Showing 210001 words to 213000 words out of 237425 words

Chapter 71 - ZAKI COMPLETE

daban ce da wadanda suke airport din Nigeria.

Motar biyar aka jera a filin j

irgin ban yi zaton na Mai marta ne ba har da na ga ya doshi can wasu fadawan sun fito daga motar da sauri suna tarbarsa, motar da ya shiga dabam da wacce mu muka shiga. Duka motocin bakake ne masu bakim gilashi a hankali suke tuka motar har muka hau babbar

hanyar garin. Yawacan mutanen da na ke kallo a titi da inda muke wucewa mafi yawansu suna sanye da rawani da ginuka su sum sha banban da na Nigeria domin su zaka ga wasu ginin na su tun na al'ada ne ba su zamanantar da shi ba, wasu kuma an kawata su kamar

garin sokoto.

Tun daga unguwar da muka shiga na gane cewar ana yin sarkin a unguwar yadda na ga mutane suna tsayawa kallonsa da daga masa hannu da masa kirari a cikin yaren buzanci. Wata irin katuwar masarauta muka shiga mai haske kamar rana sakamako

n kwan lantarki da aka saka ta ko'ina, ga kuma ginin da zanen masarautar irin an al'adar masarautar mai hawa biyu ce, wani bangaren kuma hawa daya ne, ga fadi kamar wata unguwa dukam wadanda suke cikin masarautar daga mai rawani sai mai hula manya da yara,

mutane da dama suka fito daga cikon gidan zuwa inda aka faka motarmu suna mana lalle marhabun a cikin kuwa har da manyan mazan da nake saka ran yayun Mama ne, ganinta ya bawa kowa, sai Mai Martaba ya fito sannan ta fito, muma muka fito ni dai sai wara ido

na ke abun ka da bakauyen mutum kuma mai son ganin masarauta. Kowa mamakin ganin Mama yake wasu kuma kallonta kawai suke wanda hakan ke nuna cewar ma su kallon nata ba su santa ba ne ko kuma sun manta, domin matasa me ko da yake a akwai manya a ciki, saur

an kan mamaki ya hana su magana, ta yadda na ga suna mamakin ne ya fahimtar da ni cewar Mai marta be fada musu cewar ya hadu da Mama ba sai dai zuwan da yai da ita na ba zata. Tare da Aliyu muka karasa gurin da Mama take tsaye shi kan Mai martaba tuni yayi

cikin fadarsa tare da manyan amsu take masa baya, Mama kuma ta fashe da kuka har sai da aka rakata a ka shiga da ita ciki.

Nima hawayen na ke har muka shiga cikin katuwar fadar wacce akaiwa ado da kwalliya irin ta mutanen da sai dai an zamanantar da ad

on ta yadda zai burge kowa gwanin sha'awa. Kwatatan fadin fadar da girma ta abu ne mai wahala ga mutum irina ne, domin kallon kwaliyar fadar ya hana ni tsayawa na lura da wadanda suke cikin fadar ma. Ban an kara da hakan ba har sai da masu yi ma Mai marta

ba kirarin cikin yalshen buzanci suka hankato da ni na dawo daga duniyar kallon fadar. Ashe tuni Mai Martaba yai gaba ni da Aliyu da wasu masu take mana baya tafiya muke zuwa wani bangare na fadar ban sani ba. Duk inda muka bi indai da mutane wasu kallon t

ausayi suke mana wasu kuma kallo ne akwai ma Mamaki, Mama kan sai aikin kuka take ni kuma ina taya ta da hawaye har muak shiga cikin gidan ni da ita da kuma Aliyu. Shi ka Mai Martana tuni ya kama wata hanyar dabam, Yusuf ne yake mana ja gaba har muka shiga

inda Mata da yaya da yawa suke. A tsakar gidan Mama ta gurfana ta fashe da wani sabon kuka mai taba zuciya, matan gaba daya suka zagaye ta suna kallonta kamin wasu su kama ta su shiga da ita ciki ciki. A bangaren da ke farko aka shiga da ita wanda na ke k

yautata zaton na mahaifiyarta ne ganin hoton Mai Martaba da wasu da ga kuma wati dattijiwa wacce tuni ta kawo bakin kofar falon tana kuka sosai har da saka hannunta ta dafe zuciyarta, Mama ta fadi a bakin kofar tana rike da hannun matar matar ma ta rike h

annun Mama gam tana kuka sosai, ba ni kadai ba kowa da ke gurin sai da ya tausawa Mama da matar saboda kukan da suke da kuma wasu ma har da kukan sai da sukai.

