Showing 99001 words to 102000 words out of 237425 words
ya saka yaji ba zai iya zuwa gurin Rahma a haka ba, can din ma yasan ba bacin rai zai kwaso domin ba fahimtarsa zata yi ba. Canja hanya
yai ya dauki hanyar da zata sadashi da Arkilla phone dinsa a dayan hannunsa yana driving da dayan, sako ya shigo wayarsa ta saman screen din ya karanta abunda Muhseen ya turo masa.
_Ka fara bawa Ataa wayar zan yi magana da ita then zan zo gobe_
Wa
ni murmushin haushi Aliyu ya buga wayar a front seat yana wani irin huce how on earth Muhseen zai saka masa doka wai sai ya bawa Ataa ya yi waya da ita sannan zai zo, har ya isa gida be daina jin zuciyarsa na tafasa ba. A harabar gidan ya samu Momy zaune t
ana gyara giďa daman ta kan zauna wani lokacin har ita da Daddy ko da yara, tana ganin yadda Aliyu ya fito mota tasan akwai bacin rai a tare da shi, kai tsaye inda take zaune ya nufo ya zauna kusa da ita.
“Wai ni Muhseen zai sakawa doka?”
“Miya faru
?”
A nan ya labarta mata abunda ya faru sai Momy tai murmushi.
“To yanzu kiran waya ka bata su yi magana shine wani abu?”
Yayi shiru be ce komai ba. Momy ta dauki wayarta ta kira Siyama tace ta fito tare da Ataa su same ta harabar gidan, a tare s
uka fito Siyama da Ataa sai dai Ataa ta fi sauri gurin karasowa gurin domin a tunaninta wani abun ne.
“Miya faru? Ina Nana”
“Waya za ki yi da Muhseen yanzu, shi zai zo ya duba Maman ki gobe”
Momy ta fada tana kiran Muhseen din waya. Sai da suka g
aisa sannan ta ce masa.
“Ga Ataa din”
“Momy ba a wayarki na ke son magana da ita ba, a wayar Aliyu”
“Naga kamar duka daya ne ai”
“Na sani Momy amman wayarsa na ke so please”
Katse kiran Momy tai ta kalli Aliyu.
“Da wayarka yake son maga
na da ita, ka kira shi yanzu nan ka bata”
Har ya bude baki zai yi magana sai Momy ta tari numfashinsa.
“Umarni ne ka kira shi ka bata wayar ta ce”
Ta fada da kamar fada tana kallonsa fuskarta babu alamun wasa.
“Wayar tana mota”
“Je ka dauko
”
Tashi yai ya nufi motar ya bude ya dauko wayar ya dawo ya zauna sannan ya kira Muhseen ya mikawa Ataa wayar. Bata karba ba ta tsaya kallonsa sai ya daka mata tsawa.
“Ki karba mana...!”
A razane ta mika hannu biyu ta karba idonta na kokarin cika
da hawaye ta kara wayar a kunne.
“Karka sake daka mata tsawa balle kuma ka ce zaka nuna nata dan yatsa, bata jidadi a wani gurin ba ba zaka zo nan ka hana ta ba, abunda kake yi ma kannenka da kowa ita ba zan daukar maka ba”
Momy ta fada tana nuna sh
i da yatsa cike da jin haushin yadda ya razana ta sannan ta mike tsaye ta dauki gyaďarta ta bar masa gurin, dafe kansa yai a gurin har yanzu gumin bacin rai ne yake sauko masa.
Gaisawa Ataa ta fara yi da Muhseen cikin sautin kuka sai ya ce.
“Mi aka
miki kike kuka?”
“Ba a min komai ba”
“Zan zo na duba Mamanki gobe kina so?”
“Eh”
“To zan zo, ki kula da kan ki kinji? Idan na zo za mu yi magana da ke”
“To”
Daga haka ya kashe wayar, sai ta mikawa Aliyu wayarsa.
“Gashi”
Dagowa yai y
a kalleta kamin ya kai hannu ya karbi wayar ya buga ta da kasa iya karfinsa a take wayar ta watse Ataa kuma tai ihu tai baya a zatonta wani abun zai mata.
*ZAKI
By Khadeeja Candy
30...
