Showing 63001 words to 66000 words out of 237425 words

Chapter 22 - ZAKI COMPLETE

zai iya dukan nata ba, da ace yau wani tsaye agabansa ba Ataa ba ya fada masa bakar magana kamar haka babu abunda

zai hana shi taka shi yadda yake so.

Jin be ce komai ba sai kallonta da yake da jajayen idonwansa naman fuskarsa na rawa yasa ta juya da zimmar fice, sai ya kai hannunsaya fisgota ta juyo da ita ya nuna ta yatsa bakinsa na ta rawa kamar zai ce wani abu

kuma ya kasa furta komai. Kamar wanda ya tuna wani abu sai yai saurin sakinta yana kallon hannunsa kamar mai kyama, ita hannun nasa ta kalla kamin ta kalli kafadar daya rika.

“Gaskiya ne, be kamata ka rika ni ba, kar na saka maka talauci, talauciabun

gudu ne na sani, ni kaina ba dan talauci ba da baka isa ka saka a cire kodar mahaifiyarta da matar da bakin likitan nan kuma na barku kuna yawo ba, ba dan talauci ba da baku isaku gan ni a wannan asibitin ba balle har ku zalince mu, da ba dan talauci ba da

ba mu raba a kangon gidan babansu Rahma ba da har wulakanta mu, ba dan talaucin ba da baka isa ka shigo inda na ke kwana ka taka shi da kafafunka da suke da takalmi ba, ba dan talauci ba da ban zo aiki cikin gidan har a wulakanta ni ba, ba dan talauci ba

da yau Mama Fulani bata daga hannu ta mareni ba balle yar ta kirani yar iska, komai saboda talauci ne komai komai ina nufin komai”

Ta fada tana durkushewa a gurin ta fashe da wani irin kuka mai ratsa zuciyata. Kasa cewar komai yai yana ta sauraren yadda

take rare kukan yana shiga har kasan zuciyarsa. Shigowar Mama Fulani da Muhseen ne yasa shi juyawa zai fito da idonta da suka gama renewa.

“Mi kai mata Aliyu?”

Muhseen ya tambaya cikin mugun bacin rai. Mama Fulani ta tari numfashinsa.

“Mi yai ma

ta? Wace irin magana ce wannan Muhseen? Ya wuce tai masa ba daidai ba ya mareta”

Muhseen ya karasa kusa da Ataa ya dago hannunta yana kokarin ganin fuskarsa.

“Who do you fucking think you're wai Aliyu? Kawai sai kai ta tunanin taka kowa yadda ka ga d

ama?”

Juyowa Aliyu yai yana masa wani mugun kallo ya ce.

“Saboda na isa ne ko akwai abunda za kai?”

Muhseen zai yi magana Mama Fulani ta daga masa hannu.

“Enough of this, saboda yarinyar nan yau fadan ku biyu, ya kuke abu kamar ba yan'uwa juna

ba what?”

Jin muryar Mama Fulani kamar zata fasa kuka yasa Aliyu saurin fita daga garejin cikin bacin rai kala biyu na Ataa da kuma na Muhseen. Motarsa ya nufa ya shiga ya dauki hanyar kamfaninsa, kana ganin yadda yake driving kasan yana cikin tsananin

bacin rai. Duka ma'aikatan kamfanin sun yi mamakin ganinsa a wannan lokacin domin babu wanda ya san da zancen zuwansa balle kuma har ya shigo kamfani, he choose yaje kamfani sama da ya ji gida Rahma ta ganshi a haka ta zargi wani abu har ta kara bata masa

rai. Duk inda yabi gaisheshi ake amman be amsa gaisuwar kowa ba har ya isa office dinsa ya saka katinsa kofar ta bude masa ya shiga ciki. A one of visitors chairs ya zauna yana jin kansa na mugun sara masa, kirjinsa kuma kamar zai fito saboda zafin da yak

e masa. Wani zafi yaji yana sauko masa da sauri ya tashi ya je ya kara gudun ac ya zo gaban teburin ya buga shi da karfi yana fitar da numfashi kamar wani zaki. Hannunsa yasa cikin gashin kansa ya matse kan sosai he tried to make himself calm, shi kansaba

zai iya fadar ya fi saka shi wannan bacin rai a take ba, a cikin maganganun da Ataa ta fada masa ko wacce ta masa zafi amman ya fi jin zafin kukan da take fiye da maganganunta, and the way da Muhseen yake shige masa hanci yana bata masa rai, daman can shi

da Muhseen basa shan inuwa daya. Freezer office din ya nufa ya bude ya dauko gorar ruwa mai sanyi sosai ya bude ya kafa kansa bakinsa ya sha rabi, ya zuba rabin a jikinsa saboda zafin da yake ji, haka yake ji a duk lokacin da ransa ya bace, sai dai ba kara

min abu ke saka shi bacin rai kamar haka ba, sai an tona. Zuwa yai ya zauna a kujerarsa ya dauki files din gabansa yana dubawa, duka sababin files ne da be san da zamansu a office din ba kamin ya tafi. Telephone din dake gabansa ya danna.

