Showing 36001 words to 39000 words out of 200647 words

Chapter 13 - Farkon-Ganin-Idona-Book-Compeletex

08 Sep 2026

40

gama bayar da sadakar ya nufi gida almajiran sun bi shi ya maido dubansa kan Aba a tausashe ya ce" Yaya maganar mu? ina fata ka sanarwa yarinyar?"

Aba ya yi murmushi yana gyada kai ya ce" Na sanar musu har mamansu, Allah ya tabatar mana da alkhairi,

yaushe ne zai je gidan?"

Elhaji Hamza ya dan sauke numfashi, shi da ko zancen bai masa ba? yana tunanin ta inda zai hau shi, ama zai barshi ya huta yanzu, zuwa dare sa zauna, su fuskanci junna sosai su tsayar da maganar nan, dan baya so ya yi tafiyar ka

i tsaye basu gama magana ba

Da kula ya ce" In sha Allah idan ya gama hutawa zan sanar maka"

Aba ya gyada kansa ya ci gaba da ayyukan gabansa, a ransa kuwa abu dayan nan da ya tsaye masa yana son tambaya ama baya so Elhaji Hamza ya ga ko wani abin ne,

wato yarinyar nan mai tafe da masu tsaronta da kowa ya gama Sannin budurwar Elhaji Al Walid din ce, gatanan yanzu haka a cikin gidan ta zo ta wuce ciki, yaya ita tsakanin nasu? Wane ake ciki ne? shin duka biyun zai aura rana daya ko yayane? shi dai yana

son ji ama zai yi jira ya gani

Sai da kurma ta gama ya kama hannunta suka nufi gidan yana yi mata nunin yanzu malamin islamiyarta zai zo, dan haka su je ta dauki litatafanta ta yi bita

Mufeeda kuwa tana dakin Hajia inna lokaci zuwa lokaci sai ta du

ba agogon dakin sannan ta duba kofar shigowa, sai dai tun tana sa ran ganninsa har ta cire ranta

Zuciyarta na kunna kwarai da gaske, a zaunen nan da take ita kadai ta san halin da take ciki , ta kai dubanta kan Hajia inna da barci ya dan figeta ya fi a

irga, babu irin abinda bata sakawa zuciyarta ba har ta gama yarda cewar du inda yake warhaka lokacin barcinsa ya gama yi, yana bangarensa ne

Manya manyan kulayen da aka shake da girki na alfarma kawai take kallo, tun daga baban garin kasar Nijar Mahai

fiyarsu ta hado su da manyan kuku da zasu ringa yi musu dahuwa da kuma abincin da zata ringa kaiwa Al Walid, kafin ta yarda ta dauki mai aikin sai da ta tabbatar da sun iya duk wani launin abincin da yake so sannan aka dauke su,

A yau tun karfe biyar na

asubahi suke kicin din gidan da suka sauka, sun yi girki mai rai da lafiya ko su da suka dandana sai da suka yaba, gashi ta kawowa wanda aka yi domin sa ko kallo girkin bai ishe shi ba bale ya yaba din

Mikewa ta yi ta bar komai a nan ta fita ta karasa c

ikin motarta ta shiga ta zauna a lokacin ta ringa sauke wani irin numfashi a jere a jere na bacin rai

Ihu ta yi ta daki sitiyarin motar, lokaci daya kuma ta cusa hannayenta cikin kanta ta rintse ido tana fitar da numfashi a hankali a hankali tana fadin"

Ki nutsu Mufeeda, ki nutsu, ki kwontar da hankalinki Mufeeda, kin sani sarai ba da irin haka kika kawo matsayin da kike a gabansa a yanzu ba, kin sani sarai ba da wannan halin har kika tako matsayin da kika tako ba, kuma kin san kin take umarninsa, ke dai

zaki yi hakuri ki nutsu, in kika yi haka zaki ci ribar tafiyar Mufeeda....."

