Showing 126001 words to 129000 words out of 237425 words

Chapter 43 - ZAKI COMPLETE

mikewa tsaye, shi kuma ya juyo ya kalleta.

“Akan me za ki nemi takurwa yar mutane? Ce miki nai ina sonta? And what makes you think abunda kika saka ka mata zai sa na canja na fasa taimakonta ne? Wallahi abunda kika yi be kara min komai ba sai taus

ayinta, yarinyar da ke jinyar mahaifiyarta saboda ke a maimakon ki tausaya mata ki taimake ta sai neman saka ta kike a cikin wata fitinar, matace ke ina martaba ki ina mutuntaki ba zan bari wani ya zaga miki rigar mutunci ba, kamar yadda ba ba zan bari ki

yagawa wani ba wanin ma kuma wacce ta taimake ki rayuwarki”

Ya fada cikin daga muryar fuskarsa a hade kamar bakin hadari.

“Abunda kake yi abun kunya ne Aliyu namiji mai daraja mai kima da mutumci kamar ka ace yana bibiyar wata banza yar talakawa yar

bara a titi wacce bata san mutuncin kanta ba, namiji nawa na kwanta da ita lokacin da take bara baka sani ba, amman abun kunya har ka dauki robe da cake ka bata zobe ma mai tsada wanda na yi imani bata taba ganin irinsa a rayuwarta, ka yi kuskure Aliyu ku

ma kana shirin aikata kuskure idan har ka ce zaka hada ni kishi da wata kazama wacce ba a san ubanta ba balle asalinta, wannan ne kuskure mafi girma da zaka aikata hada ni kishi da yar talaka, abunda za ka yi ka burgeni ka nemo yar wani minister ko yar wan

i mai ji da kansa ka hada ni shi da ita amman ba yar iska yar gantali a titi ba, wacce ta kwana a titi yan sanda suka gama amfani da ita Doc Asim ya gama amfani da ita kai kuma yanzu kake son kawota cikin gidanka”

Tana fadar hakan ta juya sai Aliyu ya j

uyo da ita da dukan karfinsa yana kallonta naman fuskarsa har rawa yake saboda bacin rai.

“Idan zan so Ataa ba zan so ta dan wani abu nata ba, kamar yadda ke ma ban so ki dan wani abu na ki ko na gidanku ba, ban taba son mace dan wani abu nata ba kin f

i kowa sanin wannan”

“Ba haka ba ne, ka so ni a yadda na ke saboda ka san cewa baka haihuwa saboda kai juya ne, so that sai mu taru mu mutu a haka, yanzu kuma kana ganin ka gaji da ni mahaifiyarka ta saka ni a gaba shine zaka fara son wata ko? Watan ma

yar titi wacce kai da kanka kake nuna mata kyama amman mahaifiyarta take kokarin gyarata saboda kana sonta, daman na sani yan'uwanka gaba daya ba so na suke ba”

“Ba ki da kunya Rahma, kina magana kamar ba ki san da wanda ki ke magana ba, mi yake damun k

i ne?”

“Abunda yake damunka Aliyu, abunda ya saka ka canja ka koma kamar mahaukaci akan wata dabba can, shiyasa na gano matsala da kai idan har zaka iya runtse ido a halin da muke ciki ka ce zaka min kishi to sai an bata guri ta zo ta zauna da kai fa ha

ihu na gani”

“Za ki yi nadama matukar kika ce Zabin Rai za ki bi, ina daga miki kafa ne saboda sanin abunda yake tare da ke, ina tausayin ranar da za ki yi nadama Rahma, wulakanta dan 'adam ba shi da kyau musamman wanda ya taimaki rayuwarka”

Wani kal

lon mamaki tai masa

“Haka ka fadan to sai kaje ka aureta ka zauna da ita, daman ai haka halin ku maza yake”

Ya nufi hanyar dakinta a fusace tana wugar da zoben.Aliyu ya juyo gurin Muneera ya kwada mata mari mai kyau sai da ta jishi har cikin kanta.

“Karki sake zuwa ki ce za ki taba yarinyar mutane, duk wani abu a tsakanina da Rahma ne babu ruwanku a ciki”

Ta dafe kuncin hawaye na sauko mata tace.

“Saboda wata banza yar talakawa za ka mare ni Aliyu?”

Kara mata marin yai a dayar fuskarta s

ai ta hada hannu biyu da dafe fuskarta tana fashewa da kuka.

“Talaka ai ta muku rana, ko ba kodar talaka ce a jikin yayarki ba? Ku ba ku san darajar talaka ba amman kun iya wulakanta shi? Bana son wuce gona da iri, ki tsaya a matsayinki na kanwar matat

a babu ruwanki da rayuwarmu, kuma ki fice min daga gida yanzu nan”

Kamar kyaftawar ido haka ta fice daga falon har lokacin da ta kai gurin motarta bata dauke hannunta daga kan fuskarta ba dan har lokacin bata daina jin zafin marin da yai mata ba.



