Showing 222001 words to 225000 words out of 237425 words

Chapter 75 - ZAKI COMPLETE

yarinya saboda shekaru ko kuma wani abun da za ki na shirme ko rashin tunani, ballantana yanzu da kike dauke da juna biyu”

Na kasa yin kasa da kaina saboda kunya.

“Mi

jinki na bukatar kulawarki a yanzu fiye da ko yaushe, na san ba ki san wata dawainiyar ba, amman kula da abincinsa ya ci ko be ci ba yana wuyanki a yanzu, karki zamana shi kadai zai dinga damuwa da ke, mijinko ya rasa daya abokiyar rayuwarsa hakan kuma ba

karamin jefa shi yai a matsala ba, sai da taimakonki zai iya dawowa dai da ya manta komai kamar be faru ba, ki shimfida masa kalar rayuwar da kike son yai kuka ya bi saboda yana tsananin son ki ni na sani, na san ke ma kuma kin san da haka, ki rika yi masa

abunda zai kwantar masa da hankali da saka shi natsuwa, hakan ba karamin kara mishi son ki zai yi, a yadda yake damuwa da ke kuma yake son ki idan kina nuna masa damuwarki akan rashin cin abincinsa zai ci saboda gudun damuwarki kuma zai sa ya rage damuwar

, tun da akai mutuwar bana jin ya saka wani abu a cikinsa har yau sai ruwa, sannan ki rika yi ma mijinki addu'a a duk sallah musamman a sujadar karshe da kuma bayan tahiya kamin ki sallame, mace mai aure ma ba akarbar addu'arta har sai idan tana yi ma miji

nta da kuma iyayenta”

“In-Sha-Allah Momy”

“Kuma ke ma ki kula da kanki, wani abun ba sai ance ki yi ba, ya kamata ace kin san aure kike a yanzu, kuma ke ce kadai a gurin mijinki, mijinki na bukatarki a yanzu fiye da ko yaushe, ina fada miki wannan ne

saboda na san zaki iya kuma ke kadai na ke da tabbacin za ki saka shi cikin walwala a yanzu, mijinki be iya so ba, be iya ki ba, ba kuma iya sakawa rai abu ba, idan yana so gaba daya yake so baya ganin aibun abun har sai yayi zurfi a ciki, idan kuma ya ts

ane abu gaba daya yake tsanarsa baya iya ganin kyaun abu har sai yayi nisa a tsanarsa, idan kuma ya sakawa rai abu yana sakawa sosai ta yadda rashin abun nan zai yi ta damunsa yana cinsa a rai, daga ke har shi ni duk kallon yara na ke muku wani abu dole sa

i an nuna muku, saboda mun fi ku tunani da hangen nesa, na san ba ki yawance a komai ba, sai dai ke din jajirtacciya ce saboda gwargwarmayar rayuwa da kika sha, da kurciyarki kin fuskanci kalubale kala kala na rayuwa kamin yanzu, kuma da Allah ya tashi mik

i sakamako sai yai miki duka a lokacin da kike bukatar hakan, hakuri yana da kyau kuma yana da riba sosai duk wanda yai hakuri be ga riba ba to kadan yayi”

Sosai na jidadin magangannun Momy, a natse ta fada amin komai kuma na fahimci manufar da nufi, da

ga lokacin na sakawa kaina zan iya, kuma na fara jina a matsayin mace mai aure mai daraja wacce zata iya kula gidanta da mijinta da kuma yayanta duk kuwa da irin karancin shekaruna. Idan na waiwaya baya kadan na tuna abunda ya faru da ni irin halin rayuwar

da muka shiga da fadi tashi da nai sai na ga wacan rayuwar kamar labari aka ba ni ba ni ce na wanzu a cikinta ba.

“Tashi ki bi mijinki ku kwana a can”

Maganar Momy ta katse min tunanin da nake.

“Ba ki bukatar komai dai ko?”

“Babu”

Na fada i

na mikewa tsaye na dauki Hijabina na saka, sannan na fara takawa a hankali har na fito falo.

“Matar yaya ina za ki je?”

Siyama ta tambaya tana kallona da murmushi a fuskarta.

“Gida zamu je”

“Ba anan za ku kwana ba?”

“Eh”

Na amsa mata mu

ryarta da kamar damuwa. Sannan na karasa kusa da Mama Fulani na dan risina na ce mata.

“Mama za mu tafi gida sai gobe”

“To Allah ya tsare”

Ya mayar min tana kallona, sannan na karasa gurin Ammy ita ma nai mata sallama da wasu kannen Momy da yan'u

wan Daddy sannan ya fito harabar gidan. Na yi mamakin ganin Muhseen tsaye jikin motar Hamma yana magana da shi, ban san mi yake fada masa ba na ga dai Hamma ya gyada kai sannan ya bude min gaban motar tun kan na karaso.

