Showing 81001 words to 84000 words out of 237425 words

Chapter 28 - ZAKI COMPLETE

irin wannan dukan ba, tasan halinta sarai tana da zafin hannu a wajen yayan wasu ban da yayanta, ita kam nata yayan baka isa ko yatsa ka nuna musu ba balle ka ce za ka dake su.

“Mi tai miki kika mata wannan irin marin? Ta

suma fa”

Jin hakan yasa Kamal ya dago daga kokarin rika Ataa da yake ya kalli Mama Fulani cikin bacin rai.

“Ba lallai sai ta yi mata wani abu ba, ai zalinci ne zata iya dukanta tun da ba Maryam ba ce ko Rukaiya, waya isa ya taba Baby ma da take kar

ama a cikin yayanki amman kin iya duka wata saboda ba ke kika haife ta ba”

Da mugun mamaki Mama Fulani da Rukaiya kai har Momy suke kallon Kamal jin abunda ya fito daga bakinsa, Mama Fulani ta nuna kanta tana kallon Kamal

“Kamal ni kake fadawa wanna

n maganar? Ni Fulani?”

“An fada miki ko nima dukana za ki yi?”

“Kai Kamal karka kuskura ka ce...”

Maryam bata karasa ba ya daga mata hannu yana daka matsa tsawa.

“Yi min shiru shashashar yarinya, ba ku iya komai ba sai bakin girman kai da zali

nci haka kawai ku saka karamar yarinya a gaba kuna azzabtar da ita saboda kawai tana karkashinku, babu wanda zai baro iyayensa ya zo karkashin wani ya tare yana musu aiki sai da babban dalili ba ku san abunda ya rabota da iyayenta ba amman kun saka ta gaba

kuna mata wulakanci kala kala son ranku, ku ku yi mata mahaifiyarku tai mata arziki hauka ne? Shikenan ku mutum idan ba shi da kudi ba shi da daraja a gurinku? Wannan wace irin rayuwa ce?”

Momy ta ce.

“Kamal be dace ka shigo har cikin gidansu aboki

n ka ba ka fadawa mahafiyarsa irin wadannan kalaman sam be da ce ba”

Kamal ya kalleta

“Ko ke kikai ba daidai ba dole na fada miki gaskiya balle kuma ita da ba haihuwarsa tai ba, sai mummunar akida da ta saka masa na rashin ganin kan kowa da gashi”

“Yar aikin mu ce dan haka duk yadda muka ga dama haka za mu yi da ita, babu uban da ya isa ya hana idan kuma a akwai sai yai na gani, ai ban san ka isa da ita ba har sai ka dauke ta daga gidan nan ko kuma ka rama mata marin da aka mata, sai na san na isa

da ita ko kuma na san zumuncin uwa kuka hada ko na uba”

Cewar Rukaiya tana wani irin marmadi kamar zata matsa kusa da shi ta dake shi.

“Zumunci musulunci muka hada wanda ya fi na jini, kuma zan nuna miki na isa da ita, kuma zan nuna miki ita ma tan

a da gata kamar ke”

“Ba dai kamar ni ba Wallahi, karyar makaskanciya irinta Wallahi abun kunya kana son yar aikin gidan abokinka kuma budurwarka tirr Wallahi”

“Ke ce makaskanciya ke da baki san darajar dan adam ba, kuma ni ban taba cewa ina son Marya

m ba, duk zuwan da nake gidan nan ina kiranta mu gaisa ban taba cewa ina son ta ba, gata a nan tsaye idan na taba fada mata cewar ina son ta sai ta fada, kuma na gode Allah da ban taba furtawa ba, domin yanzu na gane irin tarbiyarku ba kuma za a je a tarbi

yantar min da yaya haka ba, a gurinki yake abun kunya son yar aiki, a gurina abun alfahari ne ko ba komai zan zama mutum na farko da zan fara jiyar da ita dadin rayuwa, kuma zan auri mace mai tarbiya ba irinku ba”

Kamal na aje numfashi Muhseen dake sauk

o daga upstairs ya dauka yana yatsina masa fuska.

“Kai ne marar tarbiya marar hankali wawa wanda be san darajar na gaba da shi ba, ban da rainin wayo da rashin kunya ka isa ka shigo har cikin gidan nan ka ce zaka fadawa Mama maganar banza, waye kai a d

uk fadin Abuja? Kai kana da tarbiyar ne zaka nemi fada mata magana son ranka? Ko kuma saboda baka san darajar iyayenka ba shiyasa baka ganin kimar uwar kowa a duniya, kai ne baka da tarbiya kuma ba san inda ta fito ba, domin mu ba za mu iya ciwa uwar wani

mutunci ba, amman kai zaka iya dan tsabar rainin wayo, ina ruwanka da yar aikin gidanmu? Ubanta ne kai? Ko yayanta? Sakare kawai mahaukaci daman sojoji ba ku iya komai ba sai hauka da fitsara”

Kamal ya tabe baki.

