Showing 9001 words to 12000 words out of 237425 words
zai mika maka hannu yace ka bashi tabbatas oa fishi kuma dan kana da shi ne ake zuwa nema a gareka amman mutane da yawa ba su fahimci hakan ba. Sai da na karasa
har bakin kofarta ina sallamar sannan ta amsa min na gaisheta ta amsa ciki ciki.
“Dan Allah turminku za ara min zan jajjaga tarugu ne”
A tsaye ta bar ni a gurin na kusan minti biyar tana ta kallon arewa 24 a karamin tv ta sannan ta dago ta kalleni.
“Gashi can gidan kin gama ki dauraye”
Ta fada min a cikin yanayin da ke nuna alamar bata son ara min kamar yadda take yawan yi min idan na zo nema abu, shiyasa bana son zuwa idan ba Farida ce a gidan ba ita ce mai min maraba wani lokacin har ta tay
ani dakawa duk kuwa da irin fadan da mahaifiyarta take mata na kin jinin abotarmu da take. Ni kuma babu wani gida da zan iya zuwa na roki abu kamar irin gishiri ruwa ko ashana ko daka wani abu kamar wannan gidan, domin duka gidanjen da suke kewaye da mu na
manyan mutane ne, a ina zan iya shiga roko ayi min kallo banza wani gidan ma ko gate din su ka taba sai mai gadin yace maka basa nan saboda kawai anga yanayinka na masu bukata ne.
Daf da zan gama jajjagen ne take tambaya wai ance maciji ya tsari mahaif
iyata, ni kuma na amsa mata na kuma bata labarin yadda abun ya faru har ma da taimakon da aka mana a asibiti, sannan na kwashe jajjagen na wanke mata turminta kamar yadda ta bukata na yi mata godiya na juyo na fito.
Hura wutar na fara yi na dora tukuny
ar na zuba mai da sauran abubuwa a take saboda tsananin yunwar da nake ji, haka nai ta bankawa girkin wuta har ya dafu na zubawa Nana a wani kwanon mai murfi Lukman kuma na saka
masa a nasa kwano na zubawa kaina, na kwashe saura a wani kwanon na rufe, sai
na zauna na tisa abincin a gaba na kasa ci babu komai a zuciyata sai kewar mahaifiyata da tunanin ruguje mana bukka da akai, a take na nemi yunwar na rasa, kuka ya maye min gurbinta har sai da Lukman din ma ya fashe da kuka ganin yadda nake ta kuka. Abinci
n na aje na shiga ciki na daukowa Nana riga da zane na saka a jakar da kudin suke ciki na jira Lukman ya gama cin abinci ya wanke hannunsa sannan na dauki abincin Nana muka fito bakin titi na tari Napep muka shiga ni da shi muka doshi asibitin.
A
LIYU POV.
Bachi Rahama take ta yi tun bayan sallah asuba har goma ta gota, a saman wani katon gado mai tsada da katifa mai kyau take kwance, ta lulluba da blanket mai laushi kamar kada, ta saba da hutu da jindadi haka take bachi har sai ta gaji dan kan
ta ta farka.
A lokacin Aliyu na falo zaune saman wata lallausar kujera rike da kofin tea laptop a saman ciyoyinsa yana duba yanayin yadda aikin gas din kamfaninsu na Abuja yake tafiya. Sanye yake da short jean da farar vest, a gabansa wani katon tv ne
mai dauki da farar baturiya tana watso labarai a channel din Al Jazeera. Wayar ce dake silent tai haske sai dai be lura ba, domin ya cire ringing din, baya so hayaniya ko kadan that's why he choose Abuja a gurin aikinsa to because its a quiet place for him
, ko da wani meeting din ne ya taso wanda yasan za a iya hayaniya da cece kuce sai ya tura abokinsa Umar. Be lura da kiran ba har sai da ya gama abunda zai yi ya juya da zimmar aje laptop din sai ya hango wayarsa tana haske, hannu ya kai ya dauki wayar gan
in Doc Asim yasa shi sauri picking.
“Hello Doc”
“Ranka ya dade ina ta kira baka dauka ba”
“Yeah ina wani aikin ne, sai yanzu na lura”
“Na kira na maka albishir ne cewar an samu Kidney din”
Kofin tea dake hannunsa ya aje ya mike tsaye da sau
ri cike da farinciki marar misaltuwa har ya saka shi kin yarda da maganar da Doc ya fara masa sai da ya sake tambaya duk kuwa da yasan be taba masa karya ba.
“Doc are you serious?”
