Showing 219001 words to 222000 words out of 237425 words
ta cikin kabarinta, wa zai iya fadar yadda cikin kabari yake? Babu iyakar abunda ido ya gani ko ya ji a duniya ne kawai, the first thing da aka saka bayan gawar Rahma itace sannan aka saka
tukane sai haki da ciyayi ya biyo baya, haka aka lullube kabarinta da kasa sai aka tabbatar babu wata kusurwa da wani abun zai iya shiga sannan aka kewaye kabarin ana mata addu'ar neman Rahma. Sannan aka taso aka baro ta can ita kadai daga ita sai aikinta
. Gida aka kawo ana karbar gaisuwar, Momy kuma ta bukaci Aliyu ya koma gida su a can su yi na su karbar gaisuwar. Har lokacin Mama Fulani da Nasir ba su iso ba saboda mota suka biyo ba su samu jirgin da zai taso yau.
Aliyu na kusan shiga motarsa Ikram
ta zo ta miko masa wata wasika, idonta yayi ja sosai.
“Minene?”
“Ita ta rubuta ta, a lokacin da ka kirata bata iya magana ta miko min, na tambayeta ta waye tai min alamu da kai zan bawa”
Kallon takadar Aliyu ya rika yi na few minutes kamin ya kai
hannu ya karba jikinsa na ta rawa. Sannan ya nufi motar ya shiga, Muhseen ne ke tukawa har suka isa gida sai taba takardar yake ya kasa budewa. A can gurin Momy ma an cika da mutane yan'uwan Daddyn da Momy, har Daddyn da kansa da wasu abokansa da suke kusa
da kusa suna tare, har da yan'uwan Mama Fulani da suke yola wadanda suka zo ta jirgi. duk wanda ke gurin tausayin Aliyu yake, sai da magariba Mama Fulani ta iso ita da su Maryam da Ammy gaba daya gidan aka kwashe ba a baro kowa ba.
After Sallah isha'i
Aliyu ya shiga bangarensa da ke cikin gidan ya kulle kansa a cikin dakin ya bude takardar cike da fargaba ya fara karantawa.
_Zaka karanta wasikar nan ne wata kila, bayan ba raina domin na san ba sakan cewa ina asibiti ba, da farko zan fara taya ka mur
nar samun haihuwa da kai, kuma nai maka godiya na rufa min asiri da kai da hakurin zama da ni na tsawon lokaci, ina jin a jiki kamar ba zan rayu ba wani lokaci ba, amman ina rokon yafiyarka kuma ka nema min yafiyar Ataa da yafiyar Momy da duk wani wanda ka
san na taba alaka da shi, ka nuna min soyayyar gaskiya Aliyu ta hanyar yi min addu'a bayan raina, Allah ya hada fuskokin mu a aljanna. I love you so much ina maka fatar alheri a sabuwar rayuwar da ka fara da Ataa, na san ka nuna min so, amman ni yanzu taw
a ta kare, ka yafe min Aliyu kuma ka yafe wa mahaifiyata so na ne ya saka ta aikata maka komai, ka yi hakuri na san kana so na amman babu wanda ya iya kaucewa mutuwa, tarin dukiya ko lafiya bata amfani mai ita ba matukar mutuwa ta kusance shi, ka yafe min
Aliyu_
Fuskarsa shakaf da hawaye ya gama karanta wasikar. Kansa kamar zai bare idonsa ya kumburo kamar ba na shi ba.
“Na yafe miki Rahma na yafe miki, Allah ma ya yafe miki”
Ya furta sannan ya mike tsaye ya shiga bandaki ya wanke fuskarsa ya fito
harabar ya memi Abbah, can gefe ya koma da shi ya karbi number Mai Martaba saboda yana son kiran Ataa ya nema ma Rahma yafiyarta. Dakinsa ya dawo sai da ya fara gaisawa da Mai Martaba sannan ya gabatar masa da bukatarsa, sannan ya kashe wayar bayan Mai ma
rtaba ya tabbatar masa da za a fada mata, after like thirty minutes aka kira shi da line orange na can nijar wata bakuwar number wacce ba ta Mai Martaba ba.
Yana yin picking ya ji muryar Ataa kasa kasa kamar marar lafiya, sai da suka gaisa ya tambaye
ta ko bata jindadi ne ta fada mishi lafiyarta kalau.
“Ya jikin Rahma?”
