Showing 30001 words to 33000 words out of 237425 words

Chapter 11 - ZAKI COMPLETE

/>
raba na koma na dauko duka kayan wanke wanken na fito da su tsakar gidan, na je na siyo omo na debo ruwa a rijiyar gidan na zauna na wake su tas, na dauka na kai kitchen din wanda zan iya cewa dakinmu. Sannan na fito rike da soson wankanmu na dibi ruwan a

robarmu na shiga bandakin tsakar gidan nai wanka, na wanka jiki sau uku sannan na saka ruwa na dauraye na fito fes da ni ni kaina har wata ni'ima na ke jin tana shiga jikina. Ban ssmu na shafa mai ba saboda yanayin garin da zafi, sai kawai na saka daya da

ga cikin tufafin da na ke ji da su, na dauki bakin dankwalina nai nikab da shi sannan na saka Hijab sama na duka inda kudin sukd na dauki naira dari na dan hawan acha6a, domin akwai tazara a tsakanin unguwar mu da tasu.

“Nana zan tafi”

“Yau za ki fa

ra aikin?”

“To Allah ya taimaka ya tsare a dawo lafiya”

“Amin, ki aje wannan kudin muna cin abinci da su, idan na samu wasu wadanda suka yarda nai aikin yamma sai na rika zuwa ina musu kin ga idan an ban kudi sai na hada da wannan mu koma asibitin”

“To Allah ya nufa”

Duk maganar da nai mata da hausa nai ta ita kuma sa ta maida min da yaren da tafi kwarewa akai wato buzanci. Sai da nai mata sallama sannan na fita, ban yi nisa sosai na samu mashin na tara na hau yana sauke ni na bashi hansi ya kar

ba ya wuce ni kuma na buga kofar gate din a hankali. Mai gadin ne ya leko yana ganina sai ya fito gaba daya.

“Baiwar Allah lafiya”

“Lafiya kalau, ni ce wacce na zo neman aiki dazu kuma suka ce sun dauke amman sai naje na shirya”

Wani kallo yai mi

n tun daga sama na har kasa, nasan kallon baya rasa nasaba da bakin kyallen da na saka na rufe fuskata, wata kila yana munanamin zato ne.

“Bari dai na fara fada musu tukuna”

Haka ya barni tsaye a gurin ya koma ciki, ba dauki dogon lokaci ba sai gashi

ya dawo ya bude min gate din.

“Ance kin shigo”

“Na gode”

Na fada ina saka kafata cikin gidan, sai a yanzu ne nake kara kare masa kallo babban gida ne da za ayi iya kiransa da aljannar duniya, ko a harabar gidan kadai aka barka zaka sha kallo tun

daga kan furanni da kuma manyan motocin da ke gidan, ko wace kofa an kawata ta da furanni. A inda na naga sun fito dazun na na bi stairs din na isa gaban katuwar kofar mai kyau na yi knocked a hankali, shiru ban ji an bude kofar ba, hakan yasa na sake kno

cked, nan ma shiru ba a bude min ba, sai da na yi na ukun sannan aka soma motsa kofar aka bude. Mijin matar ne ya bude min yana sanye da kananan kayan, bakin wando da jar t-shirt, fukarsa kamar ta kullum babu alamar murmushi ma balle kuma ayi zancen dariya

.

“Ina wuni”

Be amsa min ba, sai kallon fuskata yake kamar nai son tantace abu, ni kuma nai tsaye a gurin cike da tsawalla, gabana sai faduwa yake ina jin kamar cewa zai yi ya fasa baya so. Sakin kofar yai ya juya ya koma ciki ya barni a gurin tsaye

shi be cena shigo ba, kuma be ce min na tafi ba, ganin hakan yasa na yi tsaye agurin kamar an dasani, har sai da na ji muryar matar tana ce min na shigo.

Kamar wata hawainiya haka na rika taka tile din mai tsantsi gudun kar na taba da karfi su ce na mus

u ba daidai. A kan wata babban kujera suke zaune tun na shigo falon daga ita har shi babau wanda ya kalleni balle ya

ce min wani abu. Haka ma zauna a gurin kamar daman sun biyana dan na zo na zauna gabansu ne.

“Ke anya macen kwarai ce? Miyasa kika rufe

fuskarki?”

Matar ta fada tana min wani kallon uku saura kwata.

“Ba komai, na fi jindadi idan na rufe fuskar ne shiyasa na rufe, ina da konuwa a fuskar ne”

Ta tabe baki.