“Ataa”

Kiran da Siyama tai mi

n ne yasa na juyo sai ta nufo ni da yar karamar dogowar kular silba a hannunta.

“Ga shi wai Momy ta ce ku tafi da shi”

“Mun gode”

Na fada bayan na karba, ko da na juyo ban ga Muhseen ba balle mafarinsa sai Hamma tsaye yana ta kallona har na karas

a, hannu ya kai ya karbi kular hannuna sannan ya matsa daga jikin motar wanda hakan ya bani damar shiga ciki na zauna shi kuma ya rufe motar, ya zagaya bangarensa ya shiga yai ma motar key.

  A hanya ya rika tambaya ko ina son wani abu, sai na ce masa ba

na bukatar komai, amman duk da haka sai da ya tsaya ya siya min gassashiyar kaza da yoghurt.

“Bana jin yunwa fa”

“Za ki iya bukata da dare ai, kuma ba dan ke kadai na siya ba”

“Dan wa?”

“Babyna”

Ya fada min fuskarsa babu walwala. Har muka is

a gida ban sake ce masa komai ba shi ma kuma be ce min ba, har sai da ya faka motar na kai hannu zan bude.

“Tsaya ba ri na bude miki”

Fita yai ya zagayo gefena ya bude min motar na fito sannan ya rufe, ina gaba yana bayana har muka shiga cikin falon

, sai ya zauna saman cushion yana ta kallona.

“Na hada maka ruwan wanka?”

“Zo nan”

Zuwa nai na zauna saman kafafuwansa kamar yadda na bukata sai ya rumgume yana sauke ajiyar zuciya a hankali sai dai hakan be hana ni jin saukarta. Mun dade a haka

kamin ya barni na daga jikinsa mu shiga daki, rumguma a cikin abunda Hamma ya ke so kuma ni ma nake so domin ina jin natsuwa sosai idan ya rumgume ni hakan kuma yana kara min jin son kusanci da shi sosai. Cikin jikinsa na kwana kamar kullum sa'a daya nai b

an farka cin abincin dare kamar yadda na saba ba. A lokacin da muka gama sallah asuba kuma sai na nufi kitchen na bar a dakin yana karatun qur'ane ni kuma na shiga na kunna gas din na sarrafa dan abunda na iya na ruwan zafin tea da suya wainar kwai da dank

ali sai kuma doya, sannan na bude kular da Momy ta ba mu jiya, farfesun kayan ciki ne a ciki, sai kawai na dora su akan wuta na dumama na juye a wata kular.

“Wow da kanki kike girki, na fada miki bana son wahalar nan da kike miyasa ba ki jin magana”

“Dan na yi aiki ba komai cikin zai yi ba, kuma ni bana son abincin waje”

“To amman sai ki bari idan na gama karatu Quranen na hada ko?”

“Bana son girki na namiji”

Wannan karon yayi kokarin fadada  fuskarsa da abunda ya rasa daga lokacin da akai m

utuwar nan zuwa yau wato murmushi shi ma kadan.

“Kin taba jin inda da zai ce baya son abincin babansa”

“Haka dai yace wai babansa be iya girki ba, idan ma yayi babu dadi shiyasa nake turo min shi nai amai”

Na fada ina yatsina fuska, sai ya kara m

atsowa kusa da ni ya rika hannayena.

“Karki masa karya, na san ba zai ce haka ba, ta ina ma kika ji ya ce haka? Yaushe kika iya karya”

“Yanzu”

Na fada da kamar kunya, sai yai murmushim gefen fuska yana aje numfashi. Shi ya taimaka min na karasa h

ada komai, sannan muka karya, be wani ci da yawa ba shi ma kuma dan na matsa masa ne, ni kan na ci abincin sosai kamar wacce ta kwana da yunwa, ni kaina har mamakin yadda na ke cin abinci sosai na ke kamar ba cin lafiya ba.

