Showing 15001 words to 18000 words out of 237425 words

Chapter 6 - ZAKI COMPLETE

duk a cikin Nurse din Shukuwa ta fi s

ake min sai dai a yadda na lura kamar shi likitan baya son shirinmu da ita, wata kila akwai rashin jituwa a tsakaninsu ne ko kuma wani abun oho, domin na lura da ita ma kamar bata jindadin yadda muke yabonsa muke saka masa albarka da addu'ar alheri.

Haka

nan kawai wani lokacin idan bata aikin komai sai ta shigo dakinmu mu yi ta fara kamar mun saba, ta haka har na san unguwar da take zama wato tudun wada da kuma inda ni ma nake zama har take ce min tana da wata kawa a kusa da mu, akwai ranar da take fada m

in cewar tana tausayina ni da

Lukman jin cewar ba mu da kowa a nan Nigeria ko ma muna da su ni ban sansu ba, domin Mahaifina be tana fada min ba Nana ma bata nuna fada min ba, har take ce min ya kamata na nemi yan'uwa ko'in suke saboda wata rana. A lokacin

na samu Nana na tisata a gaba ina tambayar wasu daga cikin yan'uwanta har take fada min harma da na Babana ma.

Misalin karfe biyu da yan mintuna na fito daga dakin na nufo gurin da muke zama a harabar asibitin inda shuke-shuke na zauna. Ban yi minti hu

du da zama gurin ba sai ga kawata Farida ta zo, na jidadin zuwanta domin yau harabar babu mutanen da muka saba fira wasu an sallame su wasu kuma suna ciki gurin kula da masara lafiya, wadannn bakin fuskar kuma sun tsare ni da idonsu, dukuwa da nasa wannan

kallon baya rasa nasaba da irin kyauna da kuma manyan idanuwan da Allah yai min haka zalika gashin kaina, shiyasa ba kasafai na ke son yin alwala a waje ba sai gaka hankali kowa ya dawo kaina duk da kasancewar gashin nawa a cinkushe yake guri daya har wani

warin tsami yake, domin ba kitso nake masa ba idan am anyi kitson sai warware saboda sulbin gashi, kuma ba damuwa nai da na wanke ba balle har na shace shi ko na gyara.

Dambun da suka na masara ne ta riko mana, duk da kasancewar bana jin yunwa amman h

akan be hana ni ci ba domin ina son dambu kusan duk wani abu da za a sarrafa shi da masara ko shimkafa ko dawa ina sonsa. Na ci dambu da yawa saboda yajin da aka cika a ciki domin ni ma'abociyar cin ya ji ce sosai, bayan mun gama fira ta shiga ciki ta duba

Nana tai mata ta jiki sannan ta fito na rakota har bakin titin ringin sambo ina ta jin kamar na bita dan har ga Allah zaman asibitin ya fara ci min rai. A hanyata ta dawowa ne na hadu da Nurse Shukura tana sanye da uniform dinta amman ta dora bakar abaya

sama ta rataya jakarta da alama ta tashi daga aikin ne zata tafi gida.

“Anty Shukura kin tashi ne”

“Eh sai kuma gobe, na kika fito?”

“Wallahi kawata na raka ina jin kamar na bita, zaman asibitin nan na ishemu”

Na fada ina yar dariya kadan, sai

tai murmushi ta ce.

“Zama kan ai yanzu kuka fara tunda har kika ga Doc Asim ne yake kula da ku, in ma kina son mahaifiyarku ta samu lafiya to ki dauke ta daga asibitin nan ki kaita wata ko ku koma a gida, idan ba haka ba Wallahi za ki iya rasa mahaifiy

arki asibitin nan ballantana yana ganin ba ku da kowa kin ga asirinsa rufe ba wanda zai san dalilin mutuwar mahaifiyarku”

Hankali na tashi da ji kalamanta har ya kasa boyuwa a fuska ta.

“Me kike Nufi Anty Shukura?”

“Bana nufin komai kawai baki g

anin ciwon mahaifiyarki na ki ci ya ki cinyewa kullum kuna nan, ai ya kamata ki yi tunanin canja mata asibiti, kuma karki ce ni na baki shawara idan kin tashi kawai ki ce ke kin gaji gida za ku koma, Wallahi da masu kudi ne ku ko masu yan'uwan da yanzu an

yi tunanin wata hanyar daban amman ba zama haka nan ba har kuna kokarin shiga wata na biyu asibitin nan, akan saran maciji kawai haba Ataa ke ma ai ya kamata ki yi tunani”

Tana gama fadar hakan ta yi wucewarta ta bar ni nan tsaye ina ta nazarin magangan

unta, gaskiya ta fada wani gurin tabbas da masu kudi fa yanzu an canja nata asibiti amman kuma mu ba kamar su ba ne, kuma idan muka ce za mu canja asibiti kudin magani dawainiya wa zai yi da mu? Na san dai ba za mu hadu da dan albarka likita kamar wannan b

a. In ta wannan sake saken na nufi cikin ward din tare da tunanin wata kila likitan be kware sosai ba shiyasa ka Nana ta gagara warkewa garau.

