Showing 156001 words to 159000 words out of 237425 words

Chapter 53 - ZAKI COMPLETE

sam be son ya ji mai zagin Ataa a

yanzu.

MUHSEEN POV.

tun bayan da yai maganar da Nana a waya ya zuba ido yana sauraren abunda zai faru, yasan indai tana da hankali da tunani ba zata bari yarta ta zaba tsakanin shi da Aliyu ba, da ace Aliyu ya samu shi ya rasa kara dai su rasa ga

ba daya, domin shi be ga ta inda zai rika kallon Ataa a matsayin matar Aliyu ba, a cikin Familyn a yanzu haka yana ganin kamar abu ne mai wahala ya ce zai samu wacce ta yi mishi ta kwanta masa a rai kamar Ataa, shi da ya dade yana burin auren mace da aboka

nsa zasu susuce idan sun ganta kuma mai jini a jika kamar Ataa yanzu kuma ace Aliyu ne madadinsa, har ga Allah ya hakura da aurenta amman baya son Aliyu ya aureta kara dai ace bata cikin familynsu gaba daya. Tun daga ranar da ya bawa Momy hakuri be sake ya

rda sun yi ido biyu da Aliyu ba, kwata kwata baya shigowa gidan a lokacin da ya san Aliyu na cikin gidan, idan ya shigo yana part dinsa sai Aliyu ya fita sannan zai fito, dukan abunda kunnuwanta suke son ji wanda Ataa zata zaba, idan shi ne zai yi farincik

i sai dai ya cire rai saboda ya san ba zata zabe shi ba kamar yadda yake ganin cewar ba zata taba zabar Aliyu ba.

ATAA POV.

wasa wasa akwa kwashe kwana biyu har uku Aliyu be dawo ba, ban kuma ji Momy na zancen dawowarsa ba, sai dai bana wasa da

zuwa makaranta na da lokaci yayi rashin fara bokon kuma sai ya fara damuna wanda na san da Aliyu na nan da yanzu ya saka ni ko ya samu wanda zai saka ni, domin ina ganin sha'awar yadda Siyama ta ke shiryawa ta tafi makaranta da safe har jin na ke kamar na

bita.

Ranar Alhamis ranar da Momy ta cika kwana hudu da dawowa daga Abuja, Daddyn ya dawo da rana ya aiko Momy da kanta ta kira ni ni da Nana, tun daga lokacin da na ji kiran sai gana ya soma faduwa domin ina jin cewar zai tambayi idan na yanke shawara

ne. A part dinsa muka taru gaba dayanmu har Momy da ni da Nana da kuma Daddyn kansa. Ni da Nana muka zauna kasa Momy kuma tana zaune a kujera daya da Daddy, babu yadda ba tai ba Nana ta tashi ta zauna saman kujera amman Nana ta ki. Bayan Daddy yayi gyaran

murya ya soma magana da Nana kamin ni.

“Hajiya tace ta tatauna da ke akan maganar auren Aisha, kuma kim fahimta ina fatar ba mu danne miki hakki ko tauye ki a wani abun ba”

“Babu ko kadan”

“Mashallah, Aisha kwana ki na kiraki tun Hajiya bata nan

na fada miki kije ki yi shawara ki fadi min kuma ki fadi a gaban kowa cewa ga wanda kike so, saboda kar ya zamana mun tauye miki hakki ko saka ki abunda be kamata ba ko kuma ba ki tashi ba a yanzu, dan haka muna saurarenki karki ji nauyin baki ko kunyar fa

dar komai ni na baki dama, idan ma ba ki da wanda kike so a yanzu ko kuma kina ganin kamar abun ya yi kusa za a iya daga miki kafa har zuwa lokacin da kike so”

Kasa cewa komai nai kaina yai mugun nauyi har ya sauko min ciki ido, gaba daya falon ji nai y

ana juyawa gabana ya shiga faduwa.

“Aisha... Ke mike saurare”

Ya maimaita jin na yi shiru har na wani lokaci, yawun bakina na hade ina da motsa yatsuna a cikin hijab.

“Yana da wahala ta iya furtawa, ba al'adar mu bace furtawa ka tsaye ka ce ga w

anda kake so”

Momy ta fada, sai Daddy ya ce.

“Muhseen kike so?”

Na girgiza masa kai alamar a'a.

“Akwai wani wanda kike so ne?”

“Kamal kike so?”

Momy ta tambaya sai na girgiza mata kai a nan din ma ina hade yawu.

“Kina da wani wanda

kike so ne?”

Na kasa cewa komai ko matsin sai na kasa yi.

“Aliyu kike so?”