Rahma na shiga dakinta ta dauko makullin motarta da mayafinta ta fito cikin fushi ta fice daga gidan.

A gidan Aliyu ya kwana cikin bacin rai, be taba jin zamansa da Rahma ya zame masa matsala ba irin yau, iyakar hakuri zama da ita yana yi iya

kar kauna da kulawa yana nuna mata amman bata gani, abu kadan ta shafa mayafi zuwa gidansu bayan ta sani kuma ya sha fada mata ba komai ake fadawa iyaye ba, ba kuma komai ne zaka dauka kace ka tafi gida kai ka yi fushi ba, yawan fushi da kai karar miji yan

a raba kan in-laws da rashin ganin kimar juna da ganin kamar wani na dannen hakkin wani.

Tashi yai zaune yana murmushi ya shafa kansa.Gorin haihuwar da tai masa ne ke bashi dariya daman mace haka take idan ma ita ke daukar dawainiyarka wata rana sai ta

goranta maka balle kuma ace lamari ne irin wannan babba. All these years da Aliyu ya dauka na zama tare da Rahma bayan san matsalar daga ita ne ya juyar izuwa ga kansa dan ta samu salama yau shi take gorantawa, sai dai yasan saboda kishi ne komai tai sabo

da shi ne that's why yake daga mata kafa. Tunawa da zancen roben dazun yasa ya tashi ya sauka kasa ya je gurin data jefarta zoben yana duba har ya hango shi yaje ya dauka yana kallonsa.

“Waya bata zobe?”

Shine abunda ya fara zuwa masa a rai, Doc Buka

r ya fara tunanin sai kuma yake ganin kamar Doc Bukar ba zai yi wannan shirmen ba, ba kawo Muhseen a ransa domin ya san Muhseen ya bar garin nan, bayan su baya tunanin wani kuma sai dai idan a boye yake shi be san da shi ba.

Da tunanin wanda ya bata zobe

n ya kwana a ransa, da kuma tunanin zuwan Rahma gida, shi dai ya daukarwa kansa alkawarin ba zai je bikonta ba domin ba wani abun ya aikata mata da zai sa ta dauki kafa ta tafi gida ba, duk abunda ya fada ya fada nata ne dan ta gyara, beside shi ba son At

aa yake ba to miye abun kishi a ciki after ta san halinsa ba kula mata yake ba ita ma wannan saboda daliline dalilin ma nata.

Misalin takwas da rabi na safe ya shirya cikin kananna kaya ya sauko downstairs ya nufo dinning area, rasa yai mi zai a gurin

sai kawai ya koma sama ya dauko keys din motarsa ya shiga ya dauki hanyar arkilla. Ataa ce kawai a falon tana gyara Momy kuma tana kitchen, ba karamin dadi ya ji na samun Ataa ita kadai a falon ba, daman yana son ya tambaye wanda ya bata zoben.

“Ina kw

ana”

Ta dan risina tana gaishenshi be amsa ba har ya karaso kusa da ita.

“Ataa akwai wanda kike so a ranki?”

Wani kallo tai masa kamar bata fahimci abunda yake tambayarta ba.

“Kina da wani a ranki wanda kike so? Fada min karki baye komai”

Kasa tai da kanta tana watsa da kyallen hannunta kamar mai tunani.

“Kamal....”

Aliyu ya dade yana kallonta kamin ya bude bakinsa ya ce.

“Kamal kike so?”

Ta yi shiru bata sake cewa komai ba. Sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro zoben ya nuna ma

ta.

“Shi ya baki wannan zoben?”

Sai tai shuru bata ce komai ba.

“Ataa ke nan har kin san soyayya?”

“Ba son sa na ke soyayya ba, kawai dai ina jindadi idan na tuna dan zaman da muka yi lokacin da muke abuja, ba ya kyamata kuma yana kokarin sakan

i nishadi”

“Lokacin da yai miki wacan siyayyar ne ya siyo miki wannan zoben?”

“Ba shi ya ba ni ba”

“To waya baki Doc Bukar Ko Muhseen ko wani dabam?”

Shiru Ataa tai tana kallonsa kamar wata kurma.“Minene?”

Momy ta tambaya tana fitowa daga ki

tchen ta nufo inda suke.

“Je ki kawo min ruwa na sha”

Ataa ta nufi kitchen din shi kuma ya matso baya ya zauna saman kujera yana gaishe da Momy.

“Lafiya kalau, mi kake tambayarta?”

