Showing 162001 words to 165000 words out of 200647 words
na zata shine ya min magana, to ama a
i babu mai kirana sai yaronsa kawai, shi kuwa bai jima da barin gidan nan ba tare da iyalinsa, Ni na yi zaton kamar muryarsama na ji....."
Maganganu dai a rarrabe, a sanyaye ainun, ga ajiyar zuciya wata na korar wata
A hankali khadeeja ta ce" Mama shin
e ya kira, mun yi kiran ki ne dan mu ji sauƙin jikin ki"
Ido mamansa ta bude sosai sai kuma ta saki murmushi hadi da hawaye a hankali ta ce" Gudaliya ne ya kira? Kai, ashe zai yi kirana? Alhamdulilah"
Khadeeja ta yi murmushi zuciyarta na sake karyewa
da tausayin matar nan, a hankali ta ce" zai yi kira Mama, zai zo ma da kansa Mama in sha Allah zai zo da kansa ne Mama"
A hankali mahaifiyarsa ta kankame hannayenta Muryarta na rawa ta ce" Yaya sunnanki yarinyana? Ke ce matarsa ko?"
Khadeeja ta sauk
e ajiyar zuciya a hankali ta ce" Eh, sunnanmu daya da ke Mama"
Mama ta sake bude ido da mamaki tana maimaita maganar khadeeja ta ce" kina nufin sunnanki Nana khadeeja?"
Khadeeja ta gyada kai a nutse ta furta " Eh"
Mama khadeeja ta langwabar da kan
ta a hankali ta ce " Ta yiwu baba ya yafe min, tunda a da cewa yayi ko mai sunana ba zai kuma bari a yi a gidansa ba, sai gashi ya aura wa jikan da ya fi so mai sunan nawa? Ikon Allah tabbas zuciyarsa ta
ɗ
an sassauta min, ta yiwu tun da raina zan ga ya yaf
e min ne ko yarinyana?"
Khadeeja ta gaza sake bude baki saboda kukan da take ji na neman sake kamata
Mama ta ce" ina son gudaliya sosai yarinyana, kema ki so shi
ɗ
an Allah saboda kiran nan nawa da kika sa yayi na tabbata ba ƙaramin tasiri kike da shi
a zuciyarsa ba, dan Allah ki so shi, ama ki ji tsoron Allah kar ki yi masa mummunan so wanda bashi da anfani irin wanda na yiwa mahaifinsa "
A hankali khadeeja ta ce" Mama"
Mama khadeeja ta yi gaggawar amsawa
A hankali ta sake fadin" Mama, kowan
i bawa da yannayin kadararsa, ki yi hakuri Mama, ki yafewa baban litle, in sha Allah zamu zo"
"Ban taba kwonciya barci ba tare da na fadawa Allah cewar idan na mutu a cikin daren nan na yafewa gudaliya gaba da baya ba yarinyana, haka bana fara wuni ban
fadi haka ba, Ni ce nake da bukatar yafiyarsa, nice nake da bukatar yarona a tare da Ni, Allah ya baki ikon saka shi dubana yarinya ta, Allah ya yiwa rayuwar aurenku albarka, kwarai kin sakani farin cikin da na jima ban yi ba, Allah ya nuna min ranar da za
n ganshi a gabana"
A hankali khadeeja ta furta" Amen ya Allah "
Haka dai suka
ɗ
an sake yin magana kafin su yi salama
Khadeeja ta jima a zaune tana duban wayar kafin ta mike ta nufi wajen kayan turarukanta
A nutse ta yiwa jikinta wanka da turar
e, sannan ta juya ta dauki hijabinta ta saka ta kashe komai ta bar wayoyin a nan ta rufe dakin nata ta nufi nasa zuciyarta na bugawa da tsoro, sai dai ta riga ta sakawa ranta cewa abinda bai kashe wasu ba, ba zai kashe ta ba,
A nutse ta tura ta shiga a
hankali tana yin salama hadi da nemansa a dakin da tunanin ko baya nan?