Daddy ya tambaya. A take wata irin kunya da ban taba sanin ina da ita ba, ta rufe kai kasa da kaina gabana sai faduwa yake idonuwana suka cika da kwalla. Tasowa nai na baro

musu falon da sauri kafafuwa har hadewa suke kamar za su tarde ni na fadi. Da gudu na nufi Bq na fada saman katifa na fashe da kuka na rashin dalili.

ALIYU POV.

Yana zaune falon Momy Husna ta kira, sai ya ki ya daga kasacewar yana cin abinci

ne, after few minutes Amina da kira shi nan ma be daga ba sai da ya gama cin abincin, yana kokarin bulbula zuwa ya sha Maryam ta zo da waya ta miko masa wai Amina tana son magana da shi. Ya dade yana kallon wayar sannan ya karba ya kara a kunnesa yana kai

ruwan a bakinsa.

“Ya Albishirinka....”

Shiru yai ya kasa cewa goro jinin zuciyarsa na gudu da sauri ya rika shan ruwa har kana jin wucewarsu a makoshinsa.

“Ataa ta ce kai take so kai kai kai”

Mikewa yai tsaye da sauri sai sa ruwan da ke baki

nsa suka tsarke shi a take ya fara tari a gurin. Ya sauke wayar ya kalla ya sake maida a kunnensa.

“Say it again....”

“Ataa tace kai ta ke so, kuma mamanta ta yarda a daura auren wannan week din”

Bude baki yai kamar zai yi magana sai kuma ya kasa

, ya mikawa Maryam wayar ya shafa kansa ha zauna da sauri yana da mamaki, before yai sujada a gurin yana ma Allah godiya, then ya mike tsaye ya dauki wayarsa ya nufi motarsa Nasir ya kira ya fara labarta masa abunda ya faru. Sai shafa kansa yake yana ganin

kamar ba gaske ba, ko da ma tirsasata akai a gurinsa ba komai ba ne zai iya kula da ita. Ba shi da wanda zai taya shi murna a nan daga Mama Fulani har Muhseen and he don't want to celebrate it with Ammy saboda kar Mama Fulani ta ji haushi.

“Nasir za a

samu jirgi yanzu?”

Ya tambaya with full farincikin a ransa da jikinsa da ruhinsa.

“I don't think so amman bari na kira na ji”

“Now pls”

Kamin Nasir ya kira ya fada masa cewar babu jirgin yau sai dai gobe har ya matsu. Haka nan kawai farinciki

ya saka shi shiga mota ya zaga garin Abuja da kewaye sai murmushi yake kana ganinsa kasan yana cikin farinciki da jindadi. A gangan ya ki dawowa gida gurin Mama Fulani ranar dan baya son ta bata masa farinciki a yau. Da dare ya kira Momy baki har kunne ta

kara tabbarta masa da hakan. Kasa kwana yai a daren saboda farinciki yana ta ganin Ataa a fuskarsa, kamin gari ya waye duk ya matsu. Tun 7 ya isa airport bayan jirginsu sai 10 zai tashi, a gurin Nasir ya same shi ya taya shi murna haka yai ta kira har ten

sannan jirginsu ya tashi.

Na dade ina kukan har na shigo ta same ni a dakin, hankalinta ya tashi sosai ganin kukan nawa ba na wasa ba ne.

“Lafiya Ataa?”

Tashi nai zaune Ni kaina ba zan iya fadar dalililin kukanawa ba, sai dai na kasa daina hawaye in

a jin wani bakon yanayi na rabata har yanzu na kasa daina jin nauyin a kaina da kuma zuciyata ban taba sanin cewar haka ake ji ba ko kuwa dai ni na ji haka Saboda ban saba ba abun ya zamo min bakon al'amari?

“Ba kya son shi?”

Na kasa cewa komai.

“Karki cuci kanki Ataa idan ba ki son shi ki fada na san yadda ake idan aka gabatar maka da wanda baka so, karki cutar da kan ki”

“Ni ma ban san dalilin kukan ba, amman har ga bana jin wani kwankwanton ko tatamar zabar Aliyu da yai”

Har lokacin da n

a ke maganar hawaye be daina sauko min ba. Murmushi Nana tai ta kai hannunta ta share min hawayen fuskata.

“Ina fatar mijinki ne na har abada, kuma ina fatar zabin Aliyu ya zame miki alheri a rayuwarki, rayuwar da na ke miki fatan samu ina fatar ita ce

a yanzu take rabarki, kuma fatar wannan zabin da kika yi ba zai raba kan iyalan gidan nan ba”

A cikin raina na amsa da amin sannan na kwantar da kaina jikinta. Na kara fashewa da kukan, sai da nai mai isata na samu natsuwar ruhi da zuciya sannan na tas

hi na shirya na wuce makarantar islamiya, yau a inda na zauna jiya na zauna kusa da wata budurwa mai far'a wacce na zauna da ita jiya, sosai na maida hankalina gurin karatu amman na kasa karanta komai sai tunanin abunda ya faru nake har aka kusa ta shi.

