Showing 1 words to 3000 words out of 128353 words
Documented by H.M.G
.IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! Takun Haske Batch A*
*Free Page*
*Na K
udine ki Bada 500 ki cafki garabasar novel bakwai da program Uku*
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin kai....
Daga gareshi muka zo gareshi zamu koma, Allah ya bani ikon rubuta abinda zai amfani jama'a ya kuma tsareni da rubuta abinda zai gurbata al'umar
ma'aiki Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wa Salam....(Ameen)
*mg's skincare*
Shin Ina matan suke
🗣
️
🗣
️
🗣
️
maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi
😃🤩
Hakika tabbas
duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaranjiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's orga
nic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum
👌
hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasaur
an mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar
❣
️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?g
Shin
fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki
😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clea
r Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy
🤗
ga amare duk wnd yy using set
dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali
😘
just start placing ur orders dearies DNT be left behind
Av
ailable product
👇
Herbal whitening black soap:3k
Beauty kit:11k
Blacksoap/molato whitening soap: 3500
Bridal kit:20k
Muna maraba da masu siyan daya ko sari
Chat
08062991549
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Do
you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go
🤩
Then @mgs skincare gat you covered
💯
Now is time to glow
😍
Pamper ur skin
🦵
Shine like bride
👰🏻
♀
Glow
🧖
♀
️
💯
tested nd trusted
🤝
Guarantee
Sannan munada frames masu ky
au shima siyan daya ko sari 07046881166
08062991549
Sannan gamai bukatan abinci, cakes,meatpie,samosa nd spring rolls, traditional juices nabiki shima yy hanzari yy mgn 08062991549
Mungode
🤝
Shafi na Farko.
🤸🏼
♂
️
KANO STATE (BUK NEW SITES
)
Sanye take da doguwar rigar abaya, ta yane kanta da mayafi dark purple, hannunta dauke da handbag irin babbarnan, wacce ke cike da litattafai, kafarta wani flat shoe ne kalar mayafinta. Doguwa ce sai dai ba irin cancan ba, fatarta ba mai haske bace
haka kuma bamai duhu bane, batada jiki dan a koda yaushe Mamanta fada take mata akan rashin maida hankali gun cin abinci, tana ganin kamar shi yasata rama.
Gefenta kawayenta ne wanda da alama tare suka fito daga lectures, suna tafe ana hira ana dan shewa
, suna kokarin shan kwana tai trus taja ta tsaya tare da kurawa wani bangare daga can nesa kallo da idanunta. Runtse idanunta tai a kuma take yanayin fuskarta ya canza, kallan gun sukai suka kalleta sai suka sheke da dariya a tare harda tafa hannu. Fuskart
a a daure tace "Dalla dariyar ku kuma ta menene?" Wacce ke kusa da ita tace "Ibtisam anya mutumin can ba ya wadudu kikamai ba? Mutum kamar mara aikinyi sai bibiyarki?" Dan karamin tsaki taja tace "Ainah bansan iskanci, dadinta dai yayana ne in ma da biyu k
ikai maganar."
Dayar ta sa dariya tace "Wannan ko cikinku daya ai cewa zamuyi bashida lafiya balle kiri-kiri duk munsan sanki yakeyi." A ranta tace ni wannan soyayyar tun kafin ma aje ko ina ta isheni. A fili kuwa kallansu tai kawai tai dan murmushin yak
e, dan batasan ma me zata kuma ce musu ba.
Fara tafiya sukai tare da daga mata hannu alamar bye-bye, itama dan daga musu tai tace "Sai gobe in Allah ya kaimu."
A hankali ta fara takawa zuwa inda yake sam fuskarta babu fara'a, hannunta yadan daga ya rik
e jakar dake kafadarta, hakan yasa dan saman hanunta ya fito.
Shikam tunda ta taho ya kafe ta da ido yana jin wani azabar santa na sake ratsashi, idanunsa ne yakai kan hannunta sake waje, a take ya daura fuska tamau, harta karaso gun bai dauke ido daga ka
nta ba.
Cikin dan sanyayen murmushi wanda kana gani zaka fahimci bai kai zuci ba tace "Yaya ina wuni?" Kallanta kawai yake ya kasa amsawa, itakam wannan kallan na bala'in kular da ita, can ta daure ta sake cewa "Yaya!"
Cikin daurewar fuska ya juya ya k
alli gefe da gefe ganin ba namijin dake kallanta yasa yadanyi ajiyar zuciya yace "Ba ba kiga hannunki a waje ba?"
Kallan hannun tai sannan ta saukeshi wani abu ya kara tokare mata magogwaro.
Fuskarsa haryanzu a daure yace "Na na na siyo miki hijabai kink
i sakawa yanzu ina amfani haka?"
