Showing 141001 words to 144000 words out of 237425 words
da baya sonta saboda ya san hakkin aure, kuma mutumen da ya zauna da Rahma zai iya zama da ko wace irin m
ace a duniyar nan, duk wani guri da fada na Rahma da mahaifiyarta akan Ataa ne shiyasa na yanke shawarar Aliyu ya aureta ko dan gorin da suke mata na kuma nuna musu na isa da shi...!”
Wani irin abu ya ji ya daki kirjinsa sai yai murmushi yaja numfashi y
a sauke.
“Ya fada miki cewar son iskanci nake wa Ataa ke nan? Kuma kin yarda duk da kin san ni bana neman matan banza, dan na ce ina son Ataa saboda tana da kyau ai ban yi laifi ba, kina tabbaci idan bata da kyau Aliyu ma zai so ta? Kina da tabbacin sh
i din Mama Fulani zata bar shi ya aureta? Kawai dai kin nuna ke kika haifi Aliyu da kanki kuma kin nuna masa son kai, kuma Ina masa farincikin samun uwa kamar ki wacce zata so abunda danta yake so har ta fishi son abun”
Yana fadar hakan yaja kujerarsa b
aya ya mike tsaye. Tuni idon Momy ya cika da kwalla zuciyarta kuma tana mata babu dadi.
“Allah shine shaidata, ban aikata hakan dan nuna son kai ba, sai dan ganin kamar Ataa zata fi samun kwanciyar hankali idan ta aureshi, kuma Rahma ta raina kanta gud
un yar talaka sai ta ga ta aure mata miji ma gaba daya, idan har bana son ka ba zance Amina ta aureka ba, ba zan baka yar cikina ba Wallahi ban rike wani dabam ba, kai da Aliyu duka daya ne a gurina, na dauke dana wanda zan iya sakawa na hana, na zaba masa
ko na canja masa zabi”
Juyowa Muhseen yai ya kalleta.
“Ashe kin dade da yanke hukunci kika barni ina da lalabe cikin duhu, ni da Aliyu ba daya ba ne a gurinki da ni ma kin dauke ni da da kin hana Aliyu son Ataa ko da zai mutu kin ba ni, domin na fi
shi sonta kuma na fi cancanta na aureta fiye da shi ita kanta idan kika tambaye ta zata fada miki ni take so, kin sani Momy na tun yau ba ina son Ataa amman yau ni za ki zauna a gabana ki fada min gaskiya cewar kin ba danki ita, good luck wish you all the
best”
Yana fadar hakan ya fice daga falon a fusace, ya bar Momy tana aikin hawaye.Sai a yanzu take jin cewar bata kyauta, sai a yanzu take jin girman kuskuren da ta aikata, da tasan cewar Muhseen ba zai fahimce kamar haka ba da bata aikata ba tun farko.
Fashewa tai da kuka a gurin ta tashi da sauri ta shige dakinta, Husna da Amina suka fito suka bi bayanta jin kukanta hankalinsu tashe.
“Momy lafiya?”
Husna ta tambaya tana zama kusa da ita.
“Sam be dace nai haka ba, yayan fulani ba su cancanci
komai a gurina ba sai farinciki da goyon baya, ban za ci cewar Muhseen zai min fahimta baibaiye ba ban tsammaci zai dauki haka ba, Wallahi ban yi wannan abun dan son kai ba sai dan dukansu su samu farincikin”
“Kema kin sani Momy ba zai taba fahimta ba,
tsakani da Allah fa ya riga Ya Aliyu sonta, kuma shi Ya Aliyu ba ma cewa yai yana son ta ba kawai dai kina son yin hakan ne saboda Rahma, kuma ya dace ki yi hakan amman za ki iya yi da wata dabam ba dole sai Ataa ba”
Momy ta dauke kanta daga barin kallo
n Husna wacce take maganar ta dafe kanta tana hawaye.
ATAA POV.
bayan mun gama karyawa, Nana ta ce na je na taya Momy aiki domin yau ko yar sharar da na ke ban mata ba, ni kuma na ki zuwa domin a tunani Aliyu yana nan kuma idan har na je sai Mu
hseen ya kula idan kuma ya kula ni Aliyun zai iya cewa zai min fada ko ya dake ni ma wata kila.
“Zan je Nana amman sai Aliyu ya fita”
“Tau idan dai za ki tafi sai ki saka mayafi”
Na dan turo baki domin ni dai a cikin gida a ce ka saka mayafi yan
a takura min sosai. Muna haka ni da Nana na hango Muhseen tsaye a balcony yana kallon kofar dakin mu.Da sauri na tashi tsaye na fito daga dakin domin yanayin fuskarta ya nuna akwai damuwa sosai a tattare da shi.