“Jikina na ga tana aiki da safen nan”

“Eh nayi na yi ta aj

e tace tana son ta yu shiyasa na kyaleta”

“Okay”

Ya fada numfashi na tsinkewa shi dai be jidadin jin wani Kamal a baki Ataa ba domin yana ganin kamar ba soyayya ce abunda ya dace da ita a wannan lokacin ba, bata san ma miye duniya ba amman suna kokar

in chusa mata wani abun da be dace da ita ba. Kallonta yake har ta kawo masa ruwan a kofi ta mika masa.

“Shaye su ni ba a zuba min ruwa a kofi, je ki dauko min na gora”

Momy tace

“A a bari ni na dauko maka, ai bata san kan gidan ba”

“No Momy

ba ri na dauko”

Ya tashi ya nufi kitchen din yana jin wani sabon haushin Ataa na lullube shi domin ya fahimci sam bata san kanta ba.

ATAA POV.

A haka muka tafi be sake tambayata cewar waya ba ni zoben ba, ni kuma ban damu sai na sanar da shi

ba, wata kila ma idan ya san gaskiyar Muhseen me ya bani zai rika ganin laifina ne ko kuma wani fadan ya shiga tsakaninsu, domin na lura ko kadan Aliyu baya son ina kula kowa ciki kuwa har da Doc Bukar da nake ganinsa da kima da mutunci, idan ya tarar ina

fira da shi ko wata gaisuwar ta hada mu sai ya hade rai ya bata fuska, ko kuma yai ta fushi da ni, ko da yake yanzu fushin nasa ya zame min jiki, ban zan iya fadar laifin da nai masa ba, amman tun daga lokacin da Momy tai masa fadan nan akan matarsa washe

n garin daya dawo ya tambaye waye ya bani zobe sai na lura da daina sake min kamar da, ni kuma ban damu ba daman ai matar da ta zo min fada ta fada min cewar na shiga hankalina domin be son talaka, daman kuma ni mi zai kai ni sakewa da mutum kamar Aliyu ma

i ji da kai da ganin kowa na kasa da shi.Satin Nana biyu a asibitim suka sallame ta a tsawon satin biyu da muka yi a asibiti babu ranar da ba ma gaisawa da Muhseen a laptop tun ina tsarguwa har na soma sabawa, a kullum kuma matar sai ta ba ni cake tace dag

a shi ne. Sau daya ya kawo mana ziyara a asibiti ba tare da sanin kowa ba, domin sai da ya gargade ni akan kar an fadawa Momy cewar ya zo garin nan wai aiki ya zo yi ba zai samu bi ta gidanta ba, ni kuwa a nawa tunanin ya ki sauka a gidanta ne ko yaje sabo

da Aliyu. Idan na kebe ni kadai bana tunanin komai sai Kamal dan nishadin da muka yi tare da labarin rayuwarsa da ya soma ba ni, tun bayan dana baro gidansu ban sake saka shi a idona ba, hakan kuma ba karamin haddasa min damuwa yai ba, ko yana ina yanzu? A

wane hali yake oho? Wata kila ma ya manta da wata yarinya mai irin sunana. Daddy Siyama sau uku ya zo ganin Nana yana da son mutane sosai ya nuna mana kulawa har ya dauki kudi ya bawa Nana bayan irin dimar da Momy take da mu.

Ranar da aka sallamo Nan

a asibiti da kafafunwanta take tafiya, Momy na tare da ita yayinda ni da Siyama muka yi gaba muna tafiya, motar Amina muka shiga ni da yan uwanta Momy da Nana kuma suka shiga motar Aliyu. Na yi zaton Clapperto road zasu nufa da mu domin sauke mu acan sai n

a ga an nufo gidan Momy da mu. Aliyu ne ya budewa Nana mota da kansa ta fito tana takawa a hankali tana bin bayan Momy wacce ta wuce gaba zuwa cikin falon. Ina lura da yadda Nana take karewa ko'ina gidan kallon, wata kila ita ma ya burge ta kamar yadda ni

ma burge ni a farkon zuwana.

A falon muka zauna Momy na ta murmushi ta ce

“To Nana kin ga gidanmu idan kin dan huta za ku koma bq na saka an gyara muku can za ku zauna ke da Ataa, kuma dan wajen Fulani yace zai nema mata makaranta nan kusa sai ta fa

ra zuwa islamiya, ta bokon ma za a samu wanda zai fara koya mata a gida kamin a saka ta makaranta”

Ban san lokacin da idona ya cika da kwalla ba, na dade ina jiran zuwan wannan ranar da zan koma makaranta na samu ilimi, amman ban samu ba. Kallon Aliyu n

ai sai naga yanayi ma Nana murmushinsa kadan muna hada ido ya murtuke fuska kamar be taba dariya ba wai kar na ga damarsa.“Na gode”

Na fada murya kasa kasa. Be amsa ni ba sai ma dauke kansa da yai daga barin kallona ya kalli wani gurin dabam.