“Nana ce ta dawo, Nana ce, Nana, Nana”

Shine abunda yawancin matan da ke gurin suke fadi

tare da wasu dattijan mazan, wadanda suka tsaya rumgume da hannunsu suna kallon Mama. Sai da akai ta ba su hakuri sannan Mama ta tsagaita kukan da take ta shiga cikin katon falon wanda sanyin ac da kamshin turare ke maka lale marhabun. Muma shiga cikin fal

on ni da Aliyu sai aka dawo kan mu ana ta kallon mu wasu har da bude baki, ina jin lokacin da wasu ke fadar ni da Aliyu duka yayanta ne wai Aliyu ne yaya ni kanwa, wasu kuma su ce rakota mu kai. A lokacin da Dattijiwar ta zauna a falon sai ta daga kanta sa

ma hawaye nata mata zuba sai girgiza kai take.

“Mama ki yafe min, Mama ban kyauta miki ba aikata daidai ba, kuma ban kyautawa kaina ba na sani, kuma na cancanci ko wane irin hukunci ko fushi daga gareki”

Mama ce take fadin haka tana daga kasa zaune

rike da hannun matar tana kuka, matar ma kukan take irin na tsofi gwanin ban tausayi da taba zuciya, ta hanyar kalaman da Mama take na fahimci cewar dattijiwar Mahaifiyarta ce duk kuwa da kasancewar ba a su yi kama sosai ba domin Mama ta fi kama da Mai Mar

taba.

RAHMA POV.

daga idonta har makoshinta da fatar jikinta abushe suke kamar wacce. Ta shekara ashirin a gadon asibiti, kallo daya zaka mata ka fahimce akwai damuwa sosai a cikin zuciyarta, tun daga lokacin da aka kawo ta asibiti ta farka b

ata ce da kowa komai ba, ciki kuwa har da mahaifiyarta da ke kai da kawo tana yawan tambayarta idan tana bukatar wani abun, sai dai ta gyada kai ko ta girgiza, likitan da ya zo dubata ma sai dai ta girgiza masa kai ko ta gyada kai, rashin maganar ya damu k

owa domin an kasa gano matsalar rashin maganar tunda tana ji maganar ce kawai bata furtawa, wata kila damuwarta da ke ranta ce ta hana ta magana da kowa ko kuma wani ciwon ne, na daban ya same ra a yanzu.

“Ya kamata a sanar da mijinta Mommyn wannan abu

n, tun da ta tashi ba tai magana ba, idan kuma aka takura da magana ta fara hawaye wannan abun yayi yawa”

“Ya san da ita ai, tun da yai aure be waiwaye ba, idan ma ya zo ba wani maganin zai mata ba, koda ce take bukata kuma ta mu In-Sha-Allah”

Mahaif

iyarta ta mayarwa da Ikram amsa cikin hawaye, kallonsu kawai Rahma ke yi ba tare da tace komai ba.

“Ko jiya ya kirata amman ban daga ba saboda ban san mi zan fada masa ba, amman kyaleta a haka ba shine mafita ba, ya kamata ace ya san matarsa tana asibi

ti ko da ba zai mata komai ba”

“Idan ya kira ki daga ki fada masa cewar matarsa bata da lafiya tana asibiti”

“To Mommy”

Mommyn ta fice daga dakin cikin damuwa tana share hawayenta. Rahma ta bita da kallo, irin kallon na tausayin mai jinya idan yan

a jinyar kansa, tana son mahaifiyarta kamar yadda mahaifiyarta take sonta, zata mata sadaukardar da take jin ba lalle ne ta rayu bayan an dasa mata kodar ba, zata iya mutuwa bayan cirewa mahafiyarta kodar an sada mata ya zama an yi ba ayi ba kenan! Abu da

ya take da bukata a yanzu mutuwarta kamin a cire kodar mahaifiyarta a dasa mata, domin ta san zata bar duniyar komai daren dadewa, and mutuwarta zata fi mata rayuwarta a yanzu, domin bata da tabbacin idan an dasa mata wata kodar za ta rayu.

Abu daya ta

ke fata kuma take ta jira a yanzu zuwan mutuwarta kamin jibi da mahaifinta ya fada mata za a fita da ita waje ayi mata aikin kodar a can.

“Rahma?”

Ta juyo ta kalli Ikram tana hawaye kamar yadda yar'uwata take yi.