“Babyna jiki da sauki sosai ta ce a fada miki tana gaishe ki kuma na nema mata lafiyarki, tsabanin da kuka samu a baya”
Aliyu yayi kokari wajen ganin yayi magana da ita normal
ba tare da muryarsa ta canja kuma ba tare da nuna akwai damuwa a tare da shi ba, sai dai kana jin muryar kasan baya cikin walwala. A maimakon Ataa ta tace ta yafe mata sai kawai ta fashe da wani kuka da cikin wayar har Aliyu ya kasa saurare ya kara wayar
a kirjinsa yana hawaye.
Mutuwa....!
💔
Allah kai mana kyakkyawan karshe, Allah ka jikan Babana da Rahma
😭😭😭😭💔
*AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke
hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.
Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutuk
ka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanc
iya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number
+60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.*
Kuka na ke sosai jikina na raya min cewar Rahma ta rasu daman tun a lokacin da ya tafi na ke jin ba dadi, yanayin yadda na ji muryarsa ma na san ba lafiya ba, domin alamu ya n
una ba ya cikin walwala duk dai ban san ainahin abunda yake damunsa ba, sai dai jin cewar Rahma na neman yafiyata na san mutuwa ce kadai zata saka ta neman yafiyata, idan kuma ba haka ba, wata kila kuma Aliyun ne ya nema mata da kansa saboda ta mutu.
“
Babyna kukan ya isa haka”
“Hamma ba a boyon mutuwa, idan ma ta mutu da gaske ba zan iya dawowa da ita ba, kuka ba ya dawo da wanda aka rasa, da yana dawowa da ya dawo min da Babana da Lukman, amman duka na rasa su kuma kuka da bakinciki be dawo da su ba
, zan yi kuka saboda tausayinta ne da kuma kai”
“Bana son kukan ko tunanin ya janyo miki wata matsala, ke kadai kika rage min a yanzu sai abunda yake cikinki, idan na kara wani rashi ban san ya zan yi ba, rashi akwai ciwo sosai gashi ba zaka iya dawowa
da wanda ka rasa din ba, akwai ciwo sosai ka rasa wani abun da kake so a lokacin da kake tsananin bukatarsa, akwai ciwo rabuwa da abokin rayuwa da ka shirya yin rayuwa da shi”
Hannu na kai na share hawayen fuskata, na san yadda Hamma yake ji saboda be t
aba rasa kowa ba a rayuwarsa sai yau, mahaifiyarsa mahaifinsa duka suna raye, wani karin gatan ma sai Allah ya kara masa da Mama Fulani da Abbah duk shi kadai, ni ko na san zafin rashi saboda na rasa mahaifina da dan'uwana kuma na san zafin babu saboda ana
tashi a cikin babu din, shi ko be san babu ba sai akwai kuma be san zafin rasa komai ba a rayuwarsa sai yanzu.
“Fada min kina nan lafiya kalau”
“Lafiyata kalau, kuma na yafe mata abunda tai min wanda na sani da wanda ban sani ba, Allah ya jikanta y
ai mata Rahma”
“Amin na gode, cikinji fa yana lafiya?”
“Komai lafiya kalau, zan fadawa Mama yanzu”
“Okay ki kula min da kanki pls”
Na gyada kai kamar yana gabana sannan na aje wayar akan gadon na zauna bakin gadon ina ta kuka, ban taba tsammani
n jin labarin mutuwar Rahma zai sakani shiga damuwa ba balle har nai kuka, amman sai ga ni ina kuka kamar wacce na rayu da ita na tsawon lokaci na shaku da ita, a yau duk wata kiyayya da kishi da jin haushi ta kare, mai rabawa ta raba. Kaico mai rai ba aba
kin komai yake ba, lokaci daya idan Allah ya so kama ka sai ka raina kanka har makiyinka ya tausaya maka. Sai da na ci kuka na koshi sannan na fito falon Hajiya wato kakana idona a kumbure da kuma sauran hawaye na nufi inda Hajiyar take zaune na mika mata
wayarta wacce ta ara min na kira Hamma da ita.
“Lafiya kike ko?”
“Rahma ce ta rasu”
“Wace Rahma?”
