Showing 132001 words to 135000 words out of 237425 words
zai hana wannan auren ba”
Husna dai ta kalli Momy ta janye fuskarta tana tunanin yadda za ayi wannan chakwakiya domin Muhseen ma ba kyalle ba ne, kuma yadda yake nuna yana son Ataa yana da wahala ya iya yarda ta au
ri Aliyu yana kallo.
Haka Momy ta kwana da bacin ran abunda ya faru ta tashi da shi, Daddy kan dariya kawai yake mata daman haka yake mata idan ta saka kanta a wani abun at the end kuma be yi kyau ba, sai dai bata fadawa Daddy kudirin na na aurawa Ataa
Aliyu ba, domin ta san ba zai zabi Aliyu ya bar Muhseen ba, duk kuwa da kasancewar be san Muhseen na son Ataa ba, bayan maganar tafiya Abuja da suka aje jibi babu wata maganada ta sake masa.Lokacin data dawo part dinta bakwai da kwata ne na safe, sai da t
a fara shiga kitchen ta kunna gas ta dora ruwan zafi sannan ya fito falon tana dauke da dankalin turawa ta shiga dakin Siyama, sai ta same ta zaune tana home work din da bata samu yi jiya da dare ba.
“Momy ina kwana?”
“Lafiya kalau rubutu kike?”
“Eh homework ne da ban yi ba jiya”
“Okay ba ri na kaiwa Husna ta gyara min dankalin”
Ta fada tana juyawa ta fice daga dakin Siyama zuwa na Husna, ita ma zaune ta sameta sai dai waya take tabawa, tana ganin Momy tai saurin saukowa daga saman gadon da
kayan bachinta ta karbi robar hannun Momy.
“Momy ina kwana?”
“Lafiya kalau kin tashi lafiya”
“Lafiya kalau? Ya bacin rai?”
“Ba zai gushe ba ai sai na cika burina, kar wannan maganar ta fita ki barta tsakanina da ke ko Amina bana son ta ji”
“In-Sha-Allah Momy”
“Idan kin gyara dankalin ki kawo kin kitchen, kuma kin san bana son kazanta ki fito waje ki gyara ba a daki ba”
Momy ta juya ta fice daga dakin Husna, da kanta ta shiga dakin Amina ta taso daga guntun bachin data fara na safe.
“Amina ta so muje kitchen ki min wanke wanke”
“Tau”
Ta fada tana sauko daga kan gadon sanye da doruwar rigarta, Momy na gaba Amina na baya har suka shiga kitchen din, sai da ta soma hada kayan wanke wanke ta tana wankewa Momy kuma na shirya abun kar
in kumallo ta ce mata.
“Amina Muhseen fa ta fadawa Daddy ku wai a tambaya masa ke idan kina son sa?”Amina ta ji abun wani banbaragwai. ta tambaya har tana nuna kanta
“Ni...?”
“Ke fa”
“Ya Muhseen ba Ataa yake so ba?”
“Nima haka nai zato, ya
ce idan zan je yi ma Abbahsu murna na wuce masa da sako”
“Yaushe za ki je?”
“Jibi shiyasa na ke son jin ta bakinki tun yanzu, idan ma tunani da shawara za ki yi sai ki yi kamin na tashi”
Dariya Amina tai domin sam bata dauka da gaske Momy take ba.
“So dai suke ku hada mu Momy, amman Ya Muhseen ai Ataa yake so”
“Karya zan miki kenan?”
Amina bata sake cewa komai ba bayan dariyar da tai.
ATAA POV.
Da wani kallon haushi na bi Aliyu bans an dalilin son nuna isa da yake min ba, abunda
yake min ko kanensa baya yana ma haka, domin su ai suna wayar be taba hana su ba sai ni. Haka na tashu ta tunzure bakina na tafi bq din mu na zauna bakin kofar dakin da Nana take ciki kwance, ina ta jin haushin karbe wayar da Aliyu yai domin ban gama waya
da Muhseen ba, kuma ina son idan mun kai karshe na tambaye ko yana da labarin Kamal amman wannan bakin Aliyu ya zo ya karbe wayar.
Bayan sallah isha'i Siyama ta kawo mana abinci a wata kula da plates mai kyau, tuwon shimkafa ne da niyar ganye ban wani
ci sosai ba amman Nana ta ci shi sosai har sai da ta rasa masokar tsintsiya a cikinta. A katifa daya muka kwanta, kasancewar yarwantacciyar katifa ce ba kamar gadon asibiti ba da iya mutum daya yake dauka, katifar mai fadi ce sosai amman na matse bayan Nan
a na kwanta jikinta kamar zan tsaga bayanta na shige ciki, nai bachina cikin kwanciyar hankali har safe.
