Showing 195001 words to 198000 words out of 237425 words
sai ya saka dayan hannunsa yana shafa cikina.
“Kamar haka, idan kin haihu”
Zaro ido nai
sai yanzu na gane komai barobaro da sauri ya juyo.
“Ina ciki kenan?”
Juyar da ni yai ya rungume.
“Muna da ciki dai Baby not just you, ko ma na ce ina da ciki Baby i love you”
Ya fada saitin kunnena. Sai na fashe da kuka.
“Aa yanzu kowa sai
ya san abunda ya faru ko? Idan aka gan ni da ciki”
“Daman ai an san dole wani abun zai faru”
“Amman dai akwai kunya kuma ciki da wahala”
“Ba wani wahala, kunya kuma ai tunda kika yarda kika zauna gidan miji ta wuce”
Ban san dalilin rashin jind
adin cikin ba, sai ma tsoro daya kama ni yo ni ya ma zan yi na haihu? Kuka na fara bana wasa ba tun yana rarrashina a hankali har abun ya koma bashi tsoro.
“Haba Babyn wannan fa abun farinciki ne, wannan shekarar ina cikin ta tara da aure amman ban sam
u haihuwa ba sai yanzu, Momy Mama Fulani Abbah Daddyn da duk family and friends da sisters idan suka ji dadi za su ji kuma su so ki sosai”
“A a nidai ba yanzu ba nidai bana ma so gaba daya”
Zaunar da ni nai saman gadon ya zuba min ido yana ta kallona
.
“Dan girman Allah Babyna ki daina kukan nan, kar kukan ya cutar da abunda ke cikinki”
“Ba zan iya iya kallon kowa ba idan nai ciki, kuma ba zan iya haihuwa ba”
“Ciki ai kin riga kin yi, yi hakuri ba za a sake wani cikin ba”
“Da gaske?”
Da
riya yai ya gyada min kai. Sannan na sausauta kuka shi kuma ya tashi yaje debo min ruwa. Yana fita na daga rigata na leka cikina sa nai sauri na rufe.
ALIYU POV.
Ya sauko downstairs wayarsa a hannunsa yana kiran Nasir, wannan karon be jira Nasir
ya fara magana ba kamar yadda ya saba yana kiran daukar kiran Aliyu ya ce
“Congratulations to us na kuma zama Daddy nima na yi ajiya a cikin Ayusher”
“Wowooooooooooooo Aliyu are you serious? Oh my God”
“Na rantse da Allah Nasir har ban san irin f
arincikin da zan yi ba, na rasa abunda zan yi Wallahi ji na ke kamar na hadeye Ayusher a yau”
“Wannan abun murna ne a garemu gaba daya ai, amman Momy ta ji da Mama Fulani?”
“Ban fadawa kowa ba sai kai, nima yanzu na ga result din”
“Ni zan yi musu
albishir karka ce zaka fada musu na san baka da kunya”
“Ai na zancen kunya a nan Nasir, wane irin kunya a gurin farinciki? Ai ba wannan zancen shi dan na fada na ce tana da ciki kuma wani abun kunya ne? Ita ma yanzu ta gama kuka wai idan suna ji zata ji
kunya”
“Ai kai ba saka gane ba ne saboda ka saba yin abu normal ne”
Murmushi Aliyu yai ya kashe wayar, har ga Allah shi be ga abun kunya a fadar matarsa ta yi ciki ba, shi ba duk abunda ya san idan ya aikata ba haramun yai ba to be ga abun jin kunya
a ciki ba, da dai zina ya aikata ko wani alfasha shine abun jin kunya, domin shi ya fi dacewa ka ji kunyar Ubangijinka sama da na kowa. Freezer ya bude ya dauko ruwan gora ya zuba sai da ya sha dan ya ji yanayin sanyinsu kar su cutar da abun cikinta sann
an ya sirka da wasu ruwan sai ya dauko kofin ya dawo dakin da take. Inda ya barta a nan ya same ta zaune da kansa ya kai mata ruwan a baki yana bata a hankali har ta sha rabin kofin sannan ya aje ya zauna kusa da ita ya zuba mata ido. Be san abunda zai mat
a ba, rumgumatar ba zai wadatar da shi ba, kallonta ba zai wadatar da shi ba, saurarenta ko yi mata wani abu ba zai wadatar da shi ba, yana jin cewar hadeye ta kawai zai yi ta zauna tana cikin cikinsa ita da abunda ke cikinta sannan hankalinsa ya kwanta sa
i dai kuma babu wannan damar ya rasa inda zai sakata tsabar farinciki.
