Showing 36001 words to 39000 words out of 237425 words
kit
chen, can na ke ra'ayin na fara gyarawa tun da na ga shi yana zaune a falon, waya sani ita ko bata tashi bachi ba, balle na gyara bedrooms. Ina cikin aikina na ji tsayarwar mota a harabar gidan, sannan na ji sallama da muryar da na ke kyautata zaton kamar
na san mai ita, sai da na gyara kitchen din tsaf sannan na riko tsintsinyar ya fito daga kitchen da zimmar gyara dinning area da falon idan magajin izzar ya tashi.
Arba idanuwa sukai da mummuna mutum wanda zan iya kiransa da bakar jaddara, da bana son
na sake saka ta a idona har a bada, Doc Asim ne sanye da suit ya dora labcoat sama yana zaune akan kujerar da ke fuskantar wacce Rahma take zaune ita da mijinta...
_____________________
Page biyu ya rage mana mu gama free pages In-Sha-Allah. i
f you want to subscribe pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt Bank. sai ku turo shaidar biyan wato screenshot ta wannan number 08036126660, ko kuma katin mtn na 300 ga marasa account ta wannan number 08036126660. yan nijar za ku tura 500fc na line Orang
e ko Airtel ta number nan +22790165991 sai ku min magana ta wannan number 08036126660 Za'a saka ku Group.
Thanks
🙏🏻
Ku ziyarci YouTube channel dina, ku danna min subscribe kuma kui sharing.
👉
https://www.youtube.com/channel/UCpAkml0pIh6MUnzt9nLh_q
Q
*Z A K I*
By Khadeeja Candy
1
️
⃣
4
️
⃣
Bana bukatar na tambaye abunda ya kawo shi gidan, kasancewarsa likita, da kuma yanayin da naga Rahma na tabbatar bata jindadi, sai dai ina tabbacin ba su san ko waye Doc Asim ba, shiyasa har suka ki
ra shi har cikin gidansu, akwai yiyiwar ya sake samun damar sake cutarsu kamar yadda ya cutar da ni. Kallonsa kawai da na ke ina jin kamar naje na shakeshi ya mutu.
“Ke lafiya kika tsaya kallon mutane ba za kije ki yi aikin ba?”
Rahma ta daka tsawar
data saka ni dawowa hayyacina. Sai mijinta yai saurin rike hannunta yana alama da tai shiru kar ta wahalar da kanta gurin magana.
“Karku yarda da wannan mutumen Wallahi azzalumi ne macuci, mugu wanda ba zai taba gamawa lafiya ba”
Da sauri Doc Asim
ya dago yana kallon inda nake tsaye da mugun mamaki, da alama sai yanzu ya san da tsayen da nai jikin kofar.
“Wacece wannan?”
Ya tambaya yana kallon Mai gidan da ke kallona shi da matarsa.
“Ba ka gane ni ba?”
Na fada kana na saki tsintsiyar han
nuna na juya na koma kitchen din na cire Hijabina abun ka da marar dankwali sai gashi na sauko har gadon bayana, na zuba omon da ke gurin na wanke bakin fuskata na juyo na fito a fusace na karasa har kusa da inda yake zauna na nuna masa fuskata.
“Ka ga
nene yanzu? Bayan ni wace yarinyar ka cuta? Bayan ni wace macen ka sani mai kama da ni?”
Miyewa yai tsaye ya wanke min fuska da mari.
“Ba ki da hankali ke kin taba ganina ne?”
Tasss na mayar masa da martanin marin da yai min cikin zafin rai, duk
da kasancewar ya girme ni a shekaru da jiki.
“Na mare ka da hujja sai ka samu damar sake saka yan sanda su kulle ni a cell kamar yadda ka sa aka min saboda ina talaka”
Yadda muryata take fita kadai ta isa ta karantar da kowa irin daci da dafin baki
ncikin da ke raina, ga wasu zafafan hawaye da suke sauko min, ina yi ma Doc Asim wani irin kallo mai guba. Mamaki ya hana shi motsi sai sakin baki da yai yana kallona, Rahma ce ta mike tsaye.
“Ke ashe baki da hankali ba ki da tarbiya? Za ki daga hannu k
i mari babban mutum mai daraja kamar Doc Asim? Kina yar talaka?”
“Ba yin kaina ba ne talaucin, ke ma da Allah ya zabi a gidan masu arziki ba yin kanki ba ne, ba wata gwaninta kikai wa Allah ba ya zabe ki ya bar ni, saboda kawai ina talaka ba shi yake nu
fin ni ba mutum ba ce, a gurin ki Doc Asim yake mai daraja amman a gurina konanniyar ashanar bola ta fi shi, zan fi jindadin sunan mutuwa fiye da sunan wannan azzalumin, ganin bakin duhun zai fi min ganin wannan mutumen”
Na fada ina nuna shi da yatsana,
mamaki ya cika Rahma, mijinta kuwa kallona kawai yake sai kuma ya kalli Doc Asim kamar mai son tantance abu. Doc Asim ya jinjina kai yana kallona yai kwafa.
