Showing 42001 words to 45000 words out of 237425 words

Chapter 15 - ZAKI COMPLETE

dauko duka kayanmu tare da Farida na dawo da su dakinmu, ni da Farida muke ta zagin masu kudi da irin wulak

ancinsu, Mahaifiyarta kuma nata shigar musu wai idan ban musu wani abun ba ai ba za su zo har cikin gida su mana haka ba. Ni dai ban ce da ita komai ba, ni da Nana muna ta jiran tsammanin idan mahaifin Farida ya dawo ya kore mu ya ce mu bar masa gida, amma

n be kore mu, kirana kawai yai ya tambayi ba'asi sannan yai min jan kunne akan gaba kar na yarda irin hakan ta kara faruwa, na jidadin yadda yai mana daman sanin darajar talaka sai talaka dan'uwansa, ko da yake wasu talakawan ma basu san darajar talakan da

n'uwansu ba kamar Maman Farida.

A daren taliya na dafa mana, muka ci ni da Nana sai da muka koshi nas sannan muka kwanta bayan mun kashe kyandir din dake haska mana dakin duk dare, yau ma kamar yadda na sabawa kaima da tashi da wuri na tashi sai dai b

ayan na yi sallah asuba na koma na kwanta tun da bana aikin komai kuma ina da bukatar bachi. Ko da na farka ranata fito ko'ina kusan duk wani abun da ake saidawa na kari kama daga koko ko waina sun kare a lokacin sai dai na yamma idan anyi, dan haka na dim

ama sauran taliyar da muka raga ni da Nana jiya mu ka sake cinta da safe. Sannan na shiga nai wanka na fito na shirya cikin yadinmu na gado na rufe kaina kamar yadda muka saba yi idan zamu je bara, wannan karon har da gashin kaina na saki ya sauko har guri

n mazaunaina, sannan na dauki dubu daya a cikin yan kudi da suka rage mana dan na siyo takalmin zuwa Abuja domin takalmina sun cinye daga kasa.

“Ki siyo mana tuwon ruwa daga can (bula) da kuli da zogale sai mu yi kwado”

“To Nana sai na dawo”

Na a

msa ina saka kafata na bar gidan, misalin sha biyu na rana na kama hanyar kasuwar yar murna, domin bana son zuwa tsohuwar kasuwa ko sabowa saboda cinkoson mutane, alhalin ba wani abun kirki zan siya ba, a kafa na tafi duk kuwa da irin nisan da ake akwai am

man ina jin kamar hasara ne na biya kudin achaba bayan muma muna da bukatarsu, kara dai idan zan dawo sai na hawo achaba ko Napep na dawo shi ma idan na rago canji.

Abun ka da wanda ya so tafiyar kafa, kuma gwanim tafiyar nan da nan na isa kasuwar murn

a, wata karamar kasuwa ce wance za a iya kiranta da

unguwa ma domin mutane da yawa suna da gidaje a cikin kasuwar ba kamar sauran kasuwani ba. Daga bakim titi ma tsaya na siye takami na roba sai da natsaya na gwada wandanda suke yi ma kafata sannan na biya

kudin dari shida da hansi, murna ta cika min zuciya domim rabon da na saka talkami mai tsada kamar haka har na manta duk talkamin da zaka gani a kafata ko dai an bani ne ko kuwa wasu sun gaji da amfani da su ne sun jefar na tsinta na gyara ina sakawa, kus

an ma sai na ce ko a lokacin sallah da ake siyayya ni ba asiya min sabon kaya ba balle wani sabon takalmi. Bayan na bashi kudin na shiga cikin kasuwar na siyo abunda Inna ta aike ni sannan na fito na tsaya titi jikin wata mota ina jiran wasu motocin su gam

a wuce saina tsallaka na koma ta dayan bangare na hau Napep da naira hansin din da suka rage min. Ina kokarin tsallakawa wata motar na kokarin parking kusa da wance na ke tsaye sai ji nai motar ta ture ni da karfi har sai da na fadi zaune. Lambar motar kaw

ai na kalla na gane cewar mutumenan mijin matar nan, wani abun isa yaga ya kade mutum amman ba zai iya fitowa ya duba waya kade ba, waya sani ko da gangan ya kade ni. Unkura nai na tashi na nufi inda yake na daki gilashin motar da karfi sai ya sauke gilash

in yana kallona da cat eyes dinsa.