Bayan mun gama sallah Nana ta ce shiga bangaren Momy na taya ta aiki, ni kuma ban shiga ba sai da rana ta fito domin a tunani ba su farka ba a wann
an lokacin duk kuwa da na san suna tashi sallah asuba amman ai suna komawa. Har na fita haka sai kuma na dawo na dauki Hijab na saka gudun kar na hadu da Aliyu ya sake min masifar ban saka Hijab ba, ko da na shiga part din a samu Momy a kitchen Amina kuma
tana zaune falo rike da remote tana kallon tv sai dai kana ganinta kasan hankalinta ba a gurin tv yake ba. Sai da na gaishe ta sai na sannan na nufi kitchen din dan gaishe da Momy sai na same ta tana waya, da alama da Mama Fulani take wayar domin na lura t
ana cikin far'a har ma tana fadin jibi za mu zo, sai da ta gaka wayar ta sauke sannan na gaishe ta amsa, na nufi inda kofar bayan kitchen din take dan dauko tsintsiya na ce.
“Momy Abuja za ki je?”
“Eh jibi In-Sha-Allah ko za ki je?”
“Eh Momy”
“To ki shirya da wuri yata”
“To na gode”
Wani irin dadi ne ya lullube ni, babu wanda na kawo a rai na sai Kamal, zan jure wulakanci Mama Fulani tun da da Momy za mu je kuma saboda Kamal zan je, haka na share gidan tsaf cikin nishadi, a dayan bangaren
kuma ina tsoron kar Aliyu ya zo ya hana ko kuma ya iya zama tafiyar mai dadewa cewa ba zai yi naje na bar Nana ba, sai idan tafiyar kwana biyu ce.
**ZAKI
By Khadeeja Candy
38...
Juyi yake ta yi akan gadon idonsa biyu ba dan yana jin bachi b
a sai dan kishin da ke tare da shi, lips din bakinsa ya ke cizo kamin ya unkura ya tashi zaune yana shafa kansa. Short and white ves ne a jikinsa ya samu minti goma a haka sannan ya mike tsaye ya ware red curtains din dakin, ya bude class windows din haske
ya shigo sai ya juya yana kallon bed dinsa. Sai kuma ya nufi kofar fita daga bedroom din, kasa ya sauko kai tsaye ya nufi kitchen ya kunna electric kettle ya dauko wani kofin ya matsa lemun tsaki da kanwa a ciki, ruwan zafin na tafasa ya zuba a cikin kofi
ya bar shi a haka ya dauki wani kofin ya hada Lipton da suga kadan, sai da ya jira lemun tsamin da kamwar sun dan huce sannan ya dauka ya sha ya dora da ruwan Lipton din. Freezer ya bude ya dauko kankara a gorar ruwan faro ya dawo bedroom dinsa ya shiga b
athroom ya fashe kankanrar ya zuba a cikin bokiti ya sirka da wasu ruwan ma su dan dumi yai wankan da ruwa mai sanyi sosai sannan ya fito daure da tawul yana jin ya samu relief. Be dauki minti talatin ba tsakanin shafa mai da saka tufafinsa wani irin kuzar
i yake ji sosai, kamar ba shi ne ya kwana a gado jiya kamar marar lafiya ba. Maroon shirt ya saka da white jean colar shirt din ta karbi jikinsa sosai ta kara fito da farinsa da kuma kyan fuskarsa, haka ya firo harabar gidan fuskarsa har ya wani annuri tak
e. Tun kan ya karasa gurin motar ya danna keys din hannunaa yai kara hakan ya hankaltar da mai gadinsa yai saurin isa gate ya bude masa tun kan ya tashi motar. Yana shiga yai mata key ya dauki hanyar arkilla wato gidan Momy, daman ba shi da gidan zuwa sai
can ko lokacin da Rahma take nan balle yanzu da bata nan. Sau daya ya danna horn mai gadin ya bude masa gate, kusa da inda Ataa take zaune tana gyaran doya ya faka motarsa, zaunawarsa yai a motar yana ta kallonta ta cikin gilashin motar, ita ma kallon baki
n gilashin motar take ba dan ta san wanda ke ciki ba, sai dan yau murna take Momy tace zata je da ita Abuja, murmushi kawai take abinta kana ganinta kasan tana cikin farinciki sosai. Ya dade yana ta kallonta kallonta na burge musamman idan shi kadai yake k
allon nata ba tare da ita din tana kallonsa ba, domin yana tsarguwa idan tana kallonsa. Samun kansa yai da murmushi ganin murmushi a fuskarta duk kuwa da be san silar farincikin nata ba, but seriously ta burge shi and he like her smile more than everything
yanzu, bude motar yai ya fito har ya rufe ita yake kallo ita kuma sai murmushi take mishi har da wani.
“Laaa kai ne? Ina kwana?”
