikon bata da wannan gatan, mahaifiyar tana raye ko ta mutu babu wanda ya sani, wane hali suka shiga bayan wannan babu wanda ya sani, ina jiye maku tsoron abunda ta zai biyo b

aya, amman gaskiya an zalinci yarinyar nan”

“Momy kin san inna sani ba zan zalince ta ba, na yarda bana kula kowa amman bana zalintar kowa?”

“Ka bude zuciyarka kai tunani... Na san kana son matar ka kuma zaka iya komai akan samun lafiyarta, amman ina

son na fada maka wani abu, ka ji tsoron addu'ar wanda aka zalinta, kuma ka ji tsoro mutumen da zai ce ya barwa Allah Allah shine zai isar masa, hakan yana nufin babu komai tsakanin shi da kai Allah ne zai wakilce shi ya fidda masa hakkinsa akanka.....”

Kallon Momy yai zuciyarsa cike da tsoro da be taba jin irinsa ba, jikinsa yai mugun sanyi, tsoron abunda zai biyo baya kamar yadda Momy ta ce yasa zuciyarsa rauni...

_____________________

Page daya ya rage mana mu gama free pages In-Sha-Allah. if

you want to subscribe pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt Bank. sai ku turo shaidar biyan wato screenshot ta wannan number 08036126660, ko kuma katin mtn na 300 ga marasa account ta wannan number 08036126660. yan nijar za ku tura 500fc na line Orange

ko Airtel ta number nan +22790165991 sai ku min magana ta wannan number 08036126660 Za'a saka ku Group.

Thanks

🙏🏻

Ku ziyarci YouTube channel dina, ku danna min subscribe kuma kui sharing.

👉

https://www.youtube.com/channel/UCpAkml0pIh6MUnzt9nLh_qQ



*Z A K I*

By Khadeeja Candy

1





5





Ya dade a gidan Momy zaune gaba daya jikinsa ya gama yin sanyi, yana ta jin kamar akwai laifinsa a cire mata kodar da akai, and if da laifinsa ya akai laifinsa ya shiga ciki bayan shi idan ma ba yanz

u ba be tana ganin yarinyar ba, idan yai duba ta wani bangaren yana ganin cewar ba shi da laifin komai, shi dai kawai matarsa yake nemawa lafiya and shi be ce a cire da karfi ba. A masallaci yai sallah magariba sannan na ya dawo cikin gidan, jikin ba kwari

kusan sai ya rantse shi be taba jin jikinsa a wannan yanayin, wata kila saboda ba a taba cutar wani a gabansa ba, ko kuma shi din be taba cutar wani da dukiyarsa ko da ikonsa ko karfinsa ba, sai wannan karon, duk kuwa da kasancewar wani bangare na zuciyar

sa na fada masa cewar ba shi da laifi.

Yana shigowa falon Sisters dinsa sika make kyam kamar babu wani abu mai numfashi a falon, ko wacce ta shiga natsuwarta, tsayawa yai kallonsu kamar yadda ya saba idan ya shigo cikin gidan domin lura da yanayinsa da k

uma halin da ko wace daga cikin kannen nasa guda hudu suke cikin.

“Ina Umar?”

Ya tambaya da irin fuskarka nan ta ba wasa.

“Be dawo ba”

Duka su hudu suka hada baki gurin bashi amsa dan sun sani sarai baya son kyaluwa, Momy zata iya tambayarsu

abu su tsaya tunani ko wani sha'anin kamin su ba da amsa amman ban da Aliyu baya daukar wannan shashancin a time din da ya tambaye ka time din zaka ba shi amsa, idan kuma kai kuskure wani abun ya fito daga bakinka kuma kai ne a matsala. Juyawa yai ya shig

a dakin Momy sai ya same ta zaune saman carpet tana jan carbi. Guri ya samu kusa da ita a kasan ya zauna yana fiddo wayarsa.

“Dan waje bata Fulani ina ta tunani anya likitan nan Asim zai kyale ta kuwa?”

Dagowa idonsa daga jikinkin screen din wayar ya

i ya kalleta.

“Ban gane ba?”