“Me na maka za ka kade ni? So kake ka kashe ni? Wulakancin da ka tura aka mana a gida be wadatar da kai ba, sai ka kade ni? Kai wa wane irin mutum ne? Kana son matar ka kasa cire kodarka ka bata sai da kasa a zalince

mu aka cire aka dasa mata, kuma yanzu dan tsabar zalinci na yi magana shine zaka aiko har gida a ci mana mutunci a wulakanta mu? Hakan bw maka ba yanzu kuma ka ganni zaka nemi wulakanta ni?”

“Ba a nuna ni da yatsa”

Shine kawai abunda ya fada yana hak

imce cikin motarsa yana kallona ido cikin ido kamar ba da shi na ke masifar ba, ba dan cewar na ji maganar ba da sai na rantse ba daga bakinsa ta fito ba. Ni sai a yanzu na lura da cewar na nuna shi da yatsa din ma, a maimakon daya sai na saka yatsuna biyu

na nuna shi da su.

“Saboda kana wa? Mai arziki? Mai arzikin da ba zai iya zuwa gida da ko naira ba? Mai arzikin da bai iya komai da duniyarsa ba sai zalinci? An nuna ka ka yanka ma idan ka iya, bana tsoronka kai da muguwar matarka da mugun likitan nan

, babu tsoronku babu kaunarku ko kadan a zuciyata”

Ina gama fadar hakan na tofa masa yawu a motarsa na koma inda nake tsaye, na tsallaka titi ina ganinsa yana ta kallona har na tari achaba na na hau, shi da mutanen da suka fahimci fadanmu. Sam babu tsor

onsu yanzu a zuciyarta ko kadan, sai ma tsanarsu da nai har na isa gida zuciyata zafi take saboda bacin rai. Sai dai ban fadawa Nana ba, kuma ban nuna mata cewar wani abun ya faru ba, ina shiga na shirya mana tuwon ruwan na gyara zogale na kwada mana muka

ci, sannan na cigaba da shirye shiyena a yar ghana must go dita da na siyo sabowa.

Bayan sallah isha'i muka kwanta ni da Nana, sai da na tabbatar ta yi bachi sannan na taso na baro mata dakin na zauna a tsakar gida cikin farin wata ina ta kallo taurari

kamar mai kirgasu, tunani a zuciyata lallai ba dan talauci ba babu abunda zai nisanta ni da mahaifiyata. Kukana nai ni kadai babu mai bani hakuri har nai na gama sannan na wanke fuskata na koma dakin na kwanta amman bachi ya kasa daukata, sai na juyo

da f

uskata kusa da ta Nana ina ta kallonta kamar ance idan na tafi ba zan dawo ba.

Tun kiran sallah fari na farka, domin maman salma ta fada cewar da na yi sallah asuba na zo mu kama hanya, ina sallah Nana na kuka har nai na gama, ina cikin yin addu'a aka

buga kofar gidansu Farida na san ba zai wuce Maman Salma ba, a nan ni ma na fashe da kuka na kama hannayen Nana na rike ina ta shafasu a fuskata, Farida ta shigo dakin ta dafa ni tana ba ni hakuri. Sai na juyo na kalleta.

“Ga Amanar Nana nan na baki, k

i kula min da ita iya gwargwadon ikonki, ki yi mana gwargwadon abunda za ki iya, kin sani Farida ba dan talauci ba babu abunda zai nisanta ni da ita, tana da bukatata amman dole na tafi na nemo kudi. Dan Allah ki kula min da ita”

“Na miki alkwari Ataa z

an kula da Nana In-Sha-Allah”

Na rumgume ta ina kuka kamar yadda ita ma take, sai kuma na sake ta ka saka hannayena na kama kafar Nana ina Shafawa.

“Na yafe miki Ataa na yafe miki duk abunda ke tsakanina da ke, tashi kije Allah ya tsare ya kai ku la

fiya”

“Amin”

Na fada sannan na mike tsaye ina kuka sosai na fito nai ma mamar Farida sallama da mahaifinta na karasa gurin Maman Salma sai wacce ke tsaye tana jirana, sau biyu ina waigowa ina kallon kofar dakin da Nana take, ina ta jin kamar kar na t

afi na barta amman tafiyar ta zame min dole. Gidan Maman salma muka koma ta dauki kayanta a nan na gane cewar ba ni kadai zata kai ba, domin tare da yan mata shida muka kama hanyar Abuja bayan direba ya zo har gida ya same mu, da alama direbanta ne sun sab

a da juna ita da shi.

Tafiya mukai ta yi, tun ina hawayen rabuwa da Nana har na soma wayewa, tafiyar ta fara ci min rai, a zariya muka tsaya muka karya sannan muka cigaba da tafiya mai isa, a takaice ba mu isa Abuja ba sai cikin dare...