“Bedrooms din mu za ki fara shiga ki gyara komai da nan falon sannan ki

shiga kitchen ki gyara kuma ki wanke duka kayan da suke can sannan ki yi mopping ki saka mana turaren kanshi”

“To ina dakunan suke?”

Da yatsanta ta nuna inda yake har na mike tsaye sai kuma ya kira ni.

“Keee ban da sata kar ki kuskura daukar mana

wani a gida”

“Ban taba sata ba a rayuwa”

Na bata amsa cike da jin zafin furucinta.

“And secondly mijina baya son kallo, kuma daga yanzu tun bakwai za ki rika zuwa kina hada mana breakfast, kuma ki gyara gidan, kuma kullum ki wanke mana bathrooms

din mu”

Tana fadar hakan sai na ga jikinta ya kalleta, ya kalli sannan ya sake kallonta.

“Ban da girki, saboda shara da mopping kawai na dauke ta”

Yana fadar hakan ya mike tsaye yana wani irin kamshi turare mai dadi shaka ya hau sama, ni kuma na

maida hijab dina baya na daure sannan na nufi upstairs din na soma takawa a hankali kusa da sai na ce wannan shi ne karo na farko da na taba taka stairs bayan wanda na taka a asibitin uduth, dakin farko na fara kai hannuna na tura kofar dakin, da alama dak

inta ne, domin kayan mata da ke dakin suna da yawa ga gadon duk an tumurmuza shi kamar karamin yaro ya kwana kai. Bedsheet din na fara gyarawa sannan na linke kayan kayan da aje guri daban, na duba iya dubana ban ga tsinsiya ba da abun mopping ba. Hakan ya

sa na fito na sauko kasa can nesa da ita na tsaya.

“Ina tsintsiya?”

“Ni zan dauko miki na kawo miki?”

“Aa fada min za ki yi inda take na dauko”

A gurin ta bar ni tsaye har na kusan minti ashirin sannan ta ce.

“Tana can kofar baya ki je ki du

ba”

“Ina ne kofar baya?”

Sai da taja tsaki sannan ta bani amsa tana mikewa tsaye ta nufi upstairs.

“Idan kin ga dama ki duba ta can”

Inda ta nuna min na bi na je na bude kofar dake gefen falon, sai ga ni a wata karamar haraba, kusa da gen hann

u nasa na dauka da bokitin na nufi fomfon dake kallon kofar na kauna na wanke bokitin sannan na fito, tsaye nai a falon inata tunani inda za samu omo na ko man wanki na zuba a ciki. Ganin bata fito ba yasa na bar ruwan a nan na koma da Tsintsinyar bedroom

dinta na share shi tsaf na kwashe na na fito da datti sai kuma na rasa inda zan zuba, gashi ba ta fito ba balle na tambayeta, a dole na aje ta jikin kofa na koma dayan bedroom na share na gyara komai sannan na sauko kasa na share falon har karkashin kujera

na shiga kitchen na share na hada kayan wanke wanke guri daya, a kusa da tab na samu omo sai naje na zuba a cikin ruwan mopping din na koma dakin na mopping sannan na shiga bandakin na wanke na dawo falon nai mopping na goge ko'ina sai kuma na koma kitche

n din na wanke kayan cin abincin bayan na gama nai mopping din kitchen din sannan na fito na zauna a falo ina kare masa kallo a pop kadai na san ba kananan kudi aka kashe ba, balle kuma irin manyan kayan alatun kawata falo da aka cika falon da su. Ko agogo

n falon irin wanda na ke gani a tv ne.

ALIYU POV.

Yana shiga dakin Rahma ta biyo shi tana fadar ita bata yarda da wannan yarinyar ba shi ru yai be ce mata komai ba, yai kamar be ji ta ba sai latsar wayarsa yake.

“Ka ji, ni fa ban yarda da ita ba

, jiya ta shafa wani a fuska ta zo nan duk baki yanzu kuma ya saka nikab”

Sai a lokacin ya dago ya kalleta. Kamar zai yi magana sai kuma yai shiru ya sake mai da hankalinsa gurin wayar.

“Kana jina fa”

“Mi kike son? Ke kika damu a samu mai aiki ai



Ya fada ba tare ya kalleta ba, sai tai fushi tana mikewa tsaye yai saurin riko hannunta ya dawo da ita kusa da shi ta zauna.

“Kin cika son saka bacin rai a zuciyarki Dear, kuma kin san matsalarki, idan mai aikin ce ba ki so ai sai ki koreta kawai”

“8k din da ka bata fa?”

Yai murmushin kasaita yana kallon goshinta.