Be amsa ta ba ya nufi bq yana ta mamakin dalilin farincikin nata ko mi akai mata take wannan far'a oho. Ko davya shiga
Bq Nana na zaune balcony tana kallon itacen guava dake kusa da bq din, har kasa Aliyu ya risina ya gaishe da ita yana wani kasa da kai kamar mai jin kunya.
“Ina kwana?”
“Lafiya Kalau, ke tashi lafiya?”
“Lafiya kalau ya jikin na ki”
“Al-hamduli
llah, Allah ya saka da alheri mun gode mun gode sosai”
“Ba komai, idan dai kina bukatar wani abun ko kuma kinji wani abun sai ki yi magana”
“Yayi kyau ba matsala In-Sha-Allah, Allah ya biya”
Ta fada da murmushi a fuskarta har ga Allah Aliyu yana b
urgeta yadda yake hidima da ita da kuma irin kulawar da yake nuna mata tana jindadi sosai, wani karin abun farinciki ma da Ataa ta fada mata har jininsa ya bada aka saka mata sai ta ji kamar ta dauki zane ta goya shi a bayanta.Ya fito bq din yana wasa da b
q din hannunsa yana murmushi, at least now na durkusa har kasa ya gaishe da Nana bayan gaisuwar da ya taba mata a asibiti da risinawa, abun ya burgeshi shi kanshi ya ji kanshi a wani mutum daban. Murmushi da Ataa ta gani a fuskarsa lokacin da ya fito bq ne
yasa ta kyalkyale da dariya for no reason tana kallonsa, kallonta yai har sai zai wuce ya shiga falon Momy sai kuma ya ji ba zai iya ba sai ya ji dalilin wannan farincikin da Ataa take yi. Karasowa yai kusa da ita ya tsaya a akanta ita kuma ya daga kanta
sama tana kallon still murmushi a fuskarta.
“Mi akai miki kike dariya?”
“Ba komai”
“Ba koma kike jindadi?”
“Momy ce ta ce zata je da ni Abuja, kwana biyu zata yi ta dawo”
Yasan Mama Fulani bata son Ataa kuma ta yi ta gana mata zaba ita da y
ayanta, dan haka ataa ba dadin zaman dake ji a can ba, to miye abun murna dan ance za a kai ka inda ba dadi kake ji ba.
“Miye abun murna a cikin?”
“Idan na je ai zan ga Kamal ko?”
Ta fada da sigar tambaya kamin ta cigaba.
“Shine na ke jindadi
ai”
Ta fada tana murmushi ba tare da ta bude hakoranta ba, wani irin abu ya ji ya daki kansa ya soki zuciyarsa yayi cikin
ɓ
argonsa, a take ya nemi nishadin zuciyarsa da na fuskarsa ya rasa, ya wani hade rai har idonsa na canja kala.
“Ita kuma Nana k
i bar ta a hannun wa?”
Ta yi shiru tana bata fuska sai ta soma yanka doyar da karfi tana jin haushin maganar da Aliyu yai a yanzu. Be sake ce mata komai ba ya nufi kofar falon ya tura ya shiga, Amina ce har yanzu zaune a falon remote a hannunta kamar da
zun Husna kuma na kitchen ita da Momy.
“Ina kwana Yaya?”
“Lafiya Kalau”
Ya amsa mata kamar baya son karbawa. Tashi tai ta nufi dakinta shi kuma ya nufi kitchen.
“Ina kwana Ya Aliyu”
A takaice ya amsawa Husna yana mikawa Momy nata gaisuwar.
“Lafiya, Momy ina kwana?”
“Lafiya kalau, Husna ki hada da doya idan Ataa ta kawo”
“Okay”
Husna ta fada tana cigaba da soyan dankalin da take Momy kuma ta juyo ta fito daga kitchen din zuwa falo tare da Aliyu, yana ganin yanayin fuskarta ya sam
bata cikin nishadi, sai da ta fara zaka sannan shi ma ya zauna.
“Momy ke kika ce zaki tafi da Ataa Abuja?”
“Waya fada maka?”
“Ita ta fada min yanzu”
Momy ta yi murmushi.
“Eh Daddynku ya ce Abbah ya samu mai siyen kamfanin nan an har siye k
uma an biya kudi za a cigaba da komai karkashinsa, ni ban ma sani ba sai jiya shine yake cewa ya kamata muje mu masa murna ko da shi be samu zuwa ba, to ta shigo ta tarar ina waya da Fulani ta ji zancen zuwa Abuja shine ta ce tana son za ta bi ni”
“Kark
i je da ita Momy”
“Saboda me?”
