Showing 147001 words to 150000 words out of 237425 words

Chapter 50 - ZAKI COMPLETE

ta karasa maganar tana maida hankalinta gurin dora girkin. Juyowa nai na dawo bq ina ta tunanin dalilin tafiyar ta su, sai dai gaskiya na ji ba dadi na rashin dalili, daga tafiyar Momy har

Aliyun ma, ina shigowa dakin sai Nana ta jefo min wani zance.

“Mi zai saka ki zabi Kamal? Mutumen da be tana biyowa ya nemi inda kike ba?”

Na zauna kusa da ita ina murza yastun hannuna na ce.

“Yana da kirki sosai Nana kuma yana so na”

“Yana d

a kirki kamar Muhseen ko kamar Aliyu?”

Na yi shiru ina nazari.

“Muhseen ba shi da kirki Ataa to har zai iya tunkara a matsayina na uwarki ya fada min magana irin wannan ko da ko ya san na sani, irin wannan wata rana zai iya ci miki mutunci a gabana”M

UHSEEN POV.

Kamar yadda yai wacan tafiyar hakan yai wannan, domin kuwa yana baro bq ya kama hanyar Abuja cikin bacin rai be taba nadamar yin wani abu kamar yadda yai nadamar zuwa sokoto ba a yau ba, domin ba be so ba da duk wannan be faru ba da be ji w

ata maganar marar dadi daga Momy ba, balle har yau Ataa ta ce ta tsane shi.

Ya isa Abuja cikin dare kamar wacan karon sai dai yau da 11 ya shiga gidansu tsabanin wacan zuwa da ya dira karfe ukun dare.

Hango wuta a falon Mama Fulani yasa ya nufi can k

ai tsaye domin labarta mata abunda ya faru har lokacin ya kasa sauke fushinsa. Tura kofar falon yai ya shiga sai ya same ta zaune bakin saman kujera tana kallon tv. Karasa yai kusa da ita yana wani bata rai shi ala dole fushi yake yana kuma son nuna mata d

amuwar, kusa da ita ya zauna, ganin bata kalleshi ba yasa ya kira sunanta.

“Mama....”

Tana juyowa ta tsinka masa mari mai zafi da bayan hannunta ta mike tsaye a fusace tana kallonsa ta ce.

“Sha sha sha marar tunani sakaraiz ashe Muhseen baka da h

ankali ban sani ba sai yau? Waya kai ka taba Momy? Wa kake a cikin Familyn mu da zaka fadawa Momy marar dadi wa ke? Da? Da? Dan da zaka iya mutuwa yau gobe na haifi wani? Ka taba kowa ka yi ma kowa amman ban da Momy ban aminta ba, ban aminta ko inuwarta ta

kata ba, balle har ka fada mata ba dadi idan ka taba uwar Aliyu uwarka ka taba tashi ka fice min daga falon, daman kai nake jira dan sannan za ka zo, get out....!”

Ta furta a tsawace tana nuna masa kofar fita. Hawaye shar suka wanke fuskar Muhseen tuni

yai mutuwar zaune a gurin.

ZAKI

By Khadeeja Candy

41...

Kasa cewa komai Muhseen yai sai kallon Mama Fulani yake hawaye na sauko masa kamar ba shi ba. A fusace ta bar masa gurin ta haye sama dakinta. Ya dade zaune a gurin sannan ya mike tsaye ya

nufi part dinsa, keys bude dakin ma daker ya iya sakawa ya bude yana shiga ya zube a falo zaune saman kananan cushion dinsa.