“Ka fadi duk abunda yai maka dadi a

baki, ban yi mamaki ba ai kai ma dan wajen Fulani ne ko? No wonder”

Yana fadar hakan ya duka ya dauki Ataa da take sume tare da ledar da zo da ita ya juya zai fita sai Muhseen ya nufo shi da sauri.

“Karka kuskura ka ce zaka fita da ita, ko yankata M

ama tai ba zaka fita da ita ba”

“Mutuwa ce kawai zata dauke ni a yanzu na fasa kai Ataa asibiti amman ba kai ba balle wani naka”

Ya fice da ita, Muhseen zai bi bayansa Momy tai saurin rike masa riga.

“Karka je Muhseen kyale shi duk inda zai kaita

ai dawowa za tai saboda nan aka kawo ta, kar kuje kuna abu kamar yara ka ka taushe fushinka dan Allah”

Muhseen baya iya musawa Momy dan haka ya hakura ya zauna a kujerar jikinsa nata rawa kamar yadda zuciyarsa take yi. Mama Fulani kuma tana tsaye a gur

in ta kasa cewa komai gaba daya mamaki ne ya kasheta domin a rayuwarta bata taba samun mutumen da ya iya tsawa gabanta ya ci mata mutunci kamar Kamal ba, cin mutunci ma a gaban yayanta, ita zai fadawa Maryam bata da tarbiya and be taba son ta ba.

“Ni z

a a ciwa mutumcin a cikin gidana? Ni Kamal zai fadawa magana son ransa? Mi yake takama da shi dukiya ko aiki? To ya jira abunda zai same shi, ita kuma bar ta dawo”

Mama Fulani na rufe baki Zee ta shigo dakin tare da Inteesar dauke da manyan kuloli, suna

kallon yanayin mutanen falon sun san akwai abunda ya faru sai dai ba zasu iya gane ko minene ba. A gaban Momy suka dire kulolin sai Mama Fulani ta daka musu tsawa.

“Ke Zainab ku dauke abincin ku maida wai ba na ce Ammy ta daina min shisshige akan baki

na ba? An fada mata ban musu abinci ba ne ko?”

Zee ta dago ta kalleta tana kokarin danna fushinta.

“Na ga ai kamar ba bakinki ba ne bakin Abbah ne”

Muhseen ya zaburo mata.

“To rashin kunya za ki mata ko? Ban ballaki Wallahi”

“Ba rashin kun

ya ba ne Ya Muhseen magana ce kawai”

Ta bashi amsa tana kallonsa.

“Dauki abincin ki fice da shi aka ce”

Muhseen ya fada sai Momy ta dakatar da shi.

“Aa ku aka kawo wa abinci? Ai ni aka kawowa ina ruwanki, Ke tashi ki tafi Zainab ki ce na gode”

A tare suka mike tsaye Inteesar da Zainab suka fice...            Momy ta kalli Mama Fulani cikin yanayin damuwa ta ce.

“Wallahi ni dai bana son halin nan na ki Fulani, miye a ciki dan ta dauko abinci ta kawo min Fisabilillahi?”

“Shishhigi ne da

ita kuma na fada mata bana son haka, ni da gidana wani zai min ba daidai ba?”

“Amman ke ma ai ba gurinki na zo ba, ganin matar danki kawai na zo kuma gobe zamu koma, ni rigimar nan taku ban san ranar da zata kare ba, Siyama da Husna ku tashi ku yi sall

ah muje mu duba ta, Rukaiya da Maryam da Baby ma ku shirya muje”

Sai a lokacin Husna da Siyama suka motsa domin tun da aka fara fadan suka make guri daya kamar basa nan, ba halinsu bane kuma ba halin Momy ba ne masifa ta kan yi amman sai idan rai ya bac

e sosai. Gaba dayansu suka tashi suka nufi upstairs Rukaiya na fadin abunda Kamal yai be kyauta ba, Husna na taba mata duk kuwa da bata san shi sosai ba, sai dai ta taba ganinsa sau biyu tare da Aliyu.

Muhseen ma tashi yai ya fice daga falon cikin bacin

ran abunda Kamal yai wanda be sake shi ba har yanzu. Momy ta kalli Mama Fulani.

