Showing 84001 words to 87000 words out of 237425 words

Chapter 29 - ZAKI COMPLETE

da ita gaba daya kamar yadda mahaifiyarta ta fada mata a lokacin data labarta mata gaskiyar cewar matsalar d

aga Aliyu ne a wacan lokacin kamin rashin lafiyar ta kamata. Sai dai me wata kila idan babu Aliyu a rayuwarta ba zata iya rayuwa ba, wata kila ba zata iya komai idan babu shi ba, domin ta shaku da shi kuma tana kaunarsa irin kaunar da ba zata iya misaltaw

a ba.

Aliyu be juyo ba har sai da yaji an taba kofar dakin an turo an shigo. Momy ce ita da siblings dinsa. Yayi kokarin boye damuwarsa amman ya kasa har sai da Momy ta karanci yana cikin damuwar a fuskarsa. Ita kuma tai saurin share hawayenta tana kok

ari kirkiro murmushi, tsaye sisters dinsa sukai suna mata sannu Momy kuma ta zauna a kujera tana ta duban yanayinta da na Rahma. Aliyu ya yi farincikin ganin Momy domin be tsammaci za tai saurin zuwa a yau ta duba Rahma ba saboda yawan complain din da take

cewar Rahma bata son zuwa inda take, sai dai be yi mamaki ba dan yasan halin Momy da dattako da kuma maida komai ba komai ba.

“Yanzu kuka zo?”

Aliyu ya fada yana kai hannu ya riko hannun Inteesar, sai ta dawo kusa da shi ta tsaya tana dariya.



Tun dazun muka zo, ai na saka Siyama ta kiraka baka daga ba”

“Na ga kiranta amman ban dauka tare ma muka zo ba, na dauka rokonta ne ya tashi”

Sai dai duk sukai dariya ban da shi da yai maganar, sam ba zaka kalleshi ma ka ce shi yai maganar ba, daman

haka yake ko abun dariya ya fadi na kasafai yake dariyar ba.Bayan sun gama ganinta Momy ta kallesu ta ce.

“To ai sai ku wuce ku koma, kar likitocin su zo suce mun yi yawa, kuma mun baro Fulani ita kadai gashi beta gama fucewa ba”

Aliyu ya kalleta ka

mar ya tambayi abunda akai mata har Momy take fadar hakan sai kuma wata zuciyar ta hana shi. Rukaiya ce tai kwafa

“Wallahi kwata kwata Kamal ba shi da mutunci kuma ba shi da tarbiya”

A take zuciyar Aliyu ta kwadaitu da son jin abunda ya faru amman y

a kasa tambaya har sai da Zee da ke son ta ji labarin ta tambayi Rukaiya.

“Mi Kamal yai hala?”

Rukaiya da Maryam ne suka labarta abunda ya faru a nan Aliyu ya ji komai, wayarsa ya ciro kamar be damu ba ya nufi kofa rike da hannun Inteesar ya fice. S

ai da ya fito daga ward din sannan ya turo Inteesar ta kira masa Zee, ita da Inteesar har a rigengen zuwa suke domin sun san Aliyu baya son jira, kuma abu kadan ya saka ransa ya bace.

“Zainab So na ke ki kira min Kamal ki tambaye shi wace asibiti ya ka

i Ataa”

“Ya Aliyu bana da number Kamal”

Ya mika mata wayarsa ba tare da ya ce mata komai ba, tana karba sai taga number Kamal a sama sakawa tai a wayarta ta kira bugu biyu ya daga.

“Hello Kamal ina wuni”

“Lafiya kalau wake magana”

“Zainab c

e, wai Ammy tace a tambaya wace asibitin ka kai Ataa”

“Ammy? Ko Mama Fulani dai”

“Ammy dai”

“Perry Hospital female ward room 104”

“Thank you”

Tana fadar hakan ta sauke wayar ta yi karya da Ammy ne domin ta lura da Aliyu baya son asan shi ya

saka ta kira, da acce yana so da shi da kansa zai kirashi tun da abokinsa ba sai ya saka ta ba.

“Ya ce Perry Hospital female ward room 104”

Ta fada tana mika masa wayarsa, karba yai ya saki hannun Inteesar ya fice daga gurin. Ita da Inteesar suka da

wo dakin da Rahma take.

“Ku wuce kawai gida, ni zan tsaya a nan sai an jima Dan wajen Fulani zai maida ni gida”

Sai da suka mata Allah ya sauwake sannan suka fita. Bayan sun fice ne Momy ta kalli Rahma da ke cikin damuwa ta ce.

