Showing 171001 words to 174000 words out of 200647 words

Chapter 58 - Farkon-Ganin-Idona-Book-Compeletex

08 Sep 2026

71

kakan kurma ba ke nan? Ai bana gajiya da shi, idan na zo zuwa nake yi in share kafa in sha dariya kala kala, saima idan ya kawo karar gimbiya nan zaka sha dariya , shi da baba kuwa kamar sa daku haka suke wuni ama d

a zarar daya bai ga daya ba zaka ga ya bi bayansa"

Yayi murmushi kawai

Aunty shareefat ta ce" bari in je in yi isha, take Care big son "

A hankali ya furta" Good night mam"

Bayan ta tafi ya dan jima yana kallon kulolin abincin dake jere

A h

ankali ya karasa yana kallo da tunanin shin yayi kiran masu aikin su hauda masa kayan abincin ne ko kuwa ya zuba?

Gannin yana ta tsaye sai kawai yayi kiran maman baby ya sanar mata a kai dakin madame sannan ya haye saman ya nufi dakinsa

Wanka ya yi,

dan rabonsa da shi tun na safen nan, cikin nutsuwa ya cenza tufafi da turare ya dauki sakon nan da wayarsa daya sannan ya rufe ko'ina ya nufi dakinta a nutse ya tura bai nemi izinin ba ya shige a hankali ya rufe ya ajiye ledojin a hankali ya karasa inda t

ake tsaye kanta duke tana ta faman daidaita gashin ta da ta gama busarwa ta shafa mai, caje shi ne zata yi ta daure

A hankali ya saka hannayensa ta wajen cikinta ya rungumeta tsammmmm cikin nutsuwa ya kai kansa wajen dokin wuyanta a hankali yana hannata

furgitan da ta yi ta hanyar furta" Ninehhhhhhhhhhh HAJIA karamahhhhhhhh"

Khadeeja ta lumshe idannuwanta tsigar jikinta na mikewa, a hankali ta sauke ajiyar zuciya turaransa na sake shigewa hancinta

Juyo da ita yayi a hankali yana duban idannuwanta

kamar yadda ta saka nata cikin nasa..........

A nutse ta hade lips dinsu sannan ya lumshe ido ya shiga bata kular da ta dace, har sai da tsayuwar ta nemi gagararta sannan ya aureneta ya nufi wajen kujerar nan ya zauna da ita a jikinsa a hankali ya jany

o ledar nan ya ciro kwalin wayar dake ciki , ya bude ya fitar da wayar wace tuni an saka layi da komai a ciki ya kunna wayar a hankali ya saka a tafin hannayen ta kasa kasa ya ce" ga wayar ki, kin ga numbobinki nan"

Ya fada yana nuna mata a karamar waya

r da ya dauko din daga dakinsa

Murmushi ne ya subuce mata, wayar baba da ita, duda ba sanin harkar waya ta yi ba ama tana gannin a wajen kawayenta kuma sunna cewa iPhone 16 ta fito ama ta yi mugun tsada, rike ta sai manya, sai ta ga a jikin kwalin waya

r haka aka rubuta

A hankali ta furta" Allah ya saka da alkhairi, Allah ya karra budi ya......."

Janyota da yayi jikinsa ya saka ta

ɗ

an katse maganar, a tausashe idannuwansa a lumshe ya furta" Amen, but ni ba godiya nake so ba, i'm sorry , ki daina f

ushin haka"

Khadeeja ta dago ta zubawa fuskarsa ido, a'a Masha Allah ashe ya kula da fushin nata har ya yi magana a kai? Hakan na nufin fushin nata yayi dan tasiri kennan?, bari ta gwada wani abin ko a dace

A hankali ta

ɗ

an turo bakinta gaba kasa kas

a ta furta" AA, ba zan iya daina wannan ba har sai mun yi kiran wayar Mama, ina so in gaisheta"

Murmushi yayi yana dagota ya janyo wayar Tata ya ce" abu mai sauki, saka mana numbar idan ma bidiyo call zamu yi sai mu yi"

Khadeeja ta

ɗ

an noke kafada

kasa kasa ta ce" Ba fa ta Aban larabawa ba, Mama dai Mama wace ta yi kira da safe, ina son jin yaya jikin nata"

A hankali yake kallon ta har ya ajiye hannunsa daga miko mata wayar, sai kuma ya dan dauke dubansa

Sun jima a haka har ta ga bafa zai ce

komai ba, sai kawai ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta furta" i'm sorry"

Sannan ta mike daga saman cinyar tasa ta juya da nufin tafiya

Kasa hakura yayi, yana yadda yake din nan kasa kasa ya ce" ama ai dazu nace maki kar mu kuma yin maganar ko?"