Abunda ya faru ne ya tsaya masa a rai, ta ina ne be kyautawa Momy ba? Miye illar abunda yai? Har ga Allah be ga da inda yake da wa

ta matsala ba, Momy ta nuna masa son kai, kuma maganar da ya fada mata babu laifi a ciki, ta sani sarai yana son Ataa taya zata juyar abun akan Aliyu saboda yana danta? Ya sani be kyautawa Ataa na fada mata maganar kai tsaye a gaban mahaifiyarta ba, sai da

i be san cewa mahaifiyarta bata sani ba da be aikata abunda ya aikata har ta furta kalmar tsana a gareshi ba, wannan babin kam ya yarda yayi kuskure amman da wanne zai ji rashin goyon bayan Momy ko kuwa yanke masa hukunci da mari da Mama Fulani tai, ko kuw

a auren Ataa da Aliyu zai yi? Anya ma zai iya zai iya kallon Ataa da Aliyu a guri daya bayan shi ya fi cancanta ya zauna da ita? Domin shi ya ce yana son ta kuma yana da tabbacin tana son sa.

A daren be yi bachi ba duk kuwa da irin gajiyar da ke tattare

da shi na tafiya mota amman tunani ya hana shi bachi kamar wacan karo, ta ina yake da matsala ina zai samu mafita? Ta ina zai shirya da Ataa? It's necessary ya koma sokoto ko gobe? Asubar fari ya fita daga gidan zuwa masallaci be dawo ba sai takwas da wan

i abu na safe, kamar zai wuce part dinsa sai kuka ya shigo part din Mama Fulani ita ya samu tana share falon da kanta Maryam da Rukaiya na zaune sai aikin danna waya suke.

“Mama ina kwana?”

Ta yi kamar ba ta ji shi ba sai cigaba tai da aikinta.

“Mama Muhseen na gaisheshe ki”

Maryam ta fada a zatonta bata ji abunda Muhseen yace ba ne.

“Na ji ai”

Ta fada ba tare da ta kalleshi ba. Shi kuma ya mike tsaye cikin rashin jindadi ya fice daga falon.“Gaskiya Mama be kamata ki ga laifin Ya Muhse

en ba, har ga Allah Momy be kamata tai supporting Ya Aliyu ta bar Ya Muhseen ba”

Mama Fulani ta dago tana kallon Maryam wacce tai maganar tana nuna ta da tsintsiya.

“Baki san komai a kan rayuwar yara ba, babu ruwanki a ciki duk wanda zai ce kushe mi

n Momy zai yi to zai jawa kansa bakin jini ne kawai, ai Aliyu ya fi cancantar karin aure yanzu fiye da Muhseen ko dan saboda Rahma, sannan Momy mai zaba masu matar aure ne, waya sani ko ta zaba masa wata ne shi Muhseen din ya ce baya so sai ta Aliyu, ai Am

ina ta fada min mafarin fadan duk akan wata yarinya ne”

“Haka ne kuma, su ma dai ban da abun su miye abun fada kan mace ga mata nan da yawa a gari, dama Ya Aliyu ya bar masa ko wacece ya zo ya auri Rukaiya”

“ai na ga kamar bata masa ne shiyasa ban ma

tsa ba bana son abunda zai jawa Aliyu matsala, kuma namiji kara dai ka jira har kawo maka wacce yake so da wacce kai kake so, kin san dai duk yarinyar da Aliyu zai so classic lady ce, ai ko dan ya ba wa wannan yar iskar Rahma haushi zan zo ya aure ta”

R

ukaiya ta yi kunce tana danna wayarta ta ce

“Uhmm ni jikina na ba ni Ataa ce suke wannan rigimar akanta Wallahi, kin san fa tun tana gidan nan suka fara wani zafi zafi akanta”

Mama Fulani ta dan yi shiru kamin ta kalli Rukaiyah.