“Matar Hamma”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”
Shine abunda ya fito daga bakin Mama tana dafe da kirji, na san ta ji mutuwar kamar yadda
na ji, abun kamar daga sama kuma babu dadi ko kadan. A nan suka shiga tambayar wacece ita, Mama ce ta fada musu ni kan sai wani sabon kukan ya kubuce min, har ga Allah ban jidadin mutuwarta ba, dan tsabanin da muka taba samu da ita sai ya dawo min sabo in
a ta ganinta a fuskata. A cikin dare aka fadawa Mai Martaba halin da ake ciki na mutuwar Rahma, a waya ya kira Daddyn Rahma yai masa gaisuwa da kuma Abbah da sai aka sadashi da Daddyn Hamma shi ma yai masa gaisuwa sannan yai ma Hamma din, mu kuma aka ce mu
shirya domin zuwa gaisuwa, a daren ban yi banchin kirki ba saboda tunanin Rahma ina ta ganin kamar ba da gaske ne ba, sosai na ji mutuwarta kamar wani ginshike nawa na rasa, har na soma jin ciwon kai na kama ni, da safe sai ga ni da mura, tun da nai salla
h ban koma ba bachin ba, saboda tunani ashe Allah be yi zamu zauna a guri daya ba, balle ma na ga kishinta domin ni dai bana jin ina da kishin ma amman na san nata na musamman ne a yanayinta da yadda na karanci halinta.
Ko da goma tai dukan mu muna air
port, wani abu sai kudi, babu zancen siya mana tickets na zuwa Nigeria, da jirgin Mai Martaba muka tafi, ni, Mama sai kuma wasu cousins dinta mata biyu, maza biyu wadanda Mai Martaba ya turo su walkice shi su yi masa gaisuwar.
Mun sauka sokoto cikin loka
ci wani abun burgewa muna sauka motocin da za su dauke mu suka iso, a wani gidan suka so su kai mu mu huta kamin muje gaisuwar sai Mama da kanta ta ce a sauke gidan Momy su kuma Mazan sai su tafi can din su huta, haka kuwa akai ni da ita da wasu yayyunta m
ata aka sauke mu gurin Momy su kuma mazan aka wuce da su. Mun tarardar gidan da taro sai dai ba taro irin nan farinciki da walwala ba, domin kana kallon fuskarta duk wanda ke gurin kasan ba taron jindadi ne ya tara su ba. A cikin gidan kuma mata yan karbar
gaisuwa, ganin taron ya karya min guiwa na san nima wata rana haka za'ayi nawa, ayi na kowa.
Husna da Siyam su kai mana lale marhabun duk da kasancewar suma basa cikin walwala sosai sai dai sun yi murna da ganina suna ta dauki ba kuma murna na marmari
na kawai ba har da murnar cikin da na ke da shi. Mama Fulani kan ba wani sakewa sumi sumi da ita kamar ta Allah, Ammy da duka yaranta suna nan, har ma da su Maryam da Rukaiya duka suna nan.
Kar ka so ganin yadda Momy taks ta kokarin dawainiya da ni, sai
kace wata mai tsoron ciki ko kuma wacce bata iya komai, abinci ma idan za a kawo min sai an tambayi wanne na ke so gudun kar a kawo min mai saka ni tashin zuciya. A ranar kawunai na da Mama suka koma da kuma cousins din da suka rako Mama, bayan sun yi gai
suwar a can bangarensu Iyayen Rahma, ban za ci Mama zata iya zuwa tai gaisuwar rasuwar Rahma ba, sai gashi ta maida komai ba komai ba, kana kallon mahaifiyarta zaka san a firgice take, irin figirtar nan na rasa wanda kake so a lokacin da ba kai tsammani ba
, mahaifinta kan ya sha jinin jikinsa kamar ba shi ba, sai kallona suke ta yi daga shi har Mommyn Rahma.
Bayan mun dawo daga gaisuwar ne su suka kama hanya, ni kuma aka bar ni nan a gurin Momy wai sai an gama karbar gaisuwa. Ina zaune saman carpet ni ka
dai a dakin ina salatin Annabina na ji shigowar mutum, ban waiga ba amman na san ko wanene tun daga kan kamshin turarensa, ta kuma yadda yake takowa zuwa inda na ke a hankali har ya iso. Ji nai an rumgume ni ta baya, sai na sauke ajiyar zuciya a hankali ni
kaina na san na yi marmarin Hamma sosai tun a lokacin da na zo garin nan idona suke kai kayin ganinsa, amman ban saka shi a idona ba ko gaisuwar da su Mama da yan'uwanta suka masa ina kyautata zaton sai indai a can gidansa suka same shi ko kuma ya shigo n
i ban ganshi ba ya fita domin tun shigowata gidan ban ji ko alamun motsinsa ba sai yanzu. Gafen kumatuna ya sumbata.
“Fada min kina nan lafiya?”
