Showing 24001 words to 27000 words out of 237425 words

Chapter 9 - ZAKI COMPLETE

na tuna da kudin da suke hannu, ba ko tantama

sun fadi tun a lokacin da hadarin ya afku, da sauri na fita emergency din zuwa neman mutumen ko zan ganshi ya taimaka min, sai na nemesa na rasa, wata kila shi kuma ya tafiyarsa. Komawa nai ciki ina rokonsu su taimaka su kula da shi kamin na kawo kudi sai

suka ce min wai sai na zo da police za su iya taba shi, haka suka kyale Lukman a wulakance cikin gurin da duban mutane suke sai ihu yake. Ji nai kamar na je na dauke shi nai tafiyata idan kuma na dauke shi ban san inda zan kai shi ba, ba ni da wani magani

da zan iya masa.

Tasowa nai na fito daga cikin gurin ina tafiya hawaye masu zafi suna sauko min, yanzu yan kudin da suka rage min da kuma wadanda mukai bara muka samu na zubar saboda kidima, ga shi Lukman ya bugu da mota ga Nana tana asibiti tana jira

n na kawo kudin maganin da hoto. Wani abu na ji ya tsaya min a zuciya yana neman numfashina, a take tsayuwa ta gagareni, ba zan iya fadar inda na ke ba, iyakar abunda na sani na ji na zauna saman wani abu mai kamar kaya, sai kuma duhu ya rufe min ido har n

a soma jin kamar babu sauran numfashi a tare da ni.

Ban san iya awanin ko mintuna dana dauka a gurin ba, kamar wacce aka sakowa numfashi daga sama haka na farka firgigit ina maida numfashin wahala, baren kaina na ji yana min ciwo, gurin da na ke zaune

sai sukana ake, hakan yasa na unkura na tashi tsaye sai na lura ashe saman fulawoyin na ke zaune masu kaya, da na soma tafiya sai na ji jiri na ďibata idanuwana kuma suna ta lumshewa kamar mai jin bachi. Haka na fito bakin gate din asibitin ina tafiya kama

r marar lafiya, bakin titi na tsaya na tari wani mai Napep yana tare da wata mace a baya, yana tsawa na duka har kasa na hade hannayena ina rokonsa.

“Dan Allah ka taimaka min ba, kanene yai hadari mutumen daya kawo shi asibiti ya gudu ya bar mu, su kum

a sun ce baza su duba shi ba sai na kawo police kuma ba ni ko kudin siyen kati”

“Yanzu me kike so?”

Matar da ke baya ta fada tana dage nikab din dake fuskarta.

“So na ke ka taimaka min na dauko shi na saka a ciki na kai shi gida”

“Innalillahi

wa'inna ilaihirraji'u, mutane suna ciki hali, ke yanzu kudin Napep din ma ya gagara? Allah ka ba mu karfi da ikon da za mu iya taimakon bayinka marasa shi”

Ta fada tana miko min dubu daya yan dari biyu guda biyar, sannan ya ciro dari biyu ta mikawa mai

Napep din.

“Je ka kaita ni zan tari wata na shiga”

“Na gode Allah ya saka miki da alheri”

Tana fita na shiga zauna a ciki mai Napep din ya janyo ta ciki muka shiga har bakin kofar emergency. Da sauri na fita daga napep din na shiga ciki sai na sa

me shi a inda na barshi, sai dai baya motsi babu alamar numfashi a tare da shi.

“Kun kasheshi, kun bar shi nan ba ku taimaka masa ba, ya mutu kun ji dadi”

Shine abunda na fada ina kallon nurses din ina hawaye kamar ba gobe, sannan na duka na saka han

nuna biyu na tallabo shi na juyo na fito da shi mai Napep din ya taimaka min ya saka shi a ciki ni kuma na shiga, ina ta shafa fuskarsa ko zai farka amman shiru, can na kai hannuna gurin hancinsa sai na ji babu numfashi ba alamunsa.

Har muka isa Clappe

rto road kuka kawai na ke ina rike da Lukman, mai Napep din ne ya fito ya saka hannunsa ya dauko shi ya kai shi gurin da na nuna nasa wato cikin kangon gidan nan ya aje min shi sannan na saka hannunsa aljihu ya ciro dari biyar ya miko min.

“Gashi ku ka

ra Allah ya muku mafita”

“Na gode”

Na Fada cikin muryar kuka. Sai ya juya cike da tausayawa ya fice, ni kuma na zauna a gurin ina ta kallon Lukman wai ko zai motsa amman shi, har hannuna na kai na dan matsa gurin kafar inda na ga yana riko dazun ko z

ai motsa amman shiru. Kaina na daga saman ina hawaye cikin daga murya irin da masu neman dauki nan cikin gaggawa na ce.