K

hadeeja ta dakata, a sanyaye ta juyo tana dubansa, a hankali ta furta" Kana nufin kar mu kuma yin maganar mahaifiyarka?, to wace magana zamu yi mai da

ɗ

in Tata?, ai inaga babu wata magana da ta kai Tata dadi ba......., idan har za'a yi kiran maman gidan Aba

nmu a ji sanyi a zuciya to kuwa za'a yi kiran Mama ta gidan nan a ji sanyin nan.........."

Ta ajiye a hankali maganar, sannan ta

ɗ

ora da fadin" in ba baban princesse ba, kwallon mangoro ai shi ke bada itaciyarta......., Anya kuwa zuciya zata dadada idan

aka wayi gari litle na raye sai dai babu wani abinda ke hadata da mahaifinta? "

"An gaya maki babu abinda ke hada mu ne?, HAJIA karama bana son fitina da jan magana, duk wani abu da kika sani na duniya yana hada mu da ita, ko rashin lafiyar ai an je an

Kaita asibiti , babu abinda na rage ta da shi a duniya, " Ya katse khadeeja yana dan fada da dan karfi

Da ace ba rainon gidan aba bace yannayinsa zai saka ta yi shiru ba zata kuma tayar da maganar ba, sai dai a yanzu sai kawai ta sada kai, kuka a duniy

a khadeeja ta yi na banzama bale mai dalili, tana dagawa hawaye ya gama wanke fuskarta a raunane ta furta " Ka yi hakuri.........." Sai kawai ta fashe da kuka ta ajiye wayar nan a hankali gudun fashewa ta juya da dan gudu gudu ta bude dakin bata rufe kan b

a, bale ta

ɗ

an yafa mayafi ta fice a dakin ta..........

😠😠😠😠

. Daf nake da zane yar nan, koma saka hijab

😕😕😕😕😄

......., happy juma'at

46

07/12/2024, 17:30 - samiraharounayacouba: Ajiyar zuciya kawai Mama ta sauke ta maya

r da hankali ta yi abinda yace din suka shigo tare da Abubakar ya kwashi kayan ya tafi kaiwa mota

A nutse take biye da shi har suka karaso wajen mota ya bude ya shiga

A tausashe bayan ta saka kanta kadan ta ce" Aban Sadik, dan Allah idan ka je ka GA

ISHE da baban, sannan dan Allah ka yi hakuri ka yi tunanin da kace zaka yi a kan lamarin yaron nan mai neman auren Karima"

Kai ya gyada bayan ya tabe baki ya ce" to gimbiya zan yi tunani a kan aurawa y'arki mai jan ido tunda kin dage kin kuma hanna yaya

nki zuwa dauko min fansa, wato an sakani a tsakiya sai dai in yi yakin Ni kadai....ba laifi ai"

Mama dai bata ce komai ba dan ta san ita ke so ya dubi maganar ta, domin ko a jiya da dare sai da ta zaunar da karimar ta yi mata tambayoyi a kan lamarin, ku

ma ta yarda cewa itama tana son saurayinta sai dai idan an hanna tarayarsu ne kawai, wanda hakan na iya haifar da wata ilar

Bayan sun tafi ta juya ta nufi baban falonsu a nutse

Tana shigowa ta tarar da Karima tsaye tana kallon amarya dake zaune itam

a tana kallon ta, sai dai yannayinsu kamar magana Amaryar ke yi dan a irin tsayuwar da karimar ta yi kamar wani abu Amaryar ta fada da ya sakata a wani yannayi na mamaki haka

Bata wani tsaya ba tana tafe ta ce" Karima babanku yace kunna iya biyawa ku ga

jikin maman naku sai ku wuce gidan na anmy, dan haka idan kin gama ki dauki manyan kula ki zuba mata abinci na dubiya"

Karima jiki a sanyaye ta ce" to mama" sai kuma ta dubi amarya wace ta tabe baki tana yi mata kallon sama da kasa ta ce" Ba kin gani b

a?, ana anfani da ke ana cutarwa mahaifiyarki da ke din da kanki, Karima kina gani fa, ke aka zabawa mijin nan Ama matar nan ta cira ta kullu ya juye kan y'arta, in har maganar gaskiya ake bi kafin y'arta ba lubna ce a tsakani ba? In abinda take miki nufin

gaskiya ne cewar dan kin kiya aka bashi daya daga cikin y'an uwanki a kan me aka tsallake aka rasa wace za'a bashi sai khadeeja?, sai ki je ki zubawa maman naki abincin ki kai mata, salon gobe a yi mata gorin yunwa ace abinci sai an kai mata daga gidan ts

ohon miji, ke baki Sani bane a ciki ake barbada masifar dake hadasu fada har ya ringa zane maki uwa, kin wani zo kin zabi uwar wani a kan taki, ai sai ki karra hima "