Bata tankashi ba dan batasan ranta ya baci yanzun nan.
Murmushi ya mata ganin yanda ta kawar da kanta yace " Kun kun fito lafiya?" Kai tadan daga kafin su fara tafiya a tare, ba wanda yai maganar sai tafiya kawai da su
keyi, can ta daure tace "Yaya nikam me yasa kullum kake jirana? Baka tsoron randa Abba yaji ya maka fada? Yace baka maida hankali kan aikinka?"
Tafi kowa sanin halinsa magana baya yinta mai tsayi sai azabar zuciya kamar me. Cikin dan maganarsa mai dan in
-ina kadan yace " Ib Ibtisam hankalina ba-baya kwanciya in ba zuwa nai na rakaki gida da kaina ba."
Wannan abu itakam ya isheta, da batasanshi ba wlh da tuni sun hau sama sun fado, ace namiji tunkafin ya aureka yabi ya takurawa rayuwarka? Matsalar daya d
an uwanta ne tana tunanin abinda zaije ya dawo, dan a yanda yake ba abinda bazai iya aikatawa ba in ta wulakantashi.
Sun dan yi tafiya kadan, suka iso gate din makaranta, daga baya taji ana kwalla mata kira, kafin ta juya shiya fara juyawa, fuskarnan tas
a a daure kai kace makiyinsa ya hango. Juyawa tai tadan fara komawa kadan tana kallan saurayin dake gudu yana neman tarosu.
Dan hannu ta daga mai kadan alamar ya tafi a hankali, nan ya karaso yana hakki fuskarsa dauke da dariya yace "Book dinki." Yai mag
anar yana mika mata, ta amsa tana dan murmusawa tace "gudun duk na menene? Ka jira gobe ka bani mana?"
Dan bayan kansa ya dan sosa yace "Ban isa ba, kin ban aran note dinki ai dole na dawo dashi da wuri dan a sake bani aro nan gaba."
Zata sake magana y
a kalli saurayin da ya hade fuska a bayansu kamar mai shirin dambe harda dunkule hannu, yace "Hmmm! Wannan saurayin naki har tsoro yake ban, ji yanda yake kallona kamar wanda nake kokarin kwace masa ke." Bata kalleshi ba tace " Nagode! Sai gobe."
Ta juy
a ta fara tafiya, tana isowa inda yake ta kalleshi tace "Yaya mu wuce?" Ai kamar ta taboshi nan fa ya fara zabga mata masifa kamar zai daketa, "Ke baki da aiki sai yiwa maza dariya? Sannan uban wa ya hanashi yin note? Bama wannan ba meyasa bazai ari littaf
in a gun namiji dan uwansa ba? Kina irin wannan ta ina
zan yarda dake? Ta ina zan kwantar da hankalina? Ni wannan makarantar ta isheni sam ta hanani sukuni kullum tunanina me kikeyi? Da wani namijin kike magana, haba! Ni na gaji wallahi da kin aureni kafin
ki fara bazan ma soma barinki ba."
Baki kawai ta bude tana kallansa, yau kam ankaita makura, ko mahaifinta bai taba tsareta yana watso mata tambayoyi haka ba, wato da alama wannan in akai auren ma bazai barta ta gama karatunta ba.
Cikin matukar kunar
rai tace "Yaya ni na tilasta ka soni? Ko kuwa rokanka nai? Akan me soyayyarka zata nemi haukatani? Ka hanani sukuni, kawaye wannan bana zama dasu muyi magana, kullum kana tsare dani, biki wannan ko ziyarar kawayena ban isa nai ba sai dai ka tasani a gaba k
amar 'yarka, taya mahaifina bai tsawalawa rayuwata ba saurayin da ba mijina ba zai takuramin? Wannan ko na aureka zargi ma bazai bar auranmu yai kargo ba........."
"NI KIKE WA MAGANA HAKA?"
Yanda ya daka mata tsawa ne yasa ta kasa cigaba da magana. Kalla
nsa tai yau itama takai iya wuya tace "Dan Allah ka saukakemin wannan soyayyar na gaji haka nan, wannan ko auranka nake zan nemi ka sauwakemin balle....."
Abinda ta fada kenan ta fara tafiya, tana mita, "Haka kawai? Wannan wani irin masifa ne? So ya zama
hauka, gaba daya rayuwata an lalatata banda zabin kaina ko ra'ayina?"
Shikam yana tsaye a gun ya dunkule hannunsa, saurayin daya kawo mata book dazu ya kalla, wanda yake ta tafiyarsa, da gudu ya bi bayansa, shikam tafiya yake baimasan ana binshi ba.