“Wallahi da gaske nake, gani nan ma gurin Alhaji abunda muke tattaun
awa kenan”
“Wow gani nan zuwa”
Yai saurin waje wayar ya nufi bedroom dinsa cike da farinciki, labulayen dake fuskarta gadon ya bude sai ga hasken rana yana haske gadon kasancewar gaba daya gaban dakin glass ne. Jin hasken rana yasa ta
lunkumewa cikin
blanket tana bata fuska, sai ya zauna bakin gadon ya yaye blanket din ya dagota.
“Dear wake up yau ranar farinciki ce”
“Ba yau na ke birthday ba sai next month”
Ta fada ba tare data bude idon ba.
“Ba maganar birthday za ki yi birthday cikin k
oshin lafiya In-Sha-Allah, Doc Asim ya kirani ya fada min yana gurin Daddy suna tattaunawa an samu Kidney din”
Ba idonta kadai ta bude ba har da baki da da hancinta duk a bude suke jin wannan daddan labarin, da sauri ta kama hannayensa.
“Dear da gas
ke”
Ya gyada mata kai yana kallonta da cat eyes dinshi sai ta rungume shi da sauri ta fashe da kukan dadi. Dan murmushi yai kadan ya shafa bayanta.
“Congratulations Dear you save me”
“I said i would”
Ya fada yana dagota daga kirjinsa yana shar
e mata hawayenta.
“Tashi ki shirya zan kaiki gidanku ni kuma na wuce gurin Daddy na gana da likitan naji yadda za ayi”
“I love you”
Ta fada tana kuka, sannan ta daga daga jikinsa ta sauka ta shiga bathroom ta sauka cikin kankanen lokaci ta fito s
hima ya shiga yai ko daya fito har ta shirya, shima be dade gurin shiryawa ba dan ya matsu ya hadu da likitan.
“Idan munje can zaki karya promise?”
“Promise”
Ta fada tana saka bakinta cikin nashi, musanyar yawu sukai halshenta da nashi suka hada a
uratayya sannan ta sake shi ya rika hannunta suka fito tare. A tare suka sauko kasa hawayen farinciki tana cika idonta, har ya bude mata motar ta shiga sannan ya zagaya ya shiga ya yai mata key tun kamin yai horn mai gadin ya bude masa gate suka kama hanya
gidan Alhaji Nasiru Gobir.
Cikin kankanen lokaci suka isa gidan nan ma horn daya yai aka bude masa gate, tun kamin yai parking Rahama ta bude motar ta fita ta shiga cikin gidansu da sauri, shi kan sai da ya faka motar sannan ya fito ya rufa mata baya.
A falo ya sameta tana zaune kusa da mahaifinta.
“Daddy naga kamar kana cikin bacin rai”
“Wallahi wasu wulakantaccin mutane suka shige min a gidan da nake ginawa a Clapperto road, ance sun janyo har macizai suna shiga gidan, amman na ce a korasu”
Hannunsa ta kama.
“Daddy kar wannan ya dame ka yau rabar murna ce na Doc Asim ya kira wai an samu kidney din”
“What”
Gaba daya suka amsa har kanenenta suka taso ta sauri suka rumgume ta suna ta murna. Alhaji Nasiru ya kalli Aliyu irin kallon gani
n kima da kauna ta suruki da surukinsa.
“Mun gode sosai Aliyu Allah ya saka da alheri”
“Karka damu Alhaji aikina samawa Mamata lafiya ko ta hali yaya, zanje gida san na samu ganawa da likitan”
Daga haka yai musu sallama ya fito ya shiga motarsa y
a dauki hanyar family dinsu wato gidan Alhaji Garba Fayau...
_________________
Wayyo Ataa
😪
https://chat.whatsapp.com/DaDP34cM3s5FMfaQOtFM9Y
*Z A K I*
By Khadeeja Candy
5
️
⃣
Ko da mu ka isa asibitin ana ta mopping ko'ina, ni d
a Lukman muka rakube kamar sauran talakawa irinmu, wadanda suka tsaya suna jira a gama mopping din sannan mu wuce, masu hannu da shuni kan da masu galihu wucewa kawai suke ba tare da n tsayar da su ba, masu aikin sai mika musu gaisuwa suke.
Mu kam mu ka
i tsaye har aka gama mopping din sannan na mika kafata na taka sai wata daga cikin Nurses din da suke tsaye a can babban kofar shiga ta daka min tsawa data saka hantar ciki ta kaďawa.
“Ke ki ka fi kowa a nan ne da za ki tsallako ki wuce gurin be gama bu
shewa ba”
Da sauri na koma baya na tsaya gurin da na ke tsaye dazu, sosai tsawar nurse din ta firgita, da alama idan na sake taka gurin zuwa za tai ta mareni. Ina rike da hannun Lukman da jakar dana sakawa Nana tufafin dana dauko mata, Lukman kuma na ri
ke da taliyar da ke cikin kula mai murfi dabam kular ma dabam. A haka muka tsaya a gurin kamar wasu marayu har gurin ya gama bushewa, da na ga wasu sun fara takawa sannan muka taka
muka doshi ciki, sai kuma muka tarar dan cikin ward din be gama bushewa ba
wani gurin ma a yanzu ne ake mopping din.