Haka yai zaune ya sakata a gaba har aka kira sallah la'asar sannan ya sumbaci goshin nata da cikin ya fita zuwa masallaci, daga masallacin ya wuce restaurant ya siyo musu abinci, ya
so ya kira ya tambaye ta abunda take so amman babu yadda zai yi tunda bata da waya. After restaurant ya wuce wani babban shago ya siyo mata sabon phone mai tsada wacce ake yayi sannan na nufo gida, ko da ya shigo ya ji motsinta a kitchen sai ya nufi kitche
n din kai tsaye taliyar indomie ya tarar tana zubawa a plate tana murmushi.
“Yunwa na ke ji sosai shi ne na dafa indomie”
Ta fada masa ganin ya tsaya yana kallonta da murmushi.
“Wow yau Gimbiyata ta yi aiki da kanta bari na dan dana na ji, ashe
kin iya girki ko?”
“Eh na iya tuwo na iya dafaduka na iya dafa taliya na iya sararafa kanzo na iya shimkafa da miya kuma na iya da wake, amman ban iya amfani da wacan abun ba sai na daka a turmi”
“Wow amman dai ai ba sai kin yi aiki da yawa haka ba”
Ya karasa kusa da ita yana rike da ledodin a hannunsa. Fork ta dauko ta saka ya debo taliyar sai ya busa masa a bakinta sai da huce sannan ta kai masa a baki, luma daya ya rumtse ido saboda wani azababen yaji da ya ji, da sauri ya aje ledodin hannunsa y
a dauke plate din.
“Wallahi ba za ki ci wannan abincin ba”
“Mi yai?”
“Wannan uban ya jin?”
“Ji nai ina son ya ji shine an cika kadan”
“Wannan cikin be wani kwari ba za ki ce za ki ci wannan yajin, noooooo ga wani abincin na siyo miki ai zo m
u ci tare”
Ta mairairaice fuska.
“Haba Aliyu ina so Wallahi”
“Haba Baby ki tausaya min mana”
Aje plate din yai gefe ya bude dayar ledar mai waya ya dauko ya mika mata.
“Ga waya ke ma ki fara bugawa kina daukar hoto”
Ba shiri da zaro ido
ta karbi wayar da sauri da daka wani irin tsalle kamin da dire yai saurin cabeta.
“Ke yanzu fa ba ke kadai kike ba, ki daina irin wannan abun”
Ina bata ma jin me yake fada sai ihu take ya rumgume shi sabar farinciki har da yi masa kiss a fuska.
“Na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na”
Haka tai ta maimaitawa sai da ya rufe mata baki, sai kuma ta fashe da kuka kuka irin sosai din nan kamar wacce akai wani abu rasa tai me zata yi, ita a
rayuwarta bata taba rika waya ba ko karama balle babba irin wannan mai screen kato.
Rikota yai suka baro kitchen din suka dawo falo suka zauna, sai ya karbi wayar ya bude mata ya hada mata.
“Idan na fita ko kuma zan saka Nasir ya siyo miki layi mai
kyau na ki na kanki, kuma yanzu sai an saka wayar carji idan ta yi full sai a fara tabawa”
Ta yi saurin tashi daga kan kujerar tare da carjar wayar ta nufi socket ta saka ta zauna s gurin ta tsare wayar. Shi kuka ya tashi ya koma kitchen din ya dauko m
usu abincin daya siyo musu ya zo kusa da ita ya zauna ya bude abincin.
“Aliyu ka dauko Nana na nuna mata wayata”
“Ba yau ba dai, gobe ai zamu je mu gaisheta sai ki nuna mata”
“Har sai gobe”
Ya gyda mata kai yana deban abincin ya bata a baki, j
in tai bata gamsu ba har sai da ta dawo saman jikinsa ta zauna ta rumgume.
“Na gode sosai Allah ya kara arziki ya tsareka daga dukan sheri Allah ya biya maka bukatunka na alheri”
“Nima na gode da ki kai ciki”
Rankwashinta ya ji a kanta ya ji kami
n ya ji sautin dariyarta yai murmushi ya kara rumgume ta. Ba wani abun kirki ta ci ba abincin tsabar zumudin waya ya saka ta manta da wani zancen cin abinci duk kuwa da tana jin yunwar. Ranar a gaban wayar ta kwana duk yadda ya so ta dawo ciki daki su kwan
ta kin tai tana ta jiran har sai wayar ta yi full sannan ta fara tabawa, a dole ya dauko matashin kai ya aje a gurin yai mata matashin kai da hannunsa ya lulluba musu mayafi suka kwana a gurin har safe.
MAMA FULANI POV.
Tun da Abbah ya dawo ya
fada mata abunda ya faru kuma ya ce mata Mahaifiyarta Ataa zata zo kuma a nan zata sauka sai ta fasa inda zata saka kanta sabar kunya, dole ne tai mata tarba ta musamman kasancewar yar sarkin Agadaz sai dai taya? Baya ta wulakanta yarta? Ta sani har abada
ita da Ataa ba za su taba ganin kimarta ba, yadda za tai ido biyu da ita ma take tunani. Gabanta be kara faduwa ba sai da ta ji tsayawar motar Aliyu da sauri ta tashi ta shige dakinta har da hadawa da gudu.