“Nasir same ni

a office”

“Office?”

Nasir ya amsa daga dayan bangare, Aliyu be sake ce masa komai ba ya aje telephone din. Ko three minutes ba ayi ba na'urar da ke nuna isowar mutum ta fara kara tana fitar da danja ja, sai Aliyu ya kai hannunsa karkashin tebur din

ya taba wani abu kofar ta rabe biyu Nasir ya shigo da saurinsa yana sanye da Suit.

“Ban sa ran zaka shigo office daga dawowarka yau ba”

“Ka kori mutanen nan, ba san aikinki su ba za mu iya daukar wata kaddara ba”

Ya fada yana jefawa Nasir files d

in guda uku. Nasir ya duka ya dauka yana duba.

“Dukansu sun kware akan aikin nan Aliyu wannan karon ne kawai aka samu matsala kuma kasan yanayin garin ai”

“Fired them”

“Idan muka koresu za mu dade ba mu maye gurbinsu ba”

“I don't care fired th

em, kuma ka basu albashinsu”

Nasir ya kalleshi da kyau sannan ya zauna yana fadin.

“Fada min me ke damunka?”

Aliyu ya mike tsaye yana ta huci ya nufi windows ya tsaya yana bude aninin rigar shaddar da ke jikinsa, sai kuma ya juyo ya kalli Nasir c

ikin bacin rai ya ce.

“Yarinya karama zata fada min maganar banza? Yarinya karama?”

“Ka samu ganinta?”

“Na same ta a family home tana ma Mama Fulani aiki, ta fada min magana son ranta a yau, har abunda ban yi mafarki ba ta fada min and she called

me azzalumi imaging”

Ya karasa yana dora duka hannayensa a windows yana kallon wajen.

“Duk shine ya saka wannan bacin ran? Aliyu dole fa kai hakuri iyakar zalinci fa an zalinci yarinyar nan, kuma abu ne mai wahala ta iya son ku a zuciyarta, idan har

kana son ta daina maka kallon azzalumi dole ne ka fahimtar da ita, and show her your good side mana, wannan girman kan da fada da rashin tausayi duk sai ka aje shi a gafez zancen ta ji tsoronka be ko taso ba”

Juyowa yai ya kalli Nasir

“Ina da girman

kai ne?”

“Au baka da shi?”

“Kawai dai na san bana daukar raini ne”

“Amman miyasa ka damu da yarinyar nan ne har haka?”

“Saboda kawai ta daina min kallon azzalumi ne, ko akwai wani abun bayan wannan?”

“Kai ba ka sani ba ni ya za ayi na sani?

Make yourself calm Aliyu, this is the right time da zaka taimake ta maybe ta yafe maka, idan mahaifiyarta tana nan kuje ku roki yafiyarta ku nema mata magani”

Ya daga kansa sama yana ta mamakin kansa.

“She got lucky wallahi, da ba ita ta fada min ha

ka ba yau ko? Hmmm”

Nasir yai murmushi.

“Kuma ka damu ko? Ni Wallahi kai ke ba ni tausayi ba ita ba”

Kallonsa kawai yai ya karaso gurin tebur din ya dauki keys dinsa ya fice daga office din.

*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884

Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*

21.

Aliyu na fita Mama Fulani ta fice cikin bacin rai, sai ya rage dakin daga ni sai Ya Muhseen da ke ta rarrashina.

“Fada min dukan ki yai?”

“Be min komai ba”

Na fada ina share haway

ena idanuwana sun ji ja sosai, domin ba kadan nai kukan ba.

“Be miki komai ba za ki yi kuka? Fada min gaskiya mana, dukanki yai ko?”

“Be min komai ba, kawai kaina ne yake ciwo shine”

“Za mu shirya da ke idan kin fada min abunda yai miki”

Ya fa

di hakan yana nuna ni sannan ya juya a fice cikin yanayin da ke nuna yayi fushi da ni. A ganina be kamata na fadi abunda zai iya zame min matsala, nasan idan har na fada masa dalilin kukan nawa wata kila zai iya tambayar mahaifiyarsa dalilin dukana da tai

wanda hakan zai iya zama fada a tsakaninsu, idan kuma na fada masa abunda ke tsakanina da Aliyu abu ne da zai iya sakawa a koreni a gidan gaba daya ma, nai biyu babu.