A nutse ya kunna fitilar gefen gadonsa yana sake zuba mata jajayen idannuwansa
A hankali ta mayar da kofar ta rufe sannan ta nufi inda yake gabanta na faduwa a duk takun da zat
a yi dan kusanta kanta da shi
A hankali ya lumshe idannuwansa a lokacin da ta hayo gadon sakamakon hannayenta da ta saka a wajen fuskarsa tana kallonsa
Kasa kasa ta furta" Ka yi hakuri, Aban litle Please, ba zan kuma ba"
Hannunsa ya sa ya janyota
da karfi har sai da goshinta ya daki kirjinsa ya sakata a cikin jikinsa sannan ya yi shiru
Irin yadda kirjinsa ke dokawa ya saka ta rintse idannuwanta a hankali tana shafa bayansa
Sun dauki lokaci a haka, har ta yi tunanin ko barci ne ya dauke shi?
Sai dai rikon da ya mata a kirjinsa bai sassauta ba hakan ya sa ta gane idonsa biyu
Cen cikin kuryar murya ya furta" Ita ta sha maganin nata? Ko wannan ciwon ma kin shan zata yi? Yaya jikinta ne ?"
Khadeeja ta dago fuskarta tana dubansa, a tausash
e ta furta" ai ta samu maganin ta , mama na jin Muryar ka sai da ta yi dariya na kashe kiran"
Idannuwansa ya lumshe yana sauke ajiyar zuciya, a hankali ya sake matsota jikinsa yana jin wani irin nutsuwa na ratsa zuciyarsa, cen kasa ya furta" Ni menene a
tsakanin hannayena da fatar ki hajia karamahhhhhhhh?"
Khadeeja ta yi sauri sake kallonsa, wannan karon ta taki rashin Sa'a shima ya bude idannuwansa a kanta
Da sauri ta lumshe idannuwanta a hankali ta furta " a'a fa, kai da baka da lafiya?"
"Na f
ada maki?, kalau nake ai, kuma so nake yi mu yi mu daga tumbin nan, idan ba'a yi aiki da kyau ba, ba zai dagu da wuri ba"
Ido ta zarro a hankali ta nemi juyawa, sai dai bai bata dama ba a nutse ya rabata fa hijabin nan kas akasa ya ce" aa, babu wani abi
n karuwa a bayan nan, nan din dai ya fi ....., kin san me?"
Khadeeja ta bude idannuwanta tana kallonsa
A tausashe ya furta" i love You......."
Khadeeja ta wara manyan idannuwanta a kansa.......
A hankali ya furta" haka kawai......, na tsufa, a wa
ni taso min tsumi......, mu yiwa musulunci hidima hajia karama bani dama mu kashe arnan nan"
Murmushi ya kubce mata, da sauri ta boye fuskarta tana jin yadda yake yawo da hannayensa a sasan jikinta .........ya zamo tun tana jurewa har ta idasa shigewa j
ikin nasa ba tare da ta tuna azabar da ta sha a jiya ba,.....kai a matsayinta Na likitama ta
ɗ
an cewa tana iya dake jure wata azabar kawai....mema ya fi ran baban litle ne? Sai dai jikin yayi tsamin......da wannan suka baje zance har sabo ya karra jadada t
are da shedar albarka da tunatarwar kauna uwa uba gurnanin maza mai tsayawa a zuci (
😭😭😭😭
🥺
😫😫😫😠😉🙁😁😁😁
)
__________________________________
Washe gari kusan karfe bakwai da rabi
Mama ce ke kicin tana faman juya kunnun gyadar da za
'a kaiwa baba Hamza , tana yi tana ankara da girkin da ta
ɗ
ora wanda za'a diba a kai masa da kuma wanda za'a ci a gidan dan kari
Shigowar aba ta hudu ce kenan yana kai kawo da wata tsangalaliyar jalabiyarsa fara da katon carbinsa yana lekowa yana komawa