“Ya Muhseen lafiya?”
“Mamaki kike ba
ni yadda kika yarda ki auri Aliyu”
Ba zan iya cewa wani mai maganar ba Muhseen ba, domin sautin muryarsa ne bakinsa ne yake motsu kuma shine tsaye a balcony din dakinmu, amman ta ina wannan maganar ta fito mai kamada almara, dan lekawa nai ina kallon fu
skarsa to ko wani abun ya sha ko kuma bachi yai ya tashi yana mafarki? Idan ba haka taya zai furta irin wannan maganar da hankali ba zai dauka ba balle har ta zauna a kwakwalwa.
“Wane irin aure kuma? Wane Aliyu?”
“Kin fi kowa sanin abunda na ke nufi,
amman tabbas Ataa kin ba ni mamaki ashe ba ki da tunani ba ki da zuciya kuma ba ki kishin mahaifiyarki da har za ki yarda ki auri mutumen da aka hada ba ki da shi aka cire mata koda ya dasawa matarsa? Mutumen da ya wulakantaki irin wannan mutumen za ki au
ra?”
Mutuwar tsaye nai wacce ta fi ta kwance hadari da rikitarwa. Sam ban gane inda ya soba ba amman na gane abunda yake kokarin furtawa.
“Ba ka san abunda kake fada ba Muhseen, ni Aliyu be taba nuna min so ba balle har ya furta min, kuma ba zai tab
a so na ba har abada saboda ya tsani talaka, ni ma kuma ba zan taba son sa ba saboda na sani dan masu arziki, babu wannan a tsakanin mu idan ma wani yai maka karya to karya ce kawai ba gaske ba”
Na fada ina girgiza masa kai, tuni Nana ta taso ta fito da
ga dakin ta kawo bakin kofa tana kallon Muhseen. A tsawa ce ya ce
“Gaskiya ne Ataa Momy ta fada min Aliyu za ki aura, mutumen da ya cirewa mahaifiyarki koda ta yi wata da watanni tana jinya, saboda kawai ya dauke ta ya kaita asibiti ya kawo ta nan be is
a ya goge tabon abunda yai mata ba, domin har abada kodarta ba zata taba dawowa ba, ta koma rabin mutum ba cikakkiyar mutum ba”
“Ni Ataa ni a aka cirewa koda? Ni?”
Nana ta tambaya cikin yaren buzanci tana juyowa da ni dan na fuskance ta, tuni hawaye
suka gama wanke min fuska a yau Muhseen ya tona abunda Nana bata san da shi ba, a yau Muhseen zai saka Nana cikin wani halin na damuwa da tunani da zullumin mutuwa a kullum.“Na tsane ka Muhseen na tsane ka, bana kaunar ka, idan ma ka burge ni kai to baka b
urge ni ba, kai da Aliyu duka na tsane ku, bana son ka bana son sake ganin fuskarka karka sake shiga rayuwa ta”
Na fada da iya karfin muryarta ina hawaye, matsowa yai kusa da ni yana girgiza min kai sai na kada masa tsawa.
“Dukan ku kuna juya rayuwa
ta yadda kuke so saboda ina talaka, Nana bata taba sanin wannan maganar ba ayau ka tona ta ka bude komai, na tsane ka Muhseen na tsane ka”
Ihun muryata ne ya fito da Momy da Husna da Amina suka shigo bq din hankali a tashe. Nana kuka take tana dafe da c
ikinta ni ma kukan na ke ina rike da dayan hannunta, idan ma zan mata bayani ta ina zan fara? Ya za ayi tai fahimta? Har ta kwamtar da hankalinta.
“Ataa....”
Muhseen na kiran sunana na daka matsa tsawa ina nuna shi da yatsa.
“Karka ce min komai,
ka riga ka gama fada mata cewar an cire mata koda sai me kuma? Ka riga ka fada mata abunda bata sani ba, bana son ganin fuskarka na tsaneka na ce na tsane ka”
Kallonsa Momy tai ta kalleni sai kuma ta sake kallonsa.
“Me ka ce mata?”
“Ai ke kika ba
ta komai Momy ke kika ja koma... ”
Be kai Ayaba Momy ta tsinka masa mari, har sai da Husna tai saurin zuwa ta rike mata hannu.
“Muhseen kai ba mutum ba ne, ba ka da tunani irin na mutane, kai sakare ne sha sha sha”
Tana fadar hakan ta juya ta fic
e daga bq din a fusace ta bar Muhseen tsaye dafe da kuncin idonaa sun kade sun yo ja sosai. Sai da ya kalleni sannan ya kada kai ya fice aka bar ni daga ni sai Nana muna ta kuka babu mai rarashin wani.