Tabarmar na daga na kabe saboda takawan da Aliyu yai sannan na sake shimfiďata na kwa

nta a kai ina saka hijabina na rufe kafafuna, sai ga Anty Maryam ta shigo garejin fuska a hade hannunta rike da wayar carja.

“Ke uban wa kike wa rashin kunya? Ya Aliyu sa'anki ne?”

Saurin tashi nai zaure a take jikina ya dauki rawa.

“Ban masa ra

shin kunya ba”

Ban gama rufe bakina ba ta watsar min wayar chajar a jiki iya karfinta, ban san lokacin da nai tsalle na dire ba, rabon da a saka wani abu a dake ni a jiki har na manta, amman yau saboda rashin gata na zo aiki gidan wasu yar gidan tana du

kana akan abunda bata san gaskiyarsa ba. Haka ta bi ta bulale min jiki ko ina ta samu dukana take da wayar idan nai ihu ta ce na rufe mata baki. Ta fini girma da jiki sosai domin ita irin manyan yan matan nan ne masu kamar matan aure masu yaya shida, ba ka

mar Anty Rukaiya dake da karamin jiki ba.

“Kuma idan na ji muryarki a waje sai na ci ubanki”

Ta fada tana nuna ji da wayar da ke hannunta sannan ta fice ta barni a gurin ina ta murzar jiki ina hade kukana, duk inda ta bulalar ta same ni ya yi min ja

kamar na jimu abun ka da mai farin fata, farin ma irin nawa mai ja sosai na jajayen buzaye. A gurin na kwanta ina ta hawaye, domin babu danar nai kuka sauti ya fita ta dawo ta kara min kamar yadda ta fada. Ana gaf da sallah magariba zazzabi ya rufe na rik

a jin sanyi na sauko min ga bulolin nata min zogi, kaina kuma yana ta ciwo har bana son daga idona.

Ban iya fita karbar abinci a gurin Mama Fulani da Ammy ba, da yake kuma ba ni da gatan da wani zai da mu ban ci abinci ba babu wanda ya zo dubani ko a a

iko min da abincin. Haka na kwana a gurin cikin rashin gata da galihu har gari ya waye, ina ta jin wuyar tashi amman ba ni da gatan da wani zai fanshe ni a aiki, na san ba ma za su yarda da uzurin cewar bana jindadi ba. A dan karamin madubin hoda ta na dub

a yadda idona da gefen kumatu na ya kumbura bulalar ta kwanta min har saman fatar ido. Wani ruwan hawayen ne ya sake cika min ido na fashe da kuka marar sauti ina ta jin kewar Nana da rayuwata da baya, na sani ba mu cikin jindadi amman a haka muke rayuwarm

u babu wanda ya taba dukana, amman a nan ga duka ga wulakanci saboda kawai ina neman halalina.

Ganin kamar zan bata lokaci ina kukan yasa dole na tsagaita kukan da ke kara min ciwon kai da damuwa na daura dankwalina na fito ina jin nauyin jikina saboda

zazzabin da ke kara sauko min, na nufi part din Mama Fulani kamar yadda na saba, part din na fara gyarawa na ma komai tsaf sannan na nufi part din Ammy na gyara mata falonta, yanayi kawai ta lura da shi ta fahimci bana jindadi.

“Jiya Fulani ta aiko ta

ce karna baki abincin dare da safe, wani laifin kika mata hala?”

Kaina kawai na daga na kalleta, ina bude baki nai magana sai kuka ya kubce min na saki tsintsiyar hannuna na durkushe a gurin ina ta kuka. Sai ta zauna a cushion tana ta kallona cike da ta

usayawa.

“Mamana ki yi hakuri, duk wanda ya ce zai nemi halal dole sai yayi hakuri, musamman aiki a gidajen wasu, dole za ki iya haduwa da abubuwa da dama, ban san dalilin na aiki a nan ba, amman dai ki yi hakuri wata rana sai labari zai zama kamar ba

ayi ba kinji”

Na gyada mata kai ina share hawayena.

“Baki da lafiya ne naga kamar fuskanki ya kumbura”

“Kaina yana ciwo, kuma ina jin zazzabi”

“Me mikai wa Fulani hala?”

“Wallahi ban mata komai ba, kawai dai na fita ne bakin gate ina dawowa

sai sai ta mare ni, kuma shine Anty Maryam ta dukeni da bulala”

Na karasa ina kara fashewa da kuka. Sai ta girgiza kai cike da tausayawa.

“Fulani bata da imani Wallahi, Allah ya kyauta”

Tashi tai ta nufi upstairs bata dade ba ta dawo rike da kwa

yoyin magani ta bani.