“Ai ko kowa zai y

i ban da Aliyu, ai sam ba zai taba son wannan banlagarar yarinyar ba”

“Mama tana da kyau fa sosai, kuma nan zai iya rudarsu, shi dai Ya Muhseen tun da a nan ai ya furta”

“Ai yau Momyn zata zo za mu idan ita ce din, amman ni nasan Aliyu ba zai taba so

n irin wannan yarinyar ba”

“Uhm Mama ba ki sani ba kenan, ai Wallahi Ya Aliyu zai iya jin cewar zai gyarata ya zauna da ita”

“Yarinyar da ke bara a titi dan Allah ki bar ma wannan maganar bakinki ya sari danyen kashi amman dai ba akan yayana ba Walla

hi”

Mama Fulani ta karasa tana tofarda yawu, a take ranta ya bace domin ko maganar Ataa bata son a mata a yanzu sam ta ma manta da ita a duniyarta.Misalin goma na safe Momy da Aliyu suka sauka Abuja, suna sauka yai ma Nasir waya ya zo da mota ya dauke

su zuwa gidan Mama Fulani, a motar ne Nasir yake karantar damuwar Aliyu domim tsakanin jiya zuwa yau har wata rama yai idonsa sun dan fada kana ganinsa kasan akwai damuwa a tare da shi, sai dai fuskarsa na nan a daure kamar ko yaushe. Suna isa gida Aliyu y

a fara bude motar ya zai fita sai Nasir ya hana shi ta hanyar ce masa.

“Aliyu ina son mu yi magana da kai”

Jim hakan yasa shi zaunawa a motar Momy kuma ta bude gidan baya ta fita zuwa cikin gidan sai da ta shige sannan Nasir ya kalli Aliyu ya ce.

“Wani abun ne kuma ya sake faruwa?”

“Babu komai Nasir”

“Ga fuskarka nan ta nuna damuwa”

“Ina jin zaman jirgi ne”

“Zaman jirgi daga sokoto zuwa Abuja zai saka cikin damuwa”

“Babu wata damuwa a tare da ni Nasir kai ne kake ganin haka”

Yan

a fadar hakan ya fice daga motar zuwa cikin gidan, yana jin cewar matsalarsa da Rahma private matsala ne da ba lallai sai aminnsa ya ji irin zaman da suke ba, matsalarsa da Muhseen ma yana jin ta su ce ta cikin gida da wani be kamata ya ji ba, balle kuma n

a son Ataa daya hana shi walwala wata kila ma idan ya fada masa dariya zai masa.

Ko da ya shiga Momy na falo zaune ita da Mama Fulani ta jera mata fruits domin abincin rana be kai ba kuma bata jin zasu fito ba su karya ba. Kusa da Mama Fulani Aliyu ya

zauna yana murmushi karfin hali.

“Mama ba ki fada min maganar Kamfanin nan ba sai a gurin Momy na ji”

“Ai da gangan na ki fada maka, wai ka tashi ta wuce sokoto ta waya ma kake fada min cewar ka wuce sokoto kai mai mata duk inda take kafarka na nan”

Dariya yai ya ahafa kansa yana kallon Maryam da Rukaiya da suka dauko kular farfesu Maryam kuma ta dauko plates da spoons. Maryam ce ta fara gaishe shi kamin Rukaiya ta dora da nata sai ya amsa musu fuska a hade kamar yadda ya saba.“Oh to sai na zuba m

asa ido yai miki rashin kunya kuma na kyale shi? Dan kin zaba masa mata ma ya isa ya ce ba zai aureta ba balle kuma dan kin zabawa Aliyu ita, yau ba ni burin da ya wuce na Aliyu ya kara aure”

“Wannan dalilin ne yasa na so Aliyu ya aureta amman ai Muhsee

n ya kasa fahimtata, kwana biyu da suka wuce Rahma dai fushi...... ”

Momy ta labartawa Mama Fulani abunda ya faru ciki har da jawabin da Mahaifiyar Rahma tai mata, a take ran Mama Fulani ya bace

“Uban me suke takama da shi a duniyar nan? Su har suna

da bakin yi ma mutane iskanci? Ai shiyasa na ke son ya kara aure mu nunawa amaryar kauna in yaso ita sai ta mutu, ya yana bukatar aure ko Allah zai ba shi haihuwa ma, ta san da maganar auren ne? Amman zan cen ba aza ayi kishi da talaka ba kam tana da gaski

yarta wa yake son rabar talaka”

Momy ta hade yawun bakinta kana ta ce.

