Showing 132001 words to 135000 words out of 200647 words

Chapter 45 - Farkon-Ganin-Idona-Book-Compeletex

08 Sep 2026

8

ta ce" Kin ga, zuwa na yi in karra jaddada maki kin ga shigo ko yaji idan kika yarda kika daka sai mun kifar da d'an iska, ba zaki min bakin cikin ziyara ba, ah to, ina fatan kina tune da lesson din da ki

ka dauka a saman majalisa"

KHADEEJA ta sada kai kasa kasa ta ce" Iya dan Allah ki bari mana"

Iya ta saka y'ar shewa suka tafa ta ce" Allah mai alkhairi dama y'ar nan da kisarta aka haifota kuma ta rike koyarwar samun mafita, ki ga dan Allah yadda ta

yiwa ido Fati"

Mama FATEEMA kam ta ga abin ba na karewa bane ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Uhum, yaya jikin naki? ban kirayi mai kitso da kunshin ba nace sai na zo mun ga sauƙin jikin"

KHADEEJA ta shagwabe ta koma jikin Mama Fateema ta

ɗ

ora hannunta

a wuyanta ta ce" Mama karama taba wuyana, sai ki gasa biredi a jikina , ai sauki kam babu gaskiya yanzu haka asibiti za'a je dan Allah kar a min kitson nan"

Murmushi aunty shareefat ta saki bayan sun karaso tana nunawa kurma Khadeeja ta yi mata alamun i

tace ta je mana su gaisa, haka kuma lokaci daya tana amsa gaisuwar da Khadeeja ke yi mata da kula, sannan ta sake fadin" Litle jeki mana, ga maman naki, ki je...., daughter ya kwanan sabon gidanki? ina fata jikin ki da sauki?"

Khadeeja dake kallon kurma

, itama kurmar ita take kallo, a dan nesa da ita domin a tsorace take da matan da ake ha

ɗ

awa da mahaifinta, Mufeeda na yi mata kisan mumuke ne, ta ta

ɓ

a amsar ipad dinta ta rubuta mata sai ta kasheta da wuka idan tana zuwa inda suke fira da babanta ta tarda

su, ta sha fakar ido ta dungureta da karfin tsiya, kuma bata yi mata a gaban mutane shi yasa yanzunma a tsaye dai take ama ta kasa zuwa kusan Khadeeja

Khadeeja ta dubi aunty shareefat dake hada mata kayan kari a wasu plate na alfarma a tausashe ta ce

" Aunty, kanwarki ce? bata magana ne?""

Aunty shareefat ta yi murmushi ta ce " Kurma ce, ama tana karantar lebe, kuma tana rubuta amsa a ipad dinta....., no ba kanwata bace, jikata ce, y'ar Elhaji karami ce wato AL'WALID "

Da sauri Khadeeja ta kall

eta tana neman karin haske, domin mamaki ya kamata da tambayar kanta nan take cewar dama yana da wata matar?

Aunty shareefat ta dan dubi kurma ta ga ba ita take kallo ba dan haka ta ce" Mahaifiyarta ta rasu ranar da ta haifeta"

KHADEEJA ta Dubi kurm

a zuciyarta na cika da rauni da tausayin yar matashiyar yarinyar wace kamar ka tabata jinni ya fito tsabar hutu

Dan matsawa ta yi a gefenta ta kalli wajen ta ga zai isa ta zauna ta dubi Litle a hankali ta nuna mata gefenta sannan ta ce" Zo ki zauna.....

, kin ji? yaya sunnanki?"

Kurma sarai ta karanci me tace, ama ta kasa motsawa, sai ta kalli aunty shareefat ta kalli su Mama Fateema da aka yi sevng din abinci sannan ta kalli Khadeeja, har sai da Aunty shareefat ta dubeta da kula sosai ta ce" Je mana l

itle, ba nace maki mamanki ce ita ba?, je mana ta miko hannu kar ta gaji ko?"

"ki je ki fada mata sunnanki ko ?" ta karashe tana ajiyewa Khadeeja nata abincin bayan ta janyo dan karamin table

A hankali litle ta karasa kusan Khadeeja

Khadeeja ta k

ama hannunta a hankali ta dan rike shi da kyau tana kallon fuskarta ta ce" Me sunanki?"

Litle ta ciro ipad dinta ta shiga wajen rubutun wps ta rubuta mata sunnanta kamar haka "My name is Rahamatulah AL'WALID"

KHADEEJA ta zubawa sunnan ido, haka kawai

sunnan ya birgeta da mahadinsa, ta sakar mata murmushi tana dubanta ta ce" Ni kuma i'm NANA KHADEEJA EL YA'U"

litle ta dan dubeta a dan tsorace saboda sunnan da aka yi mata hannin kamawa koda wasa, sai kuma ta kalli aunty shareefat da sauri ta yi rubut

u a ipad dinta ta mikawa aunty shareefat

KHADEEJA na kallonta da dan mamaki ta ce" Aunty me ta rubuta?"