“Ciwo fa ba mutuwa

ba ne, dan ba ki da lafiya ba shi yake nufi zaki mutu ba, ko babu kodar a jikinki idan Allah ya so sai ki ga ya raya ki”

“Ba neman lafiyar ne abunda ya dame ni yanzu ba Momy, haihuwa ce abunda ta dame ni a yanzu, ina son na haihu kamin na mutu”

“Duk

a dai na Allah ne, kuma idan yace yanzu abu ya kasance za ki ga ya kasance”

“Wata kila da matsalar daga ni ne da zan iya samun sauki ko kuma wata mafitar, amman matsalar daga Aliyu ne na san ba zan taba samun waraka ba”

Momy ta kalleta irin kallon na

n na ban fahimci zancen ki ba.

“Matsalar daga Aliyu ne? Kamar ya?”

Rahma ta yi shiru bata ce komai ba, domin ta fahimci be fadawa Momy ba. A take hankalin Momy ya tashi fiye da da, domin a da tana daukar daga shi har Rahma ba su da matsala kamar yad

da yake fada mata likitoci sunce yanzu kuma Rahma ta ce matsalar daga shi ne, amman miyasa be taba fada mata ba? Daman Rahma ta san da wannan ta rufa masa asiri take zaune da shi a haka ko kuwa daga baya ne abun ya bullo? Anya Mama Fulani ta sani ma kuwa?

Har Momy ta bude baki zata sake tambayar Rahma sai ga wani Doc ya shigo tare da nurses kusan biyar suka hau duba Rahma suka bata magani sannan suka bawa Momy takardar sallamarta domin su a gurinsu ta ji sauki tun da ta farfado kuka bata jin ciwon komai san

nan kuma an riga an san matsalar koda ne, sun kuma dorata akan magani. Daman haka suke yi sai dai idan mutum yana son ya cigaba da karbar magani a asibitin sai ya bukaci su barshi yai ta biyan kudi yana karbar magani har ya kare. Momy ta yi kokarin nuna fa

rincikinta duk da irin tashin hankalin daya same ta na jin gaskiyar maganar cewa matsalar haihuwar daga Aliyu ne, har ga Allah ta jidadin samun lafiyarta domin ko bata san inda Rahma ta fito ba za tai farincikin samun lafiyarta a matsayinta na musulma ball

e kuma matar danta ce dan ta take aure. After like thirty minutes da fitar likitan Mommyn Rahma ta shigo da kanenta ai ko suka hau murna kamar su cinye Rahma sun jidadin ganin an sallame a take hakan na nuna jikin nata da sauki keman kuwa da kasancewar kod

ar na ta a kone yake.

“Mahaifinki ya ce ya saka cigiya a gurin likitocin daya sani a nemo duk inda koda take kuma ko nawa take za a siya miki, kin kwantar da hankali lafiya zata samu In-Sha-Allah”

Mommyn Rahma ta fada tana dariya sai dai ita Rahma b

ata wani farinciki sosai, domin tana cikin damuwa a yanzu. Momy ce ta kira Aliyu ta fada masa an sallami Rahma kuma ya zo ya maida ita gida, da murna ya amsa mata sannan tai hanging call din ita da farinciki tana kallon Rahma, sannan gaisuwa ta biyo bayan

tsakaninta da Mommyn Rahma har suka dora da labari.ATAA POV.

Ban san adadin wannin dana dauka a sume ba, shin sumar ma nai ko kuwa dai wata duniyar na tafi na dawo domin Nana nai ta gani da kuma wata rayuwa da muka kai da ita a can baya, da kuma ganin

da cikin wani daki mai kamar na kasa ba kuma kasar ba, shin haka suman yake ko kuwa fitar hankali ne kawai daga jikin duk ba zan iya tantancewa ba. Da wani irin karfi marar misaltuwa na ji na dawo duniyar motane da dabbobi har ma da sauran hallitu, duniyar

da ke cike da kazanta da gurbatacciyar rayuwa da ba kowa ke tsira cikinta, wasu abu nake gani su ba mutane ba kuma su ba aljannuna ba, ganina nai kasa bana iya tantance ko mienene sai dai ina ganin kan abun yana yawa kuma suna sanye da fararen kaya. Daga

bakina har hanci da ido numfashi suke fiddawa da karfi wani kuma na shiga da karfi, wani abu ne a kirjina kamar dutsin guga da zarar numfashin nawa yai kasa sai su goga shi da dan'uwansa su manna min shi a jiki sai na ji makamancin abunda na ji dazun, haka

sukai ta min har numfashin nawa ya daidaita, sai sannan na soma ganin likitoci su uku ashe mutane ne ba aljannuna ba kayan likitocin na su ne nake gani farinsu kamin idon nawa ya waye.

“La'ilaha illallahu Muhammadu Rasulullah Sallalahu Alaihi Wassalam



Shine abunda ya fito daga bakina sai na lumshe ido ina fitar da numfashi a hankali. Dayan daga cikin su ne naji yai hamdala ga Ubangiji da alama shi din musulmi ne. Sai na ji dayan ya kira sunana da hausar da da bata fito sosai.

