Showing 96001 words to 99000 words out of 237425 words

Chapter 33 - ZAKI COMPLETE

maza biyu sun doso dakin kwanon da muke ciki.

“Ina marar lafiyar take?



“Gata nan”

Na fada da sauri ina mikewa tsaye sai suka shigo suka dauki Nana suka fita da ita zuwa cikin motar asibitin Farida da Mahaifiyarta suka fito suna kallo har da wasu makota da ke kusa.

“Ni ina zan shiga?”

Na tambayi mutanen da suka

shige cikin motar. Sai na ji muryar Aliyu yana fadin.

“Nan za ki shiga”

Da sauri na nufi motar na shiga daman ban rufe ba, shi ma kuma jin kai ya hana shi rufewa. Da na shiga motar sai yai mata keys muka bi bayan mutane sai da muka fara nisa sai na g

a sun bi hanyar Uduth shi kuma ya dauki hanyar arkilla da ni.

“Kai ba fa ita za a cirewa koda ba ni, ita ba kasa an cire mata daya ba, idan aka kara cire wannan mutuwa za tai”

Na fada ina shirin fashewa da kuka.

“Karki sake min maganar kodar nan

karki sake”

Shine Kawai abunda ya fada min ba tare daya kalleni ba ya cigaba da tukinsa ni kuma na cigaba da rare masa kukana har muka isa arkilla, wata hanyar ya biyo inda manya gidaje na alfarma, bakin wani katon gate ya tsaya wanda saman gate din du

k iccen fulawa ne da yai rassa ya sauko har gurin gate din. Da karfi zai saka a cire min kodar ya sakawa matarsa ni ya kyale ni shine kawai abunda zuciyarta take raya min. Da muka shiga harabar gidan sai na ga manyan motoci uku a fake kusa da ta farkon ya

faka tashi motar ya bude ya fita ba tare da ya ce min komai ba. Nima na bude na fito na tsaya gurin motar ina hawaye gaba daya tsoro ya gama kamani dan a nawa tunanin wata kila ma tsafi yake. Da kai yai min alama da na wuce ciki ni kuma na lake kafadata ta

alamar ba zanje din ba, gaba yai abunsa ya bar a gurin ina karewa gidan kallo ina hawaye, gidan be min kama da na yan yankan kai ba amman ba ni da tabbacin ba cutar da ni zai yi ba, gashi kuma ya saka an tafi da Nana waya sani ko sani abun za a mata. Kara

r bude kofar falon naji kamar yadda na ji lokacin da zai shiga, sai na hango wata farar mace ta fito daga falon ta doso inda nake tsoro ne ya kamani a zatona wani abun zata min sai ta kusan karasowa kusa da ni sai na ga ashe matar da na taba gani gidan Mam

a Fulani ce wacce ta ba ni cake, fuskarta da tausayi ta karaso inda nake ta kai hannunta ya rika fuskata sai na ga idonta da hawaye.

“Alhamdulillah Allah mun gode maka, sannu kinji”

Na gyada kai ina hawaye sai tasa hijabina ta goge min fuskar.



Daina kuka kinji zo muje ciki”

“Ina nan ya kawo ni?”

“Ya kawo ki inda za ki samu gata ki samu jindadi a nuna miki kauna”

“Mamana tana asibiti ya saka an tafi da ita ban san abunda zai mata ba, bana kwanciyar hankali har sai naji halin da take ciki



“Ba cutar da ita zai yi ba, shi ma ya dade yana nemanki da inda kike ni da shi, ban san cewa ke ce ba sai bayan da Fulani ta koreki, ki aminta da mu Wallahi ba za mu cutar da ke ba”

“Mahaifiyata fa?”

“Ita ba zai mata komai ba”

Matar ta fada t

ana hawaye sai ta rumgume ganin ina kuka. Shi kuma ya fito daga falon ya nufo inda muka na yi zaton ko wani abun zai fada min sai na ga ya bude motarsa ya shiga.

“Dan wajen Fulani komai ake ciki ka kira ni saboda hankalinta ya kwanta”

“Okay Momy”

Ya fada yana kallona daga cikin farin gilashi motar. Sannan taja hannuna ta nufi hanyar falon da ni, da muka shiga ciki sai sai yan matan nan da na gani idan Mama Fulani su Biyu Siyama da Husna da kuma wata wacce ban sani ba suka ce min

“Sannu”

Kai

kawai na gyada musu na zauna a kujerar da matar ta zaunar da ni. Sannan ta zauna kusa da ni ta rike hannayena.

“Dan Allah ki daina kuka Wallahi raunana min zuciya kike idan kina kukan nan sai ki saka nima nai”

Sai kuma ta kalli Siyama tana share ha

wayenta ta ce.