, wannan shigowar da yayi ya ja ya tsaya yana kallon mama dake ta aikinta ya ce" Rainani ma ake son yi, so ne ake yi a wulakantani kawai a kuma wulakanta min uba, sai da nace maki bashi da lafiya yau ki yi safiya ki masa kunnun nan ko zai sha, ama tsabar w
ulakanci irin naki gimbiya ga rana ta hudo tsuntsaye sun koma lambu ubana bai karya ba"
Mama ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" ka yi hakuri baban Sadik, girkin nan ne ke daukan lokaci wajen gyaransa, ama na gama ai dan Allah ka dan kara hakuri ka
dan"
Tsaki aba ya ja ya shigo da kyau yana fito da kulolin masu Kyan gaske da abin zubawar, ya juyo yana murmushi ya ce" gimbiya gimbiya, wadannan kwanonin yaushe kika siye su? A ciki zan kai masa saboda kallonsu kadai zai sa tsohon cen cin abinda ke ci
ki"
Mama ta
ɗ
an dakata ta Dube shi ta ce" zaka kai? Wani irin zaka kai? Ama ka san yanzu anmy ke aure a gidan nan ko? Kuma mijinta na gari, ya zaka ringa shiga lokacin da ka so ne? Jiya fa nan ka ce min a gabansa ka ringa abin nan, haba baban anmy kar k
a janyo mata magana mana, kuma ka manta ne jiya na fada maka yau za'a kai mata kayanta tare da sisters dinta harma na sanar maka maman kareema fa ba lafiya ya dace ta je ta ganta kace ai sai dai su je tare da yan uwanta kai baka yarda da ita ba?, yaya za'a
yi daga kai yarinya sai mu yi ta shige da fice a gidan nan fisabililahi?"
Aba ya yi shekeke yana kallon ta kafin ya dage kansa ya ce" Ai sai ki yi, ku yan gargajiyar nan sai balakin saka ido, gimbiya ina daf da kai karar ki inda za'a min maganinki WALA
HI, wajen uwata!, au yaushema Aka haifi hajiyar? Kafin ta zo duniya ma ina tare da ubana, zuwan ta babu abinda zai hanna, abinda bangarensa daban nasu daban? Ni tunda nake shiga Allah ne shaidata ban ganta Bama, Ama yau zan je in ga dakinta da kaina in sak
e fada mata idan bata yiwa elhaji karami biyayya ba ubanta zan ci, bari dai in saka dogon wando a kasa in tafi juye min duka kafff, kara mulda masa madarar nan dan so nake yi ya mike sak, babu mai kashe min uba!"
😉😉😉😉
Hello jama'a, kun s
an me? Da muka dawo ne comment ba karfi.....shine lamarin sai a slow...., Ama ga bonusssss
46
07/12/2024, 17:27 - samiraharounayacouba: Ajiyar zuciya kawai Mama ta sauke ta mayar da hankali ta yi abinda yace din suka shigo tare da Abubakar ya kwash
i kayan ya tafi kaiwa mota
A nutse take biye da shi har suka karaso wajen mota ya bude ya shiga
A tausashe bayan ta saka kanta kadan ta ce" Aban Sadik, dan Allah idan ka je ka GAISHE da baban, sannan dan Allah ka yi hakuri ka yi tunanin da kace zaka
yi a kan lamarin yaron nan mai neman auren Karima"
Kai ya gyada bayan ya tabe baki ya ce" to gimbiya zan yi tunani a kan aurawa y'arki mai jan ido tunda kin dage kin kuma hanna yayanki zuwa dauko min fansa, wato an sakani a tsakiya sai dai in yi yakin
Ni kadai....ba laifi ai"
Mama dai bata ce komai ba dan ta san ita ke so ya dubi maganar ta, domin ko a jiya da dare sai da ta zaunar da karimar ta yi mata tambayoyi a kan lamarin, kuma ta yarda cewa itama tana son saurayinta sai dai idan an hanna taraya