“Allah kai ka so haka a garemu, komai ya samemu da saninka ne da yardarka, Allah ka sani ba ni da wata mafita sai ta ka, Allah kana

ganin halin da na ke ciki Allah ka kawo min dauki”

Sannan na tashi na je nai alwala nayi Sallah, ban tashi daga gurin ba, sai da na gabatar da sallah la'asar, sannan na mike tsaye ina murza kudin da ke hannuna zuciyata sai wani abu take min babu dadi, d

a kafa na taka zuwa asibitin uduth wannan karon babu masu gadin dakunan kasancewar la'asar, cike da nauyin kafa na ke taka ward din ina sakesaken abunda zan fadawa Nana, idan ma na boye mata dole zata san gaskiya, idan kuma na fada mata zata iya shiga wani

hali sai na kasa za6a tsakanin fada mata da kuma akasin haka.

Kwance na sameta ba kamar dazun da na bar ta jingine ba, ban san hawaye na min zuba ba har sai da ta nuna fuskar tawa.

“Miya saka kike kuka Ataa? Wani abun ya samu Lukman ne?”

Saurin

share hawayen nai ina girgiza mata kai.

“Aa babu abunda ya same shi”

“Karki boye min, fada min babu abunda zan iya da lamarin Allah”

“Mota ta kade shi Nana, kuma an kai shi asibiti amman baya motsi na dauko shi na dawo da shi gida, kuma kudin da

na samu da ragowar duka sun fadi”

Kamar wacce aka yi ma allurar karfi da kuzari, haka ta tashi zaune kamar ba ita ba.

“Lukman din ya mutu ko?”

“Ban sani ba amman dai baya numfashi kuma yai ta ihu lokacin da aka kade shi ya rike kafarsa yana da ku

ka sosai”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u ”

Ta fada tana mikewa tsaye har mamaki ta bani dan zaka rantse da Allah cewar ba ita ce ke kwance malala dazun ba.

“Mu tafi”

Ta fada tana jan dayan zanen da ke saman gadon ta rufe jikinta. Ni kuma n

ai saurin rikata n zaunar.

“Ba za su bari mu tafi ba sai mun biya kudin gado Nana, ki zauna zan je samo wasu kudin na biyasu sai mu koma gida”

Zaunawa tai a saman gadon sai ta fashe da wani irin kuka mai taba zuciya. Ni kuma nai saurin fita daga gur

in ina sauri kamar zan halde kafafun.

Lokacin da na fito bakin kofar asibitin sai na rasa abunda zan yi, wace hanya zan bi na samu kudi? Baran zan sake komawa ko kuwa sata zanje na yi ko mutuncina zan siyar, idan ma sata zan yi ina kudin suke da har za

n sata? Ina mai siyen mutuncin yake da har zai siya, a nawa zai siya, mi zai biyo bayan wannan?

Wani tunanin ya zo min, da sauri ma tari Napep na shiga na ce ya kaini ofishin yan sanda, yana tafe gabana na faduwa abunda da wacce ba ta saba ba, musamma

n a lokacin dana sauka daga Napep din na doshi cikin ofishin, sai bugun gabana ya karu ina jin kamar ba zan iya ba, ganin irin manyan

bingogin da suke rike da su. A haka dai na daure na shiga gurin ina sallama muryata na rawa kamar mai jin sanyi.

“As..

sa.. La.mu...Alai..kum.”

Mutum biyu suka amsa min, sauran kuma suna ta kula da wasu mutane da ke kusa da su suna musu wani complain din dabam.

“Wa kike nema?”

Wani mai babban muryar ya tambaya yana kallon yanayina.

“Karar wani likita na kawo”

“Likita kuma? Me yai miki?”

“Kodar mahaifiyata ya cire, ba tare da saninmu ba, kuma ni ban ce ya cire mata ba”

Na fada ina kuka. Sai daya daga cikinsu ya zaro ido.

“What...?”

Sai dayan ya ce.

“Koda? Babbar magana, Robot bude nata file

ka dauki statement dinta”

A take na zayyana musu komai yadda ya faru cikin har da maganin da ya bani da kuma abinci, sannan na fadi yadda wacan likitan na uduth ya fada min.

“Amman ke ai ba ki da shaida”

“Amman ai hoton ya nuna bata da koda kamar

yadda likitan ya fada, kuma ashe ba ayi ma dafin maciji tiyati ni ban sani ba”

Cikin kuka nake wannan maganar ina share majina da Hijab dina.

“Dan Allah ku taimaka min ku kawto min hakkin mahaifiyata, yanzu haka tana asibiti babu kudin jinya sakamak

on kodar nan da ya cire mata”

“Kin san inda likitan ya ke?”