“Dan Allah ki cire damuwa a ran

ki ki yarda da duk abunda ya same ni daga Allah ne kuma babu mai iya miki maganinsa sai shi”

Kai kawai ta gyada mata ta hade yawun bakinta. Alama tai maga da ta bata wayarta sai ta ciro wayar daga jakarta ta mika mata. Kamar hadin baki tana karbar wayar

kiran Aliyu na shigowa wayarta da layinsa na Airtel. Kara wayar kawai tai a kirjinta ta lumshe ido tana hawaye.

“Ki dauka mana idan ba za ki iya ba ki ba ni”

Mika mata wayar tai ita kuma ta koma ta kwanta saboda numfashin da taji yana yin sama sama

kamar zai fita daga jikinta. Ikram ya dauki kiran ta saka wayar a hands-free tana kokarin danne kukanta.

“Hello Dear”

“Ba ita ba ce, Ikram ce”

“Ina Rahma?”

“Tana asibiti tun shekaranjiya”

Ikram ta fada cikin kuka.

“Mi ya same ta?”

“Ci

wonta ne ya taso har bata iya magana”

Sai kawai ya kashe wayar, Rahma har lokacin kuka take marar sauti tana dafe da zuciyarta gwanin ban tausayi, ga jikinta babu sauran karfi.

*Ayi hakuri a gafarce ni, dukan wani tsaikon da ke sakani typing da

dare na gama shi yau, Al-hamdulillah. In-Sha-Allah posting din dare ya kare da yarda Allah.*

*Ina mata son rage kiba? Ina mazan da kiba ta hana su sukuni? Ina masu jikin yai kyau kamar na yarinya? Ina masu fama da kujera ko wani ta bo a fuska? Ina masu

fama da hawan jini? Masu diabetic? Ag cera an gwada yayi an tantance ingancin babu shakku ko kadan. AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda

ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.*

*Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi f

atar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata ma

su fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziya

rci shafin mu http://agnutritioninternational.com.*

Daker Mama ta tsagaita kukan da take, har suka samu damar magana da juna.

“Babu wanda ya fada min za ki dawo, na yanke kauna daga ganinki na dauka kin mutuwa gaba daya, ko kuma kin tafi kin tafi kena

n ba zan sake saka ki a idona ba”

Mahaifiyarta ta fada tana hawaye, Mama kan kasa magana tai sai hawaye take, wani da na ke kyautata zaton Yayan Mama ne ya ce.

“Dukan mu mun san da maganar kawai dai mun boye miki ne saboda Mai Martaba ya bukaci haka

, mun san idan har kika sani za ki damu kanki sai kin ganta kuma ki katsa natsuwa”

Hannun Mama kawai take murjawa tana hawaye da motsa baki irin wadanda kuka yake cinsu.

“Nana Asma'u tana can ta kafa wata sabuwar rayuwar har ta yi ya ta aurar da yar

ta ba tare da sanin kowa ba, wata kila da Mai Martaba be ganta ba, da ba zata dawo garemu ba”

“Ina jin kunyar abunda na aikata, ina jin cewar ban yi daidai ba, shiyasa ba zan iya dawowa ko tunkarar kowa ba”

Mama ta fada sai Mahaifiyarta wacce zan iya

kira da kakata ta daga kanta tana kallon inda na ke har tana girgiza kai alamar mamaki da takaici abunda aka fada mata a yanzu. Ba mutanen gidan kadai ba, har da wadanda na ke ganin kamar daga wata unguwar suke shigo duk wanda ya shigo ya ga Mama sai ya f

ashe da kuka kuma yai mamaki, hakan na nuna cewar an dade da shafe tahirinta a cikin gidan ne, wanda ya santa ya san wanda kuma be santa ba sai dai a bashi labari wata kila ma wanim ba za a fada masa cewar masatautar na da wata Gimbiya mace daya ba, sai ab

un bakinciki a alakanta Gimbiyar da guduwa saboda soyayyah. Mun yi awa biyu a gurin sannan aka kai mu masauki, na yi zaton dabam za bara mu sai gashi an sauke mu daya daya  a wani bangare na gidan ni da Aliyu.

  Sallah ce ta zame nana wajibi sai da muka

sauke nauyinta sannan na fara shiga a bandakin da aka tanadar masa komai kamar an san da zuwanmu.

“Babyna”

“Na'am”

Na amsa daga can cikin bandaki sai kuma na leko domin na riga da na cire tufafin jikina, tawul ya miko min ban san da yayi gurinsa

ba sai yanzu, karba nai ya turo kofar sannan na fara kunna ruwan, ban wani dade ina wa kam ba na fito, ko da na fito Aliyu ya hada min tea a cikin kayan tea da aka kawo mana da kuma abinci.