ALI

YU POV.

Yana rike da jarida a hannunsa amman ya kasa karanta komai, abunda Ataa ya fada masa jiya kawai yake tunani, wani be taba karfin halin fada masa magana mai zafi kamar ta jiya da Ataa ta fada masa ba, beside shi be san ya tura kowa gidansu ba, b

e ma san inda gidansu yake ba, and kadewar da yai mata ma bada gangan yai ba. Sai dai ko ba komai yadda take ta karfi hali ta burge shi, and yana da right din yi mata excuse tun da Azzalumi take ganinsa, kuma zalintarta akai? But waya tura wasu gidansu? Ko

Doc Asim ne kamar yadda Momy take masa hasashen cewar zai iya cutar da ita? Ko kuwa mahaifin Rahma ne wanda shi ma yasan ba a zai kyale ba? Ko dai wanene he need to know ta dalilinsaba zai yarda sake zalintar kowa ba.

Zaman da Rahma yai kusa da shi yasa s

hi dagowa daga dogon tunanin da yake ya kalleta yana kai hannu ya shafa gefen kafadarta.

“Dear na gaji da garin nan, bana son mu sake neman wata mai aikin wani abun ya faru, kuma gidan nan zamansa da datti ni bana so kyankyami na ke ji”

Be ce mata k

omai ba, daman can ta san ba zai ce ba.

“Ni mu koma Abuja kawai tun a can komai yi mana ake”

Ya aje jaridar hannunsa ya janyota jikinsa.

“Ba yanzu ba”

Da mamaki ta daga kai ta kalleshi.

“Saboda me?”

Shiru yai for like five minutes befo

re ya bude baki ya ce.

“We need to help her”

“Who?”

“Yarinyar da aka cirewa mahaifiyarta koda, zata iya shiga wani hadarin saboda mu, be kamata mahaifiyar yarinyar nan a jikinki ba, tana kallon mu a matsayin azzalumai, kuma ta rayu a cikin kallon

zalintar za mu sake yi wani zai iya fakewa da mu ya zalince a again”

Wani irin zaranannen kallo tai masa kamar ya ce mata za a cire kodar jikinta ne a mayarwa mahaifiyar Ataa....

______________________________

Assalamu Alaikum.

Kamar yadd

a na fada yau na kai karshen free pages wato page 15, nace 12 zan kare free pages wasu suka roki n kara na kara to 15.

Masu niyar siya za su iya sending 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt Bank, sai ku turo shaidar biyan ta number nan 08036126660. Yan

nijar kuma za ku turo 500fc ta number nan +22790165991 sai ku min magana ta number nan 08036126660 zan saka ku group.

And for our yan kasuwa da suke son a tallata musu hajarsu it's 4k via 08036126660.

Masu niyar siya da marasa niya duka Allah ya wada

ta mu da arzikin na halal. Thanks

🙏😍🌹

1





6





A wani babban gida muka kwana da alama ta san mutanen gidan domin na ji sai tambayarta wasu suke tana cewa suna lafiya. Shayi da biredi aka kawo mana da safe muka karya sannan muka shiga bandakin mukai wa

nka da shower abun ban taba ba kuma na dade ina mafarkin yi. Bayan mun shirya aka sai ta waremu mu uku muka shiga motar da muka zo da ita, ni da wata Murja da Humaira.

   Tafiya ake ta yi ni dai ban gane inda muka dosa ba, ban kuma zan iya cewa ga inda a

ka bi ba, domin akwai tazara sosai tsakanin unguwar da muka saka da kuma wance za mu je, har ya zamana da za ace na dawo da kaina ba zan iya ba. Sai dai abunda na kura da shi unguwar ta manyan mutane ce, domin manyan benaye ne a unguwar sai kuma wadanda ba

benaye ba amman masu kyau sosai da daukar hankali, a bakin ko wane kofar gida an kawata shi da furanni, kuma babu kowa a unguwar sai manyan motocin alfarma da ke wuce shi ma jifa jifa. Ba dan na san halin Maman Salma ba da na zargi ko wani abun za a min a

unguwar domin a rayuwata ban taba zuwa irin wannan unguwar ba, hasalima ban taba sanin cewar akwai irin wadannan manyan gidaje da benaye masu kama da ma'aikatu a Nigerian ba.