Saman gado ta haye ya lulluba da blanket tana
jin sallamar Aliyu ta fara rawar sanye abunda bata taba ba a rayuwarta.
“Mama ba ki da lafiya ne?”
Ganin shi kadai ya shigo yasa ta tashi zaune cikin yanayin damuwa tana kallonsa ta ce.
“Aliyu ina jin kunyar hada ido da Ataa da mahaifiyarta, ba
ni da wannan idon na kallonsu ko na ce zan musu wata magana, waya taba tsammanin haka Aliyu? Ko daman can ka sani?”
Zaunawa yai kusa da ita cike da damuwa da damuwarta domin ita din ma uwarsa ce kuma mai damuwa da abunda ya dame shi.
“Ban sani ba Ma
ma ban ma taba kawo wa a rana cewar wata wana haka zai faru ba, iyakar abunda na rike wata rana dole yan'uwanta za su bayyana, amman ban taba kawowa kaina cewar masu kudi ba”
“Ka huta, Momy ma bata mata komai ba sai ni oh ni Fulani yau na jin kunya na s
higa uku, Wallahi ko a mafarki aka fada min cewar wata rana yarinyar zata zama haka ba zan yarda ba, amman ji abunda ya faru? Ina ta zagin yarinyar nan ina ta ci mata mutunci ashe ma har ta fi mu komai”
“Mahaifiyarta tana can falo, Ayusher kuma tace zat
a tsaya bangaren Ammy”
“Eh ta tsaya can ai tana gaskiya, ni ai muguwa ce na san haka take kallona, ka ji fa rashin rabo jiya na hana yarinyar ruwan sha a gidan nan ashe ashe.... ”
Wannan karon har da kwalla gaba daya duniyar ta rikice mata, domin yad
da take son zuri'ar masu hannu da shuni da ace ba tai wa Ataa haka ba da yanzu sai ta kulla abota da Nana, kuma ta sake jikinta da ita amman ina ta bata komai. Tashi Aliyu yai ya fice daga dakin, ya barta ita kadai tana da tufka da warwara, har da dan leko
wa ta leki fuskar Nana ta koma cikin dakin, gaba daya kunya take ji kamar wacce tai sata ko. Maryam ce ta shigo cikin dakin sai Mama Fulani ta juyo da sauri ta kalleta.
“Ke kin gaishe ta?”
“Eh na gaishe ta ni da Rukaiyah”
“Ta karba miki?”
“Ta
karba mana amman tana ta kallonmu”
“Kunyar sauka na ke ji”
Ta fada gumi na karyo mata.
“Wallahi Mama da kunya wa ya saka ran haka zai faru? Kara ma Ammy bata taba mata komai ba, ita da Ya Muhseen da balle Ya Aliyu da yake mijinta gaba daya”
Mam
a Fulani ta dora hannu saman kai.
“Kai ni dai kan na shiga uku naga ta kaina, ni yanzu ya zan yi na fita na ganta?”
“Ai ita bata san ki ba, kuma kin san Ataa kila ma bata taba fadar abunda kika mata ba, kuma ai dole ki fita tunda Abbah yasa an kawo
ta nan”
Babu yadda Mama Fulani ta iya da abunda ya fi karfin wuta, dole ta kulle kunyarta a baren zane ta fito tana saukowa a hankali.
“Lale lale mara da Hajiya ashe har kin iso da yake ina wanka ban san shigowarki ba”
Ta fada tana dariya da far'a
kamar ba ita ba, Nana kan kallonta kawai take har ta zauna saman kujera tana gaisheta kamar zata risina.
“Hajiya Ina wuni? Ya gida ya hanya?”
“Lafiya kalau Alhamdulillah”
Nana ta amsa a hankali ba tare da ta saki fuskarta ba.
“Aa ya ba a kawo
mata komai ba? Ke Rukaiyah me kike yi baki kawo mata komai ba”
“An kawo mata ruwa da lemu ta ce a dauke wai ta koshi”
“To ko kin fi son na gida irin wanda ake hadawa wannan?”
“Bana jin kishin ruwa ko yunwa a yanzu, ki ce Fulani?”
Mama Fulani t
a ji kamar ta nitse cikin kasa.
“Eh ni ce, ai ni ce na rika Aliyu a hannuna na girma tun yana dan yaye, ai shi mai gidan nan mijina shi da mahaifin Aliyu uwa daya uba daya suke, mijina shine yaya sai mahaifin Aliyu ne kane, da yake a wacan lokacin ni d
a Momy a makaranta kawayen juna ne sosai tare mukai karatu a ABU zariya, mahaifin Aliyu dan'uwanta ne sun hada kakanni daya kuma......”