Daga gidansu Rahma gidansa ya dawo, sai ya tsaya a cikin
mota ya kwantar da kujerar baya ya kwanta hannayensa rumgume a kirji. Gaba daya wunin yau be masa dadi ba, tun da yake a rayuwarsa be taba samun kansa ciki matsala irin wannan ba. Rahma a gafe ga Ataa and now Muhseen, sai a yanzu yake nadamar sanar da Momy
abunda ya faru tsakaninsa da Muhseen da bata cilasta masa ya kira shi ba, da ransa be bace kamar haka ba. Ya dade a zaune cikin motar sannan ya bude ya fito ya shiga cikin gidan kai tsaye dakinsa ya wuce, ya kwanta be tashi ba sai kusan sallah magariba, t
ufafin jikinsa ya cire ya shiga bathroom yai wanka tare da alwala ya fito ya sake shiryawa cikin wasu tufafin ya feshe jikinsa da expensive perfume sannan ya fito ya sake shiga motar ya dauki hanyar gobirawa, a masallacin unguwar ya tsaya yai sallah kusa d
a wani mai siyardar nama, bayan ya gama ya shiga wani babban shago ya zabi waya mai tsada ya biya da ATM dinsa sannan ya fito ya shiga motarsa a cikin motar ya fiddo wayar ya kunna sannan ya soma driving da hannu daya. Har ya isa family house dinsu Arkilla
, kusa da inda ya fasa wayar ya faka motarsa ya sauke gilashin motar yana kallon yadda wayar ta watse, da duhun magariba amman ko'ina haske ne kamar rana, ya dade yana kallon gurin sim dinsa da memory yake son cirewa ya saka a wannan wayar amman baya son t
aba wayar gaba daya ta fice a ransa. Fita yai daga motar ya nufi kofar falo ya shiga, Siyama kawai ya samu a ciki tana kallon rawar babban yaro a plasma tana koyon yadda suke, sai dai ganin Aliyu ya saka ta saurin zaunawa tare da canja channel din da take
kallo zuwa wata dabam.
“Sannu da zuwa Ya Aliyu”
Sai da ya karewa falon kallo sannan ya ce.
“Ina Ataa da Husna?”
“Ataa tana asibiti Husna kuma sun fita ita da Anty Amina Momy ta aike su”
“Waya kai Ataa asibiti?”
“Kuka tai yi shine Momy t
a saka Anty Amina ta kaita”
“Je waje ki dauko min sims dina da Memory”
Shine abunda ya fada sannan ya nufi dakin mahaifiyarsa, zaune ya samu Momy gaban madubi tana cire gulagulan hannunta, a gafen gadonta ya zauna yana cirewa wayar murfi, bata ce mas
a komai ba har Siyama ta shigo ta kawo masa sims din da memory ya karba ya saka a wayar sannan ya kunna.
“Ga abincin dare can zaka je ka kaiwa Ataa asibiti”
Momy ta fada bayan Siyama ta fice daga dakin.
“Momy ba za a bawa Siyama ko Amina ta kai
ba?”
“Kai na ga dama, ka ce kana son taimakawa yarinya amman kana kokarin bata kanka a gurinta, wata rayuwa kake daukarwa kanka wace zata kara saka yarinyar ta tsane ka kuma ta yarda cewar da hadin bakinka aka cutar da ita, fasa waya a gabanta daka mata
tsawa, ko zare mata ido ba ba zai kara maka komai a gurinta ba sai tsana”
“Ba saboda ita na fasa waya ba”
Ya bata amsa yayinda yake kunna wayar.
“Saboda Muhseen ko? Kana jin cewar ka ragu saboda ka kira Muhseen ka bata sun yi waya right? Shi bat
a waya suyi magana wani laifi ko abun jin zafi”
“Momy Muhseen kanena ne, be kamata yai min haka ba”
“Shikenan dan yana kanenka ba zai iya cewa ka kaiwa wani yai waya da shi ba? Wannan wane irin jin kai ne da kai haka?”
Yayi shiru be ce komai domin
yana tunanin duk abunda zai fadawa Momy ba fahimta za tai ba, Mama Fulani ce kawai take fahimtarsa har ta goya masa baya, kuma bata taba masa magana akan wannan ba.
“Zaka je ko na tashi naje da kaina”
Dagowa yai daga kallon wayar da yake ya kalli M
omy wacce ta daure fuska.
“Zanje Momy amman kamar kina fushi da ni, kuma kin san ina damuwa idan ke da Mama kuka fushi da ni”
“Bana jindadin yadda zamantakewar ku da Muhseen yake sam, ita ma kanta na san ba dadi take ji ba, tana kyale ku ne kawai sa
boda babu yadda za tai”
“Momy matsalar ba daga ni ba ne daga Muhseen ne ya cika son shiga rayuwata ne kawai”
“Ka gani ba, wannan halin na ka shi yake bashi haushi yake ba kowa ma haushi, kai baka taba yarda cewar ka yi laifi ba, baka tana yarda ace k
aine mai laifi sai jin kai da son wulakanta kowa, babu abunda ka rage a halin Fulani kuma Wallahi wannan dabi'un ba su da ce da kai ba”
“Momy kawai kina son ganin laifina ne ki bawa Muhseen gaskiya bayan shi ne yake abunda be da ce”
“Na sani wani lok
acin yana yin abunda be dace ba, amman ka fi zurfafa sama da shi, and dole na bawa Muhseen gaskiya na kare shi kamar yadda nahaifiyarsa take maka, ba zan taba yarda ka ce zaka ciwa danta mutunci ba ko ka wulakanta shi ba, ku rika abu kamar ba yan'uwan juna
ba, kana ikirarin kai babba ne amman baka iya kawar da kai daga ganin wani abun ka ka kyale?”