  A bakin wani kato gate direban mu ya tsaya, yai horn, wani matashi mai siffa

r karfi da kuzari ya leko ya zo har gurin motar suka gaisa da Maman Salma sannan na koma ya bude mana gate din. Da muka shiga gate din farko sai na hango wani gate din a tsakanin tafiyar wacan gate din da na farko yai taku sittin bayan shi kuma akwai wani

dan karami da aka kawata da furanni, banbancin gate na biyu da na uku na ukun irin wannan ne da aka saka kawai dan kwalliya wanda zaka iya hango na ciki na ciki kuma ya hango mai shirin tahowa, na biyu kuma be kai na farkon girma ba, na farko shine kato ga

shi dogo kamar yadda ginar gidan take.

  A wani kato fili direban ya aje motarsa, yamma da filin an kafa wata katuwar rumfa mai kala wance ta lullube wasu manyan motoci da ban taba ganin irinsu a sokoto ba, da alama gidan kashi uku ne, bayan bangaren da

ke fuskarta mai shigowa ga wani can yamma da motoci, kuma akwai wani arewa da motocin, gaba daya gidan da duk wani abu na kwalliyar gidan na glass ne, ya wasu furanni kananan da suka kara haska gidan, bayan wadancan na nesa da mu da na ke hangowa masu tsay

i da hudu an musu yar karamar kofa, da alama Garden ne kamar yadda na ji ana fadar cewar gidajen masu kudi suna yin Garden, muna rufe motar sai ga barewa ta fito da gudu daga Garden din da kahoninta tana kallonmu kamin ta juya da gudu ta koma ciki.

Tsunt

sun maka ne Peacock har guda hudu ke ta yawo a harabar gidan yana bude fukafukansa abun sha'awa, wani irin shauki ne ya kamani da kuma tsoro a lokaci daya, domin irin manyan masu kudin nan ba su cika ganin kimar talaka ba, balle kuma ace za ka yi aiki a ka

rkashinsu ne.

  Daya daga cikin part uku da suke gidan muka nufa, Maman Salma na gaba muna biye har muka isa, gaban kofar ma duk furanni ne irin na kaskon nan an kawata katuwar kofar da su. Wani dan maballi ta danna taja baya ta tsaya jiran bude mata amm

an ba a bude ba, sai ta sake danna bayan wasu mintuna, nan ma sai da aka kara bata lokaci sannan aka bude kofar falon. Ba mu ga wanda ya bude mana kofar ba, da alama wanda ya bude komawa yai ya zauna a daya daga cikin manyan sofa din da suke katon falon ma

i kama da falo uku.

Wani kamshin masu arziki da turaren mai tsada ne ya fara yi mana marhabun kamin ac da ke falon ya karaso garemu. Wasu manyan yan matane su hudu hakince saman kujera suna kallon wani kato tv wanda ban taba ganin irinsa ba tun da Nana n

a haifo ni duniya. Babu wacce ta juyo ta kallemu daga

cikin yan matan balle ta amsa mana sallamar da muke, duk kuwa da irin daga mana hannu da Maman Salma take na alamar mu sassauta muryarmu.

 

“Hajiya Rukaiya da Hajiya Maryam ina kwananku?”

Maman s

alma ta fada da dukan far'arta sai a lokacin ne yan mata suka dago suka kallemu, wacce na ke zaton ita ce Maryam din ta amsa a kaikaice tana mana kallo ba uku saura kwata, yayinda Rukaiya ta sakarwa Maman Salma Murmushi kadan, sannan wacce ta fi su kurciya

ta dago ta kallemu sai ta maida kanta gurin zeeworld din da suke kallo.

“Na ce ko Hajiya tana nan?”

Maman Salma ta tambaya kamar da tsoro, sai wacce aka kira da Rukaiya dazu ta kalli karamar ta ce.

“Baby je ki kira mata Mama”

Da kamar ba zat

a je ba, sai kuma ta mike tsaye tana sanye da wasu guntayen kaya irin na turawa wato dogon wando da be kai kasa ba, da kuma t-shirt ta mata mai guntun hannu kanta ba dankwali an yi mata kitson attach tsorayen sun sauko har bayanta. Wata katuwar mattakala t

a nufa irinta ta indiyawa mai fadin ta fara takawa a hankali har ta haye sama gaba daya, daya daga cikin dakunan da muke hange ta tura ta shiga. Shiru shiru bata fito ba har kusan awa daya sannan muka hango an bude kofar wata kasaitacciyar mace mai isa da

ji da kai ta fito daga dakin tana sanye da wata dakankiyar shadda mai kamar kamfala sai shining take kamar an shafa mata mai. Da ďai-ďaya matar take takawa tana saukowa stairs din wani saurayi mai kama da ita na gafenta fuskarsa dauke da murmushi ya zuba d

uka hannayensa aljihu.

“Mama ba ki yarda da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login