Ib
tisam ganin shirin yayi yawa yasa tadan juya dan ta tabbatar ba lafiya ba, idanu ta zaro ganinshi daf da yaran dazu, kafin ta gama tunani ya kaiwa yaran wani wawan duka wanda yasashi faduwa a kasa.
A rikice ta fara sauri sauri gudu gudu tana kwalla mai k
ira ai shikam baisan tanayi ba dukan saurayin kawai yake, ganin yanda ake makarsa yasa yaran ya fara kokarin kwatar kansa.
Mutane sun fara taruwa a gun maza sunata kokarin rabasu. Karasowa tai takaici kawai yasata zubar da kwalla cikin murya ta kunar rai
tace "Ya Umar ka bari nace! Na rokeka da Allah." Tai maganar cikin dan daga murya, kallanta yai yana wani huci, ganin tana kuka yasashi sakar yaran ya nufota da sauri yace "Ibtisam menene kike kuka?" Yai magana duk a rikice kallansa tai ji take kamar tait
a zunduma ihu, juyawa tai kawai ta fara tafiya tana tafe tana share hawayenta.
Binta ya farayi da sauri yanaji saurayin nan na zabgamai Allah ya isa amma baibi ta kanshi ba, tana fita daga school din ta tari adaidaita, cikin sauri ta shiga shima ya shiga
duk ya rikice, tafiya suka fara yanasan yi mata magana bayaso mai adaidaita yaji, haka yai shiru yanata maimaita kalamanta na rabuwa data furta mai ba shakka ko za'a mutu a dawo ba wanda ya isa ya rabashi da Ibtisam, ai ko wani ne yai gigin auranta to lal
ai ya shirya sakinta dan wallahi sai yasa an saketa ya auri abarsa, ko ubanta daya haifeta bai isa ya hanashi auranta ba, tashi ce ita kadai bayaji zai iya rabuwa da ita ba kuma yajin duk duniya akwai wanda ya isa rabasu.
**************
Tsaye take a c
ikin kitchen, gefenta mata ne guda uku suketa zuzuba waina, sinasir, panke a cikin takeaway suna rufewa.
Kallansu tai tace "Ankusa gamawa kuwa?"
Daya daga cikin masu zuzuba abincin wacce da alama tadan girmi ragowar tace "Ummy ankusa insha Allah!"
Wa
cce ta kira da Ummy tai dan sansanyan murmushi tace "ina ganin kafin a gama zubawa a fara fita da wadannan ko?"
Matar tace "To shikenan, bari Zulaiha ta fara fita dasu."
Kai Ummy ta girgiza da sauri tace "A'a kuyi aikinku bari Ainah tazo ta fita dasu."
Tai maganar tare da juyawa, dan murmushi sukai tabbas suna jin dadin aiki da matarnan a koda yaushe girmamasu take tana basu darajarsu duk kuwa da kasancewarsu 'yan aiki.
Ummy kam daki ta nufa, ta tura kofar tare da sallama.
Ainah tana kwance akan makeke
n gadanta tana ta daddana waya, dawowarta daga makaranta kenan ta baje akan gado tana chatting.
"Ki ajiye aminiyar taki kizo kiyi aiki."
Juyowa tai tare da ajiye wayar tana dan dariya tace "Kai Ummy yaushe waya ta zama aminiyata?"
"Inba aminiyarki ba m
ecece? Ki zauna a falo ayi hira dake ma baso kike ba, yau kinfi kowa sanin ranar mecece amma kin shige daki kinata dane danen da kika saba."
Dan ido ta zaro kadan tare da mikewa ta yayo hijabi ta zura tace "Ummy wlh na manta sam, hankalina ya tafi....."
Dan kai ta girgiza tace "Taso ki fita da abincin sadakarnan Mamman yana jira a mota."
Da sauri ta nufo Ummy kafin tace "Ikon Allah sai kallo yanzu wai har Aunty Na'ima tayi shekara biyar da rasuwa?"
Kai kawai Ummy ta daga jiki a sanyaye, Ainah ce ta fi
ta tana gyara hijabin ta.
Fitowa daga dakin Ummy tai sannan ta nufi fallan Abba gaba daya jikinta a sanyaye.
Daga bakin kofar falan ta tsurawa wanda yake zaune akan sallaya ido, matashi ne wanda a kalla yakai shekara talatin da tara sanye yake da farar
jallabiya yana zaune akan sallaya yana jan carbi, fari ne dan kana ganin Ummy zakasan ita yayo saboda kalarsu da kamaninsu, ya dan tara kasumba a fuskarsa wanda ta kara nuna girman shekarunsa, gefensa Qur'ani ne da alama ya gama karantawa ne, shiru tai ta
na kallansa a hankali taji kwalla sun taru a idanunta.
Tana neman juyawa taji ance "Ummy?"
Kallansa tai tare da sakar mai murmushi sannan ta shiga cikin falan.