***  ***   ***

Har akai

zaman makokin aka gama Mommyn Rahma bata koma normal yadda take ba, damuwa ta taru a ranta ta tsaya mata, ba ita kadai ba gaba daya gidan babu wanda mutuwar Rahma bata taba shi ba, yau duk wani abu da Rahma ta mallaka na jindadi da dangi da kaunar iyaye d

a miji yau ta tafi ta barsu, mutuwa ta ishi kowa wa'azi, yau iyayenta sun ga Abunda kudi ko iko ko milki ko isa basa badawa wato rayuwa, komai ikon ka da isarka da milkinka baka isa ka hana mutuwa daukarka ba, kamin mutuwarta sun ga abunda ya kamata yace y

a zame musu ishara, na juyarwar al'amarin da ba su taba zaton zai zame musu haka ba, duk wani abu da Daddyn Rahma ko mahaifiyarta ko ma ita Rahma da kanta take takama da shi na familyn Ataa ne yarinyar da suka wulakanta suka maida ba komai ba, a karkashin

inuwar kakanta suke takama ta gidansu ce, ita din da suke gani ba komai ba Allah ya mayarda ita saman su, wani karin bakinciki ma ta zama ita kadai a gidan Aliyu babu yarsu a gidan balle tai kishi da ita. Yau sun koma sune kasa ta ko wane bangare.

Sai

da akai aka gama karbar gaisuwa sannan Mama Fulani da Ammy suka koma Abuja tare da Abbah daman shi Muhseen kwana biyu kawai yai ya koma saboda yanayin aikinsa. Nasir ma da matarsa sai da suka kara kwana daya saboda Aliyu sannan suka wuce. Aliyu da kansa ya

raka su har airport lokacin da za su tafi, Nasir yayi ta bashi hakuri da kuma kalaman da za su karfafa masa guiwa su akan rashin Rahma.

  After ya raka su ya dawo gidan Momy duk ya zama wani silent kamar ba shi ba, lokaci lokaci Rahma take fado masa a r

ai, idan ya tuna cewar be cutar da ita a zamantakewar su da aure ba sai ransa yai fari tas domin babban abunda yake gudu a rayuwarsa zalintar wani ko danne masa hakki da ikonsa, and wani abun godiya ga Allah da Allah ya saka ba Ataa ce ya rasa a yanzu ba,

domin da ita ta tafi a yanzu maimakon Rahma wata kila da zai fi shiga damuwa sosai fiye da Mutuwar Rahma, duk wani abu da yake game da Rahma sabo ne kawai da kuma tuna irin rayuwar da akai ko makinyin ka ne ya rasu sai ka ji babu dadi balle kuma matarka, y

ana yawan ayyanawa kansa wata rana zai mutu Rahma ma zata mutu saboda matsalarta tun daga kan cire mata koda da akai na farko da ta biyun ta lalace aka canjin mata wata da ta mahaifiyar Ataa ta zo ta kone abun ya soma ba shi tsoro. Wata kila ta kone ne sab

oda Allah ya nuna musu ikonsa akan abunda suka aikata sai dai hakan be zame ma Rahma da iyayenta ishara sai ma kokarin aikata wani suke, yanzu kuma da mahaifiyarta zata bata nata sai Allah ya gwada musu ikonsa ya karbe abarsa a lokacin da suke tsananin buk

atarta kuma babu yadda suka iya da ikon Allah. Yar da suke kishi da fada akanta mai abu ya karbi abarsa kuma ya maida wacce suke kishin da ita asaman su sai kuma ya?

ATAA POV.

kamar yadda Momy ta fada min ina kokarin ganin Hamma ya ci abinci ko da

ba da yawa ba, kamar yadda ni ma yake tsare ni na tisani a gaba dole sai na ci na koshi a cikin satin sai ya zama ni da shi muna bawa junanmu kuwawa ta musamman da kuma ganin tausayin junanmu, yana ganin tausayin cikin da na ke dauke da shi da kuma tausayi

Rahma sai ya dawo kaina ni kadai daman can kuma ga kaunata a ransa, yadda yake tallalina kana ganin abunda yake min kamar mai tsoron ya rasa ni ne, ni kuma tausayinsa ya cika raina sosai na rashin Rahma da yai da kuma yadda baya iya bawa kansa kulawa ta m

usamman amman yana kokarin kula da ni. Wanda ya rasu shi ya tafi babu abunda za a canja daga rayuwar wani ko kuma duniya gaba daya, daga lokacin da rayuwarka ta yanke shikenan kai na manta da ka taba wanzuwa a wata duniyar ma, kana ciki kabarinka kana fusk

arta abunda ka aikata idan alheri ka fara gani idan kuma akasin hakan ne shi ma zaka gani. Na karu da abubuwa da dama a mutuwar Rahma a ciki akwai na tunatar da ni cewar saboda na samu jindadi da kwanaciyar hankali a yanzu ba shi yake nufin mutuwa ta manta

da ni ko kuma ni na manta da ita. Abu na biyu kuma na yarda wanda ya mutu shi ya mutu duk kuwa irin son da ake masa, domin Hamma ya dan fara sakewa ba kamar da ba, daman kuma ai ba zai dawwama a cikin bakincikin mutuwarta ba kamar yadda take tsammani sabo

da Allah ya musanya masa da ni, wata kila da ace ta tafi a lokacin da be aure ni da zai fi shiga damuwa sosai, a kokarinsa na faranta da saka ni nishadi ni da abunda yake cikima kamar yadda yake fada, sai shi ma ya saka kansa ba tare da ya sani ba, ban ayy

anawa a raina cewar wata rana Hamma zai so ni kamar haka ba, kuma zan rayu a gidansa daga ni sai shi sa abunda zan haifa inda da rai da rabo.