Aunty shareefat da jikinta ya dan yi sanyi ta dago daga karatun abin ta dan dubi Khadeeja tana basarwa ta yi murmushi ta ce" Ba komai daughter, k

i karya mana"

Mama fateema ta ce" Ai fa in dai Anmy ce idan ta samu fira ba lalle ta tuna cikinta ba, dauki ki karya mana ke da baki da lafiya?"

Da sauri kurma ta amshi ipad din ta mikawa Khadeeja ta dan yi abin kuramen nan ta bata

Khadeeja ta kar

anta maganar kamar haka " Kai, kaka S ta kama sunnan Maman mama bayan yace zai min duka idan na yi maganarta a rayuwata"

Cikin wani yannayi ta dago tana duban kurma wace ke kallonta itama , cike da son karrin bayani

Aunty shareefat ta mike tana fadin

" AM, bari dai in kaita wajen su inna ko ta barki ki karya"

Khadeeja ta basar itama sunna hada ido da mama fateema ta mata alamun ta yi shiru hakan ya sa ta yi murmushi kawai tana kallon kurma wace ta toge ta ki bin Aunty shareefat din Ta nuna zaunawa z

ata yi

Mama fateema da kula sosai ta ce" Aunty shareefat a barta wajen mamanta mana kafin ta dawo da kayanta nan ko Amu?"

Kurma ta ringa gyada kai tana kallon Mama Fateema dake yi mata murmushi tana son gane lalle lalle idan aka barsu daga ita sai

ita zata ci gaba da yi mata murmushin ne ko zata yi mata irin na Mufeedan

Jiki ba karfi Aunty shareefat ta zauna , tana kokarin turewa itama a ranta tana ayana' Ya Salam, litle sai ta janyo wata fitinar ne? koda yake yarinya ce ita ina ruwanta ga kuma

wannan larura Tata wace masu irinta yara dama sunna da wuyar sha'ani , Allah ya rufa asiri'

Kadan Anmy ta ta

ɓ

a abincin, ita kurma kuwa dama da zasu shigo ta ajiye robar kosanta da Kakan kurma ya shigo mata da shi tunda zasu shigo, yau da wahala ma ida

n zata je cin kosan dan ta yi damm, ama ta san kakan kurma zai ajiye mata wani ne sai in ya ga bata zo nema ba zai bada sadaka ko ya cinye abinsa

Su Mama Fateema ne suka tashi sunna kokarin tafiya Khalisat ta shigo da sauri bayan ta yi salama ta gais

he da mutane ta yiwa Anmy gaisuwarta daban da girmamawa sosai ta karasa kusan Aunty shareefat ta zauna jiki a mace ta ce" Aunty, kin kuwa san cewa su MUFEEDA ne suka zo da iyayenta?"

Da sauri Aunty ta kalleta, hakama kurma dake kallon bakinta sai da gab

anta ya fadi sosai

Aunty shareefat ta ce" Ban gane ba, wace Mufeedan? ta zo neman uban meye kuma?, ina shi son din yake ba yana tare da Kakan kurma da baba ba?"

Khalisat ta girgiza kai ta ce" Kakan kurman ai bai jira Big Son fitowa ba ya yi tafiyars

a Shago yace idan su Aunty baki sun fito su same shi a cen, kawai ana tsaye dai ana tatauna cewa dole za'a amshi Gara da su Mama mai gadi Ya zo yace security sun sa a tambayo idan a bar su malan Abdullahi shigowa iyayen Mufeedan, ke dai shi big son abin ma

maki ma ya bashi bai bada amsa ba sai baba ne yace a barsu su shigo mana baki ne?, in fada maki sai gasu sun shigo, su hudu a mota inaga mahaifinta da ita, da shi malan Abdullahi da direba ne, sai kuma wani a mashin dinsa, walahi aunty baki ji yadda hankal

ina ya tashi ba, yarinyar nan fa yar balaki ce Walahi tana iya bin hanyar da za'a daura mata aure da Big Son a yau, da kuwa mun shiga uku!"

KHADEEJA na magana da Mama FATEEMA ne ama gaba daya hankalinta a kan abinda yake faruwa dan har jikin khalisat ra

wa rawa yake yi

Aunty shareefat ta bige bakinta tana mikewa ta ce" Daughter Muna zuwa, bari mu dawo mu je asibitin nan kin ji? ina zuwa yanzu"

Ta wuce gaba kasa kasa tana cewa Khalisat " Ba fa zai yiwu ba, na rantse tunda baban Imane ya barni in yi s

ati a gidan nan sai inda karfina ya kare, ba fa zai auri yarinyar nan ba ko da uban me take takama, karya take yi ta zo ta wulakanta mana iyaye a gabanmu da bayan idannuwanmu sannan tace jikansu zata aura, ai shashashai muke kennan, walahi ba zai yiwu ba!"