“Ina tunanin kamar ta jefa kanta a matsala ne, baka tunanin zai iya yi mata wani abun da nan gaba ba zata sake shaidarsa ba? Babban likita mai asibitin kansa kamar Asim ba zai dauki wannan matsalar ba, ba zai yarda ta ka

rya masa aiki ba”

Aliyu yai shiru yana nazari.

“Wannan abu be min dadi ba sam Wallahi, saboda ban jidadi abunda ya faru da yarinyar nan ba, duk kuwa da ban santa ba, amman na san irin zafin da ake akwai ace an cuce ba gashi baka da hali jan hakkinka



Mikewa yai tsaye yana fitarsa numfashi a hankali ya ce.

“Momy zan tafi gida, na san yanzu Rahma ta farka”

“To ka gaisheta”

“Za ta ji”

Ya juyo yana tafiyarsa kamar yadda ya saba har ya sauko kasa, ya nufi gurin motarsa yana shiga yai mata

key ya dauki hanyar gidansa. Yana tafe yana tunanin abunda ya faru da kuma maganar Momy, he find himself in middle of tausayin Ataa da yarda cewa an zalince, every words of her yake tunawa da yadda take furta su, idan har ba zalince ta ba, ba zata iya daga

hannunta ta mari babban mutun kamar Doc Asim ba, yadda ya lura da rashin tsoron da ke cikin idonta a lokacin da idanuwansa suke yawo a fuskarsa, ya tabbatar ko kashe Doc Asim zata iya yi a gaban kowa, and Momy was right ba lallai ne Doc Asim iya kyaleta b

a.

‘Allah ya isa’

Haka maganarta ke ta dawo masa sabowa a kunne, ga wa zai isar mata, ga Doc Asim ko ga shi ko kuwa ga su dukansu? Haka yai ta saka tunani kala

kala har ya isa gida, yai mamakin ganin Motar surikinsa a wannan lokacin, the first thing

that come his mind is ko ciwon Rahma ya tashi ne, amman kuma idan ciwon ta ne ya tashi ai shi zata kira ba Daddynta ba. A bude ya samu kofar falon tun ka ya shiga yake jiyo muryar Alhaji Nasiru Gobir. Da sallama Aliyu ya shiga, surukinsa da wani yayan Rah

ma suka amsa masa, Rahma kan ko inda yake bata kalla ba.

Gurin ya samu kusa da ita ya zauna yana kallon Alhaji Nasiru Gobir wanda fuskarsa ke dauke da damuwa.

“Rahma ta fada min abunda ya faru, daman ta fadawa mahaifiyarta tun a waya, wannan wace irin

yar iskar yarinya ce marar tarbiya haka?”

Aliyu ya juyo gefensa ya kalli Rahma sai kuma ya sake kallon mahaifinta ya ce.

“Ba ta fada maka abunda akai wa yarinyar ba?”

“Ko ma mi akai mata ai ba mu muka ce ta siyar da kodarta ba, irin talakawan na

n da kake gani Aliyu ba su da komai a ransu sai hassadar nai arziki, idan suka ganka da arziki ji suke kamar su kashe ka su kwashe dukiyar, shiyasa tsakaninmu da talaka aiki kawai mu biyashi, wata banza a banza bata isa ta shigo har cikin gidanki ta fada m

iki maganar banza ba, watan ma kuma talaka!”

“Daddy har da kai ta ciwa mutunci, wai a gidanka ta raba ka koreta ni da kai duk ba musan darajar talaka ba”

“Zan sa a binciko yarinyar da iyayenta sai na nuna mata ruwa ba sa'an kwando ba ne”

Duk abund

a ake Aliyu ba ce uffan ba, har Daddy yai musu sallama ya fita, a lokacin ne Rahma ta tashi ta nufi dakinta, shi kan sai da yaji tashin motar surukinsa sannan shima ya mike tsaye ya bi bayan Rahma. Gaban madubi ya same ta zaune tana cire dankunnen da ke ku

nnenta, kusa da ita yaje yai mata kissing sannan ya zauna gefen gadon yana kallonta.