  Kusan kullum ina waya da Nana wacce na ke kira da Mama a yanzu saboda canjin da Hamma yai min tama tambayar la

fiyata da ta Hamma na fada mata muna nan lafiya, har take fada min akwai yan'uwa da yawa da ban gani ba sai idan komai ya laba na dawo, ni dai sai dai na amsa da to amman na san yadda Hamma yake daukin cikin nan da ni ba zai iya barin nai nisa da shi ba, i

dan muna gida a jikinsa na ke wuni idan kuma mum taho gurin Momy idonsa na kaina da na yi wani abun da ba daidai ba sai yi kin alama da ido. Momy ma tana kula da ni har zaman da ke kusa da kofa sai ta fada min wai mai ciko bata zama a bakin kofar dakin ko

kusa da kofa aaboda aljanu, ni dai abun har dariya ya ba ni sai dai ban yi a gabanta ba, ni dai ban taba jin haka ba wata kila saboda ban zauna da tsofi ba ko kuma ban yawance akan irin waennan abubuwa, wata kila kuma saboda suna son cikin ne suke ganin ko

mai be dace nai yi ba. Shi kanshi Hamma da safe sai ya min addu'a har a cikin haka ma da dare idan zan kwanta. A ranar da muka wuni idan Momy take masa maganar karatuna sai ya nuna mata baya so.

“Momy ga ciki kuma ace tai karatu? Haba abun ai sai yai d

awo, da karatunta zan ji ko cikin?”

“Wai dan wajen Fulani kanka farau ciki ne? Karatu ko na islamiya sai ta fara da shi a yanzu, saboda kula da kanta da addu'oi, ai ilmin mace yana da muhimmanci ba wai ko dan aiki ba, saboda kula da yayanka ma ta koya m

u su, kuma idan babu ilmi tarbiyar ma ya kake tunanin za ayi ta? Miyasa ake son auren mace mai ilmi ba dan wannan ba”

“Momy ki ma kinsan dan wajen Fulani da Mama Fulani komai na su dabam ne, gaskiya ni ba zan iya daukar wannan ba, ke ma fa Momy kin san

yadda ake bukatar abun nan yanzu kuma ki kawo wasu maganganu haba dai Momy”

“Haba dai? Yanzu kana ganin idan a gurin Kakanta take kuma ya samu labarin bata iya komai ba batai karatu ba zai zuba mata ido haka? Yanzu ka fi son tai ta zaman banza a wata ba

kwai ko takwas da ke tafi wanda za tai nan gaba? Ai ya kamata ka saka ta ilslamiya ko kuma na nemo malamin da zai rika karantar da ita a gida, in so shi bokon idan ta haihu sai ta yi, baka sani ba ma ko tana da burin yin wani abu da karatunta”

Momy na f

adin hakan ni kuma nai karaf na ce.

“Eh ina son nai likita ko nurse abun na burge ni sosai Wallahi”

Harara ya watso min.

“Eh ba ri ki sake magana na buge miki ba ki a nan, haka nan za ki je ki yi karatun likita shekara nawa tare da maza?”

“Ai

ansan ina da aure kuma zan rika saka hijab har da niqab ma”

“Ba za ki yi shirun ba? Ba ki san kyaunki hadari ne ba, kuma ba ki da wayo da za ki iya tattalin abunki balle har ki kare martabarki, ni ko ko tafin kafarki aka kalla aka yaba Wallahi zafi zan

ji”

“Allah ya sauwake maka wannan bakin kishin daya cika maka zuciya, amman karatu kan dole ne tai yarinya ba za tai zama haka ba, kai ma da yarka ce ai ba zaka barta haka ba”

“Momy za tai karatu, karatuna yana cikin burin da na ke da shi akan Ayush

er amman sai ta haihu ta yaye abunda ta haifa ya yi kwari sannan a fara maganar karatun shi ma idan bata samu wani cikin ba”

“Yanzu a maimakon zaman da za tai ai sai ka sakata ta fara daga matakin farko kamin ta haihu dan yai kwari ta san wani abu ka ga

ci gaba kawai za tai”

“Momy mun ma kusa barin garin nan Abuja

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login