Zama tai akan kujera tace "Gashican ana zuba abincin a mota, Mamman ne zai kai ko tare zaku
wuce?"
Yace "Tare zamu wuce dan Hajiya batajin dadi zan sai mata magani na tafi mata dashi."
Dan yanayinta ne ya canza wato dan ta tura mata sako jiya akan tanasan magana da ita shine yau tace batada lafiya?
A fili ta daure tace "Aminu haka zamu ciga
ba da zama? Sai yaushe ne zaka sallami matarnan ta koma garinsu? Sai yaushe ne zaka sake aure? Ka nemawa 'ya'yanka guda biyu uwar dazata maye gurbin mahaifiyarsu?"
Yanayin sa ne yadan canza, bata damu ba dan raban da ko murmushi ta gani a fuskar Aminu tu
n randa matarsa Na'imah tabar duniya tayi tayi ya dawo yanda yake amma inaa abin yaci tura, ta hadashi da mata dayawa sai dai Allah baiyi ba dan babu wacce ta kwantamai. Babbar matsalarta kuma Hajiya wato uwar matarsa data rasu, wacce ke zaune a gidan tun
bayan auransa da Na'imah tayi
tayi ya maidata kauye garinsu amma yaki, ko kuma tace matar taki dan ta tabbatar itace take karyar ciwo dan karya tabar gidan.
Muryar Aminu ce ta katse mata tunaninta "Ummy dan Allah ki bar maganar Hajiya, matarnan amana ce
a gareni ni nake rike da ita tun auranmu da Na'imah taya yanzu zance tabar gidan? Matarnan fa ba lafiya gareta ba?"
Dan ajiyar zuciya tai cikin kulawa tace "Aminu baka fahimceni ba, ni nace ta dawo gurina ta zauna, ko ka nema mata karamin gida ta zauna,
dole sai a gidanka? Wace matar ce zata yarda ta aureka bayan tasan zama zatai da uwar matarka? Ko uwar miji ce mata ba so suke ba inaga matar da basuda hadi da ita? Ni na kasa gane wannan masifa, in kai ka kasa sallamarta ita bazatai hankali tabar gidan ba
? Ita kadaice zata iya rike yaranka ko me?"
Ganin yanda ran Ummy yadan fara baci yasa yace "Ummy dan Allah mubar maganarnan, matarnan zaman jikokinta takeyi ki barta dan Allah ta kula dasu."
Abinda take yaki dashi shekara biyar ta tabbatar bazai warware
yau kadai ba, sai dai tabbas sai ta sa matarnan tabar gidan, dan bata taba ganin inda akai wannan kwamacalar ba, in shi yana ganin ta zama dolensa ita ai tanada hankalin da zatasan abinda ya kamata in har kuma ba wani abin take sakawa a ranta ba.
Duk sa
a boys quarters take itadai san bata yarda da wannan zaman ba.
********
Suna sauka daga kan adaidaita tai saurin shigewa gida, biyota yai yana kiran sunanta batako amsa ba tai ciki da sauri.
Falo ta shiga da sallama, karar bude kofa yasa ta kalli
gun tare da sakin fuska, da dan sauri ta karaso ta rungume budurwar dake kan keken guragu. Tace "Sisi na."
Murmushi tai tare da cewa "Ki hau sama akwai tsarabar da Iman ta shirya miki."
Idanu ta zaro dan ta tabbatar kayanta ta taba, da gudu ta hau sama h
artana neman faduwa ta bankade kofar dakin da karfi batai ko sallama ba.
Baki ta bude tana kallan Iman dake ta daukan hotuna da kayanta, kayan ta kalla akan gado gaba daya sabbabin kayanta data dinka na salla an watsar dasu alamar ansa ancire.
Cikin ih
u tace "Wallahi yau sai naga mai kwatarki....."
Iman tana ganinta ta sake wayar ta fara kokarin guduwa, aifa nan Ibtisam ta rufa tana kokarin kamata, da gudu ta fito daga dakin tana kwallawa Ummansu kira, tana saukowa falo taga Umar ta boye a bayanshi tac
e "Yaya taimakeni wayyo shikenan yau za'ai layya dani." Tana magana tana hakki....
Ibtisam ce ta sauko a sukwane nan fa suka cigaba da guje guje a falo itakam budurwar dake kan keken guragu tana zaune sai dariya take.
Umar kam ji yake kamar ya kamo Ibtis
am ya rungumeta saboda tsananin so..... Ba shakka duk randa ya aureta sata zaiyi a gaba yai ta kallo dan shikam baisan irin so da kaunar da yake mata ba.
Ayusher Ce
🏌🏻
♀
️
[1/26, 9:32 PM] Fav
♡♡
:
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*