“Miyasa za ki kira Daddy ki fada masa maganar da bata kai ta kawo ba?”

Da mamaki ta kalleshi

“Wannan abun ne be kai ya kawo ba? Yarinya karamar yar talakawa kama

r wannan ta fada min magana son ranta ka ce be kai ya kawo ba? Aliyu ka san me kake fadi kuwa?”

“Amman ai zalintar ta akai? Yanzu kuma sai ki fadawa Daddy bayan kin san zai iya daukar wani mataki?”

“Amman mu muka zalince ta? Daman can matakin na ke s

on ya dauka shiyasa na kira shi na fada masa, tun da kai ka kasa komai sai ma rike min hannu da kai dan kar na dake ta”

“Sanadinmu aka zalince ta, kodar mahaifiyarta aka cire Rahma aka dasa miki? Kuma kike tunanin ba zatai wani hargagi na huce haushinta

ba?”

Juyo tai gaba daya ta kalleshi da kyau.

“Kana magana Aliyu kamar ba kai ba? Lafazin da ke fitowa daga bakinta yana karantar da ni cewar ba kai ne ba?”

Hannu ya kai ya kama hanyayenta ya cigaba da mata magana a hankali kamar yadda yake mata

dazun.

“Dear, zan iya juye yi wa mutum komai amman ban da zalinci, an riga an cuci yarinyar nan, kuma kodar nan an dasa miki ita wannan kadai ya isa yasa jin tausayinta waya sani ma ko mahaifiyar ta mutu”

“Tausayi Aliyu? Tausayi? Tausayi fa ka ce? M

i mukai mata da har za mu ji tausayinta? Mu muka zalince ta ne? Akan mi zaka yarda da yarinyar daka soma gani cikin kwana biyu, saman da likitan daya saba yi maka aiki shekara da shekaru? Ban taba ganinka cikin wannan yanayin ba Aliyu, ba ka taba ce min na

ji tausayin wani ba, baka taba ce min kana tausayin wani ba, wanin ma talaka irin wannan yar shekara a gidanka”

“Ba tausayinta nake ji ba, ina kallon abunda akai mata ne a matsayin zalinci, and be dace ki saka Daddy a wannan maganar ba, zai iya unkura

yi mata wani abu sanadinki, ni fa na yarda da wulakanta kowa na ci mutunci kowa kuma na kyama ci kowa amman ban yarda karfin iko ko dukiya su saka na zalinci wani ba, ba zan iya da hakkin wani a kaina ba”

Kai ta girgiza masa tana murmushi irin mai ciwon

nan idonta na cika da hawaye.

“Ban taba yin wani abu ka ce ban yi daidai ba sai yau, ban taba daga hannu da sunan dukan wani ba ka hana ni sai yau, wani be taba fada min mummunar magana a gabanka ka kyaleshi ba sai yau, na fahimcin inda ka dosa Aliyu,

ta wanke fuskarta kaga tana da kyau tana da fari tana da gashi na fahimta...”

Mikewa tai tsaye zata fice daga dakin tana share hawayen da suka zubo mata, sai yai saurin rumgumeta ta bayan ya dora kansa saman wuyanta.

“Ba kyau ba ne matsalar, ina au

na irin halin da na samu kaina ne a lokacin da aka fada min cewar za ki iya rasa ranki idan ba a canja miki koda ba, na ji tsoro sosai Rahma, kullum fargabata kar na rasa ki, na shiga damiwa sosai wanda hakan yasa na fadawa Doc Asim ya samu ko koda ta nawa

ce zan siya, amman ban san cewa zalintar wata zai yi ya kawo min ba, ni kenan da nake tsoron rasa mata ina ga ita da take tsoro rasa mahaifiya tana da daraja ga yayanta Rahma ko da kuwa talaka ce”

“Babu ruwanmu da rayuwar wasu, abunda muke so shi muka

samu, whither ya zalince ko mu muka zalince ba matsala ba ce, tun da mun samu abunda mu ke bukata, Aliyu bana son na sake jin maganar yarinyar pls”

Juyowa yai da ita ta yadda zata fuskance shi irin fuskartar da zata famince ko wace kalma da zata fito da

ga bakinshi.