“Shiga kitchen ki debo ruwa ki sha”

“Na gode Allah ya saka da alheri”

Na fada ina saka hannu biyu na karba sannan na nufi kitchen kofi na dauka na debi ruwan na balle maganin sai na kasa sha, abun ka da wanda be saba ba, da

man can magani da allura bana son su sai dole, daker na iya runtse ido na shanye maganin na fito ina ta bata baki, ko da na fito Anty Zee da Humaira, Inteesar da Batulu duk sun fito dakinsu, dan haka na shiga na gyara ko wane dakin da dakin Ammy sannan na

fito.

“Idan kin gama ki zo ki karbi abinci, amman karki bari ta sani”

“To”

Na amsa sannan na fito daga part din na koma part din Mama Fulani dan gyara bedrooms idan yayanta sun fito. Ko da na shiga duka yayanta suna dinning har Ya Muhseen, da alam

a da gaske fushi yake da ni domin ko inda nake be kalla ba, ba kamar yadda ya saba kallona ya sakar min murmushi ba, har na dauko tsintsiyar da mopper na shiga dakunansu na gyara komai na fito cikin rashin dadin rai na ke na fushin da na lura da Ya Muhseen

na yi da ni, domin har ga Allah na damu kuma na ji babu dadi. Sai da gama gyara bedrooms din sannan na fito na sauko kasa, a lokacin Ya Muhseen baya dinning din ba kamar yadda na saba ganinsa idan na gama gyara an barshi a gurin zaune ba, wani lokacin ma

shi yake miko min abincin na safe. Inda na dauki tsintsiyar na nufa na aje sannan na juyo da zimmar komawa part din Ammy na karbi abincina domin na san wannan Mama Fulanin ba bani za tai ba, sai na ji ta kirani.

“Ke.... ”

Na dawo da sauri na durkusa

a gabanta cikin ladabi na ce.

“Ga ni”

“Shiga dakin Rukaiya da Maryam da Baby ki kwaso kayan durowarsu ki je garden ki wanke, ko daya karki bari kuma ki wanke su tas”

Da to na amsa mata na taso ina tausayin kaina na nufi dakunnan na kwaso tulin w

ankin ko wanne zai kai kala goma sha biyar wani ma ashiri, sai da na kaisu garden din sannan na dawo na sake dukusawa a gabanta.

“Ina sabulu”

“Shiga store ki dauko”

“Abincina fa?”

“Sai kin gama wankin za ki ci ai tunda kika zabi rashin kunya s

ai na horaki a gidan nan”

Ban sake ce mata komai ba na tashi na ahifa store din na dauko sabulun na nufi garden din, dana isa kurawa kayan ido nai na rasa da wanne zan fara wankewa? Shikenan saboda ba ni da gata duk abunda aka ga dama sai ayi min. Ba ni

da wani iko da karfin da zan iya cewa ba zan wanke ba, dan haka na saka tufafin a gaba ina ta wankewa ga rashin karfin jiki na zazzabin da na ke ji, ga yunwar jiya da dare gashi da safen nan ma ban saka komai a cikina ba. Haka na saka kayan a gaba ina ta

wanki tun ina yi da dan kuzarina har na koma bana iya komai na gaji sosai amman a haka na tisa kayana a gaba na wanke su tas babu abunda na bari, sannan na bi na shanya su, sai na zuba ruwa robar na laba bayan itacen mangoro guda biyu da suka hade waje day

a na boya a gurin nai wanka wai ko zan dan samu karfin jiki, sai dai abunda ban sani ba Ya Muhseen na daga dakin Mama Fulani yana hange ni, sai dai a lokacin da nake wanki ban ganshi ba, wata kila be zo gurin ba sai da na fara wankan, kuma ban lura da shi

ba sai da na gama wanka. Kunya ce ta kamani duk sai na ji babu dadi ko ba komai yaga tsiraicina wanda shi kansa na san yasan haramun ne, ban tsaya saka rigata a gurin ba, na dauketa tare da dankwalina na fito daga garden din na nufi garejen, a cikin tufafi

n Inteesar da Ammy ta bani na dauki wani lace na saka na daura dankwalin sannan na nufo part din Mama Fulani dan bata ragowar rabulunta.

ALIYU POV.

A lokacin daya bar kamfani sai ya dauki hanyar gida, yana ta tunanin maganganun Nasir, tabbas shi k

anshi ya san an cuci yarinyar kuma dole zara ji zafi saboda mahaifiyarta akai wa, but he like yadda take fada masa magana kai tsaye ba tare da tsoro ba, idan ya tuna ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login