Dan Albarkar likitan nan yana tsaye da wasu nurses suna masa wani abu a takardu, yana hangomu ya ce mai mopping din ta tsaya mu wuce, cikin sauri ta tsaya muka fara takawa zuwa inda dakunan suke, wani dadi na j
i ya lullubeni ko ba komai ya nuna min karamci da kulawa a matsayina na ba kowa ba, a take na ji kimarsa da darajarsa ta karu a idona. Sai da na gaisheshi sannan na wuce dakin da Nana take ciki, nurse din nan ta jiya na tarar wacce ta ce rika girgiza min k
ai lokacin da zan saka hannu a takardun da aka yi wa Nana aiki.
“Ina kwana?”
Na gaisheta cikina cike da tsoro gani nake kamar ita tsawar zata daka min kamar waccan nurse din. Sai na ga ta amsa min da lalama tana min kallon tausayi.
“Lafiya kalau
, wannan matar mamarki ce”
“Eh mamata ce”
“Ina Babanki ya ke?”
“Baba na rasu?”
“To waya kawo ta asibiti?”
“Ni na kawo ta”
“Ba ku da kowa nan ne?”
Na dan yi shiru ina nazarin irin tambayoyin da take min da suka yi kama da wadanda likita
n can yai min dazu, ban san dalilin da ya saka suke son yi min irin wadannan tambayoyin ba. Har na bude ba ki na bata amsa sai ga likitan nan ya turo kofa ya shigo yana waya baki har kunne sai dariya yake, sai dai ganina da wannan nurse din yasa yai hanzar
i katse wayar ya hade fuska kamar be taba dariya ba.
“Me kike a nan?”
Sai nurse din ta sha jinin jikinta ko motsin kirki bata yi.
“Na na na... Zo duba... Ta..”
“Ke duba ta ke kika aje ta? How dare you? Fita ki ba ni guri”
Kamar zata 6ace 6
at a gurin haka tai saurin ficewa jikinta sai rawa yake kamar mazari, a nan nima na shafawa kaina lafiya fahimtar cewa yana da fada sosai na koma gafe ni da Lukman muna kallonsa. Yana kallona sai ya sake fuskarsa yai min murmushi yana kallon jakar hannuna.
“Miye a ciki?”
“Kudin da ka ba mu ne, da tufafin da ka ce a daukowa Nana”
Na amsa cikin tsantsar ladabi da kuma muryar da ke nuna babu ruwana.
“Wannan fa”
Ya sakw tambaya yana kallon kular da ke hannun Lukman.
“Taliyar da na dafa ce n
a kawo ma Nana ko za ta ci”
Dariya yai yana kallon murfin kular da ke daban da kular wacce ta soma koredewa wani 6angare na jikinta ma har ya tsage.
“Ya ma sunanki?”
“Ataa”
“Ataa karki sake kawo abinci a nan asibiti, zan sa a rika kawo muku na
safe da na rana da kuma na dare ke da kanenki da kuma Mahaifiyarku idan ta farko kinji?”
“Da gaske?”
Na fada ina kara girmama kirmarsa lallai a cikin dubu samun mutum kamar wannan likitan mai tausayi da taimako sai an tona.
“Yes”
Har kasa na
kai idona cike da hawaye ina masa godiya kamin na koma yi ma Allah godiya daya hada mu da irin wannan mutumen. Karasa yai ya duba Nana ya canja mata wasu abubuwan na na'ura sannan ya juyo ya kalleni.
“Ina tufafin suke?”
“Ga su”
Na mika masa da sa
uri a zatona saka mata zai yi sai naga yai baya da sauri kamar mai kyama.
“No no bari na kira wata ta saka mata”
Daga haka ya juya ya fice, ni kuma na kuma kusa da ita na tsaya ina ta kallon fuskarta ga ta a kwance kamar ta mutu, amman fuskarta na k
yalli kamar zata bude baki tai mana magana.
“Ataa yaushe Nana zata tashi?”
Lukman ya tambaye ni yana kallonta.
“Ni ma ban sani ba”
Na amsa masa idona taf da hawaye tausayin mahaifiyata ya cika zuciyata, na san Allah ne ya kaddaro mata haka amm
an macijin nan be kyauta min ba. Ina tsaye wata mata mai zubin marasa mutuncin ta turo kofar ta shigo
fuskarta ta tsage tana sanye da uniform din nurse sai wani kallo take watsa mana a hankade.