“Ni kika mara? Sai kin yabawa aya zakinta, ni ban sanki ba ban san inda kika fito ba amman sai
na nuna miki ko wanene ni”
“Babu abunda zaka nuna wanda ban san shi ba, na sanka na san zalincika tun har ka iya cire kodar mahaifiyata ba tare da saninta ba, saboda kawai
ka maida ni zahila marar galihu, ka sa na saka hannu kai mata aiki ka cire mata
koda, kuma kasa aka kulleni a gidan yan sanda saboda na nemi hakkin mahaifiyata, to wane zalinci zaka nuna min da ya wuce wannan? Idan kashe ni kaka son yi, to mutum baya mutuwa biyu, domin ni na dade da mutuwa tun daga lokacin da kasa mahaifiyata ta rasa
lafiyarta, sanadin haka na rasa kanena, to me zaka min yanzu? Duk abunda kake jin zaka iya yi kaje kai, ba a duniya za a tabbata ba, akwai kiyamar Allah zata tsaya, kuma ni da kai za ku amsa ko wace tambaya daga Ubangiji...”
Na karasa ina fashewa da kuk
a tare da juyawa da zimmar zuwa na dauki tsintsiyar na cigaba da aikina, sai naji muryar mijin matar nan yana wata irin magana mai rikitarwa.
“Kardar kodar da aka dasawa Rahma take magana....?”
Juyowa nai idona na hawaye na nuna Rahma.
“Kodar Na
na ka sakawa wannan matar? Matar da mahaifinta ya koremu a kangon gidansa saboda mun taba a gidan? Matar da mahaifinta be san daraja talaka ba? Matar da mahaifinta yasa a ka wulakanta mu? Ita ka sakawa kodar talaka? Talakar ma wacce ya wulakanta? Ka cuce n
i ka cuci nana Allah ya isa tsakanina da kai, da kai da duk wanda yasa kuka aikata min wannan aikin ba za ku ga da kyau ba, Wallahi Allah ba zai barku ba”
Na fada cikin daga murya iya kar karfina, sam na manta da a gidan wani mai kudi nake, yau duk wani
tsoro da fargabar gudun laifi ya fita a raina, daga Rahma har mijinta da Doc Asim yau kananan mutane na ke kallonsu kuma azzalumai.
“Uban waye yace ki siyar? Akan mi za ki rika fada mana magana son ranki cikin gida? Ubana sa'arki ne da zaki rika saka
ko a maganar ki?”
Rahma ce ke wannan maganar tana matsowa kusa da ni, har ta ka hannu zata mare ni sai mijinta yai saurin rike duka hannayenta ya matsar da ita jikinsa yadda ba zata iya ko da kwakwaran motsi ba.
“Talauci ba hauka ba ne Rahma, kuma b
a kaskanci ba ne, jarabawa ce daga Ubangiji, ba kuma zan sake yarda marar sanin darajar dan adam irinki wacce ta more da kodar mahaifiyata ta sake wulakanta ni ba, kin ci riba da ni tun da nayi aikin kwana biyu a karkashin ki, amman ba za a koma ba, ya zam
a na karshe, sai dai ki wulakanta wata amman ba ni ba, kuma tun da har kuka zalinmu lafiyar nan da bata yi amfani komai a jikinki ba”
Ina kawai nan na nufi kitchen din a fusacw na dauki Hijab dina na saka na fito fuuuu na fice daga gidan kamar iska. Kan
kace kwabo har na kai gate na bude na fita raina na min mugun zafi zuciyata na ciwo sosai. A rayuwata ban taba ganin mutane masu son kai da tsantsan zalinci kamar likitan nan da mutanen nan ba, babban bakincikina sun ci riba da ni na aikin da nai a karkas
hinsu, wanda hakan ya fi komai yi min ciwo.
Tun da na kama hanyar gida sai na nemi kukan zuciyata da na ido na rasa, wani karsashin da karfin zuciya dana ruhi suka rufe ni, na jaddawa kaina nemawa Nana lafiyata ta rayu ko dan bakincikin masu son ganin
bayanta, a yau na gane ba kuka na ke bukata a yanzu ba, lokacin kuka da bakincikin abunda ya faru a baya ya kare, wannan lokacin na fuskartar
gaba ne da inganta rayuwata da ta Nana, na yarda abunda ya tafi baya dawowa amman abunda be zai zo za a iya tarbar
sa gabannin ya zo, zan jure ko wane kalar wulakanci da cin zafi daga duk wanda zai iya zama dalilin samun lafiyar Nana.