“Yau ba za ki biya ba?”

Na dago daga tunanin da nake na kalleta.

“Zan biya”

“Na ga an kusa tashi ne, ban ma san sunanki ba”

“Sunana Aisha”

“Okay ni kuma sunana Asma'u”

“Kai ashe ke mamana ce”

“Ina da sunan Mama kenan?”

“Eh sunan M

amana ne”

“Eyee daga yau Mama zaki rika ce min”

Na yi murmushi tare da tashi na nufi gurin da malamin yake zaune ana biyawa, na biya harufan da na iya ya kara min wani na taso na dawo inda na ke ma zauna sai yarinyar ta ba ni yasin kanzo wai ko ina s

o, rai na biya dan haka na karba ina lasawa na ji yaji kamar zan hauka ce da sauri na mika mata ragowar ina fiddo halshena waje ,sai ta saka min dariya ita da wata yarinya da ke gefenta.

“Aisha Aliyu ta so ana kiranki”

Malamin nan da Aliyu ya danka

ni hannunsa ranar ne ya shigo yana fadin hakan, ni kuma ban kula ba domin ban dauka da ni yake ba duk kuwa da kasancewar ni yake kallo kuma na san gurin saka sunan form din daya tambayi ni Aisha Umar na fada masa.

“Aisha Aliyu”

Ya maimaita yana kall

ona sai na nuna kaina.

“Ni...?”

“Eh ta so ana kiranki”

Na tashi ina ta tandar baki saboda yajin na fito na biyo bayan malamin sai ya juyo ya ce min.

“Dauko littafanki?”

Ba musu na juya na je na dauko na biho bayansa, ina ta mamakin dalilin

kirana Aisha Aliyu da yai.

“Kije waje ana jiranki”

Na nufi gate din cike da tunanin mai kiran nawa a wannan lokacin da ba a tashi a makaranta ba. Ina fitowa ya hango Aliyu jikin motarsa sanye da kakanan kaya yana kallon inda na ke tsaye da alama

daman ni yake jiran na karaso, wani irin tattausan murmushi da ban taba sanin yana tare da shi ba ya rika aiko min yana min wani irin kallo mai wuyar fassara, yayi masifar kyau saboda Murmushin ya kawata fuskarsa har sai da ya saka gaba faduwa, kasa karasa

wa nai a na tsaya a gurin gate din ina kallonsa sai ya gyara tsayuwarsa ya rumgume hannayensa a kirji yana ta kallona kamar zai cinye ni, daga bisani ya dago daga jikin motar ya daso inda na ke, kamin ya karaso nai kasa da kaina kunyarsa ta rufe kamshin tu

rarensa kuma ya zagaye ni siffar zatinsa ta hana ni sukuni. Hannu ya miko min na san be saba taba ni ba dan haka na mika masa littafan hannuna sai yai gaba ya bar a gurin, sai da ya isa gurun motar ya bude front ya juyo ya kalleni sannan na fara takawa da

sauri gudun kar wani ya fito ya hango mu daga dalibai ko malaman makarantar. Ina isa na shiga na zauna sai ya rufe motar ya bude gidan baya ya saka littafan nawa ya zagayo mazaunin direba ya shiga yai mata keys muka hau babban titin unguwar, na yi zaton ko

gida zai maida sai na ga mun wuce hanyar gida sai tafiya yake da ni, ni ko sai tandar baki na ke saboda yajin da na ke ji tun ina yi a hankali har sautin ya fara fitowa, da sauri ya maido da hankalinsa gurina kamar ba tukin mota yake ba ko kuma na ce ba a

kan titi mike ba.

“Kin ji ciwo ne?”

Na kasa magana.

“Ko yaji kika ci?”

Na gyada masa kai alamar eh, sai ya faka motarsa gefen titi ya fita daga motar ya tsallaka titi ya shiga wani shagon be dade ba ya fito rike da leda ya dawo cikin motar,

da kansa ya bude ledar ya fiddo gorar ruwan mai sanyi ya bude ta ya miko min.

“Na goge”

Na fada ina kokarin karbar ruwan, sai ya saka min murmushi as respond ya kai ruwan a bakina na sha ka dan na rike sauran.

“Sun ishe ki?”