“Ban sani ba, amman na san asibitinsa kuma can yake aiki kusan ma can yake zama kullum”

“To yanzu kin san yadda za ayi kina da na mai?”

Na mika masa dubu da dari biyar din da ke hannun

a.

“Wannan kudin ne kawai ban sani ba ko za su isa”

Daya daga cikinsu ya karba sannan ya zagayo tare da wasu polisawan uku suka fito daga ofishin, sai da suka janyo motar yan sanda suka ce da ni

na zo na shiga na nuna inda yake, cikin kuzari na shig

a motar ina ta jindadi da ganin kamar za su kwato min hakkina ne, ashe ban sani ba gwanwo ne zai juye da mujiya.

_______________

Ayi hakuri na yau be kai yawan na kullum ba, gobe zan cika In-Sha-Allah.

https://my.w.tt/PWohUhlPv9.

*Z A K

I*

By Khadeeja Candy

1





1





“Momy muna neman mai aiki wacce zata rika gyara mana gida”

Ya fada yana aunar jalof din taliya da Momy ta zuba masa.

“Yar talakawa za'a nemo maka kenan, kaga ko dan za a ci amfaninta”

“Za tai ci amfaninmu

ai biyanta za a yi”

Momy ta yi murmushi.

“Dan wajen Fulani har yanzu ka ki yarda da cewar za ka ci ribar talaka ko?”

“Momy kece ai kin ji ki gane, idan ba wani abu zaka saka talaka ba ka biya shi me zai hada ka da shi, Mama Fulani tana yawan yi

min bitar kar na yarda ko rigata talaka ya rika balle kuma har ta kai ga alaka, kin san talaka dan hassada ne”

“Lallai kuwa, ina jiye maka tsoron ranar da zaka fara kaunar talaka, wata kila abun ba zai zo maka da sauki ba”

“Kamar ya?”

“Ba a son f

ariya, Allah zai iya jarrabarka ya koma talakan cikin talakawa, ko kuma Allah ya jarrabe ka da son yar talakawa wacce zaka duka har kasa kana rokon ta so ka?”

Ya tofar da ragowar abincin da ke bakinsa.

“Allah ya tsare ni Momy, ni ai bana da ra'ayin m

ace fiye da daya, Rahma ce kawai bayan ita babu wata”

“Wallahi yayan talakawan nan akwai tarbiya, da ace Rahma yar talakawa ce da zata fi ganin girma da girmanka fiye da yanzun”

“Ko a yanzu tana ganin girman ki Momy, kawai dai ita ta tashi a rayuwar

turai ne, kuma kin san irin Rahma bata tashi gidan wahala ba shiyasa....”

“Hmmm To Allah ya kyauta”

Shine abunda Momy ta fada daga karshe sannan ta tashi daga dinning din ta nufi kitchen. Sai bayan sallah magariba ya biya gidan family house dinsu Rah

ma ya dauko matarsa suka dawo gida. Kamar wata marar lafiya haka ta shigo cikin falon tana takawa kamar mai jin wahalar tafiyar.

“Wani abun ne Dear?”

“Aa Daddy be dawo ba, kuma ance yai hasara kudi da yawa a shopping mall dinsa daya kone”

“Shine k

uma za ki dauki damuwar ki saka a ranki? Bayan kin san lalurarki?”

Tai murmushi tana kai hannayenta ta zagaye wuyansa.

“Ina kokarin kawarda damuwar fa ko dan saboda na rayu da kai”

Kissing din lips dinta yai sai kuma ya rumgume ta a kirjinsa.

“Ka yi Momy maganar mai aikin? Ni wallahi har kyamar shigowa dakin nan na ke, duk datti”

Yai shiru be ce da ita komai ba.

“Bathrooms din mu duka suna son gyara fa, ga tarin wanke-wanke, ga kitchen din mu and bedrooms duka datti, ko mopping an dade

ba ayi ba, kuma kasan ba zan iya ba”

“Shiiiiiiiii”

Ya fada yana shafa bayanta, yasanta da  yawan magana wani lokacin kamar radio, ga shi kuma baya son yawan magana sai idan da Mama Fulani ne ko Momy.

“Doc Asim zai rika zuwa yana duba ki kullum”

Ya fada bayan ya saketa, sannan na nufi upstairs.

ATAA POV.

Mun taki sa'a domin kuwa mun isa cikin asibitin a lokacin da yake tsaka da aiki, ina gaba polisawan ba bayana kowa sai kallon mu yake har muka isa ofishinsa, da muka shiga sai muka tarar

baya ciki wai yana dakin tiyata, a ofishin mukai tsaye cirkocirko muna jiransa har ya fito daga dakin tiyatar ya shigo ofishin, da fari tsayawa yai yana kallon polisawan kamin ya maida dubansa a zuwa gareni, da alama an labarta masa zuwan mu tun kan ya sh

igo ofishin.