A hankali ta ringa fitar da huci daga bakinta dan ta karra samawa kanta nutsuwa

A nutse ta shafa fuskarta bayan ta janyo madubin motar.....

Gaba daya ta dame kwaliyar, gaba

daya ta hade komai

Dan kwalin dolen da ta dauro ta lalubo ta dauko sannan ta kunna motar ta yiwa yan rakiyarta alamu suka taso , dan tunda ta shige motar hankalinsu ke kanta

fita ta yi ta koma baya suka dauki hanyar gidan da ta sauka sai sake dantse

lebenta take yi , bukatarta

ɗ

aya ce jal, ta samu wajen da zata sauke fushin ta ko zata iya shaƙar numfashi mai dadi

Kamar kanwarta ta san a rina, tunda ta tafi take zaune ta ki komawa barcin gajiya tana jira ta ga ko ta kwana

Ai kuwa sai gata ta shigo

a fujajen ,a yannayin da bashi da dadi, uwa uba irin yadda yayarta ke kuka idan har abu ya shafi wannan bawan Allahn

gannin ta ki daina kukan ta yi mata kiran Mahaifiyarsu ta saka a handsfree sannan ta mike ta bata waje dan kuwa maganar mamansu kadai

zata ji a irin wannan lokacin

Itama mahaifiyar tasu hankalinta ya tashi da jin kukan y'ar Tata

Dama a cikin fada suke ita da mahaifin Mufeeda, ya fada musu ba'a yiwa namiji irin haka, bale Al Walid ba yaro bane, da girmansa da kuma girma irin na aljihu

, idan har Mufeeda na gannin nuna masa soyaya ne take yi gwara ta kama kanta, dan babu namijin dake son mace kamar macen titi sai gararamba da rawar kai kamar me, idan har sonta yake yi ba sai ta wahalar da kanta ba, zai dauki abinsa ne a mutunce da dukan

tsarabe tsaraben da zai fuskanta, sun dai san ba matsalar kudi ta hanna shi auren nan ba ko? to yayi.....wadinan magangannun su suke daga mata hankali, ita ba yarinya karama bace, kuma ta san gaskiya mijinta ke fada, sai dai ta kasa tsayawa waje daya bale

ta fuskanci y'arta su daidaita kansu tun kafin a zo bigirin da kunne ba zai ji rarashi ba

A tausashe ta ce" Ya isa haka kukan nan Mufeeda, dukan ki ya yi?"

Mufeeda ta tsagaita kukanta, duka? kai, a'a, ai zata iya cewa gaskiya Yaren duka ba yarensa ba

ne........, domin Allah ta san ba zata taba nuna inda ta ga ya daki wani Bama bale ita

Sai dai zata iya rantsewa gwara ya daketa da irin horon nan da yake yi mata idan ta bata masa, yana iya share ta yayi banza da ita fa...., ita kuwa wannan abin ya fi k

omai kasarata, ya fi komai lalata mata nutsuwa da farin ciki

Murya a hargitse ta sanarwa mahaifiyarta abinda ya faru

Ajiyar zuciya uwar ta sauke a tausashenta dan so take yi y'ar ta bar kukan hakanan , ta ce" Mufeeda, ki daina kukan nan, to ai kin ga

laifinki ne, kuma kulun fada maki nake yi tunda kika ce kin ji kin gani a haka zaku yi tafiyar dole dai ke zaki yi ta hakuri, ba fa shi zai yi ta rarashi ba, bale ba duka maza suke rarashi ba Mufeeda, ki kwontar da hankalinki ki daina kukan hakanan, idan

ya huce sai ki bashi hakuri shikenan kin ji?.."

Da wannan ta yi ta rarashinta har ta yi hakuri , sai dai gaba daya wunin ASABAR yau din an gama lalata mata farin cikinta.