“Shiga ciki ki hada mata ruwan wanka”

“Aa ba zan yi wanka ba, na fi son naje asibitin kusa da ita hankalina zai fi kwanciya”

“Za a kula da ita za a mata duk abunda take bukata idan ma kinje ba wani abun za ki mata ba, kuma ba cutar

da ita zai yi ba taimakonta zai yi”

Kai na girgiza.

“Aa ni ban yarda ba, wacan karon ma cewa aka yi taimakona za ayi ashe koda za a cire mata a bar mu da lalura, kuma mutanen da sukai wacan aikin sune a yanzu, a gabana ya kira wani likita ya aiko da

mota aka tafi da ita ni kuma ya kawo ni nan, hankalina be kwanta ba, zai iya cirewa ya sake kasawa matarsa, dan girman Allah ku tauyasa min ba ni da kowa a duniyar nan sai Nana ban san kowa ba a cikin danginmu Wallahi idan ta mutu ban san inda zan je ba”

Ina rufe baki matar ya saka a kirjinta ta rumgume ta fashe da kuka sautin kukanta har ya fi nawa dagawa. Husna da bakuwar da ban san sunanta ba suma suka saka kukan dakin yai tsin ba ka jin komai sai sautin kukan mutane hudu, ni Matar, Husna da bakuwar

ban da Siyama da ita hawaye kawai take. Mun dauki lokaci muna kuka duka aka rasa wanda zai bawa wani hakuri balle kuma har ya rarrashi, Siyama ce ya shiga daya daga cikin dakunan ta hada ruwan wankam sannan ta fito tana fadin.

“Momy ga su can na hada d

akina”

“To”

Wacce aka kira da Momy ta amsa cikin muryar kuka, ni dai ina rumgume a kirjinta ina fitarda numfashi a hankali, na jidadin rumgumar da tai min rabon dana kwanta jikin Nana a haka har na manta amman yau wata uwar ta rumgume ni na yi kuka a

jikin rigarta ba tare da ta nuna min kyama ba. Ko da yake ba a fuska da hali ake gane mugun mutum da na kwarai ba, domin da a fuska ne da Doc Asim be mana haka ba, daga nai daga jikinta ina jan majina sai ta sauke ajiyar zuciya ta ce.

“Ta so mu shiga

ciki ki yi wanka”

“Momy bari na kaita mana”

Bakuwar ta fada tana mikewa tsaye gaban tv dana tarar da su suna game ta nufo inda nake, wata kila ita ma yar gidan ce domin ta yi kama da Momyn sosai. Hannuna ta rika na tashi tsaye taja har cikin dakin da

n madaidaici mai gado daya da yar karamar kujera da teburin karatu an kawata shi iya gwargwado.

“Nan za ki cire kayanki ko sai kin shiga ciki”

“Ciki zan cire”

Ta min murmushi.

“Ya sunanki hala?”

“Aisha”

“Ni kuma sunana Amina, jin ga a gi

rme na girmeki dan haka ke kanwata ce”

Bance mata komai ba sai ta nuna min bandakin.

“Shiga ciki sai ki yi wankan bari na kawo miki wasu tufafin da za ki saka”

“To”

Na nufi bandakin cikin tsoro domin ni har yanzu zuciyata bata natsu da su ba,

a dayan bangaren kuma na kasa aminta cewar Aliyu ba cutar da Nana zai yi ba. Ban wani dade gurin wankan ba na gama na dauki zanena na daura na fito tsoron gashina har gadon bayana. Ko da na fito Amina tana zaune rike da kayan tana jirana.

“Wow”

Ta fa

da tana kallona sai kuma ta aje kayan hannuna ta nufo bayana tana taba gashina.

“Ke da gaske gashinki ne? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, kamar aljana ko dai kari kikai”

“Gashi na ne”

Na fada cikin rashin sakewa.

“Ki shafa mai ki saka rigar



Ta fada tana fita daga dakin. Abaya ce yellow da under wears sai dan karami dankwali baki. Sai da na fara saka kayan ciki sannan na saka abayar na daura dankwalin a fito da tsorona sai na zauna kasa, gudun kar na zauna a saman gadon ya zama laifi koma

i ban shafa ba duk kuwa da tulin kayan kwaliyar da suke dakin tsoro nake ban sani ba ko suma kamar Maryam da Rukaiya suke. Kofar dakin aka turo sai ga Momy ta shigo dauke da plate da kofi.

“Aa ya kika zauna kasa? Tashi ki zauna saman gadon mana”

“Na

n din ma ya ishe ni”

“Aa tashi ki zauna ya za ki zauna kasa”

Saman gadon ta aje plate din da ke rufe sai ta mika min kofin hannunta ashe tea ne a ciki.