“Mahaifiyarta wa za ta barwa ita? Kuma ko tafiya kika yi da ita Muhseen daukarta kawai zai yi yayi ta yawo da ita”
“Wannan ai ba hujja ba ce, daga ni sai Husna zan je sai kuma ita, Amina da Siyama ai za su iya kula d
a Nana, tun da zata iya kai kanka bandaki ta fito da kanka”
“Momy karki je da ita dan Allah, Wallahi saboda ta ga Kamal zata je, yarinyar nan tana son sakawa kanta soyayya da kurciyarta, Wallahi idan ba a takawa yarinyar nan burki ba zata iya lalacewa”
Momy ta yi dariya.
“Ita tace maka saboda Kamal zata je? Son Kamal din take ne?”
Yayi shiru be ce komai ba ganin Ataa ta shigo dauke da robar doyar da wuka.
“Gashi Momy”
“Kai kitchen”
Kai tsaye ta nufi kitchen din, Aliyu ya kalli Momy ya
ce.
“Momy ki fada mata tun yanzu Wallahi ba zan bari taje ba”
Ban da Murmushi babu abunda Momy take har Ataa ta kai doyar ta aje ta fito rike da farce, da alama ta yanke ne.“Ataa babu zancen zuwa Abuja da ke in ji Dan wajen Fulani”
Ataa ta bata
fuska sosai tana murza yatsan.
“To mi nai? Kin fasa zuwa da ni kenan?”
“To sai mum gani dai yanzu”
Momy ta tambaya tana kallon yadda take mursa hannun nata. Ban da kallon ta babu abunda Aliyu yake ban da kallonta ya lura da yadda take murza hannun
.
“Mu ga hannun”
Kamar jira take yana cewa haka ta maida hannayen nata duka baya ta turo bako idonsa na cika ta kwalla ta nufi kofar fita, sai da ta lura da idon Momy basa kanta sannan ta murguda masa baki hawaye na sauko mata, a maimakon ya ji haush
i sai ta yi mugun burgeshi har yayi murmushi ya maida fuskarsa gurin Momy wacce ta dauko masa wani zance.
“Jiya an fada min ba dadi a gidansu Rahma, ta yi min gorin haihuwar wai baka haihuwa shiyasa kake dawainiya da Rahma, kuma wai Rahma ba zata koma
ba sai nan da wani lokaci”
“Miya kawo haka?”
A nan Momy ta labarta masa komai car ciki har da zancen Ataa da mahaifiyar Rahma tai, sosai ran Aliyu ya bace duk wani abun da mace take masa yana shayewa ya kyale amman ban da taba masa family ko da kuwa
kannensa ba sam baya daukar wannan balle kuma har ace Momy da kanta.
“Kin fada musu gaskiya Momy, Wallahi ko Rahma kadai ta rage a gidan nan ba zan je bikonta ba, ganin damar ta ce tasa ta tafi ba dan an mata wani abun ba, and zan nunawa Rahma ko waye
ni”
“Bana son ka mata komai, bana son ka ce mata komai ko ka nuna mata damuwarka, abunda na ke so kawai ka bata mamaki, ka tabbar min da alkawarin da mai musu kuma ka cika min burina na abunda nai niyar hadawa”
Kallon rashin fahimta ya yi mata.
“
Kamar ya?”
“So na ke ka kara aure...!”
Shiru yai for a while maganar Momya ta masa nauyi duk kuwa da shi kansa ya san yana bukatar auren, amman wa zai aura? Shi kwata kwata be taba kawo zancen zama da mace biyu a rayuwarsa ba, but if wannan hanyar ce
zata saka Momy ta huce haushin abunda Mahaifiyar Rahma tai mata dole ya yi, ko dan ya nunawa Rahma he can live without her and to avoid zina da alfasha.“Idan karin auren ne abunda kike so consider it done, zan kara auren daman burinku kenan ke da Mama Ful
ani”
“Na jidadin hakan, wannan kadai zaka yi ka saka Rahma ta shiga hankalinta, kai ma kuma ka samu rayuwar da kake muradi domin sai ka auri wata ne zaka gane wacece mace wacece muna mace”
Murmushi yai ya mike tsaye ya nufi dinning.
“Zan baka sat
i daya ko biyu ko sama da haka ka nemo wacce kake so, ka ga sai a hade aurenku da Muhseen ma”
Momy ta fada tana binsa da kallo shi kuma ta juyo yana kallonta.
“Muhseen ya fitar da mata ne?”
“No ba Ataa yake so ba?”
“Zan dauki lokaci kamin nai
auren ne?”
“Ni da na ke son ka y again and a xuiin watan nan ma”
“Amman kike cewa Muhseen ya auri Ataa yanzu? Waya ba shi ita? Yarinyar da zan saka ta a makaranta ta fara karatu yanzu ita kike cewa Muhseen ya aura?”
“Ai zata iya karatu a gidansa z
ai kula da ita”
“Wallahi Momy Muhseen ba zai auri Ataa ba, indai ba son jefa rayuwar yarinyar nan kike son yi ciki matsala ba, karki aura mata Muhseen ko an yi auren nan ba