“Fulani Wallahi ku canja wannan zama na ku, tun yaushe ake abu daya? Kishi fa ba hauka ba ne, Fisabilillahi haka za ku taso kuna abu a gaban yayanku kuma manyan yaya ba ko

kanana ba? Wannan ai bara kan yayanku kuke yi Wallahi”

“Alhaji be auro Ramatu ba sai da amincewata kuma sai da ta yarda zata min biyayya, dan haka bata isa ta yi jayya da ni ba idan kuma har ta ce za tai nasan tsaf Alhaji zai sake ta komai yayanta”

M

omy dai ban da kallon Mama Fulani babu abunda take, ta sani Alhaji Hamza yana son Ammy sosai amman yadda Fulani take mata yana kyaleta abun har mamaki yake ba, duk kuwa da irin masifarsa domin shi mafadacin mutum ne sosai.

Guraren la'asar Momy ta shiry

a ita da su Maryam, Rukaiya, Baby, Husna da kuma Siyaka suka fito harabar gidan sai Momy ta aika aka kira Inteesar da Batulu, Zee da Humaira suka shiga mota uku suka dauki hanyar asibitin.

ALIYU POV.

A lokacin da ya bar asibitin gidansa ya koma ya,

yana shiga ya samu guri ya kwanta ba dan yana jin bachi ba sai dan ya samu sauki abunda ke zuciyarsa, matsalar iyeyen Rahma da kuma ciwonta a dayan bangaren kuma ga Ataa ta ta tsaya masa arai a yanzu yake tunanin ta ina zai fara taimakonta, what is best no

w is ya taimaki mahaifiyarta ta samu lafiya, sai dai be san ta inda zai samu mahaifiyar ba domin be san inda take ba, and Ataa bata bashi wata dama da zai iya sanin Familynta ba, sai dai yai ma kansa alkawarin zai taimake ta tai shiga rayuwarta ya nuna mat

a halinsa mai kyau da be taba nuna kowa ba, wata kila hakan zai sa ta aminta dashi har ta bashi damar sanin inda mahaifiyarta take, and ya ma kansa alkawarin ba zai sake bari a takura mata a cikin gidan nan ba, shine mataki na farko da zai dauka. Haka dai

yai ta tunaninsa ta bangaren Rahma kuma idan ya fara sai ya rasa ta ina zai tuke, zancen neman wata kodar a yanzu be ma taso ba, ba dan kudi ba sai dan gudun kar a samu irin wacan matsalar idan kuma ba a samo mata wata ba, hakan na nufi nan da wani lokaci

zata mutu kenan? Ko kuwa akwai wani magani da za a bata wanda zai saka kodar ta samu lafiya, ya kamata ya san wannan, idan ma zaa samu kodar a yanzu to dole ne sai ya ga mai ita kuma ya yi magana da mai ita ya aminta, da kuma amintaccen likita ba kamar Doc

Asim ba. Idan kuma ba za a samu ba ya zame masa dole ya cire tashi daya ya bata domin yana son ganin matarsa a raye, and zai iya sadaukar mata da komai na sa ciki kuwa har da ransa idan da dama.

Yana kwance Siyama ta kira ya ga kiran amman ya ki ya daga

domin ba shi da time din wani magana ko wani abun dabam a yanzu, sam ya manta da zancen zuwan Momy ma tsabar tunanin daya saka a gaba. Bathroom ya shiga yai wanka ya fito ya shirya cikin wasu kayan ya fito yana ta kamshin turare ya sauko kasa ya nufi wata

motar dabam ba wacce ya shigo da ita ba ya shiga ya dauki hanyar asibitin.

  Ko da ya shiga dakin da Rahma take ya same ta zaune saman gadon mahaifiyarta kuma akan kujera suna ta kuka, ba a fada masa ba, ya san cewa mahaifiyar Rahma ta fada mata gaskiya

r ciwonta. Ganinsa yasa mahaifiyar ta tashi tana share hawayenta ta fice daga dakin shi kuma ya karaso ya zauna a kujerar da ta tashi tana ta kallon yadda Rahma take kuka. Hannunsa ya kai ya kama hannunta yana fadin

“An fada miki gaskiyar ciwonki kenan?



Sai ta kalleshi cikin hawaye ta ce.

“Ina son rayuwa Aliyu, amman rayuwa bata so na, tun ina karama na ke ta fama da matsalar kodar nan, ima gidan aurena aka cire min daya saboda ta lalace, dayar ma aka ce sai an samo wata a dasa min, duka yaushe a

ka min kashen koda da har za a ce wannan ta lalace?”

Tashi yai ya koma saman gadon kusa da ita ya zauna ya ja zuwa jikinsa ya rumgume cike da tausayinta....Gyara kanta tai a kirjinsa tana hawaye.

“Babu abunda Allah ya rage ni da shi sai lafiya da ha

ihuwa, ina da Uwa Uba yan'uwa miji duka a raye kuma duka suna so na, amman ba ni da lafiya kuma ban haihuwa, yanzu idan na mutu na zama mai yankaken baya kenan?”