“Aasha”

“Na'am”

Na amsa ina kallonsa sai dai muryar tasa har yanzu kasa kasa nake jinta. Dauke ni sukai daga saman wannan gadon suka dora ni akan wani suka turani zuwa wani dakin na musamman a akan gadon dakin suka dorani sannan sannan suka saka min drip dayan kuma ya

saka min bandeji a bayan kaina, sannan suka juya suka fita. Lumshe ido nai ina kokarin tuna abunda ya faru sai na ji an turo kofar an shigo hakan yasa na bude idona sai na ga Kamal cikin shiga ta manyan kaya ya doso inda nake cikin yanayin damuwa.

“Ata

a”

Na kalleshi ina kokarin amsawa sai ya kai hannunsa ya taba jiki.

“Kina jin wani abu yanzu?”

“Bana jin komai”

Murmushi yai ya gyara min kaina da gashina.

“Sannu”

Na gyada masa kai.

“Likito ci sun ce abarki ki yi bachi, zan je gida

na dawo ke kuma ki samu bachi kinji”

Nan ma kan na gyada sannan na ce

“Na gode”

“Ba komai Allah baki lafiya”

“Amin”

Na amsa cike da nauyin baki sannan ya juya ya fita, ni kuma na lumshe idona bachi wahala yai gaba da ni. Wata kila na kai wa

biyu ina bachi kamin na farka, idona na fara budewa ina ta kallon farin silin dakin warin asibiti na soma ji kamin na kamshin turaren Aliyu ya biyo baya, dagowa nai kadan sai na ganshi zaune saman kujera yana ta kallona da cat eyes dinsa ko kyaftawa ba yay

i. Nima idon ma sakar masa ina ta kallon fuskarta, sai a yau ake kara tantance kyauwunsa hanci ya sauko sosai ga manyan ido masu daukar hankali.

“Ba na ce ki daina kallona ba?”

Yayi maganar kamar shi ba kallona yake ba, yana takura idan ana kallonsa

sai dai shi ya iya kallon wasu har sai ka soma tsarguwa. Rumtse ido nai ina turo baki, sai na ji an buge min bakin da sauri na bude idon na kalleshi yanayim yadda yake sai yai min kamar ba shi ya bugar min bakin ba sai dai hakan be hana na zaburo masa.

“Mi na maka zaka dake ni?”

Kallona kawai yai be ce komai ba ya mike tsaye yana saka hannunsa na dama aljihu sai kuma ya kai dayan hannun sai taba kaina.

“Me zaka mata? Bayan marin da Mama Fulani tai mata wani zaka mata kuma?”

Kamal ne ya shigo

hannunsa rike da leda yana fadin yana tare da doso inda nake kwance, Maganarsa bata hana Aliyu tana kan nawa ba, kamar ma be san da shigowar Kamal a dakin ba haka yai domin ko inda yake be kalla ba ni kawai yake kallo yana taba jikina da alama so yake yaji

idan jikin nawa da zafi ko sanyi.

“Ashe dai ba Kamal kadai yake iya kula yar aiki ba, idai ko haka ne ya kama ka sauke girman kan nan naka Aliyu”

Dagowa Aliyu yai ya kalli Kamal.

“Ba a fada min abunda zan yi sai dai ni na fadawa wasu abunda za

su yi, a kasa da ni kake Kamal kasan ma kasan takarmin kafata, ya zama dole ka min biyayya kuma ka kalleni da daraja ba zan sake musayar yawu da irinka ba”

“Daman ai ba ku saba ganin kowa da daraja ba, sai mai arziki ko wanda arzikin ya nemo saninsa, ba

n yi mamaki ba kai ma ai dan wajen Fulani ne”

“Yes dan ta ne, mai sanin darajarta ,kar bakinka ya sake ambatar sunanta idan ba haka ba sai ka yi nadamar saninta a rayuwarka, and i warned you karka sake shiga rayuwar yarinyar nan? Ashe kare ne kai marar

zuciya, yanzu kuma umarni na ke baka ka dauke ta ka maida ta gida kamar yadda ka dauko ta kamin nan da one hour”

Aliyu ya fada yana hada babban yatsansa da na uku sai suka bada wata kara kamar an yi tafi, sannan ya nufi kofa ya fice ransa a bace. Da wan

i kallon wulakanci Kamal ya bishi yana tsaki kamin ya juyo kaina ya kalli ya sakar min murmushi.

*.ZAKI

By Khadeeja Candy

27...

Kallo yake da mamaki yana kara gyara zamansa.

“Waya yaudare ki Ataa wane hali ne ya jefa ki ke da mahaifiyark

i?”