Kansa ya mayar gurin wyar yana ta taba ba dan kuma yana bukatar tabawarba sai dan be san abunda zai cewa Momy ba, har tai fadanta ta gama ta fice daga dakin
be ce gama be sake cewa komai ba. Bayan ajiyar zuciya daya sauke ya fito daga dakin ya nufi dinning inda Momy take hada kulolin abinci da kwadon da saka plate a ciki da spoon ta mika masa.
“Idan ka je kuma ka daka mata tsawa idan bata karba ba”
Murm
ushi yai ya karba ya nufi kofa Siyama kuma ta dauki ragowar kulolin ta saka masa a mota har ta juya zata koma ya kirata.
“Shigo muje idan munje can za ki rika kayan”
“To”
Ta fada tana bude front seat ta zauna shi kuma yai ma motar key suka kama h
anyar asibitin. A inda ake faka motoci ya faka motarsa sannan bude motar ya fito ya bude gidan baya ya dauki kwandon plate din da karamar kula Siyama kuma ta riko mayan kulolin guda biyu ta dora daya saman daya. Security din na ganin zubinsu ya san ba irin
zubin mutanen da zai tarewa kofa ba ne, da kansa ma ya bude musu ward din Anas room suka shiga. Aliyu ne a gaba domin shi ya san inda dakin yake Siyama na biye da shi a baya har suka isa cikin dakin.
Tura kofar kawai yai ya shiga ba tare da sallama ba
, sai dai yana kokarin sakin fuskarsa duk da ba murmushi yake son yi ba. Zaune ya samu Ataa saman gadon da mahaifiyarta take kwance tana bachi, Doc Bukar kuma na zaune saman kujerar da ke fuskartar Ataa yana nuna mata abu a laptop dinsa, babu Hijab a jikin
ta sai dankwali gashin kanta a waje ta rike shi tana wasa da shi tana kallon video a laptop. Haka kawai sai Aliyu ya ji babu dadi samun su haka, baya son ganin Ataa da wani namijin a yanzu dan gani yake kyaunta zai iya jan hankalin wani namijin ya cutar da
ita. Duk yadda yai kokarin sakin fuskarsa sai zuciyarsa tai masa ba dadi. Kusa da Doc Bukar Siyama ta aje kulolin hannunta sannan ta karbi na Aliyu ta aje kasa, da gangan Aliyu ya kasa cewa Doc Bukar komai sai kokarin danne bacin ransa yake.
“Aliyu ka
shigo”
Doc Bukar ya tambaya yana rufe laptop din da murmushi a fuskarsa.
“Eh”
Mike tsaye Bukar yai yana fadin.
“Ka yi waya da Muhseen din?”
“Na yi”
Yadda Bukar yaji Aliyu na amsa masa magana da a take kuma babu sakewa ya san ransa ne a
bace sai dai be yi zaton ganinsa da Ataa bacin ran nasa ba, a zatonta wani abun ne dabam yake damunsa.
“To ni zan wuce yar Fulani sai jango ko?”
“To sai da safe”
Ataa ta fada murya kasa kasa shi kuma ya juya ya fice yana murmushi. Duka duka yaush
e aka Ataa ta zo asibiti da har zata sake da Doc Bukar haka shine abunda ya tsayawa Aliyu a rai.
“Ina Hijabin ki?”
Ya tambaya da kamar fada, har Siyama ta kalleshi.
“Gashi”
Ataa ta fada tana dauko shi daga gefen Nana ta maida saman jikinta. H
ar ya bude ba ki kamar ya sake cewa wani abu sai kuma yai shiru ya maida dubansa gurin Nana.
“Ya mai jiki”
Siyama ta tambaya.
“Alhamdulillah da sauki”
Ta fada tana kallon Aliyu da fuskarsa ke daure. Juyawa yai ya fice daga dakin ba tare da ya
sake cewa komai ba. Siyama tai saurin binta tana ma Ataa Allah kyauta. Rai a bace ya shiga motar yana ta mamakin yadda maza suke sakewa da mace da sun ga kyau su yi ta rawar jiki.