ZAKI
By Khadeeja Candy
40....
Kuka Nana tai
sosai har sai da na soma jin tsoro domin tsarkewa tana tari har na tsoron kar ta janyowa kanta wani ciwon, a take na yanke kukana na share hawayena na rumgumeta ina bata hakuri, daker na rikata na muka koma daki ta kwanta saman katifa na lulluba mata zane
na fito na baro mata dakin, a harabar gidan na fito na nufi gurin da ake ajeye moto na zauna a wani gurin da wani be zai iya ganina ba. Abunda Muhseen yai min ya fi abunda Aliyu ya aikata yi min zafi a yanzu, domin Aliyu akan rashin sani ya aikata kuma ya
ba ni kulawar da ta dace ciki har da taimaka min na samu ilmi, na san yanayin duka wannan ne saboda ya goge laifinsa a gurina da gurin Nana, sai dai duk da hakan hakam na fi jin sakewa da shakuwa da Muhseen saboda shi be aikata min komai ba, be kuma taba m
usguna min ba, sai dai Abunda yai min a yau yasa na ji na fi tsanarsa fiye da Aliyun ma. Ban san wani plan na Momy ba, wata kila ta shirya Aliyu ya aure ni ko da baya sonta saboda ya kara goge laifinsa ko kuma saboda tana so a matsayin surukarta, amman be
dace ta yanke wannan hukunci ba tare da jin ra'ayina ba, wata kila tana son ta mana milkin masallaka ne saboda muna gidanta, ko kuma saboda wani dalili na ta na dabam domin na tabbatar ba ni da kima da darajar da Aliyu da kansa zai bukaci aurena ko ya fur
ta cewar yana so na, wata kila tana son ta aura masa ni ne saboda ya rage kyamar talaka domin na lura halinta da na shi ba daya ba, idan ma har da gaske ne abunda Muhseen ya fada wata kila kuma wata ake nufi ba ni ba, a a ba ma ni ba ce sam ba zai ce ni ko
da ma cilasta a kai na san ba zai amince ba. Haka nai ta sake sake na na na kulla wannan na kwance wacan har aka kira azahar, ni dai sai na ji gaba daya gidan ya fice min rai, domin zama a ciki ne ya kawo yau har Nana ta ji wannan maganar mai daga hankali
na tabbatar da ace bama cikin gidan ko da Muhseen zai zo yayi maganar sai dai ya saka a masa sallama da ni idan na fito ya fada min son ransa amman ba a gaban Nana ba.Ko da na koma dakin na samu ta yi alwala tana kokari saka hijabinta tai sallah, bandakin
na nufa na shiga na yi alwala na fito na shimfida dankwalina na soma gabatar da tawa sallah, bayan ta sallame ni ma na sallame sai ga Amina ta shigo da sallama dauke da kular abinci da plates da Siyama na bayanta tana sanye da uniform kamar dazun da alama
bata dade da dawowa daga makaranta ba, fuskar Nana kawai take kallon wacce ta kumbura sosai.
“Sannu Nana”
Cewar Amina wani abun mamaki da Nana ta dago ta kalleta sai tai mata murmushi ta kada mata kai, Siyama ma ta mata sannu sannan suka fice. Mats
awa nai kusa da ita na soma mata magana a hankali.
“Na boye miki ne saboda kar hankalinki ya tashi ki saka kanki a damuwa, ba da sanin Aliyu akai wannan abun ba, likitan da naje neman taimako a gurinsa doc Asim shine yai wannan aikin ba da sani Aliyu ba
.....”
A natse na zayyana mata komai tun daga kan asibitin da kullen ni da Doc Asim ya saka aka yi da kuma neman mu da Aliyu yai ta yi har ma da konewar da kodarta tai da kuma irin kalubalen da na fuskanta a zamana Abuja. Hawaye shar a fuskar Nana tana
kallona da murmushi a fuskarta.
“Ba kowa ce uwa Allah ya ke azurtawa da ya kamar ki mai damuwa da matsalar uwarta da nema mata mafita ba, kin jefa kanki cikin matsala saboda ni, kina bukatar abubuwa da yawa amman kika watsar da su kika maida hankalinki
a gurina, ban yi zaton samun ya mace wacce zata kula ni kamar haka ba”
Ta fada tana kallona, wani dadi da farinciki na ji ya lullube ni ashe haka ko wane da na kwarai yake ji idan mahaifiyarsa ta yabe shi. Sai na kwantar da kaina jikinta ina jin wani i
rin shauki da rahama na uwa yana ratsani.Hannunta ta dora saman kaina tana shafani. Har na bude ba ki na yi magana sai ga Momy ta shigo cike da tsoro a fuskarka muryarta har gargada take a lokacin da take mana sallama. Ni ma amsa yayinda Nana kuma na kasa
daga kai ta kalli Momy, a gaban Nana Momy ta zauna kamin ta fara cewa komai hawaye sukai mata sallama.