#Team Ataa

#Team Rahma

#Team Aliyu



Masu yi ma Rahama addu'ar mutuwa ita ma lafiyarta kawai take

nema ita da mijinta

😀

amman kun fara dora mata tsana tun ba a je ko'ina ba

😑

https://my.w.tt/PWohUhlPv9.

*Z A K I*

By Khadeeja Candy

7





Tunanin inda zan kai Nana idan na dauketa daga asibitin ya hana ni runtsawa a daren, ba ni da hal

in da zan iya nema mata magani a wata asibitin domin na lura maganin nata mai tsada ne kamar yadda Doc Asim yake yawan fada min cewar ya siyo maganin, a yadda yake hidima da mu idan na ce zan canja asibitin zai iya zargin wani abu ko ya ji babu dadi taya m

a zan iya fada masa cewar asibiti za mu canja ai sai ya zargi ko mun raina Hidimar da yake damu ne? Da wannan tunanin na kwana na tashi na sake kwana na sake tashi a haka har akai kwana uku ban fadawa kowa ba, sai dai ta wani 6angaren Anty Shukura tana da

gaskiya ya kamata na gwada aikin wani likitan ko Allah zai sa a dace ta koma kamar da, maganarta ta cewa indai ba son nake Nana ta mutu ba na canja mata asibiti na daga min hankali sosai har na saka samun sukuni, idan na shiga bandakin da zimmar alwala ko

fitsari sai na zauna a ciki nai ta kuka, ban san abunda Allah ya tsara ba, ban san abunda zai faru gaba ba, Nana zata tashi ko ciwon zai yi ajalinta duka ban sani ba, zan rayu da ita na wani lokaci ko a'a duka ban sani ba. Iyakar abunda na sani kuma na ke

da tabbaci akansa shine mutuwa kuma Allah baya barin wani dan wani, sai dai na san ina son rayuwar Nana fiye da ta kowa duniya, na rasa mahaifiya yan shekaru kadan a baya, sai na ji kamar ba zan iya hakurin na rasa Nana a yanzu ba.

Bayan na yi kukan na

wanke fuskata na fito na zauna a kujerar da ke fuskarta Nana, ita kuma tana daga zaune ta rame sosai sai sauke ajiyar zuciya take tana kallon mutane da ke kai kawo a waje ta window dakin, wani irin tausayinta ne ya kamani da kuma tausayin kaina a lokaci d

aya mace mai kuzari kamar Nana wacce zata fita bara tun safe ba zata dawo ba sai yamma ta koma a zaune tsayin ma wahala yake mata, lallai Allah kadai ya iya haka.

“Nana”

Na kira sunanta a hankali, a lokacin da ta juyo ta kalleni sai na ga hawaye a i

donta, ba ta damu da sharewa ba saboda tasan na ga hawayen babu abunda zata boye min.

“Wani gurin ne yake miki ciwo?”

Na tambaya hankalina a tashe ina komawa saman gadon asibitin inda take zaune na zauna kusa da ita.

“Tunani na ke yi, yanzu idan

na mutu ke da Lukman ku za ku shiga wani hali, ba ku da gurin kwana ba ku da komai ban bar muku gadon komai ba sai na bara, ba ku da kowa a garin nan, a can nijar kuma babu wanda ya san inda kuke a nan balle su nemi ku, ba ku da gata yanzu sai na Allah At

aa, jo yanzu da wannan bawan Allah be taimaka mana ba da yanzu kila ka mutu”

Iyakar kokarin da nai shine na rike kuka da hana hawaye taruwa a idona saboda ta karta gani jikinta ya kara yin sanyi.

“Za ki ji sauki Nana In-Sha-Allah za mu koma can gida

nijar tare da ke da Lukman mu yi komai tare”

Na fada ina nuna mata kamar ban damu da hawayenta ba.

“Wannan Nurse din Shukura ta bani shawarar wai na dauke ni daga wannan asibitin na kai ni wata”

“A nan ma ai ana kula da kai, kuma kana samum kula

wa da abincin duk ana baka da yaranka amman can idan ka je wa se baka?”