“Lafiya kalau, tun dazun muka zo amman ban ganka ba”
“Ina ta kokarin boye kaina dan kar na yi arba da
ke har sai idan ke kadai ce, saboda ina mararin na rumgume ki na jiki a jikina kuma ba zan iya haka abun a agaban mutane ba”
Ya fada ba tare da ya sake ni daga rumgumar da yai min ba.
“Mama ta tafi”
“Na sani na gode da ta bar min ke”
Mun dauki
lokaci a haka yana rumgume da ni ta baya, sannan ya sake ni ya mike tsaye ya zauna bakin gadon Momy, juyowa nai na kalleshi sai wani irin kaunarsa da tausayinsa suka dirar min a zuciya lokaci daya, ya rame sosai kamar ba shi na har idonsa sun fada kamar m
arar lafiya.
“Hamma baka cin abinci?”
Kallona kawai yake ba tare da yace komai ba.
“Bari na saka Husna ko wata ta hada maka wani abu ko kuma idan akwai fura ka sha idan baka son abu mai nauyi”
Ina mikewa tsaye sai ya riko hannuna ya dawo da n
i kusa da shi ya zaunar ya ja ni zuwa kirjinsa ya rungume ya lumshe ido, ina jin yadda zuciyarsa take bugawa da sauri.
“Na gode Allah da be dauke min Rahma ba sai da ya ba ni ke, kuma yai min tukuici da wani dan ko ya, ni kada na san halin da na ke ciki
kuma ni kadai na san iya abunda na ke ji a zuciyata”
Ya fada yana kara matseni a kirjinsa, rashi akwai ciwo sosai na san irin yadda Hamma yake ji a yanzu saboda ni ma na taba rasawa ba ma sau daya ba. Sai da ya ji kamar muryar wata a kusa da kofar daki
n sannan yai saurin sakina ni kuma na mike tsaye cikin tsoron kar wacce ke maganar ta shigo ta gan mu a tare. Wata kanwar Momy ce ta shigo dakin da sallama ni na amsa mata sai ta miko min kofin fura.
“Ga shi inji Yaya ta ce ki sha”
“Na gode”
Na fa
da bayan na saka hannu biyu na karba, sannan ta juya ta fice. Zaunawa nai kusa da Hamma na mika masa furar wacce aka damata da kirdirmon nono.
“Ka sha”
Ba min musu ba, ya karba ya sha sai dai ba da yawa ba, ya mikon min sauran.
“Shanye”
Na sh
a rabin kofin sai na aje ina ta kallonsa, gaba daya ya koma kamar ba shi ba, so silent fuskarsa ma abun tausayi kallo daya zaka masa kasan cewar mutuwar Rahma ta taba shi ba kadan ba, ni ma da ban saba da ita ba ta taba na shiga damuwa kuma nai kuka balle
kuma shi da yake mijinta kuma su kai rayuwa da ita.
“Ina auna yadda kika rasa babanki da dan'uwanki ne, kuma ki kaita dawainiya da mahaifiyarki, gaskiya Ayusher kin yi kokari kuma ke jajirtacciya ce, wani lokacin ana jarraba bawa saboda a gwada imaninsa
da kuma irin hakurin da zai yi, ban yi tsammanin tunanin Rahma zai addabe ni kamar haka ba bayan rayuwarta, amman idan na tuna ki da abunda yake cikinki sai na jidadi kuma nai ma Allah godiya”
Ya fada a hankali yana ta kallona da murmushi a fuskarsa sa
i dai ba murmushin farinciki ciki ko na jindadi ba irin murmushin nan na godiya ga Allah da kuma jin zafin wani abun a lokaci daya. Shigowar Momy ce tasa na dan ja baya shi kuma ya mike tsaye yana saka hannayensa aljihu ya fice, ni da Momy da kallo muka bi
shi har ya fice sannan Momy ta karaso cikin dakin ta dauki kofin furar da ta aiko min tana dubawa.
“Ba ki shanye ba?”
“Eh na sha rabi”
“Ki daina barin kanki da yunwa, na san ba za ki iya cin abu mai nauyi ba wata kila shiyasa na tanadar miki da f
urar”
“To Momy”
“Zauna”
Ta nuna min kujerar da ke facing din gandon, bayan na zauna sannan ita kuma ta zauna bakin gadon.
“Ataa ki matar aure ce a yanzu ina fatar kin san da haka?”
Na gyada masa kai ina maida idona kasa.
“Ke yarinya ce
na sani, amman daga lokacin da kikai aure zancen yarinta ya kare sai dai a kira ki