“Mtssssssss”
Yaja tsakin daya saka Siyama kallonsa kadan tai saurin
kawar da kai, tana tunanin abunda tai ba daidai ba da har ya saka shi tsaki. Be shiga cikin gidan ba ya tsaya bakin gate ba tare da ya danna horn ba, Siyama na ganin hakan ta san baya son shiga ciki ne, sai ta bude motar ta fita shi kuma yai ribas ya juya,
yana driving wayarsa tai ringing kallonta kawai yai ya dauke kai rabon da yaji ringing din waya indai ta shi ce har ya manta, dan shi baya son ringing sai dai ya bar waya a silent ko vibration. A bakin gate din gidansu Rahma ya faka motarsa sai a sannan y
a kai hannu ya dauki wayar yana duba yadda Nasir da wata bakuwar number suka jera masa missing calls hudu ya saka wayar vibration sannan ya shiga text ya aikawa Rahma sako.
RAHMA POV.
“Kin ga ko Rahma ki daina damun kanki da lamarin namiji, namij
in ma wanda zai iya mantawa da ke a take, domin yana jin zai iya zuwa ya dauko wata macen ke ya barki a nan”
Cewar Muneera tana wani yatsina fuska. Ikram ta girgiza mata kai.
“Wallahi karki dauki zugar Muneera Rahma, Aliyu yana son ki kuma yana kaun
ar domin ba ko wane namiji ne zai yarda ya auri mace mai ciwo irinki ba har ya nema miki lafiya, yanzu shekara takwas kuna kokarin shiga ta tara amman be taba nuna gazawarsa akai ba, sai ma nuna miki kauna da yake, Wallahi da wata ce ke kamata ma yai ki ce
masa ya auro wata ku zauna tare domin shi babban tukuncin mace a gurin mijinta”
Muneera ta taba hannu tana dariya.
“Lallai Ikram ba ki da hankali, ke baki ganin yadda ya fara gajiya da ita? Wallahi da yana kaunar ba babu abunda zai saka ya ce ba za
a cire kodar mai son siyarwa a dasa mata ba, kuma duk inda kodar ta kai sai nemota ya saka mata”
“Wacce ta kone yanzu waya saka mata ita ba shi ba, wai ya kike haka ne Muneera zawarcin nan fa ba dadi ne da shi ba, kin kuma sani dan gashi nan kina yi, a
kan me za ki rika zugata ta kashe auren ta bar mai son tsakani da Allah ta dawo tana nadama”
“Wallahi babu nadamar da zata yi, ko sakinta yai alheri ne dan zata iya auren wani ta haihu ta barshi shi da baya haihuwar yana rabon ido, ke ce dai baki san du
niya ba tunda ba ki taba auren ba shiyasa kike wannan maganar, anyi karatu amman kamar wacce ba tai ba, ni wallahi na riga na san right dina namiji be isa ya juyani yadda yake so ba”
Muneera ce ke wannan maganar tana harar Ikram. Duk abunda suke Rahma b
ata ce koma, sai dai ta kasa daina hawayen da take saboda kishin da yake damunta.
“A tsakankanin kwanakin nan ina jin kamar na rabu da Aliyu, ko dan na samu haihu kuma na matsar da jikina daga nasa, dan ba zan yarda ya hana jiki da wata yar talakawa ku
ma ya hada da ni ba, amman sai na ji kamar ba zan iya ba, Saboda ina son Aliyu sosai ya saba min da wasu dabi'unsa da ko bachi bana jindadin yinsa ida yadda baya kusa da ni”
Tana rufe bakinta sako na shigowa yarta da number Aliyu Sweet bae kamar yadda t
ai saving number sa da dan emoji din heart a karshe. Sai da ta share hawayenta sannan ta bude sakon ta soma karantawa.
_Fito gani gurin gate muje gida_
_Na fi son zama a nan_
Ta mayar masa da amsa a take ya sake aiko mata da wani sakon.
_Na s
ani, a sokoto za mu zauna amman a gidanmu_
_Ka bar ni a nan kawai_
_Ba ke son kulawata ne Rahma? Ba kya son zama kusa da ni ne?_
_Ina so Aliyu ina so_
Ta mayar masa da amsa tana hawaye sai ya sake turo mata wani sakon.
_Then fito muje gidan
mu I'm waiting for you_
“Wai yana bakin gate”
Ta fada tana kallon kanen nata Muneera tai karaf ta ce.
“Mi ya zo yi?”
“Wai na fito mu koma gida”
“Tashi kije, ki fadawa Daddy kawai da Momy sai ki bishi ku koma can idan ma kina son zaman a nan
da safe sai ya rika kawo ki”
“Ta je fa kika ce tab hmmm”
Ikram ta kalli Muneera da tai maganar ta ce.
“Karki zuga ta akan abunda kika san gaskiyarsa, namijin da baya fushi idan yai be iya ba, duk yadda yake son ta idan tana masa irin haka zata n
isanta sonta ne kawai a zuciyarsa”
Saukar da kafafunta Rahma tai daga saman gadon tunawa da Aliyu baya son jira duk kuwa da tasan ita yana daga mata kafa, sai dai idan yai fushi da ita itace zata shiga