“Ni ma na yi tunanin haka Kuma ina jim kunyar likitan ma, kar ya ce ba mu gode ba, amman ta bani shawarar na ce masa gida za mu koma”

“Ataa kana karami kana ta wahala haka nan ku

llum, idan ka kai ka wani asibitin ina kudi?”

“Akwai kudin da ya ba ni ya ce na siya abincin ranar ba na fada miki ba? Kuma akwai wada muka dan samu da aka zo ganin ki zai kai dari takwas idan mum hada dubu goma kenan har da yan canji ma, sai mu je wani

asibitin mu gani ko za mu dace”

“To ai sai ka fada mata ko?”

Ta fada a nufinta na fadawa likitan.

“Eh zan fada mishi amman ba za mu ce masa wata asibitin za mu ce masa gida za mu koma kin ji?”

Ta gyada kai, kamar likitan ya san abunda muke ts

arawa sai ga shi ya shigo dakin rike da wasu takardun fuskarsa a sake kamar kullum.

“Ya jikin?”

“Ka ji sauki”

Nana ta amsa masa, sai ya ciro daya daga cikin takardun ya miko min.

“An sallame ku, ya kamata ku koma gida hakan nan, ki cigaba da b

ata magani da zan ba ki kinji?”

Na saka hannu biyu na kar6a cike ladabi da kuma murna.

“Ai za ki iya ganewa idan an rubuta mikia jikin maganin ko? Kin yi boko?”

“Eh amman bakin primary kawai ina karanta abu idan ba mai wahala ba ne, ko kuma idan h

ausa ce”

Sai yai murmushi.

“Ai na san ba kya ganewa kan”

Yana rufe bakinsa wasu nurses biyu suka shigo dakin dayar tana rike da ledar magani dayar kuma tana turo wheelchair. A nan ya karbi maganin ya rika nuna min yadda za rika bata su kuma Nurse

s din suka dauki Nana suka saka ta a wheelchair din, sannan ya saka suka kwashe mana duka kayanmu suka fitar waje, ban ma san an samu napep ba sai da na nade tabarmu da ke waje na yi ma mutanen sallama na janyo hannun Lukman muka biyo bayan nurses din.

“Allah ya saka da alheri ya biyaka”

Ita ce addu'ar da muke ta masa ni da Nana, har aka saka ta Napep din ni ma na shiga Lukman na shiga gaba tare da mai Napep din. Sosai na so muje wata asibitin amman Nana ta ki ganin kamar za mu kashe kudi ne kawai, w

ai a ga magani nan ya ba mu kudin sai mu siya abinci da su a cewar ta, daman can Nana ba son kashe kudi take ba sai dole, balle wannan da take ganinsa da yawa har dubu goma.

Har kofar kangon gidan mai Napep din ya kawo mu, sai na umarce shi daya shiga

ciki ba musu ya shiga ciki, ni na fara fitowa na rika Nana ta fito tana tafiya ďuke dan bata iya mikewa tsaye dai-dai, Mai Napep din ya cire mana duka kayanmu da suke bayan Napep din ya aje mana zan ba shi kudi ya ce Doc Asim ya bashi sai kawai nai masa g

odiya na shiga da Nana cikin kangon gidan na samu wani guri da anke zaton sitting room za ayi da shi na shimfida mata bargon na kwantar da ita. Lukman ya shigo da sauran kayan, ni kuma na dauki tsitsiya na hau sharar gurin dan yai datti sosai, sai da gama

share duk fadin gurin sannan na dawo kusa da ita na zauna.

Wani dadi na ji a lokacin da na kalleta lallai uwa mai dadi idan bata a cikin gidan sai yai babu dadi, idan kuma tana nan sai naji dadi duk kuwa da kasancewar ba a lafiye take ba amman ina son

ganin abata.

Ba mu dade da zaman ba akai kiran sallah la'asar sai na tashi nai alwala nai sallah sannan ita kuma na debo mata kasa tai taimama tai sallah, ba a maganar Lukman daman shi tun da ya gama saka mana kayan ciki ya fita yawonsa.