A nutse Mama Fateema ta dubi Khadeeja bayan du sun fice sun bar su su kadai sai kurma da ta rafka tagumi hankalinta du ba a jikinta ba

A tausashe ta ce" Ba ruwanki da komai, ba ruwanki da shiga abinda ba'a saka ki ba, kuma koda abinda muka jin ne ba

wani damuwa kin ji? kawai ki ci gaba da addu'a sannan ki yi biyayar aure sau da kafa....., zan yi kira a numbar wani a gidan nan dan in ji ki, idan kin sake warwarewa sai mu zo a yi kitso da kunshin nan Umani, Ni da nake so a ringa yi maki su du sati bibi

yu? ina so in ga uwata ta fi kowa kyau da

ɗ

aukan wanka kin ji ko?, kuma sun ce yau zasu kai kayan akwati da dai tadarsu ta yiwu yau dinma mu dawo idan kuwa sai mun gama yi maki dinkunna zaki ganmu to, Ni dai zuwan da bana so in yi shine wanda zan ji kina w

ani abin marar dadi, alkur'an sai na bata maki Anmy kin dai sani sarai ko?"

Khadeeja ta dan turo baki, gaba daya zuciyarta lokaci daya ta ringa cinkushewa da wani tunani marar dadi da tsari wanda bai dace ace tana yi ba...., dan bata ga dadin abin da ta

ji da har zata ji daci dan an yi magana irin haka, to akace ma yana da y'a bata ji komai makamancin haka ba sai maganar wannan sunna zai tsaye mata a rai?, ama kuma abinda mama karama ke so da wahala fa, haba dai, Yaushema aka aurota da har za'a fara yi m

ata tunanin kishiya? a bari ta dan saje da gidan ta gama gane lungu da sakon gidan mana kafin a hada mata wata rigimar , biyaya? wannan ai dole ce, ama kuma ba lallene ta juri wani abin ba gaskiya kan uba!

Mama FATEEMA da iya suka tafi, Khadeeja ta dawo

ta zauna a kusa da kurma da ta yi wani iri du ta fita hayacinta, ga tsoron an barta daga ita sai Khadeeja wace take tunanin ba idannuwan kowa tana iya cuta mata kamar yadda Mufeeda ke yi mata, ga tsoron ta bi su dan idan akoy dan adam din dake bata tsoro

a duniya bayan Mufeeda ne, sai kawai ta sada kai ta yi tsomomo da ita

A hankali Khadeeja ta mika hannu ta ta

ɓ

a hannunta, hakan ya sa ta dago da sauri kuma a tsorace

Khadeeja ta dan zuba mata ido a tausashe ta ce" Tunanin me kike yi?"

Kurma ta sauk

e ajiyar zuciya, a hankali ta rubuta abu kamar haka" Tsoro nake ji, sun ce wai ta zo, kar aje din ta auri babana ta kasheni da tace, Ni tsoronta nake ji"

Karantawa Khadeeja ke yi kirjinta na amsawa, a hankali ta dago tana kallon kurma, sosai ta so jin k

omai daga bakin kurmar , kuma ta san abu ne mai sauki saboda kurma ba wata baba bace da zata iya bambance wasu abubuwan a yanzu, du abinda aka tambayeta tana iya fada kanta tsaye, sai dai kuma haka kawai sai yannayin kurma ya bata tausayi, a bayane yake ya

rinyar a tsorace take, hakan ya sa Khadeeja cire hijabinta ta kama hannayen kurma tana dubanta a tausashe sosai ta ce" Hey, akoy wanda ya isa ya kashe wani ne bayan Allahn da ya halice shi?"

Kurma ta girgiza kai hawaye na bale mata, ta rubuta abu kamar

haka " AA, ama ita din har dukana take yi, kuma tace idan na fada sai ta yanka Ni, tsoronta nake ji sosai"

Khadeeja lokaci daya ta ringa jin wata irin tsanar matar Duda bata ta

ɓ

a ganninta ba

itama rubutun ta yiwa kurma kamar haka' Kar ki ji tsoron du

k wani mugun mutun, dan bai isa koda kwarzane yayi maki ba sai da amincewar mahaliccin ki, in sha Allah ba zan kuma bari ta yi maki komai ba, nice nan zan zaneta da bulala kin ji kawata?'