Ya tambaya yana t

a kallona kamar mai kula da yadda na ke shan ruwa, sai na gyada masa kai hannunsa ya kai ya karbi ruwan ya tashi motar da hannunaa daya dayan hannun kuma yana kurba ruwan. Yawo ya rika yi da ni a cikin garin sokoto wasu unguwannin na sansu wasu kuma ban sa

ni ba, ni dai ban tambaye shi inda za muje ba nawa idone kawai. Sai da muka yi nisa sosai sannan ya faka motarsa gefen titi ya kwantar da kujerarsa ya juyo da fuskarsa gafena yana kallona, na yi zaton wani abun zai yi ko ya ce sai na ji shiru be ce min kom

ai sai idonsa da ya tsare da su, mi kuma na kasa daga kaina na kallin gefen da yake ma balle kuma na iya hadu ido da shi.

“Ki yi hakurina da kallona, yau ji na ke kamar na hade ki ji na ke kamar na bude miki zuciyata ki shige na rufe, ji na ke kamar a c

ikin jinina aka halittoki, komai ya zo min a babin da ban yi zato ba, ban san wace karmar zan fada da zata gamsar da ke irin kaunar ki da na ji a raina ba”

Ji nai kaina yayi mugun girma, ban tana jin kunyar Aliyu kamar na yau ba, ban taba jin wani kalam

i mai girma daga bakinsa kamar wannan ba, bayan wacan furucin da yai min yau ma ya kara min wani wanda ke dora wacan a babin da zai tabbatar da wacan zancen na farko, a wacan karon na yi zaton yana rokona ne saboda kare Momy da son cika mata burinta, sai d

ai kalaman da yai min a yanzu da irin shaukin da yake ya sauya tunani na.

“Kar a tashi makaranta.....”

Na fada numfashi na fita daker kamar wacce aka taushewa zuciya.

“Na fadawa Malamin ku gida zan kai ki fita za ku yi da Momy”

“Amman yanzu a

n kusa tashi ai....”

Na furta still numfashin nawa na gargada, sai ya sake dauko ruwan da ke tsakanin ni da shi ya bude robar ruwan ya miko min.

“Sha”

Na karba da sauri na kai robar ruwan a bakina ina ta sha kamar ba zan daina ba har sai da na so

ma tsarkewa sai yai saurin rike robar ya ciro tissue ya mikon.

“Sannu”

Na karba na goge ruwan da suka zuba jikin hijab dina sannan ta zuke gulashin motar na wurgar da shi waje, gaba daya na tsawwala ina ta jin motar ta mana kada kuma kunyarsa ta rufe

duk na bi na rude. Shi kanshi ya lura da hakan, sai ya gyara kujerar ya soma toka motar muka hau titi. Kadan kadan yake tukin har muka isa gida, a bakin gate din ya faka motarsa, ya bude motar ya fita ya zagoyo gefena ya bude min motar

“Babyna fito ki

shiga gida”

Na san ma'anar Baby yana nufin jaririya mace, wato yana nufin ni jaririyarsa ce kenan. Na fito daga motar kaina a kasa sai da ya rufe motar sannan ya bude gidan baya ya dauko min tittafaina ya mika min sai da na mika hannuna an karba sai yak

i saki

“Thank you so much Love, kin cece ni na zan tana manta wannan alfarmar ba, kin cancanci komai daga gareni I love you so much”

Har zan sakar masa littafan sai yai saurin sakar min ya tsaya yana kallona har na shige cikin gidan. Ban taba dawowa

a irin wannan lokacin ba ana ciran sallah magariba, idan ma Nana ta tambaye ni ban san mi zan ce mata ba. Ina shiga bq din sai na samu Nana bata nan sai dai dakin a bude yake cikina na shiga na cire uniform dina ya shiga bandaki nai alwala, ina cikin Salla

h Nana ga shigo dakin ita ma ta wuce bandakin tai alwala ko da ta fito na sallame ina tasbihi da hannuna.

“Tun dazun kika dawo ko? Daman Hajiya ta ce kila ma kin dawo kika zauna a dakin ke kadai kina jin kunyar shigowa bangarenta”

Na yi murmushi cik

e da jindadi domin na san idan ta san na kai magariba dole ta tambaya abunda ya tsayar da ni kuma ban san abunda zan ce mata ba.

“Hajiya ce ta aiko aka kiranin na je can muka yi hira wai na daina zama ni kadai a nan”

“Allah sarki Momy ai tana da kir

ki”

“Tana da kirki sosai kam, kin yi dacen suruka indai abun ya bi haka”

Wata kunyar ce ta rufe ni ban taba tsammanin idan na yi wa mutun irin wannan maganar kunya tana rufe ba duk kuwa da kasancewar uwata ce amman na ji kunyarta sosai.

ALIYU

POV.

ido ya kura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login