“Ke kamar ki za ki ace ba ki iya sakawa mahaifiyarki riga?
”
Ta fada tana fisgar rigar a hannuna sannan ya karasa gurin Nana, yadda ta saka hannu ta tallafota sai ta tsikar jikina ta tashi dan zaka rantse da Allah ka ce karamin yaro ta dauka, a gabana gaban Lukman ta janye mayafin da aka rufe Nana da shi ni da
Lukman muka ganta tsirara haihuwar uwarta ga dinki a cikinta gurin yayi ja sosai kamar jini ya kwanta, da sauri ya juyar da fuskar Lukman ni ma na juya muka ba ta baya hawaye na sauko min, ban juyo ba sai da na tabbatar ta gama ta rufe mata zane har na wat
sa min wata magana marar dadi jin.
“Tufafin ma duk ďoyi suke yi mtswwwww”
Ni dai ban ce mata komai ba na karasa gaban Nana ina kallon yadda yake ya mutsa fuska duk da kasancewar bachi take ko kuma ma na kira shi da suma, da alama taji zafin yadda nu
rse din ta motsa ta, ji nai kamar ace ina da wata dama da zan bawa ciwon umarni ko kuma na saka hannu na dauke mata shi ta farka ta tashi mu bar asibitin nan, ga dukan alamu likitan nan ne kawai mai mutumci sauranka ko kallo ba mu ishe su ba. A kujerar da
ke gaban gadon na zauna ni da Lukman sai ya kwanto jikina kamar wani maraye yana ta tabe baki alamar zai yi kuka, ni kan daman hawayen kawai na ke ina jin wani abu ya tsaya min a zuciyata.
Kamar yadda fada haka kuwa akai misalin uku saura na rana aka a
iko mana da abinci irin na manyan restaurant mai dadi har da naman kaza, a take Lukman ya hau murna jikinsa har rawa yake ya dauki naman kazan ya kai baki, ni kan sai na ji bana son cin komai duk kuwa ni da irin kwadayina. A bandakin na shiga nai alwala na
i shimfida dankwalina nai sallah azahar, babu komai a sujida ta sai rokon Allah ya bawa Nana lafiya.
ALIYU POV.
Yadda ya ke driving sai ka rantse da Allah ba jiransa ake ba, hankalinsa a kwance yake tukin motar yana tafiya kadan-kadan duk kuw
a da irin son ganin Doc Asim da yake. A ka'ida ba ya danna horn sau biyu sau daya ya ke yi amman wannan karon sai da ya danna har sau uku sannan mai gadin ya bude masa gate, tsayawa yai dai-dai gurin mai gadin ya sauke gilashin motarsa yana watsa masa wani
kallo na marasa ganin talaka da daraja ya ce.
“Kar ka yarda na sake danna horn har uku ba ka bude min gate ba”
“Ayi hakuri ranka ya dade, Wallahi na dan zagaya ne”
Dattijon mai gadin ya fada jikinsa na rawa.
“An aje ka nan ne dan ka zagaya?”
“Ina nufin bandaki na shiga”
“Kai ya shafa ni dai na fada maka next time korarka za'ayi”
“In-Sha-Allah hakan ba zai sake faruwa ba, ayi hakuri Zaki”
Uffan be sake ce masa ba ya faka motarsa a harabar gidan sannan ya fito yana ta kanshin turare
n da ke sanar da zuwansa ya shiga falon. Khaleesat da Hauwa na zaune a falon ko wace rike da waya, ganinsa yasa sukai mugun shan jinin jikinsu suka natsu sosai ko kallon inda yake ba sa yi gudun kar ya su hada ido da shi ya ce sun masa ba dai-dai sun san s
hi sarai ya tsani kallo.
Ganin Momy da Daddynsa yasa ya saki fuska ya cire talkamin kafarsa ya karasa kusa da su da sallama. Dukansu fuskarsu dauke take da murmushi da alama suna cikin jindadi da farinciki.
“Dan wajen Fulani ka yi lattin zuwa likitan k
uma ya ce yana da aiki da yawa a asibiti be tsaya jiranka ba ya tafi”
Momy ta fada tana kiransa da sunansa da ta saba kiransa.
“Ya ce min an samu kidney din”
Ya fada yana mikawa Daddy hannu su gaisa. Sai Daddy ya dora da
“An samu, na masa maga
na ya ce zai hada ku da wani likita da za ku je London ayi mata dashen”
“Samun Kidney ba abu ne mai sauki a yanzu ba, gaskiya likitan nan ya cancanci komai daga gurina, at long last Rahma zata samu lafiya”
“Ba daga gurinka ya cancanci komai daga gare
mu ma gaba daya, amman ina fatar ba ta