“Ai kyauta na bata ba dan aiki ba”

“Aa gaskiya sai dai tai mana aikin one month sai mu koreta, dama dai ba ka ba ta kudin ba”

Kara matsawa yai kusa da ita yasa duka hannyen

sa ya rike fuskarta.

“Idan na ga mutum cikin rashin lafiya, ina tausaya masa sosai, saboda na san zafi da ake ji, musamman idan mutumen nan makusancin ka ne, na auna kaina a matakinta, kin tuna lokacin da muke ta yawon neman lafiyarki?”

“Waya sani i

ta ko karya take, wata kila ma muguwa ce shiyasa take rufe fuska”

Be sake ce mata komai ba ya kwantar da ita kirjina ya cigaba da latsa wayarsa. After like one hour ta ďaga daga jikinsa ta sauko downstairs ganin Ataa zaune tana kallo ya bakanta mata rai

sosai domin ba kowa take son yana morewa da abunta ba.

“Kin gama sharar ne da kika zauna kina kallo”

Ataa ta juyo da sauri jikinta har ba ri yake ta kalleta.

“Eh na gama tun dazu na share ko'ina na gyara”

“To daga yau karki sake rufe mana fus

karki, idan ba za ki iya bude fuska ba ko zauna a gidanku ba yadda za ki zo ki cutar da mu ki tafi ba tare da mun ha fuskarki ba”

“Wallahi ni ba na cutarta kowa”

“Ai ba za a iya ganewa a fatar ba ki ba, shiga dayan dakin ki wanke bathroom din kuma ki

gyada dakin”

Tana fada mata sannan na nufi kitchen dinta dan tabbatar idan kayan sun wanku.

ATAA POV.

Daukar tsinsiyar nai na hau sama a doshi dayan dakin wanda na ke saka ran shine dakin mijin, ciki tsoro da fargaba nai knocked, sannan na ja ba

ya kadan na tsaya ina ta jiran ace min na shigo amman shiru, sai hakan yasa ni jin babu dadi, daga fara aikina a yau na fahimci daga matar har mijin kamar ba su san darajar dan adam ba, wata kila kuma saboda na kawo kaina ne, ni da kaina ina nema shiyasa s

uke wulakanta ni oho. Na fi karfin minti talatin a tsaye bakin kofar sannan ya fito yana ta kamshin turare, har wani matsawa yake kai ya ra6o ta kusa da ni ya sauka downstairs.

  Be ba ni izinin shiga ba, dan haka ba zan shiga na taba wani abun da zai iy

a zan min matsala ba. Haka nai tsaye a gurin na kasa sauko kuma na kasa sai duk na ji na tsawwala, wani kankanci da bakincikin suka kwankwaso min kofa, na tabbatar da a ce yar wani ce ni da ba za su bar ni a gurin tsaye ba, za su nuna min kyama ba. Suna mi

n duka wannan saboda ina talaka kuma na raba jikinsu ina neman taimako.

Da gaji da tsayuwar ne na sauko kasa cike da fargabar abunda za ta ce min da Kuma irin kallon da mijinta zai min.

Tana zaune kan kujera ita kadai tana waya, da alama wayar tai mat

a dadi sai kyalkyalar dariya take tana buga kafa kasa, ni dai kallonta kawai na ke, irin rayuwar jindadi da take ciki ta burgeni ga ta cikin farinciki abunda na ke ta marmarin samu amman ya gagara, zaunawa nai kasa tile har ta gama wayar sannan na ce

“B

e ce min ya na shiga ba, ni kuma ban shiga ba, gudun kar na shiga ya zama laifi”

“Ya ce baya son ki gyara masa dakinsa”

“Yanzu zan iya zuwa gida kenan?”

“Idan kin ga dama”

“Na gode”

Sai na nufi inda na dauko tsintsiyar na maida, sannan na da

wo na dauki dattin sharar na fita da ita daga gidan gaba daya, can karshen layin unguwar n samu wata bola na zuba ta a ciki sannan na dawo na aje shi a inda na dauke shi na yi mata sallama ban jira ta amsa ba, na kama hanyar gata zuciyata na mugun kuna kam

ar an dora ta ka ce garwashin wuta.

  Ina tafe ina ta tunanin kamar ba zan iya jure aiki a gidan ba har na tsawon wata daya, saboda yadda na fahimcin hayyarsu da dabi'unsu ba kamar na kowa ba ne, sai dai idan ban yi aikin ba kudin su fa? Ai dole na biyas

u bayan kuma na riga na taba wani abu daga ciki kuma ina da bukatar kudin.