“Bata sani ba, yanzu haka tana dubai taje hutu”

“Ahhh hutu ko? Aiko kamin ta dawo za ayi auren nan, idan ma ni Aliyu zai dauki shawarata ya aika mata da saki kawai ni fa bana

son rai ni”

“Ba sai ya sake ta ba, kin san halinndan ki ai ba lallai ne ya ce zai yarda ya sake ta ba, amman ko auren ya kara ai sai samu saukinta, amman yanzu ni na janye maganar auren ma kara dai ta zaba tsakanin shi da Muhseen duk wanda take kauna sa

i a aura mata shi idan ma wani take so ba shi ba sai a aura mata?”

“Wacece wai?”

“Ataa”

“Ataa”

Mama Fulani ta maimaita tana kallon Momy baki sake.

“Kam uban nan”

Ta daki kirji ta buga kafa da kasa.

“Dan Allah idan wasa kike ma ki dai

na”

“Babu zancen wasa a ciki Wallahi gaskiya na ke fada miki, Ataa ce”

“Ataa dai wacce tai aiki a karkashinmu? Ita ta samu wannan damar da har Muhseen da Aliyu suke ribibinta ko kuwa dai wata Ataa dabam, yar aikin gidansu? Yar talakawa yar bara a tit

i? Dan kari, ita ce kike cewa za ki bata dama ta zaba? Har kike tunanin bata Aliyu? Ko dai kin manta wacece ita?”“Miye abun mantuwa a ciki? Yarinyar da a hannuna ta ke yanzu, talauci ba illa ba ne”

“Aa Wallahi illa ne idan kina da talaucin anya kina gan

in za ki iya shiga jirgi ki zo Abuja yau? Na dauka yar wata manyan mutane ce a cikin sokoto ko nigeria ma”

“A haka dai yayanki suke sonta”

“Lalala ban yarda ba, ina dalilin jayaya akan wannan banzar yarinyar? To ko dai ta shanye ku ne gaba daya? Dama

n ance buzayen nan mayu ne, ke kira min Aliyu yanzu nan”

Mama Fulani ta karasa tana kallon Rukaiya a take Rukaiya ta kira a waya ta sanar masa Mama Fulani na son ganinsa, daman yana garden yana ta kallon gurin da Ataa ta saba tsayawa ta wanke plate dint

a gani yake kamar tana a gurin. Be bata lokaci ba ya shigo falon.

“Aliyu Ataa kake so? Ko kuwa Momy ce take son taka maka ita ta cilasta maka?”

Tun kan ya karaso kusa da ita ta aika masa da wannan tambayar. Sai dai be amsa mata ba sai da ya karaso ku

sa da ita ya zauna.

“Mama na yi wani abun ne?”

“Wa kake so? Wa kake son ka kara aura a matsayin mata ta biyu?”

“Ataa Mama and i need your support”

“My support? Aliyu are you out of your Sense? Yar talakawan yar aikin gidanku”

Yayi shiru be

ce komai ba.

“Lalala ban aminta ba ka cireta a ranka tun wuri, eyy yarinya ta samu matsayi har da wani bata zabi ake tsakanin Aliyu da Muhseen ko? Eh lallai”

Daga Aliyu har Momy shiru sukai, Momy bata son saka bakinta saboda Aliyu ne, shi kuma ya ra

sa kalmomin da zai hada ya fahimtar da Mama Fulani ta ya ma za'ayi ta fahimta, yasan duk wanda zai fadawa yana son Ataa a yanzu zai yi mamaki. Fada sosai Mama Fulani ta fara masa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, tun yana iya saurare har ya ji kun

nuwansa ba za su iya daukar yadda take aibanta Ataa ba a gabansa. Harabar gidan ya fito yana sacikawa bakinsa iska ya busar.Part din Ammy ya nufa daman bata san da zuwansu ba, domin Momy ba ta kira ta fada mata tana nan zuwa kamar yadda ta saba ba. Ta yi f

arinciki sosai da ganinsa daman ita kadai ce a falon. Ba laifin ya dan sake yayi fira da ita duk kuwa da be saba hakan ba domin zancensa be eh a a ba, sai kuma tambayar wani abu idan ta kama.