Bayan kurma ta gama karantawa ta dago tana duban Khadeeja, sai ta

saki murmushi a hankali ta zauna daf da ita sosai sannan ta yi rubutu kamar haka" Ke mamana ce in ji papah, dan Allah ki zama mamana, nima ina son samun Mama irin na kawayena"

Zuciyarta a hankali ta ringa narkewa da kauna da tausayin Kurma......, bata

karra ce mata komai ba sai

ɗ

ora kanta da ta yi a saman kafarta ta shiga dan bubuga bayanta, zuciyarta na jin a yanzu ko waye ya nufo yarinyar nan da wani abin marar dadi tabas zata tarbe shi ta amshi abin sai dai ya ilatata, a ranta take jin lalle ba zata

iya kyale duk wani mai son cutarwa yarinyar nan ba, lokaci daya ita khadeeja da ta amshi auren da take gannin bata isa a yi mata shi ba da bakon mutumen da har yanzu basu yi zaman minti talatin ita da shi a hayacinta ba, har ta amshi yarinyar sa ta cikinsa

harma take ji a ranta kamar tana iya amsa kiran Mama Duda itama yarinyar ce idan har wannan babyn ta kirayeta da sunnan......Ya rab........................................kaunar abinda bata haifa ba ya gama mamaye zuciyarta , harma take ji a ranta ta yi Y

'A.

Tunda motar nan ta shiga da babur din Muhammadu d'an gidan akaramakalahu Abdullahi cikin gidan sirikinsa shi Elhaji Ya'u ya gaza zaune, ya gaza tsaye, ya kai wajen shagonsa ya fi a irga, dukkan wata hanyar da zata kai shi gidan nan ya yi tunani ya r

asa karshe ya fito ya ja ya tsaya yana duban salihu ya ce" Wai ina tsoho yau fa ya ki fitowa hankalina du a kansa"

Salihu ya ce" Ai zai fito Elhaji ka manta har karfe biyu yake kaiwa wani lokacin bai fito ba sai in ya fito sallar azahar yake zuwa nan di

n ya zauna"

Aba ya dube shi shekeke ya ce" Karya kennan, ai warhaka tuni tsoho ya isheni da surutu, bari dai in leko shi bawan Allah "

Salihu ya ce" Hakane kuma, ama inaga baki ne suka yi yawa a gidan yau shi yasa bai fito ba"

Aba ya yi turussss y

ana kallonsa , sai kuma ya duka ya shuri buta dake ajiye ko ruwan kirki bata da shi ya ce" Kai salihu dan Allah hannani zuwa in gidan cen gidan mijin y'arka ne, shegu yan saka ido har ka san lokacin fitowarsa kennan? to bari in je in shiga bayi a gidan in

ka isa hannani "

Salihu dake fitar da cafet din wata mata dake jira ya dan dubi Elhaji ya ga ya yi gaba yana baza babar riga , ya kama haba yana fadin" Mun shiga uku, zuwa zai yi, walahi dama na san tunda motar matar nan ta shiga ba fa zai iya zama ba,

Ni banma san me kuma hadi bayan an gama zumuncin ya auri wata,, kora yake Elhaji daidai yake da ku, Allah dai ya takaita, su Elhaji sai zagaye ake dan kar mu saka ido mu ce an shiga gidan y'a shine aka fake da neman Elhaji.....hhhhh"

A cikin gida, a f

alon Hajia inna bayan an fito da ita, su Hajia Binta da su Hajia zainabu duka sunna nan, ya zamo harta yan matan gidan sun taho du sun nufi inda AL'WALID ke zaune sun likun masa kowace na jiran ko ta kwana, su dukansu cike da mamakin hijabin dake jikin Muf

eeda, kuma fuskarta har ta fada na rama, kuncinta kuwa yayi wani irin dau da shi kamar kosai tsabar ja, tunda suka zauna kuwa idannuwanta a kan AL'WALID wanda suke dan maganar harkar gonaki da albarkatun gona na bana da malan Abdullahi da baba Hamza bayan

gaisuwa irin ta girmamawa da suka yiwa junna bayan zuwan su da neman alfarmar a basu lokaci sunna son yin magana

Baba Hamza ne ya karewa falon kallo, a tausashe ya dubi Aunty shareefat ya ce"

07/12/2024, 15:16 - samiraharounayacouba:

🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺

🌸🌺

*FARKON GANIN IDONA*

🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺

*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*

🇳🇪

*PAID BOOK*

*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 9381

1618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you

😍

*



LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR K

ADA

Y'AR MAHAUKACIYA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA

BAK'A CE

KUTKALE

DUK NISAN JIFA

MAGE

IDAN KA RAINA INDA KAKE

DUTSE

NI ZAN LADABI

ZAKIN SARAKAI

WATA KOKOWAR

DA CIWO A ZUCIYATA

AURE YAƘIN MATA

AZAL

WATA TAFIYAR



Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login