  Kamar yadda aka kai ni dazu haka wani mai achaba ya dawo da ni na bashi naira hansi sannan na shiga gidan, ina yin sallama Farida ta amsa tana wanke wanke, fuskarta da far'a kam

ar kullum ni ma na yi kokari aron murmushi na yaba a fuskata duk kuwa da kasancewar shi a kusa da ni.

“Har kin dawo? Nana tace min kin samu aiki?”

“Eh na samu, yau na fara”

“Allah ya taimaka, wane unguwa?”

“Nasarawa”

Na bata amsa ina shiga

inda Nana take, wanann karon a zaune na same ta ta saka dayan hannunta ta dafe gefen cikinta tana hawaye. Da alama ciwon ne ya taso mata domin ba abu kadan ke kasa nana yin hawaye ba musamman ciwo. Kusa da ita na zauna na rafka uban tagumi ina ta kallon sa

ukar hawayenta, ban san abunda zan yi ta samu lafiya ba, ban zan zwa zan kaiwa kuka ya saurareni ba, Doc Asim ya zalince mu zalince mai tsanani kuma na kai kararsa aka kasa kwatar min hakkina suka kasa bani gaskiya saboda ina talaka shi kuma yana mai arzik

i. Sai wani numfashi take wahalce ni kuma na kasa ko motsawa daga inda na ke zaune balle nai nata sannu yadda take hawaye haka ni ma na ke hawayen, kashi ya hade min goma da shirin can ba dadi nan ma ba dadi.

“Ni kadai na san irin zabar da na ke sha a

kan ciwon nan, ni kadai na san yadda zafin ciwon nan yake min, ni kam da ma na mutu wata kila da na fu samu sauki fiye da haka”

Cikin murya kuka ta fadi haka da sauki kasa-kasa. Hannu nasa na share hawaye na daga inda na hango kudin da na bata dazun na

dauka na fito jiki ba kwari na je bakin titi gurin wata pharmacy, na fada masa yadda ciwon yake sai ya ba ni magani kusan dubu uku da dari bakwai na dawo jiki na rawa na balla na bata na shafawan kuma na shafa mata, sai na koma ta bayanta na rumgumeta na f

ashe da kuka marar sauti, ji na ke kamar ace ina wata dama zan iya nema mata lafiya ta warke ita kadai ta rage min idan ta tafi ta barni ban san halin da zan shiga ba.

Na dade rumgume da mahaifiyata sannan na saketa ta kwanta, ni kuma na goge fuskata na

fito tsakar gidan ko za a samu sassaucin abinda na ke ji a zuciyata. Da na fito sai Farida ta dasa min wata sabuwar fira dama akwai da yawan magana, a nan take labarta min cewar mahaifinta ne ya ce Nana ta dawo nan ta raba ta zauna tun da mai wacan kangon

gidan ya koreta gashi bata da wani gurin zama. Ni kaina nasan indai Farida ba to ko sai mahaifinta, domin mahaifiyarta ba zata taba yarda tace ta zauna a gidan ba.

Bayan sallah magariba na dauki kudi da kwano na siyawa nana tuwon masara da miyar yauki

domin shine mai yar nasiha ba kamar shimkafa ba mai tsada, ko da na shigo na tarar ta samu sauki sosai tana zaune saman dankwalinta da tai sallah. Gaba na saka ta na cilasta mata cin tuwon ita kuma ta ki ta ci ala dole sai ni na fara ci, a dole sai na ci s

annan ita ma ta ci na kawa mata ruwa ta sha, sannan muka gabatarda Allah isha'i muka kwanta a gurin da mutum ba zai iya mike kafafuwansa ba straight ba.

  

***      ***      ***

Da wuri na farka gudun kar nai lattin zuwa gurin aiki, bayan na ayi alw

ala ita kuma na samo mata kasa tai taimama ta yi sallah asuba, cikin kudin na dauka naje na siyo mana koko da kosai da suga na kawo muka karya sannan na shiga bandaki nai wanka da ruwan sanyi duk da kasancewar akwai sanyin safiya da be gama sauka ba.

  B

ayan na fito na saka wasu tufafi, daman can shafa mai be dame ni ba bayan cikin tsarina wankan ma gudun kar suce ina wari da ba zan yi ba. Haka na shirya cikin wata kodaddiyar atamfata na sake kwaba gawayi kamar ranar na shafa a fuskata, tun da sun ce na d

aina saka nikab sai na saka bakin gawayin da na saba sakawa duk kuwa da irin kazantar da suke ganina da shi.

   Yau ma sai da na dauki naira dari a cikin kudin sannan na saka Hijab dina na yi ma Nana sallama na fito na shiga dakin Maman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login