Sama sa

ma muke ta firar mu da ita, yawancin firar da muke ta kwantar da tai asibiti ne mutanen da suka zo ganinta da kuma alherin da likitan yai mana, bayan sallah magariba na dauko maganin na sake bata kamar yadda ya fada min, da isha'i muka kwanta a gurin zuciy

ata cike da tsoro ina ta

ganin kamar macijin nan zuwa zai yi ya sake tsaran Nana ko ni ko Lukman, amman Allah ya tsare mu har gari ya waye babu abunda ya same mu, yau ma ban yi sallah da wuri ba sai da rana ta fito, bayan na gama sallah na je na samu gaway

i na wanke bakina sannan na ba Lukman kudi na ce ya siyo mana koko a inda ake saidawa da kosai da suga, ba laifi ta ci sosai ni ma na ci duk da kasancewar ina sha'awar waina amman bana son na siya bayan shan kokon gudun kar kudin mu su yi saurin karewa, ka

ra kawai na hakura har zuwa gobe sai na siya da safe mu karya da ita gaba daya.

Muna ciki zaune sai ga Farida ta zo, ashe jiya bayan dawowarmu daga asibitin ta je aka ce mata an sallame mu. Mun sha fira sosai ba tabar gidan ba sai da ta soma jin iska

n hadari na tasowa alamar hadarin daya hade sama yana daf da tasowa. Sannan tai mana sallama ta tafi, tafiyarta da mintuna kamar hudu zuwa biyar na hango wasu mutane sun doso inda muke dukansu maza. Gabana ya dan fadi kamar yadda na Nana ma nasan sai ya fa

di, suna isowa suka fara fisge dan zanen a muka saka muka tare kofar da shi saboda sanyi suka jefar.

“Wai ku wasu irin mutanen? Ko wacan lokacin ba an muku magana ba, wato shine kuka dawo ko? Mai gidan yace mu koreku dan an fada masa kun dawo ashe ma c

ikin gidan kuka shige kuka zauna dan rainin hankali”

“Dan Allah ku yi hakuri Wallahi mamana bata da lafiya kuma babu inda zata laba sai nan”

Na fada ina kallon fuskokinsu na marasa imani da ganinsu irin yan sara sukan nan ne ya turo mana marasa tarbi

ya. (Area boys)

Aiko kamar jiran suke nai magana sai biyu daga cikinsu suka dauki Nana suka kai ta can kusa da gate suka aje dayan kuma ya turani waje da karfi, Lukman da tsoro tuni na nufi inda Nana take da sauri idonta cike da tsoro, sai kuma suka shiga

ciki suka fara shuri da kayan mu da ke ciki sai da suka fitar da komai da kafa sannan suka fito suka nufo inda na ke tsaye ni da Nana muna muka suka ce mana idan muka sake shiga ciki duk suka dawo sai sun sassara mu, kuma mu nemi wani wajen tun kan dare y

ai mana mu bar gurin kwanon da aka saka dan fara zagayewa kamar za ayi gate.

A gurin muka tsaya ni da Nana da Lukman har aka fara ruwa, daga ni har Nana babu abunda muke sai hawaye Lukman na tsaye yana ta kallon ta bata fuska sosai kamar ya fasa kuka. Sa

i da naji an fara yayyafi sannan na rika Nana da zimmar mu koma ciki sai ta rike hannuna ta girgiza min ka alamar ba zata koma ba.

“Idan an gama ruwa sai mu fito”

Na fada da muryata ta kuka, sai ta girgiza min kai alamar ba zata ba, hakan yasa na nuf

i kayanmu na dauko bargon da likitan ya siya dan mu rika kwantawa ni da Lukman akai na lulluba mata na shiga ciki Lukman ma shigo muka fake a ciki ruwa na dukan kanmu. Wani abun Allah kuma sai akai ruwan da kama da bakin kwaya ga sanyi sosai domin har da k

ankanra suke. A take Nana ta fara tari jikinta na ta karkarwa jin hakan yasa nai saurin bude bargon sai na ga jini duk ya bata mata baki har ya sauko saman rigarta ashe tarin da take jini take fitarwa, rumgume ta nai na fashe da kuka ina daga kaina ina kal

lon ruwan saman da ke saukowa kamar a cikinsu wani zai kawo mana dauki....

Wayyo Nana

😪

https://my.w.tt/PWohUhlPv9.

*Z A K I*

By Khadeeja Candy

8





Sai da ruwan suka dan tsagaita sannan na samu damar mikewa tsaye ina daga

Nana daga jikina. Ta galabaita sosai har wani lumshe ido take tana budewa amman wani abun mamaki idan ta kalleni sai tai min murmushi, wata kila so take ta kwantar min da hankali ganin irin yadda na ke ta kuka kamar ba gobe, a saman bargon na kwantar da it

a duk kuwa da irin sanyin ruwa sama da ke jikinshi na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login