“Kana t

a hidima da mu, bayan nema mana magani yanzu kuma kun kawo mu a muhallinku, kuma za ku nema wa Ataa karatu? Abunda na dade ina mata burin samu amman na kasa bata, ban tana haduwa da mutane masu karamanci da sanin darajar dan 'adam ba irinku, taimakon da ku

ke mana ya yi yawa da me za mu saka muku?”

Cewar Nana tana hawaye kamar yadda nima na ke yi. Momy ta yi murmushi

“Ba komai ai yi ma kaine, lokacin sakarwa zai zo lokacin da zan nemi wani abun daga gareki ina fatar ki amsa min da hannu biyu”

“Zan

karba miki ko mienene a duniyar nan, matukar ina da iko da karfi akansa, ku ne mutanen da kuka mai mu mutum, ban tana mafarki haduwa da ku ba, kuma ba ku taimake ni dan ku samu wani abun daga gareni ba”

Har yanzu Nana hawaye take hawayen jindadi da fari

nciki. A nan muka ci abinci suka koshi sannan Amina ta raka mu zuwa bq din, wani bangare ne na gidan da aka kawata fulawoyi sam ba zaka dauka cewar bq bane sai idan an fada maka, dan madaidacin daki ne mai bandaki a ciki, haka aka jera dakunan har biyar ko

wa ne da bandaki a ciki, sai dai na mu shi aka sakawa katifa ta labule da zanen gado aka gyara ko'ina tas kamar ba bq ba.

ALIYU POV.

After Nana ta huta, Amina ta nuna musu bq ita da Ataa. Sai ya rage falon daga shi sai Momy.

“Momy Rahma bata

gida har yanzu”

Kallon mamaki Momy tai masa.

“Ban gane ba?”

“Tun wacan lokacin da muka samu misunderstanding akan matsalar Ataa shikenan tai fushi ta tafi gida”

“Kana nufi duk tsawon lokacin nan bata gidanka?”

“Tana gidansu”

“Kuma iyayen

ta ba su kira sun bincike matsalar ta ba?”

“Da za su kira ai da sun kira ko kuma Abbah ta ya kira Daddy ya ji ko mienene matsalar”

“Hmmm Allah ya kyauta, abunda suke yi ma yarinyar suna ganin kamar so ne ko gata Wallahi suna lalata mata rayuwa ne kaw

ai, abun kadan yarinya tace ta tafi gidansu sai kace wata mai shan nono”

“Ni dai Momy so na ke a shirya mu da ita na yi alkawarin ba zan je bikonta da kaina ba domin ni ne mai gaskiya”

“Ai da ka bi ta tawa ka barta can gidansu ta dandana zaman gidan

ta ji idan da dadi kamar na gidan miji, kishi hauka ne ko cewa kai tana son Ataa laifi ne balle baka furta ba, haka ake rayuwa”

“Momy ni dai ayi hakuri a dawo min da matata dan Allah”

“Na ji sai Daddyn ka ya dawo ai ko?”

“Tau na gode”

Ya fada,

ba dan komai yake son a dawo masa da Rahma ba, sai dan yasan ita kanta tana cikin damuwarsa a yanzu duk kuma abunda ta aikata saboda shi ne, domin tana son sa tana kishinsa ne, after that yana son matarsa a kusa da shi shi kanshi ya san yayi hakuri iya hak

uri har na sati biyu ba tare da Rahma a kusa da shi ba, hakan na matukar damunsa domin ya san ita kadai ce a duniyar ke iya yaye masa wannan kishin da yake ji matukar ba alfasha zai aikata ba.

Husna ce ta fito manne da waya a kunne tana tambayar Momy i

na Ataa.

“Wake nemanta?”

“Ya Muhseen ne ya ce a akai mata waya”

“Tana bq”

Momy ta bata amsa sai ta nufi hanyar fita daga falon, Aliyu ya bita da wani kallo kamar ita ce Ataa.

ZAKI

By Khadeeja Candy

37...

“Momy idan ba ki takawa Muhse

en burki tun yanzu ba, zai iya wuce guri fa”

Momy ta masa kallon rashin fashimta.

“Wuce guri kamar ya?”

“For god sake Momy taya zai rika nunawa yarinyar wata soyayya a yanzu? Allah kadai yasan irin kalaman da ya ke furta mata”

“Shi kiranta a w

aya har wani nuna soyayyah ne? Idan ma haka din ne ai sonta yake sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login