A gidan baba

kasantuwar yauma ASABAR du yan makarantar

gaba da primary sunna zuwa makaranta hakan ce ta faru da ya'yan gidan, kuma shigar da baba ya umarci Karima ta yi ita ta yi, sannan uwa uba ta kashe wayarta bayan sun yi waya da mahaifiyarta ta daina kula wayar saboda Mudansir, domin ba zata so raunin da t

ake da shi a kansa ya hannata cikar Burinta ba, ita fa ko menene tana iya mayarwa gefe in dai a kan ya'yan banki ne kamar yadda mahaifiyarta ta nuna mata sun fi komai mahinmanci a zaman auren, in dai akoy su to fa ko menene za'a iya cinyewa a yi hakuri a z

auna, ta riga ta nuna mata duka kaf mazan haka suke, kafin su aureka zasu bautawa soyayarku kamar me, da zarar sun aureka shikenan komai ya wuce ka zama tamkar abokin hamayarsu, du irin kyautatawarka kuwa sai sun wulakantaka, da talakan da mai kudin, shi y

asa ta horeta da auren gata ya fi armashi fiye da na kudin

Da suka dawo daga makaranta basu huta ba Mama ta tisa su gaba suka yi kicin su duka yan matan bisa umarnin baba , dan tunda ya je shago ya yi kiran Maman suka yi magana cikin ruwan sanyi ya nuna

mata bukatarsa Karima ta karra gogewa a fannin girki da du wani abin da ya kamata na gida, ya riga ya san ta wannan fannin bashi da matsala ama yana so a karra, wannan dalilin yasa ta yi masa list harda ta mamaki ta nade kafa tana sakacen hakori har aka k

awo dukkan abinda ta bukata cike da bayan mota guda

Wannan lamari ya sake tabbatar mata lalle akoy abinda mijinta ke shiryawa mai girman gaske, kuma du inda mijin nan da ya yiwa Karima ya fito lalle zabin cikin zuciyarsa ne

Bata yi kasa da gwuiwa ba

ta hade kan yan matan gaba daya suka yi bangarensa

Ita kanta tsaye take lamarin ta, su kuwa du a tsorace suke dan tunda suke basu taba shiga kicin din bangaren mahaifinsu ba

Lahauli, kicin irin ta Film,.kicin mai kyan gaske dauke da kayan aiki shake

, ama komai a kwalinsa, to wai menene dalilin da yasa babansu ya yi wannan kicin din kuma babu mai shiga? , su dai tunda suka ga Mama kanta tsaye tana fitar da dukan abin bukata sai suka saki jiki sunna bin dukan motsinta

Kafin su fara girka abinda zas

u girka sai da Mama ta koya musu mahinmancin gyara kicin kafin a yi girki da kuma tsaftacewa bayan an gama, Duda sun san da wannan ama basu san kicin din nan da irin tasu da aka musu a gargajiyance ba

Cikin nutsuwa da fitar da kayan tsaftace kicin din,

sai da suka cire su yanar tautau da komai tunda a rufe take ba aiki ake yi a ciki ba, sannan suka fitar da kwanuka tana tsaye tana sake gyara musu dukan abinda bai yi mata ba na harkar wanke wanken, da goge gogen komai da komai, sai dai Karima gaba daya a

gajiye yake yin aikin, dan har cen kasan zuciyarta ita bata ga dalilin da zai. sa a sakata irin wannan aikin ba,, ita fa gidan hutu zata je, gidan da tana zaune za'a yi mata komai, ba wai gidan wahala ba, gaskiya ba zata taba zuwa gidan da zata ringa yin g

irki da wahalce wahalce irin na gidan babanta ba, Sam, auren hutun da mamanta ke yi mata nunin zata yi to fa lalle lalle sai ya zama na hutun ko kuwa ta dagawa kowa hankali walahi