“Za ki samu lafiya Rahma sai mu cigaba da neman haihuwar ki daina zancen nemam haihuwar nan

a yanzu”

“Wata kila zan iya samun ciki na haihuwa ban mutu, amman zancen samun lafiya na warke kamar kowa na san ba zan taba samu ba, a da na yi zaton na warke idan aka dasa min wannan kodar amman sai gashi yanzu kuma ance ta kone”

“Dan ta kone ba s

hi yake nufin ba zaki rayu ba, kika sani ko ki samu sauki mu cigaba da rayuwarmu”

“Samun sauki ba abu ne mai sauki ba Aliyu, samun saukina yana nufin samun wata kodar, kai ma kuma na san ka fara gajiya da ni, Mommy ta fada ka ce ba za a sake samo wata k

odar ba...”

Dago kanta yai ya rika fuskarta.

“Ban ce ba ba a sake samun wata ba, amman dai ba ta bangaren Asim ba, saboda gudun abunda ya faru ya sake faruwa”

“Amman da ada ne kome zai faru ai zaka aminta ya faru ni na rayu, amman a yanzu ka canj

a wata kila ka fara gajiya da ni ne”

“Taya zan gaji da ke Rahma miyasa bakinki zai rika furta irin wadannan kalaman? Ai nasan da ciwon ki kuma na aureki a haka neman kodar nan da akai har aka dasa miki ita ba wayayi ba ni ba? Idan na gaji da ke ai ba za

n dauki duk wannan dawainiyar ba, amman maganar gaskiya ba zan sake yarda a cutar da wata saboda ke ba, zam iya komai dan ki rayu amman ba zan kashe wani ko na gulgunta rayuwar wani saboda ki rayu ba, ba kuma zan yarda a cire ko da kowa dan zalinci a dasa

miki ke ki rayu ba, ko da kuwa hakan na nufin idan ba a saka miki ba ba zaki rayu ba, ba zan zalinci wani na raya ki ba Rahma duk kuwa da irin son da nake miki I'm telling you this form the bottom of my heart, sai dai zan yi dawainiya da ke har ki samu laf

iya”

“Ko kuma na mutu ba, saboda kai ka san zaka iya auren wata mata idan bana raye amman ni na tafi kenan. What if maybe kana daukar dawainiyata ne saboda kai baka haihuwa ni kuma ba ni da lafiya, sai mu taru a haka mu mutu? Ban san yadda zaka dauki ab

un nan ba Aliyu, amman lokacin da ba Mommy ta fada min cewar koda ta ta kone, mutuwa ce farkon abunda ya fara zuwa min a rai, da kuma haihuwa idan na mutum ban bar baya ba, na tafi kenan, amman idan na haihuwa zan iya barin abunda za a rika tunawa da ni id

an ana kalleshi”

Murmushi Aliyu yai irin murmushin nan da yafi kuka ciwo, yau wai Rahma ce take fada masa wadannan kalaman yasan tana son haihuwa kamar yadda shi ma yake sonta, tabbas mai irin matsalar ta zai son ganin zuri'arsa ko ba dan mutuwa, shi ka

nsa yana son haihuwa amman gudun shiga damuwarta yasa shi kawarda tashi. Iyakar abunda zai iya yi a yanzu nuna mata kalamanta basu bata masa rai ba, domin idan har ya bari bacin ransa yai tasiri akansa zai iya fada mata magana marar dadi ko kuma yai fushi

da ita wanda yake ganin hakan be dece ba a yayinda da take cikin rashin lafiya. Ba karamin kokari yai ba na kai bakinsa yai kissing goshinta kamar yadda ya saba yana sauke ajiyar zuciya a hankali.

“Ki kwantar da hankalinki idan kin samu lafiya za mu ne

mi haihuwa”

“Wata kila matsalar da daga ni ne, da yanzu Mama Fulani da Momy sun saka ka kara aure saboda ka haihu, domin ko wannensu yai min gorin haihuwa, amman da yake ka boye musu gaskiya kace dukanmu ba mu da matsala sai suka daga min kafa suna gani

n kamar wata rana zan iya haihuwa, ni ma haka na ke ta saka rai ni da iyayena shiyasa na dage gurin neman magani ashe matsalar ba daga ni ba ne”

Sakinta Aliyu yai ya mike tsaye ya saka hannayensa aljihu ya tsaya gaban windows dakin yana kallon waje zuci

yarsa na masa mugun kuna. Rahma kuma ta bishi da kallo tana hawaye, har ga Allah tana son Aliyu kuma tana kaunarsa amman matukar ta tabba matsalar daga shi ne dole zata hakura da shi ta auri wani saboda ta samu haihuwa domin ba zata yarda ta bar duniya ba

tare da ta bar baya ba, and tana da tabbacin wata kila da ita ce da matsalar da ba zai zauna da ita ita kadai ba, da yanzu ya yi aure ko ma ya rabu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login