A kullum idan zanje gida ina zuwa da kasala da jin gajiyar tafiyar, amman a yau na isa gida da karfi kamar daman can ban yi tafiyar
ba, ban yarda Nana ta fahimci komai ba, na shiga dakinta na zauna ina ta kokarin yin far'ar da take ta zo min.
“Lafiya kika dawo da wuri haka Ataa?”
“Nana sun koreni daga aikin”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, sun kore ki kuma? Me kikai? Mun
shiga uku”
“Ba mu shiga uku ba, kuma da yardar Allah ba za mu sake shiga uku ba, ina tunanin ma kamar wata hanyar zata sake bude mana?”
“Kamar ya? Yanzu ina za ki sake samun wani aikin”
“Farida ta fada min cewar Maman Samawa tana samawa mutane aik
i a abuja, kuma a can ana biyan kusan 30k ko sama da haka, kin ga cikin wata biyu ko uku na hada kudin maganinki”
“Aa ni ba zan yarda kije can nesa ba, ban san iya abunda zai iya samunki ba, kuma nan wa zai kula da ni idan ki ka tafi?”
“Farida ta min
alkwarin kula da ke, idan har za ki iya hakurin ciwon nan na ki zauna asibiti na tsawon wata biyu, zaki iya hankurin rashin ganina na wata daya, idan na samu lokaci sai na zo na ganki ni dai amincewar ki na ke bukataka kamin nai ma maman salma magana, ina
son lafiyarki Nana, sai da lafiyarki zan iya neman dangina, hankalina kuma ya kwanta, dan Allah ki amince Nana”
Na fada ina kama hannayensa sai naga yanayinta da fuskarta sun canja.
“Ko daga nan zuwa wani gurin za ki je, ina jin tsoro Ataa sai naga
kamar ba za ki dawo ba, bana son ki zo yi ta wahala da gawa waya sani ko ba zan kai wani lokacin ba”
“Da ba zaki kai wani lokacin ba, da baki rayuwa bayan wannan lokacin da akai miki tiyata ba, kuma babu wanda yasan rayuwa da mutuwar wani sai Allah, ki
na karya min guiya, ki rika nuna min cewar zamu rayu ni da ke ko da mu kai muka rage a duniya, dan Allah Nana ki barni nai wannan jihadin, ki bar ni na samun wannan faricikin da ladar”
Magangannun nai ta mata ina lurar da ita har na samu ta aminta duk d
a kasancewar ba ta so haka ba. Bayan sallah azahar na ja Farida muka kama hanyar gidan maman salma da shiga mu kai sallama muka gaisheta, sannan Farida ta koro mata da bayanin da ke tafe da mu, wani abun mamaki da jindadi sai tai murna da hakan har take l
abarta mana cewar daman ana neman mai aikin a wani babban gidan masu kudi da ke Abuja, sai dai tace ba zata yi komai ba har sai ta zo gurin Nana ta ji ta bakinta dan
tabbatarwa, ni kuma na ce mata na yarda ta zo su yi magana, sallama muka mata muka kamo ha
nyar gida wani dadi ya lullube ni na soma yarda da cewar kukana ya kusa karewa...
ALIYU POV.
Zai iya rantsewa a rayuwarsa be taba haduwa da wata mace yar talakawa mai karfin zuciyar da ta iya tsaya gabansa ta fadawa Rahma magana son ransa ba sa
i yau, for the first time yau wata ta ciwa Rahma mutunci ya kasa yin komai, har yanzu fuskarta yake gani irin kyau da haiya ta yai arba da shi a fuskarta a yau ko a mafarki be ci karo da macen da kallonta ya saka shi faduwar gaba ba sai yau. Kalamanta da ď
ai-ďaiya suke masa yawo a kunne, kalma zalinci ita kalma ta biyu daya tsana bayan talauci, yes he's rich and he know be zama dole ya taimaki kowa da dukiyarsa ba, amman yai wa kansa alkwarin ba zai taba yarda dukiyarsa ta saka ya zalinci wani ba, ko da kuw
a talakan daya kyama ne. Yasan yadda lafiyata take da muhimmanci tun daga lokacin daya fara neman ta matarsa yana jin tsoron rasa ta a ko wace dakika ita kadai da take a natsayin matarsa hakan yasa shi fahimtar Ataa wacce ita kuma take zancen mahaifiyarta.