“Ki ci abinci kinji ki kwantar da hankalinki ki yarda da mu ba zamu taba cutar da ke ba, kuma

mahaifiyarki zata samu lafiya ta warke In-Sha-Allah”

“Bana jin yunwa bana iya cin komai a yanzu”

Na fada ina aje kofin tea a kasa sai ta dafa ni ta zaunar da ni kusa da ita saman gadon.

“Na sani an miki zalinci kuma an miki rashin kyautawa, tabba

s Dan wajen Fulani ya yi kuskura ban sani ba ko za ki yarda cewar ba da saninsa aka aikata miki hakan ba?”

“Idan ba da saninsa ba ya za ayi a sakawa matarsa? Kawai sun yi amfani da rashin ilmina ne suka saka na saka hannu a takardun da sunan taimakona z

a ayi ashe kodarta za a cire, saboda ya tambayi ne na ce masa ba ni da kowa sai yai amfani da wannan damar ya cire mata koda kuma ya saka a kulleni har kwana hudu gidan yan sanda, wai na bata masa suna”

Na karasa ina hawaye.

“Wallahi ba da wanin san

in sa akai miki haka ba, kudi aka bashi aka ce ya siyo ba mu san cewa zalinci zai yi ya cire kodar mahaifiyarki, kuma tun daga lokacin da abun ya faru muke ta neman ki da inda za mu ganki mu taimaka miki amman ba mu samu ganinki ba, ban san cewa ke ce kike

aiki a gidan Fulani ba sai daga baya, shi kuma ya fada min cewar kin ki bashi hadin kai ne shiyasa be taimaka miki ba”

“Ina tsoron taimakon kowa ballanata na shi, Wallahi Aliyuna nan bashi da imani da tausayi kansa kawai ya sani”

Wasu yawu ta hade d

a karfi tai min murmushi.

“Ba ki fahimce shi bane, amman za ki sanshi nan gaba kadan”

Ban sake cewa komai ba bayan hawayena da na share ina murza yatsun hannuna na rasa yadda zan yi zuciyata ta aminta cewar ba cutar da nana Aliyu zai sake yi ba.

ALIYU POV.

Daga Arkilla ya koma uduth din, duk wani abu da ake ma patient kamin a shiga da shi ganin likita shi yai kama daga karba kati da kaiwa a bude file. Sannan ya kira Doc Bukar ya fada masa cewar ya kawo ta har an shiga da ita ciki, ba bata l

okaci Doc Bukar ya iso asibitin sai da Aliyu yai masa bayanin cewar matsalar koda ce sannan ya shiga dakin da aka kaita ya soma bata taimakon gaggauwa shi da wani likitan. Bayan sun fito Doc Bukar ya saka wasu nurses din suka kaita akai mata hoto a aka deb

i jininta sannan ya canja mata daki aka kaita wani dakin na musamman.

“Aliyu ya akai aka bar matar nan haka? Ciwon nan yana kokarin cinye ta?”

Lokacin da suka jero suka fito daga emergency ne Bukar ke masa wannan tambayar.

“I can't tell yanzu fa

da min ba zata samu sauki ba?”

“Zata samu mana, amman dole sai mun jira Doc Muhseen ya zo shi kadai zai mata aikin nan tun da Doc Mustapha yana waje, daman sune likitocin da suka fi kwarewa wannan fannin”

“Ka kira shi?”

“No na yi request a kira sh

i dai, ai ba mu muke kira ba, kuma ko bayan nata ai zai zo ya duba wasu patients daman amman sai next week”

“Kana tunanin zata kai gobe?”

“Yes zata iya kaiwa next year ma a haka, daman yanzu jini da ruwa ne abunda ta fi bukata, to mun saka mata ruwa

jinin kuma na saka a bincika idan kawai wanda yai daidai da nata ko kuma zai iya zama a jikinta”

“Ka gwada nawa mana idan zai yi”

Doc Bukar ya kalleshi.

“Seriously?”

“Yes ina son rayuwar matar nan Bukar, ko me za ayi dai i need her alive”



Then ka kira dan uwanka ka fada masa idan zai iya ya zo ya duba ta yau ma, idan yai mata aiki ina da tabbacin nan da two weeks zata koma normal”

Wani guntun numfashi Aliyu yaja ya sauke sannan ya kalli Doc Bukar din ya ce.

“Muje a gwada jinin”

Ta

re suka juya suka zuwa lap a can aka gwada jininsa da na Nana aka ga zai shiga sai ya kwanta aka cire gora uku a jikinsa aka sannan ya taso ya fito Doc Bukar ma bashi gangon madara.

“Ya jikin Rahma tana ta samun sauki dai ko?”

“Ka ji bata da lafiya n

e?”