Sallah kawai ke fitar da su daga kicin, kasantuwar sai da yama ta yi li

sss suka shiga kicin din hakan ya sa sallar magariba ta ritsa su a kicin din suka je suka yi suka dawo wannan karron a tsorace dan sun san du inda babansu yake ya kusa dawowa, idan ya zo ya same su a kicin dinsa sunna aiki yaya za'a kwashe? sun riga sun sa

n ko ita maman tasu idan bulala ta biyo ta kanta zane mata jiki zai yi tassss a nufin su yaje duka ta tare musu, bale su kwari

Ita kuwa Hajia, ba wannan yake gabanta ba, ta san idan ya same su a kicin dinsa yana iya kirta rashin mutuncin da zai hadata d

a hawan jinni, sai dai kuma tana son karra tabbatar da darajar mutumen nan a zuciyar Elhaji, domin ta san mijinta ciki da bai, babu abinda zai yi ya boye mata yarensa, sai dai in bata gani ba

Tana yi tana duba agogo, Gannin lokaci na karra tafiya tana t

unanin inda ya makale yauma? kwanaki ukun nan a waje yake yin sallar magariba, bayan ba dabi'arsa bace, du tsiya yakan shigo gida kafin magariba

Sun kusa gamawa saura hade haden jus da ta yi niyar sai sun hada uku ciffffff a yau

Basu ji tsayuwar mo

tarsa ba, basu ma san da ya zo gidan ba domin bangarensa yana nesa da bangaren motoci, uwa uba idan aka shige dakinsa ba lalle a ji hayaniyyar waje ba sai in mai karfi ce, tsayuwar mota ba za'a jita ba in dai ba katarpila ba

Kicin din ya bude yana kama

haba, Amarya na lekowa ta bayansa tana zarro ido da mamaki kamar zai kasheta a lokacin da Khadijah ta gama zuba kayan jus din da zata markada ta juyo zata yi magana idannuwanta suka sauka a kansa, A bayane da dan karfi ta ce" Innalilahi Ba.........."

Ai

kafin ta rufe bakinta sauran suka kusa fadawa cikin wutar

A zabure ya ce" Du yar kaniyar da ta fada ta kone jikinta idasata kawai zan yi in huta da bakin ciki, dan ubanku dodo kuka gani? Gimbiya y'ayanki

basu da tarbiya, dan ubansu dodo suka gani? Wala

hi Karima idan kika yarda kwarzane ya samu wannan shegiyar fatar ta uwarki sai na idasaki na huta, yau Ni na ga jaraba daga lekowa dan in ce muku sannu da aiki shikenan sai ku nemi fadawa wuta? mtsssssssss aikin banza aikin wofi kina kallo y'ayanki na wula

kantani ko Gimbiya? ya miki kyau " Daga nan ya juya ya nufi dakinsa sai fadan za'a masheshi shashasha yake yi a cikin gidansa

Mama ta yi boyayen murmushi a ranta ta ayana' lalle Elhaji ' A fili kuwa ta dubi ya'yan da suka yi zuru zuru a tausashe ta ce"

Meye haka kuke yi? aljanni kuka gani?"

KARIMA da jikinta ke rawa ta girgiza kai ta ce" A'a mama, dukanmu zai yi shi yasa"

Mama ta girgiza kai tana dubansu ta ce" Ku ringa kiyaye duk wani abu da zai sa ya taba lafiyar jikinku, idan har kunna kiyaye wa

ba zai doke ku ba, komin abinsa ai sai an masa laifi zai yi dukkan ko?"

Khadijah ta sada kai tana hadiye dariyar yannayin Lubna a ranta kuwa ta ayana' wai baban? ta dai raya masa ya yi dukkan tsaf zai daki mutun koda kuwa kallonsa yayi, ai shi ba sai a

n masa laifi ba yake hukunci, hukuncinsa na biyowa ta kan wanda tsautsayi ya fadawa ne"

Sunna jin fitarsa sallar isha'i a lokacin sun gama ha

ɗ

a komai sun zuba sun kai nasa wajen da yake ci, sun kai nasu, dama sunna yin aikin sunna wanke wanke ne sharewa

kawai suka karra yi suka goge komai sannan ta yi tsaye suka duba sun kashe komai da suka yi anfani da shi sannan suka tafi bangarensu

Baba na dawowa daga masallaci ya zo kusa da gidansa ya ga Abubakar tsaye da Mudansir sunna magana

Karasowa yayi

a lokacin da Mudansir ke fadin " Dan Allah ka min wannan kokarin"

Kai tsaye baba ya ce" Na me fa?, wani kokari?"