rsu ne kawai, wanda hakan na iya haifar da wata ilar
Bayan sun tafi ta juya ta nufi baban falonsu a nutse
Tana shigowa ta tarar da Karima tsaye tana kallon amarya dake zaune itama tana kallon ta, sai dai yannayinsu kamar magana Amaryar ke yi dan a i
rin tsayuwar da karimar ta yi kamar wani abu Amaryar ta fada da ya sakata a wani yannayi na mamaki haka
Bata wani tsaya ba tana tafe ta ce" Karima babanku yace kunna iya biyawa ku ga jikin maman naku sai ku wuce gidan na anmy, dan haka idan kin gama ki
dauki manyan kula ki zuba mata abinci na dubiya"
Karima jiki a sanyaye ta ce" to mama" sai kuma ta dubi amarya wace ta tabe baki tana yi mata kallon sama da kasa ta ce" Ba kin gani ba?, ana anfani da ke ana cutarwa mahaifiyarki da ke din da kanki, Karim
a kina gani fa, ke aka zabawa mijin nan Ama matar nan ta cira ta kullu ya juye kan y'arta, in har maganar gaskiya ake bi kafin y'arta ba lubna ce a tsakani ba? In abinda take miki nufin gaskiya ne cewar dan kin kiya aka bashi daya daga cikin y'an uwanki a
kan me aka tsallake aka rasa wace za'a bashi sai khadeeja?, sai ki je ki zubawa maman naki abincin ki kai mata, salon gobe a yi mata gorin yunwa ace abinci sai an kai mata daga gidan tsohon miji, ke baki Sani bane a ciki ake barbada masifar dake hadasu fad
a har ya ringa zane maki uwa, kin wani zo kin zabi uwar wani a kan taki, ai sai ki karra hima "
Tana gama fada ta mike ta nufi cikin dakin cin abincin su tana dana wayarta zuciyarta cike da farin ciki da tunanin ko yayane zata saka kiyaya tsakanin gimbi
ya da yaran nan, idan ta ga irin yadda suke mata mama mama wani takaici ke kule mata zuciya, yan rainin hankali ita kuma sai dai su kirayeta da amarya, sai kace ba matar ubansu ba! Dan kuwa su samarin sarai ta kula wani gani gani suke yi mata, Bama kamar i
dan sunna yar rigima da gimbiya irin kallon da suke yi mata har tsoro ke ratsa ranta kar aje wata rana su maketa kamar ta ta
ɓ
a mahaifiyarsu, ita da kanta gimbiyar in sunna waje ko me za'a yi bata biyewa dan da bakinta ta ta
ɓ
a nuna musu cewar su guji idannu
wan yara, yara fa sun girma, ba zata so a basu muguwar tarbiyya ba ko a basu wata kafa da zasu raina daya a cikinsu ba,
Karima ta dan jima a tsaye kirjinta na dokawa kafin ta juya jiki a mace ta nufi corridor din dakunan su
Lubna ta gani a tsaye rik
e da abaya a hannunta
Irin kallon da lubna ke yi mata ya sa ta ji gabanta ya dan fadi
Sai dai ta ga lubnar ta yi dan murmushi ta ce" Ke fa nake nema, ashe kina falo? Dan in ce maki ne mu saka wannan abayar ta wajen aba wace aka kawo mana a cikin kay
an saudiyar da aka bugo masa, zamu fi yin kyau"
Karima ta yi murmushi ta nufi dakinta tana fadin" To"
Daga haka bata karra komai ba, ita kuwa lubna ta rakata da ido kafin ta juya ta shiga dakinta ta rufe ta zauna bakin gado
Ta jima tana dan tunani
kafin ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Allah ya sa wannan karon ki yiwa kanki adalci, Allah ya sa a cikin halayyar masu harin zuciyarki ki iya jajircewa ki dubi zahiri ki yiwa wace ke rungume da ke adalci Karima"
Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya
ta ajiye rigar ta mike ta shiga shirin shiga wanka
Lokaci daya kuma ta sauke ajiyar zuciya hadi da murmushi mai tsada a lokacin da ta tuna firarta da mama a jiya da dare, tambayar da ta yi mata kan idan tana da wanda take so? Da ta tabbatar mata cewa ba
bu, sai ta tambayeta shin zata iya zaman aure da ƴaƴansu na bangaren mahaifiyarta? Wato dan mijin mamanta ne baba, lauya ne mai zaman kansa , sannan dan kasuwa , kuma bai taba yin aure ba har yanzu dai yana jira ne tun lokacin da ya cewa babansa yana sont
a akace yayi hakuri har ta girma sai yayi hakurin, kuma cikin ikon Allah aba ne da kansa da maman tace masa to lubna fa? Sai yace lubna ai da mijinta , shin ta manta wanda ya yiwa alkawari? Shi yasa ai ya zabawa AL'WALED khadeeja dake bi mata saboda ita da
mijinta ai, .....abinda ya tsayar da lamarin aurensu suma na Karima da ummi ne kawai........., Ummi yace zai bata dama ta hadu da wanda ya zaba mata idan sun daidaita shikenan, Karima ce har yanzu ya ki ya ba saurayinta fuska, yaron kuwa kamar wanda ya fa
da jarabawa a kan karimar, hatta mahaifinsa jira yake yi yace an basu damar su nema masa aurenta dan kuwa sun gane da gaske yake ba da wasa ba.
A nutse ta shiryawarta, sannan ta bude dakin da ake ta buga mata ummi na fadan WALAHI zasu yi tafiyarsu ne id
an bata fito na, dan kuwa har sha daya ta yi basu fita ba
Sai da mama ta yi musu nasiha sosai sannan ta ce" Ta yiwu ku samu su Fatima a cen, dan sun tafi su tuni da kayan nata, Allah ya dawo da ku lafiya"
Lubna ce karshen mikewa ta amsa da" amen mama
, ai kuwa bari mu yi gaggawa saboda mu tayata ayyukan gyara kayan nan"
Daga nan suka karasa mota suka shige, Abubakar ya ja su
Mama ta sauke ajiyar zuciya ta yi murmushi, wato Karima bata zubawa mahaifiyarta abincin ba, bata wani rike a ranta ba saim
a zuwa da ta yi ta duba asibitin da zata yi aiki yau ta hau shiri saboda tana son fara fita aiki a yau.
Kofar gidan su Karima suka tsaya, suka fita gaba dayansu suka shiga gidan ba tare da sun sanar mata da zuwan su ba, domin Karima dai a yanzu ba way
a a hannunta shi yasa ko uwar sai da ta bi ta wata hanya kafin sako ya samu gimbiya cewar bata da lafiya saboda ta sani ta hanyar nan kawai ce zata iya gannin y'ar Tata har su yi maganar da take so su yi, ba wani rashin lafiya kalau take, ta bi duk wata
hanya ne dan ta samu gannin Karima abin ya gagara shine ta biyo ta nan ko a dace
A filin gida suka same su sunna shan innuwar dalbejiyar dake cikin gidan, kakar Karima na yamutsa tafasa da kulli, mamanta kuwa tana shan koko a kwano da ludayin roba
Ga
isheta suka yi su duka , sannan suka tambayi jikinta
Kakar Karima dake mamakin gannin ya'yan elhaji ya'u su duka ta kalli y'arta a dan tsorace da tunanin yauwa ga dalilin da ya kawo ya'yan elhaji gidan nan gaba dayansu
Lubna a tausashe bayan sun za
una maman Karima na yi musu tayin kokon ta ce" alhamdulilah mama, ai sai da muka karya sannan muka fito ma"
Maman Karima ta tabe