“Kai ne Doc Asim?”

Daya daga cikin yan sanda ya fada sai ya gyada masa kai.

“Yes wani abun ne?”

“You're Under arrest”

“Akan me?”

Ya tambaya kamar da gadara, ni kuma nai karfin halin bude bakina na ce.

“Kai ka cirewa Mahai

fiyata koda dan haka dole a kama ka kuma a kwato mata hakkinta”

“Kodar da kika siyar? Blackmailing dina za ki yi? Are you out of your sense?”

Mamakin furucinsa ya hanani ko da motsin kirki balle har na sake cewa wani abu, waina siyar da koda, yaushe

na siyar? Wa na siyarwa ya ma za ayi na siyar da kodar mahaifiyata.

“Oficer kar yarinyar tai wasa da hankalinku ta raina muku aiki, kar kuma ku isko ni har cikin ofishin ku ce za ku ci min mutumci akan aikin, muje station din ku hada da dan sanda ku day

a zan saka shi motata sai mu tafi station din amman ni ba zan shiga motar ku ba”

Yadda ya bukata haka akai, ni da sauran polisawan muka koma a motar da muka zo, shi kuma ya shiga motarsa da dayan dan sanda bayan ya dauki wasu takardu.

A motar yan sanda

sukai ta tambaya wai da gaskiya na siyar da kodar nai ta musu rantsuwar ban siyar ba, ban ma ya cire ba, idan har na siyar mi zai sa na kawo kararsa gurinsu, a nan suka min tausayawa kuma suka ce za su kwatar min hakkina, dan sanda yana ya matse ni sosai

jikinsa na ta gogar nawa.

“Yarinya kyakkyawa da ita za a ci amanarta, ki sha kuruminki sai mun kwato miki hakki”

Shine abunda ya fada yana kallona da jajayen kamar dan shaye-shaye. A lokacin da muka isa Station din sai muka shiga ciki, a nan ya fiddo

da wasu takardu ciki har da takardar da na sakawa hannu lokacin da za ayi ma Nana tiyata.

“Kin san kin saka hannu a wannan takardar ko ba ki sani ba?”

“Na saka”

Na amsa masa ina kallon takardar.

“Magani kawai na dubu nawa kika siya mata? Ab

incin da kike ci safe da rana da dare daga Hotel ake kawo miki duk ina kika samu kudin?”

Kasa magana nai sai hawaye na ke gaba daya ya gama dauren kafafu kai har ma da jikin gaba daya. Sai kuma ya juya gurin polisawan ya ce.

“Yi ma Babban likita iri

na sheri abu ne mai sauki domin ta samu kudi, yarinyar nan ina zaman ta dauko mahaifiyarta ta kawo wai maciji ya tsareta, kuma babu yadda zata yi ita bata da gabas bata da yamma, na ce ni ba zan taba ba, sai an kawo kudi, sai kawai ta ji ina magana da wani

mai neman koda a nan tace zata siyar kuma babu yadda ban yi da ita ba akan ta nemo manyanta sai tace daga ita sai mahaifiyarta suke wai basu da kowa a nan, kuma idan ban taimaka na siye kodar mahaifiyarta ba, babu inda zata samo kudin da za ayi mata allur

ar dafin macijin, a haka tai convince dina na yarda na bata takarda ta saka hannu, na bata kudinta ta ce aa na aje gurina na siya mata magani ragowar canjin na bata wannan ne kawai abunda na sani”

Cikin kuka na nuna shi da yatsa na ce .

“Allah ya isa

, karshenka ba zai yi kyau ba, kuma za ka ga abunda zai same ka?”

“Kaji ko? Oficer nima bude min file sai na ji akan me take kokarin bata min suna”

Ya fada yana nuna ni. A maimakon polisawan suyi wani abu sai na ga kamar suna tsoronsa, ashe ya siye d

ayan sandan daya shiga motarsa, sai kawai na ga sun fita waje har da shi Doc Asim din sun kebe suna ta magana da juna, suna kawowa sai suka fara tuhumata wai waya biyani na bata masa suna.

“Babu wanda ya saka ni, amman wallahi karya ya fada”

“Kina d

a wata shaida ne? ”

“Ba ni da ita, amman Allah shine shaidata”

“Aikin banza, haka kawai za ki nemi batawa mutum aiki da suna?”

“Wallahi ba bata masa nai ba, gaskiya na fada”

“Wannan duk shairin makiya ne, so kawai take ta bata min suna, dan hak

a su saka ta a cell sai ta fada muku wanda ya saka ta yin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login