Cikin Abubakar sai da ya juya, da sauri ya dubi baba, kafin yayi magana Mudansir har ya yi gaba bayan ya yiwa baba gaisuwar gagawa Baima

tsaya ya amsa ba

Baba ya kure Abubakar da kallon idan baka fada min ba komai na iya faruwa

Jikin Abubakar ya kwashi rawa, muryarsa da gargada ya ce" Dama ba komai bane dan ajinmu ne, sakon karatu muke tataunaw......."

Kafin ya rufe bakinsa Baba ya

daga ky din shagonsa da yake yawo da shi du inda zai je ya maka masa a gefen kunne, ky din dauke da kys da yawa ya zuba masa shi da karfin gaske

Da farko kamar za'a zare ransa zai ce ya ji ko menene? shi dai wata azaba da bai taba Sannin akoyta a duniy

a bace ta ziyarce shi,, daga baya kuwa sai ya ji kamar zai summa kafin zafin ya shige shi sosai

Du girman saurayin nan sai da ya ji kamar fitsari zai sako masa, a guje ya nufi gida, babansa kuwa ya daga kafa ya bi shi, Duda shi nasa gudun ba mai girman

na Abubakar din bane, dan kafin ya isa tuni Abubakar ya nufi dakin Hajia yana ihu yana fadin" Innalilahi wayo Allahna Mama Mama ya kasheni"

Mama ta bude humurarta zata shafa, Khadija na zaune ta ja turaran wutar da ta gama turara tufafinta itama ta rufa

tana turarawar ta mike zurbat, Maman kuwa ta saki ƙatuwar kwalbar turaren ta tartsatse a kasa lokaci guda tana tare Abubakar da ya rukunkumeta sai ihu yake ga kuka, ga jini ya gama wanke masa duka kafff jikinsa

A rikice ta riko kan tana kallon wajen da

jinnin ke zuba daidai baba ya shigo yana fadin" Dan ubanka Ni zaka yiwa karya? in tambayeka uban waye shi kace min dan makarantar ku? wannan mai askin yan daudun? a makarantar taku harta aski ba a cen ake maku ba du bayan mako biyu? ko sun zama yan iska

ban sani ba? zaka yi bayani ko sai na wulakantaka?"

Da sauri Mama ta ture hannunsa da yake son sake shako Abubakar Rai bace ta ce" Walahi walahi idan ka yarda ka yi kisa in ba sai an rataye ka ba idona idonka kace ba jinnin larabawa ke yawo a jikina ba,

kullll, ka yarda ka kashe sai an kasheka Elhaji "

Baba ya zarro ido yana kallonta ya ce" Yanzu kina tsaye kina kallo zai kasheni Ni da raina? kin ga yaron ne? dan daudu sak wa bilahilazi, gimbiya da yayi daudu gwara na rage mugun iri a hademu a kashe,

bani shi in gwada Mai wando yake sakawa dan ubansa!"

"Walahi walahi ba daudu nake yi ba, shima ba dan daudu bane, Karima yake nema, shine yace in duba masa ita walahi daga wannan Ni babu abinda ya hadani da shi baba!" Abubakar ya fada da ihu yana sake r

ushewa da kuka

Lokaci daya Khadija ta dora hannu a kai tana fadin" Lah shikenan, Habu ka kashe y'ar uwarka"

Baba kuwa kamar bai ji da kyau ba sai da ya sake duban Abubakar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login