Tana gama fada ta mike ta nufi cikin dakin cin abincin su tana dana wayarta zuciyarta

cike da farin ciki da tunanin ko yayane zata saka kiyaya tsakanin gimbiya da yaran nan, idan ta ga irin yadda suke mata mama mama wani takaici ke kule mata zuciya, yan rainin hankali ita kuma sai dai su kirayeta da amarya, sai kace ba matar ubansu ba! Dan

kuwa su samarin sarai ta kula wani gani gani suke yi mata, Bama kamar idan sunna yar rigima da gimbiya irin kallon da suke yi mata har tsoro ke ratsa ranta kar aje wata rana su maketa kamar ta ta

ɓ

a mahaifiyarsu, ita da kanta gimbiyar in sunna waje ko me za

'a yi bata biyewa dan da bakinta ta ta

ɓ

a nuna musu cewar su guji idannuwan yara, yara fa sun girma, ba zata so a basu muguwar tarbiyya ba ko a basu wata kafa da zasu raina daya a cikinsu ba,

Karima ta dan jima a tsaye kirjinta na dokawa kafin ta juya j

iki a mace ta nufi corridor din dakunan su

Lubna ta gani a tsaye rike da abaya a hannunta

Irin kallon da lubna ke yi mata ya sa ta ji gabanta ya dan fadi

Sai dai ta ga lubnar ta yi dan murmushi ta ce" Ke fa nake nema, ashe kina falo? Dan in ce ma

ki ne mu saka wannan abayar ta wajen aba wace aka kawo mana a cikin kayan saudiyar da aka bugo masa, zamu fi yin kyau"

Karima ta yi murmushi ta nufi dakinta tana fadin" To"

Daga haka bata karra komai ba, ita kuwa lubna ta rakata da ido kafin ta juya t

a shiga dakinta ta rufe ta zauna bakin gado

Ta jima tana dan tunani kafin ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Allah ya sa wannan karon ki yiwa kanki adalci, Allah ya sa a cikin halayyar masu harin zuciyarki ki iya jajircewa ki dubi zahiri ki yiwa w

ace ke rungume da ke adalci Karima"

Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye rigar ta mike ta shiga shirin shiga wanka

Lokaci daya kuma ta sauke ajiyar zuciya hadi da murmushi mai tsada a lokacin da ta tuna firarta da mama a jiya da dare, tambayar da

ta yi mata kan idan tana da wanda take so? Da ta tabbatar mata cewa babu, sai ta tambayeta shin zata iya zaman aure da ƴaƴansu na bangaren mahaifiyarta? Wato dan mijin mamanta ne baba, lauya ne mai zaman kansa , sannan dan kasuwa , kuma bai taba yin aure

ba har yanzu dai yana jira ne tun lokacin da ya cewa babansa yana sonta akace yayi hakuri har ta girma sai yayi hakurin, kuma cikin ikon Allah aba ne da kansa da maman tace masa to lubna fa? Sai yace lubna ai da mijinta , shin ta manta wanda ya yiwa alkaw

ari? Shi yasa ai ya zabawa AL'WALED khadeeja dake bi mata saboda ita da mijinta ai, .....abinda ya tsayar da lamarin aurensu suma na Karima da ummi ne kawai........., Ummi yace zai bata dama ta hadu da wanda ya zaba mata idan sun daidaita shikenan, Karima

ce har yanzu ya ki ya ba saurayinta fuska, yaron kuwa kamar wanda ya fada jarabawa a kan karimar, hatta mahaifinsa jira yake yi yace an basu damar su nema masa aurenta dan kuwa sun gane da gaske yake ba da wasa ba.

A nutse ta shiryawarta, sannan ta bude

dakin da ake ta buga mata ummi na fadan WALAHI zasu yi tafiyarsu ne idan bata fito na, dan kuwa har sha daya ta yi basu fita ba

Sai da mama ta yi musu nasiha sosai sannan ta ce" Ta yiwu ku samu su Fatima a cen, dan sun tafi su tuni da kayan nata, Allah

ya dawo da ku lafiya"

Lubna ce karshen mikewa ta amsa da" amen mama, ai kuwa bari mu yi gaggawa saboda mu tayata ayyukan gyara kayan nan"

Daga nan suka karasa mota suka shige, Abubakar ya ja su

Mama ta sauke ajiyar zuciya ta yi murmushi, wato Kar

ima bata zubawa mahaifiyarta abincin ba, bata wani rike a ranta ba saima zuwa da ta yi ta duba asibitin da zata yi aiki yau ta hau shiri saboda tana son fara fita aiki a yau.