   Fried rice da miya ta kawo masa ya karba ba dan yana jin ya

na son ci ba, domin ko da safe da Lipton kawai ya karya be sake cin komai ba. Wayarsa ce tai ringing yana dubawa ya ga Number Abbah, yayi mamakin ganin kiransa domin ba kasafai yake kiransa ba sai idan wani abun ya taso.

“Assalamu Alaikum Abbah”

“Wa

'alaikassalam, Aliyu kun shigo abujar ne?”

“Eh Abbah”

“Ka same ni office yanzu”

“Okay Abbah”

Yana sauke wayar ya aje plate din abincin ya mike tsaye.

“Ammy Abbah yana nema na bari na je na dawo”

“To a dawo lafiya abincin sai ka dawo ko”

“Eh”

Ya fice da sauri cike da son sanin dalilin kiran da Abbah yake masa. Sai da ya shiga part dinsa ya dauki keys din motarsa da ke gidan,sannan ya fito ya bude motar ya shiga. Cikin ka kannen lokaci ya isa kamfanin kamin ya isa office dinsa ya kira

a waya ya sanar masa ga shi nan zuwa, sai Abbah ya ce ya jira shi office din yana wani gurin meeting a kamfani, haka Aliyu ya shiga ya zauna har aka kira sallah Azahar ya fita yaje yai sallah ya dawo ya zauna a ciki yana jiran Abbah. Sai kusam uku da yan m

intuna Abbah ya shigo office din rike da takardu a hannunsa. Cikinnl girmamawa Aliyu ya gaishe shi ya sama masa yana murmushi sannan ya zauna a kujerarsa mai lilo yana kallon Aliyu ya ce.

“Hajiya Fulani fada abunda ya faru”

Aliyu ya yi kamar be san k

omai ba.

“Na me Abbah?”

“Ance Momy ta zaba muku mata kai da Muhseen ko? Shi Muhseen ya ki yarda ya ce ta ka yake so?”

Aliyu ya yi kasa da kansa.

“Na kira Daddynku na yi magana da shi, indai yarinya tana son ka kana son ta za a aura maka ita”

Da sauri Aliyu ya kalli Abbah, sai ya rasa abunda zai ce, sam be tsammaci haka daga gurin Abbah ba.

“Amman Abbah Mama bata so, saboda yarinyar ba yar masu kudi ba ce, tana ganin kamar kaskanci ne a gurina da gurinta?”

“Yarinyar bata da tarbiya ne

?”

“Tana da Abbah talauci ne kawai matsalarta”

“Kar wannan ya dame ka idan ka ce zaka biye fulani da tsare tsarenta zaka sha wahala kamin ka samu wacce zata dace da ra'ayinta”“Abbah idan bata so zai zama da matsala a ciki, yanzu haka fadan da ta gama

min kenan?”

“Kai iyayen yarinyar sun tashi aurar da ita? Kuma ka tabbatar tana son ka?”

“Momy ce zata mata komai, kuma ba dole ne idan a daura ta tare a lokacin ba, amman daurawar zai kwantar min da hankali Abbah”

“To ka shirya assabar mai zuwa z

a a daura muku aure”

“Abbah da gaske?”

“Na taba maka wasa? Ka shirya kuma ka sanar da iyeyenta ka sadani da su ni nan zan daura maka aure”

“Abbah....”

Sai kuma yai shiru Abbah ya kalleshi da kyau.

“Wani abun ne?”

“Gaskiyar yarinyar bata

kowa a yanzu, daman yan nijar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login