Ganin Nana ta zuba mata ido sai ya saka ta ji kunya har da yin kasa da kai.
“Ataa na yawan ba ni labarinki ai”
“Ehhh Wallahi ni ce fa Mama Fulanin dai, Allah sarki Ataa baiwar Allah, Wallahi Ashe abun haka ne, Wallahi ehh huh”
Mama Fulani sai kame kame take cike da kunya. Sai ta mike tsaye ta nufi kitchen.
“Ban ma dora girkin rana ba da yake bana dan jindad
i, Rukaiya ki kaita gurin Ammynku su gaisa kamin na gama abincin, sai dai ban sani ba ko kina da ra'ayin wani abun da za a dafa miki?”
“Aa”
Nana ta amsa tana mikewa tsaye ta bi bayan Rukaiyah wacce tuni ta nufi kofa, sai da ta fice Mama Fulani ta fad
i zaune a kofar kitchen ta dafe kanta.
“Wai ni Allah wannan abun be min dadi ba, ai dai kam ba zata ci komai nawa ba, tun da yarta zata fada mata cewar na hanata ita, ai idan da kunya ni ma ba zan ce zan bata ko?”
Magana take kamar mai yi da wani gab
a daya abun ya dameta a yanzu, wacce suke wulakantawa suna gani ba komai ba, yau ta koma sama da su, a cikin arzikin kakanta suke tsoma ludayinsu su ci.
Kamar kallon yadda Ammy take da far'a haka ta amsa mata sallamarta tai mata lallen marhabun, sa
i a lokacin Nana ta dan saki jiki har tai murmushi Rukaiya sai kallonta take ganin ta sakewa Ammy, kamin ta juya da fita.
“Aiko yanzu yanzu nan Aliyu ya fita tare da Ataa”
“Allah sarki ke ce Ammy ko?”
“Eh ni ce Allah dai ya sa lafiya?”
Ammy ta
fada tana dariya sai Nana ita ma tai dariyar.
“Lafiya kalau labarinki na ji a gurin Ataa, har da kowa da wa yaranki”
“Allah sarki ina ruwan Ataa, yaran duka basa nan sai Humaira ita ma yanzu ta fita ko bangaren Hajiya Fulani tai ban sani ba, ya gid
a ya hanya?”
“Alhamdulillah”
Ammy ta shiga ciki ta kawo mata ruwa da da dan abun tawa, a nan kam Nana ta sha ruwa har da cin abinci ma domin ita ta gama nata abincin rana tuni, Mama Fulani ma abunda ya faru ne yasa jikinta yai sanyi har taji kamar ba
ta da kuzarin girkin.
Mama Fulani na zaune bakin kofar kitchen din tana jimami sai ga Rukaiya ta dawo tana labarta mata cewar Nana ta sake a gurin Ammy har da dariya. Mama Fulani dai abun duniya ya isheta ta bata ce komai ba sai domin ta san duk abun
da akai mata bata da bakin magana a yanzu kuma ta cancanci fiye da hakan ma. Maryam ce ta fito rike da wayarta ta sauko kasa ta kawo mata. Ganin number Nasir yasa tai saurin picking.
“Mama ina wuni?”
“Lafiya Nasir ya gida”
Ta amsa da muryarta kam
ar ba ita ba.
“Lafiya Kalau Mama kira nai na miki albishir kamin kowa ya riga ni”
Gabanta ya fadi domin a halin da take yanzu tsoron jin komai take.
“Albishir kuma?”
“Eh Ataa ce bata jindadi Aliyu ya kaita Asibiti shine suka ce ciki ne”
Di
f Mama Fulani tai daukewar wuta, ta zaro ido ta mike tsaye da sauri sai kuma ta cire wayar daga kunnenta ta duba mai kiran ta ga Nasir din dai ne ta sake mayarwa a kunnenta sai idonta ya cika da kwalla.
“Allahu Akbar, Allah mai iko Allah sarki”
Ta k
ashe wayar sai ta koma saman sofa ta zauna sai hawaye suka fara mata sallama.
“Lafiya Mama? Miya faru?”
“Wai Ataa tana da ciki, kiji wani al'amari daga Allah, duka abubuwan nan sun zo mana ta hanyar da ba za mu iya nuna farincikinmu ko kulawarmu ba,
a da idan wani abun farinciki ya samu Aliyu ni yake fara yi ma albishir kamin kowa, amman yau ya fadawa Nasir wannan albishir din bayan ya san na fi kowa bukatar ya samu haihuwa, be fada min ba saboda yana tunanin bana son Ataa ba zan yi farinciki da samu
n cikin ba, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”
Tashi tai jiki ba gwari ta