“Ban san yadda za ki dauki abun ba, ban san da wace fuska zaki kalli abun ba, ba dan ni na haifi Aliyu ba, wallahi idan za ki tambayi kowa a garin na
n wanda ya san halin Aliyu ya san rayuwarsa, zai fada miki cewar Aliyu ba zai aikata hakan ba, yes na sani Aliyu yana da wulakanci amman Wallahi ba zai taba yarda ya zalince ka ba, ba da saninsa a kai komai ba.....”
Daki daki Momy ta jerawa Nana komai c
iki har da dalilin hana Muhseen aurena da tai wanda shine dalilin janyo duk abunda yake faruwa yanzu da kuma dalilin aurena da take son ya yi , ashe wai gori Rahma tai mata kuma ta kirani da talaka ta ce ba za a hada ta kishi da yar talakawa ba, a zatonta
Aliyu so na yake, a take na ji Momy ta kara burgeni, domin a yadda suke da kudi da arziki da suna a garin sokoto, ba ko. Wace uwa ce zata yarda danta ya aureni ba yar bara a titi wacce ba a san kowa na ta ba, na sani ta cilasta Aliyu yin hakan ne saboda ka
wai karancinta, tausayinta na cika min zuciya wanda na ke zaton shi ne a zuciyar Nana har ta daga kai ta kalli Momy tana hawaye kamar yadda Momy ma take nata hawayen.
“Kina da damar yanke ko wane irin hukunci, ciki har da maka Aliyu kotu idan har zuciya
rki ta natsu da cewar shi ne ya aikata miki komai, kuma na miki alkawari nai ko alfarmar kowa ba za mu nema ba dan a bamu gaskiya a baki rashinta, kina da damar hana Ataa auren Aliyu ki aura mata Muhseen ko wani dabam wanda zuciyarta ta natsu da shi, amman
ina rokinki dan girman Allah kar ki ce za ki bar garin nan zuwa wani gari ko wani gidan dabam, ki zauna da mu dan girman Allah”
Momy ta fada tana hade hannayenta guri daya tana rokon Nana.Shiru da Nana tai ne yasa Momy ta juyo gurina tana kallona.
“Ban yi niyar aikata komai a gurinki ba sai alheri, dukan kudirina na kiji dadin rayuwar ki a gaba ne, ina da yakinin Aliyu zai rike ki amana, kuma zai zauna da ke ya rike ki da kima saboda yana son ki, kuma ke din kamar kyauta ce daga gurina, Allah shine
shaidata”
“Momy kin rike ne kamar yar da kika haifa ko da rana daya ba ki taba nuna min kyama ko banbanci da yayanki ba, lokacin da kanwar Rahma ta dake ni ki yinta ma Aliyu fada kamar ki dake shi kina fadin ba zaki dauka ba, duka wannan abun da kika mi
n kina kara amsa sunanki an uwa ne a gurina, Wallahi na yarda da ke Momy na rike uwa ta gari.... ”
Murmushi na gani a fuskarta sai ta kai hannunta ta dafa ni.
“Na gode da kika fahimta Allah ya miki albarka”
Tana fadar hakan ta tashi ta fice daga
dakin. Nana ta bi Momy da kallo tana min magana cikin yaren buzanci.
“Aliyu ya aikata kwatankwacin abunda na aikata kuma nake ganin kamar ban yi aikata laifi ba, sai ga shi alhaki yana ta bibiyana na bijerawa iyeye, cikin har da samun rayuwara a bara,
da rasa kudin magani, babban a ciki shine na cire min koda ba tare da sani na ba, ko wane shafi na rayuwa darasi ne, ko wani littafin kaddara ilmi ne, da ban gudu na bar gatana ba, na bijerawa iyayena ba, da wani be isa ya nuna min yatsa ba, balle har ya t
aba jikina abunda na aikata ne shekara ashirin baya yake ta bibiyata har yau”
“Nana me kika aikata?”
Sai tai saurin share hawayenta ta girgiza min kai.
“Ban aikata komai ba”
Amsar da ta ba ni kenan ni kuma gudun an dame ta yasa ban sake cewa k
omai ba.Tashi nai na fito daga dakin na koma can gefen bq din na zauna ina ta tunanin maganar Nana lalai akwai abunda take boyewa kuma abunda ta aikata