Haka sukai tsaye a falon bayan fitar Ataa har na tsawon mintuna talatin ba tare da kowa ya ce uffan ba, daga Aliyu har Rahma da Doc Asim dake ra sake saken yadda zai kare kansa. Rahma jiran take mai kare yace wani abu tun daga lokacin da Ataa ta fada ma
ta ba daidai ba, amman bata ji yace komai ba, sai ma rike mata hannu da yai a lokacin da zata mareta. Aliyu kuma yana ta jiran abunda zai fito daga bakin Doc Asim amman ya kasa magana kamar an daure shi.
“Kodar mahaifiyata ka cire aka sakawa Rahma ba t
are da sanin ba?”
Doc Asim yai saurin kallon Aliyu.
“No karya ta ke yi? Ita ta siyar da kodar da kanta, zan iya nuna maka shaida ma, ita ta siyar da kanta”
“Mi zai saka tai maka karya? You know what na yarda da komai amman ban yarda da zalinci ba
, ban yarda na zalinci wani na kuma na kwanta nai bachi mai dadi ba, dan ina neman lafiyar Rahma ban ce ka zalinci wata ba, na fada maka ka nemo wacce zata saida zan biya ko dala dubu nawa ne, amman ban ce ka cire ba tare da sanin mai ita ba”
“Amman Dea
r ai yace siyarwa tai...”
“Silent”
Ya fada sai dai ba cikin daga murya ba, tare da dagawa Rahma hannun wacce ke kokarin kare Doc Asim da nuna abunda yai ba dai-dai ba ne.
“Ka bani amsa da saninta ka cire ko ba da saninta ba”
“Ni ban san wannan
yarinyar ba”
Shine kawai abunda Doc Asim ya fada ya dauki akwatinsa ya fice a fusace har gumi na karyo masa idonsa su yi ja alamar ransa ya bace sosai. Yana fita Rahma ta kalli Aliyu sannan ta nufi upstairs cikin bacin rai da zazza6in da da ke kokarin
rufeta. Zaunawa Aliyu yai saman cushion yana ta auna irin zalincin da akwai wa Ataa idan har ta tabbata Doc Asim ya cirewa mahaifiyarta koda ba tare da sani ba, mikewa yai tsaye ya bi bayan Rahma a bedroom dinta ya same ta zaune bakin gado tana waya be san
me ta fada masa ba, kuma be san da wa take wayar ba, sai dai yana alamar kuka da hawaye a idonta, saurin fisge wayar yai ya kashe kiran sai ya kashe wayar gaba daya, ya zauna kusa da ita.
“Kin sani idan kina ciwo bana son kina wani dogon motsin, za ki
yi street kanki ne kawai”
Kallonsa tai da duba mai mai ma'anoni da yawa idonta har ya fara ja.
“Miyasa zaka yarda da yarinyar nan ka karyata likitan da ya shekara biyar yana maka hidima?”
Be ce mata komai ba, ya kai hannunsa ya share mata hawaye
nta sannan ya rika fuskarta da hannayensa biyu yana mata magana a hankali yadda hankalinta zai kwanta.
“Za mu magana daga baya, for now ina son ki kwanta ki huta, and promise me za ki yi bachi?”
Ta dauke kai tana hadeye yawu. Sai ya jata zuwa kirjin
sa ya rumgume, ya dan kishingida da gadon yana ta kallon sillin kamar mai tunani. Ya dauki awa daya a haka sannan ya soma jin sauka numfashinta mai zafi alamar bachi ya dauke, sai ya kwantar da kanta saman fillo ya lullube ta da blanket ya mike a hankali y
a fita daga dakin dare da jan kofar dakin a hankali.
Fitowa yai daga cikin gidan gaba daya, tun kan ya karasa gurin motarsa ya danna key motar ta bude, yana shiga yai nata key tun kan ya kai gate mai gadin ya bude masa gate din yana daga masa hannu, ko
kula shi be yi ba ya dauki hanyar gidansu wato gurin Momy, as usual idan babu Nasir ko Mama Fulani a kusa da shi Momy ce abokiyar shawararsa, ko da ma suna nan wani lokacin ya kan kirata a waya ya shaida mata, yau ma yana da bukatar fada mata abunda ya fa
ru yaji nata tunani. He arrived in time a daidai lokacin da Momy ta kara Daddy ya shiga mota tana tsaye tana kallon yadda mai gadin gidan yake rufe gate, sai ta ya sake budewa da sauri jikin har bari yake, ashe Aliyu ya hango tafe. Murmushi tai domin ta sa
n a duk duniya Aliyu kadai ya isa ayi masa haka a gidanta, baya danna horn sau biyu kuma bayana son jira saidai a jira shi, idan kana son kaganin bacin ransa ka kwada bata masa lokaci ko kuma saka shi jira na rashin dalili.
Tana ta kallon dan na ta har
ya faka motarsa a inda ya fi masa soyuwa a harabar gidan sannan ya fito fuskarsa ba yabo ba fallasa kamar kullum ya doshi inda