Kofar gidan su Karima suka tsaya, suka fita gaba dayansu suka shiga gidan ba

tare da sun sanar mata da zuwan su ba, domin Karima dai a yanzu ba waya a hannunta shi yasa ko uwar sai da ta bi ta wata hanya kafin sako ya samu gimbiya cewar bata da lafiya saboda ta sani ta hanyar nan kawai ce zata iya gannin y'ar Tata har su yi maga

nar da take so su yi, ba wani rashin lafiya kalau take, ta bi duk wata hanya ne dan ta samu gannin Karima abin ya gagara shine ta biyo ta nan ko a dace

A filin gida suka same su sunna shan innuwar dalbejiyar dake cikin gidan, kakar Karima na yamutsa taf

asa da kulli, mamanta kuwa tana shan koko a kwano da ludayin roba

Gaisheta suka yi su duka , sannan suka tambayi jikinta

Kakar Karima dake mamakin gannin ya'yan elhaji ya'u su duka ta kalli y'arta a dan tsorace da tunanin yauwa ga dalilin da ya kawo

ya'yan elhaji gidan nan gaba dayansu

Lubna a tausashe bayan sun zauna maman Karima na yi musu tayin kokon ta ce" alhamdulilah mama, ai sai da muka karya sannan muka fito ma"

Maman Karima ta tabe baki ta ce" Dama na san ai ba iya sha zaku yi ba lubn

a bismillar dai na muku saboda ido , ina zaku je haka?"

Lubna jikinta yayi sanyi dan ita ba haka take nufi ba, a hankali ta ce" Gidan anmy ne zamu je"

Maman Karima ta Dube ta a yatsine ta ce" kina nufin gidan khadeeja?"

Lubna ta dago ta Dube ta, t

a dubi Karima, sannan ta dubi ummi da Sadik

Maman Karima ta girgiza kai ta yi murmushi ta ce" uhum, koda yake ai dama HAKANE idan mai kudi aka aura har uwar yarinya sai ta je bale yayunta, Ama kuwa elhaji ya bani mamaki da har zai tura ku gidan da kanw

arku ke aure, koda yake ba komai shi din a gaban mai gidan kanwar taku shima ba kowa bane face mai neman arziki da neman sunna"

Abubakar ya dubeta da mamakin halaya irin na matar nan, sai kawai ya mike yana fadin" Ga dukkan alamu lafiyar ta samu, Allah

ya sa a wuni lafiya, idan kun tashi ina mota"

Sai kawai ya wucewarsa dan ba zai iya zaunawa matar nan na zagin iyayensa a banza a wofi ba, shi yasa sam baya son harkarta, ta cika fitina da neman balaki, yaya za'a yi wai ka zagi uba a gaban d'ansa? Yana

daf da ajiye fadan mama gefe ya fara tijara a kan darajar su WALAHI!

Yana fita lubna ta yi murmushi bayan sun raka shi da kallo ta ce" Allah ya karra lafiya maman gidan iya, zamu wuce"

Daga haka ta mike tana riko hannun ummi suka kama hanyar fita ba

su tsaya sun jira abinda zata ce Bama bale har ya bata musu rai

Karima a sanyaye ta ce" Mama, baban namu ne kike zagi haka? Kin san ai ba zasu iya jurewa ba ko mama? Haba mama"

Mamanta ta zabga mata harara ta ce" ke dan Allah rabani da gafalalun yan

uwan nan naki yan bakin ciki, kin san ai ba tsoronsu nake ji ba bale in kasa fadin gaskiya, Ni yanzu maganar da nake so mu yi da ke a kan wannan auren da aka kwace a hannun ki aka ba wancen y'ar gidan jajayen mahaukatan, kin yi tunanin abin yi ne ko shima

sai na maki?"

Da mamaki ta dubi mahaifiyar Tata da kyau sannan ta dubi kakarta, a hankali ta ce" Mama ban gane ba"

Kakarta ta tabe baki tana sauke ajiyar zuciya ta ce" ke kya fada, ai lamarin uwarki ba karami bane, sai fatan Allah ya rage wahala"

Rai bace ta yabuwa ta ce" kin ga dai iya ba da ke nake ba, ke Karima dubeni nan, kin san dai ba zama zaki yi kina ji kina gani khadeeja na aure a gidan nan tana auren elhaji AL'WALED ke kuwa a hadaki da wanda bai taka kara ya karya ba ko?, dan a wulakanci

n ubanki yana iya baki yaron shagonsa dan kawai ya wulakanta Ni ya nuna min iyakata"

Karima ta yi wani sakalau, kafin ta ce" To mama ko wa aba ya zabi yanzu ai sai mu masa biyayya, kin dai ga rashin yi masa biyayar abinda ya janyo, bayan wannan Mama ai

anmy haka Allah ya tsara itace matar elhaji AL'WALED din, Ni yanzu kin ga adu'a nake yi Allah ya sa a min zabin alkhairi mama, Ama ina ga kamar mudansir ne za'a bani saboda ko jiya sai da Mama ta min tambayoyi a kansa"

Rai bace maman Karima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login