Hade kukana nai sannan na sauka daga kan gadon nai tsaye ina kallonsa.

“Na ji sauki za mu iya zuwa gida?”

“Gida gurin Mama Fulani ko gida gidanmu?”

“Ka dauke ni daga asibitin nan ya kai ni wani guri inda ba zan ji kamshi magani ba”

Ido

ya sakar min yana ta kallon fuskarsa na bayyana irin tarin tambayoyin da ke zuciyarsa. Sai kuma ya mike tsaye ya aje kazar a kan wani karamin dorowa ya fice daga dakin, ya bar ni ina ta zullumi da tunani wata kila idan an koma Mama Fulani korata za tai da

gaske ko kuma ta sake min wani dukan, ni da sam ban jidadin da Kamal ya kawo ni asibitin nan ba domin na san ba da amincewar ta ya kawo ni ba, kuma yadda Aliyu ya fusata ita zata iya fusata ko dan shi. Tare da wata likita mace ya dawo ita tai min umarni da

na zauna na zauna kamar yadda ta ce ta duba ni sannan tai rubuta a wata takarar guda biyu ta mika masa ta fice.

“To muje”

Ya fada yana kallona sai na wuce gaba ina ta jin kunya domin kaina babu dankwali gyale ma balle Hijab, ya dauko ledar kazar ya

biyo bayana, ni dai tafiya kawai nake ba dan inda zan biba domin ban san kan asibitin ba ina ta bin inda nake sa rai da zaton hanya ce har na fito daga ward din ina jin kunya sai dai na lura kowa be kula da ni ba.

“Nan za mu bi”

Ya fada yana daukar

wata hanyar dabam ba tare daya jira ni ba. Haka na bi bayansa har muka isa wani gurin da ake aje motoci ya nufi motarsa ya bude ya shiga ni kuma na bude front seat na shiga na zauna, be kalli inda na ke ba har muka isa gidan, a tsakanin asibiti da unguwar

tafiya ce mai nisa ban san ko'ina ba a garin Abuja balle na ce ga unguwar da muka fito ko muka wuce amman duk da tsaye tafiyar Kamal be ce min komai ba kuma be kalle ni ba har ya faka motarsa a harabar gidansu. Ban tana shiga gidan ba sai yau, shi ma gida

ne babban mai bangarori da dama domin shi ya fi part hudu duk ban tsaya na tantance ba sai dai shi gidan kasa ne ba kamar na su Mama Fulani da yake gidan sama ba. Shi ya fara fitowa ya rufe motar sannan na sauko daga motar na rufe na fi bayansa cikin rash

in sakewa da bakunta a wani gidan da ban ta6a shiga ba.

Yana gaba ina baya har muka isa cikin gidan, da kunya sosai na shiga cikin gidan, su kan na su gidan tsakar gidane farko kamin ka kai ga kofar shiga falon, wasu yan mata biyu na gaban murhu suna s

uya naman rago sai kuma wata dattijiwa mai kamar yar aiki tana yanka nama ita da wata mata da na ji Kamal din ya kira da Mama.

“Mama ga bakuwa na kawo muku”

Matar ta kalleni tana murmushi sannan ta kalleshi ta ce.

“Maraba da ita ina ka samo mana

wannan bakuwar?”

“A fara bata guri da abinci ta ci ta koshi zata ba ku labari da kanta”

“Ina wuninku”

Na gaisheta cikin ladabi sai ta amsa min tana ta kallona sai kuma ta kalli Kamal tai murmushi.

“Sai Soja”

Daya daga cikin yan matan ta fad

a tana dariya sannan ta doso inda nake ta rika hannuna nufi cikin falon gidan. Ba laifi an gyara ko'ina an kuma turare falon da turaren Awwaba ko ina sai kamshi yake irin na yan sudan. Da kanta ta zaunar da ni saman cushion tana ta kallon gashin kaina daya

bazu a jikina.“Karki ji tsoro babu abunda zai iya yi”

Kamal ya fada min yana murmushi ganin kamar hankalina ya tashi da jin kalaman Aliyu.

“Ya ce ka maida ni gida”

Kallona yai sai kuma ya kai hannu ya bude ledar hannunsa kaza ce mai zafi da yogh

urt ta sha mai har takardar da aka saka ta ciki ta narke da mai.

“Ban san me zan siyo miki ba shiyasa na siyo miki kaza yar marmari, wata kila kuma ba ki ci abu mai nauyi domin na ga jikin na ki kamar na baby doll”

Ya fada fuskarsa da murmushi yana

daukar cinyar kazar ya miko min, sai na kasa karba, na kuma kasa sakewa ba duk irin son nama da nake sai na ji ya fita rai, gaba daya hankalina yana can gurin Mama Fulani da Aliyu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login