“No ba haka ya dace ba, idan har ba mu bata hakurin zalincin da akai mata ba, be kamata ba, be kamata mu kara mata da wani abun ba, Daddy zai iya yi mata wani abu, and maybe Doc Asim ma ba zai kyaleta ba”

Kallonsa take tana ta kokarin f

ahimtarsa amman sai ta kasa, zuciyarta nata raya mata cewar Aliyu ya fara son yarinyar nan ne, hawaye ne suka shiga nata zirya ta fasa cewa komai, ganin hakan yasa shi saka bakinsa cikin nata ya tsotse bakinta tas sannan ya matso da ita baya suka zauna bak

in gado ya rumgume ta.

ATAA POV.

Tunda aka tsayar da maganar zuwa aikina Abuja na fara koyon wanka akai akai kamar yadda Maman Salma ta fda min cewar Abuja ba a kazanta, baa gulma ba a wasa duk abunda ya kai mutum shi yake yi, wani lokaci a rana

sai nai wanka biyu ma, wankin baki kuwa ba a magana, akai akai na ke saka gawayi ina wanke bakina gudun kar na je ace yana wari, yadda na ke ta jin labarin Abuja a gurin Maman Salma sai ji duk na gagara na je kamar wacce zata je wani guri gurin jindadi ba

aikatau ba.

Sai duk wannan zumudin da murnar da nake idan tuna cewar zan tafi na bar Nana sai hankalina ya tashi na ji babu dadi, duk kuwa da nasan cewar ina bukatar aikin, kuma idan har na daure nai na san zan samu kudi kuma, kudin za su mana amfani s

osai. Sai kullum Nana cikin nuna bata son tafiyata take, tana ta ganin kamar idan nai nisa da ita zan dawo na tarar ta rasu ne.

Ana saura kwana biyu mu tafi Abuja kamar yadda Maman Salma ta fada mana, na shirya ni da Farida na raka ta bayan unguwarmu g

urin kitso, ba mu dawo da wuri ba, kasancewar mun tararda mutun hudu suna jiran kitson, ga shi idan muka hadu da Islam mai kitso abun ba dama gurin fira da dariya, muna hanya ana kiran sallah la'asar muna tafe muna fira har muka iso gidan sai dai yadda na

tararda gidan wan wulgar mana da kayan dakin Nana ya sa ka gabana faduwa, a tunanina ko mahaifiyar Farida ce tai mana haka domin bata son zaman mu a idan, yana daya daga cikin abun ya saka na ke son na samo kudi ko dan mu tashi mu bar mata gidan.

“Muna

zamanmu Malam zai janyo mana masifa, ai bari ya dawo sai ya san matakin da zai dauka tun wuri dan ni ba zan yarda da zaman mutanen nan a cikin gidan nan ba, wannan iskanci har ina?”

Irin kalaman zagi da na ji suna fitowa daga bakinta ya saka na fahimci

ba daga ita har ba ne. Da sauri na nufi dakin da Nana take ciki sai na sameta ta zaune tana kuka.

“Lafiya Nana miya faru?”

“Wasu mutane ne suka shigo cikin gidan nan suna nemanki, aka nuna musu ni saka ce na fada miki karki sake zuwa ki fadawa Rahma

wata magana marar dadi, idan kika sake sai sun wulakanta ki, wacece Rahma kuma?”

Ta karasa tana tambaya ta.

“Matar da ta koreni aiki ce”

“Fada kuka yi?”

“Kawai dai mu samu dan sabani ne, ta ce talaka ni kuma na fada mata bakar magana”

“Ataa

dan Allah ki kama kanki, kin ga dai ke ba yar kowa ba ce, kar ki janyo mana wata matsalar muna neman abunda za mu ci”

“In-Sha-Allah ba zan sake ba, wacan din ma kuskure aka samu”

“Ina son ki min alkawari idan kin je Abujar nan, duk abunda za a miki

za ki yi hakuri ki hade, ba za ki saka shi a ranki ba”

“Na miki alkwari Nana”

Na fada ina sakar mata murmushi. Sannan na tashi naje na waje na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login