“Ki fara shan wannan kamin ki ci komai kar cikinki ya kumbure



Sai da na zauna a bakin gadon da yake zaune sannan na mika hannu biyu zan karba, sai da ya shafi hannayen nawa kamin ya sakar min cup din ya nufi bathroom. Sai da na saka doguwar riga na gama shirya kaina sannan ha fito daga wankan.

“I can't wait n

a ganki da cinin cikin nan, abun yana burgeni fa”

Ya fada yana gyara daurin tawul din dake kogunsa, ni dai ban ce komai ba domin tuni kunya ya sauko min, ni wani lokacin har mamakin yadda Aliyu yake fadin wadansu maganganu nake ko aikata wani abun ba ta

reda kunya ba.

“Sauka kasa ki ci abinci”

“Kai ba zaka ci ba?”

“Zan ci mana, kin san dai ke a jirgi ba ki ci komai ba yunwa tana tare da ke, idan kuma ba kya bukatar wannan kalar abincin sai a siyo miki wani”

Na saka masa dariya jin irin karfin

halin da yake da shi.

“Ka san garin ne da za ka siyo min wani?”

“Dole sai an san gari ake yawo? Ga waya kuma zan iya bin hanya ina kallon abubuwa ina karantawa har na isa, ko kuma nai ta tambaya har na dace”

“Idan kuma ka bace fa?”

“Sai Mai M

artaba ya saka cigiyata, surikin masarauta ya bata kuma ga jikarsu da ciki”

Ya fada kamar ba shi yai maganar ba. Nikan dariya ce aikina har ya saka tufafinsa ya zauna kusa da ni, a tare muka ci abincin ba laifi ina sha'awar abunda aka kawo mana kuma na

ci sosai, kamin a bugo kofar dakin wai na fito ana son ganina. A yadda yanayin Aliyu da fuskarsa suka nuna kamar be jidadin kiran nawa ba, domin a ganinsa mun yi tafiya mai nisa haka kamata yai ace mun huta musamman ni da yasan ina da cikin na san wannan b

aya rasa nasaba da abunda ya saka yake kin bari na nai wata tafiyar ni kadai. Ni na fara fita na gaisa da wasu da aka fada min cewar iyayena da kuma kawunnai na sannan aka saka na dawo na kira Aliyu shi ma suka gaisa da shi. Bayan sun wuce shi ya koma daki

n da aka sauke mu ni kuma na bi wata buduwar gidan na ce ta kaini dakin da Mama take. Ban same ta a falon ba sai wasu yan mata da suka fara bachi akan kujerar, har cikin dakin Hajiyar aka kai ni a nan na samu Mama zaune mahaifiyarta kuma a tsaye tana rike

da wata sandar karfe wacce na ke kyautata zaton tana taimaka mata ne a tsayin ko tafiya. Ina shigowa sai suka maida kallonsu gurina dukansu kana ganin su ka san suna cikin damuwa ba kuma damuwa ta bakinciki ko zullumi ba ta nadamar abunda ya faru da kuma g

anin junansu ta inda ba su yi tsammani ba.

“Ace wai ki gina wata rayuwar a can har ko aurar da ya ba ki nemi familynki ba”

Mahaifiyarta ta fada tana kallona har na zauna kusa da Mama.

“Auren ya do mana ta inda ni da ita ba mu yi tsammani ba, kum

a ko da ace an dauki lokaci kamin auren bana jin cewar zan ka kawo mijinta ko ita ta ganmu saboda na san abunda na aikata”

“Wa ake aikatawa laifi be yafe ba? Allah ma muka masaba daidai ba yafe mana balle mu? Na san kin aikata kuskure amman Mai Martaba

ma bayan tafiyarki ya ji cewar be aikata daidai ba ta hanyar nuna cewar zai aura miki wanda ba ki so, shi kan shi abun ya dame shi domin da be yi hakan ba da duka komai be faru ba, da yanzu wannan ciwon zuciya da na ke fama da shi na ki be same ni ba, da y

anzu kina nan cikin yan'uwanki ana yin komai da ke, a duk lokacin da kowa ya taru sai na ji kamar ace kema kina nan, idan jikoki suka taru sai na tambayi kaina ko ina nake suke wane hali kike a yanzu, a mace ko raye ko kuma a cikin wata mummunar rayuwa”

“Ba laifi ba ne dan uba ya zabawa yarsa ko dansa abokin rayuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login