“Yes ba mahaifinta ya saka cigiya gurin likitoci cewar yana bukatar kodar siyarwa ba, sai dai samun koda yanzu ba abu ne mai sauki ba ba kowa ke iya siyarda wani bangare na jikinsa ba, kamar wannan maybe ita ta siyar muku da na farkon gashi yanzu sa

i an sake mata aiki”

Sai da Aliyu ya shaye madarar sannan ya jefar da gongon ya kalli Doc Bukar kamar zai yi magana sai kuma yai shiru dan yasan daya fadi gaskiya kara ma kawai yai shiru dan babu wanda zai yarda cewar ba da amincewar Doc Asim ya cire ko

dar ba.

“What is better now is ka kira Muhseen ka fada masa cewar kana da patient ya zo ya duba maka ita, na san zai yi ai”

“Zan kira”

Ya bashi amsa sannan ya rako shi har gurin motarsa ya shiga ya sannan Doc Bukar ya juya ya koma cikin asibiti A

liyu kuma ya amsa wayar da Rahma take masa.

“Aliyu ka shigo garin nan?”

“Eh”

“Amman ban sani ba”

“Shigowar dare nai, ya jikinki?”

“Aliyu yarinyar nan ka biyo ko?”

Yayi shiru be ce mata komai ba.

“Aliyu wai ba zaka fita harkar yarinya

r nan ba? Shikenan daga yarinya ta zo tayi karya kai kuma ka zauna akai ka yarda cewar hakan din ne?”

“Babu ruwanki a cikin lamarin nan, ban nemi shawararki ba akaran kaina nake komai, and bana son yadda kike min magana kamar kina saka ni nai dole”

A

jiyar zuciya ta sauke daga can cikin wayar sannan ta dora da dalilin daya saka ta kirashi.

“Adamu mai gadi ya fada min wata ta zo zata siyar da kodarta kuma ka yi magana da ita ina take?”

“Ataa ce yarinyar da kike fada akanta, ta zo ta siyarda kodar

dan kawai ta nema mahaifiyarta magani irin wannan yarinyar ce kike cewa kar a taimakawa? Haba Rahma”

Kashe wayar tai bata sake cewa komai ba, shi kuma ya sauke yana mai jin haushin abunda tai masa dan shi ba a kashe nasa waya sai dai shi ya kashe maka i

ndai ba Momy ba ko Mama Fulani ko Abbah Daddy, sai ko Nasir shi ma kuma ba kullum ba. Sai ya tuka motar ya dauki hanyar gidansu Rahma dan zuwa ganinta and yana son yin wasu maganganun da ita, a dayan bangaren kuma yana jin kamar ya kira Muhseen yai masa ma

gana, duk da yasan ba abune mai sauki a gareshi ba kiran Muhseen har yai requesting wani abu a gurinsa, he can't remember when last yai waya da shi, wani bangaren na zuciyarsa yana fada masa ya hakura kawai har sai next week idan Muhseen din ya zo, sai kum

a yaji kamar ba zai iya kyale Nana a cikin wannan halin ba bayan sune silar shigarta halin kuma yana da yadda zai yi. Cikin wayarsa ya shiga ya nemo number Muhseen yana ta kallonta kamar ba zai kira ba, sai kuma sata zuciyar tace masa ya aika masa kawai da

sako, wata kila kuma kiran ya fi dan zai fi daukar abun da muhimmanci, ba shi da wani zabi daya wuce kiran idan ma ya koma gida be san ta yadda Ataa zata dauki abun ba idan ya fada mata likitan da zai mata aiki sai next week zai zo wata kila ba zata yarda

da shi ba. Ringing tai har ta katse Muhseen be dauka ba, bs karamin jihadi yai na sake kiransa tare da alkwarin idan har be daga ba ba zai sake kiransa ba, tana yin ringing daya Muhseen ya daga.

“Ya akai?”

Aliyu yai shiru na wani lokaci ba tare da

yace komai ba tana jin zafin tambayar da Muhseen yai masa. Har Muhseen zai kashe wayar sai Aliyu ya ce.

“Akwai wata patient mai matsalar koda, ina son ka duba ta gobe”

“Yaushe ka zama ogana ne da har zaka ba ni umarni?”

Aliyu yai shiru be ce koma

i ba sai dantsar hakora yake gumi na karyo masa a take. Can Muhseen ya ce

“Idan ma wani abun ne ai ba kai zaka fada ba, daga can asibitin za a turo min mail, sai idan alfarma kake nema then say it”

A fusace Aliyu ya katse kiran ya gwammace yai hakan

da ya furta neman alfarma a gurin kowa balle kuma Muhseen da furta hakan zai ba shi damar ganin ramarsa. Bacin ransa ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login