Showing 120001 words to 123000 words out of 200647 words
har suka layu a wajen da suka tsara zasu layun
Masu guda na yi, masu daukan vidio na yi a lokacin da yaya Sidiku ya bude ya fito da Khadeeja yana talabe da ita a hankali ya furta " Anmy, kar ki fadi fa, ki daina kukan nan kuma alkur'an zan kifa m
aki mari"
Muhammad ya dan harareshi kasa kasa ya ce" Easy mana Habu, ka barta ta zuba bacinta yau ai ranar ta ce"
Mama FATEEMA da ta gama gyara jakar Anmy ta hannu da ta riko a tausashe ta ce" To bismillah, kar ku manta ta yi addu'a a duk wajen da z
a'a shiga, kuma ku tayata, mu je"
Ya zamo yanzu Mama FATEEMA na take sawayensu ne dan zata fi gani da kyau, su kuwa samarin gidan Aba sunna talabe da kanwarsu suka nufi matan gidan Elhaji Hamza dake zazaune domin Imane ce ta sanar da su nan za'a fara zu
wa, sai su yi musu jagora zuwa dakin Hajia inna, daga nan sai a kaita dakinta
A hankali suke tafe da ita har suka karaso gaban kakanni da iyayen AL'WALID
A nutse suka duka da ita a gaban iyayen bayan makeriyar famillyn ta sanar masu su waye su Hajia
Binta da su aunty shareefat a duniyar AL'WALID
Kan Khadeeja a kasa yake, hannayenta cikin na yayunta, Mama fateema a tsaye cikin girmamawa ta fara gaisar da su kafin a tausashe ta ce" Ga jika kuma y'a a wajenku, ga mata a wajen jika kuma d'a a wajenku
wato Nana KHADEEJA Elhaji Ya'u, Allah ya bata ikon yi muku biyaya, a yi hakuri , a yi hakuri da yarinta, a yi hakuri , ke kuwa ki bi manya ki wanye lafiya da kowa shine darajar ki a gidan nan"
Hajia Binta ta yi murmushi, domin irin yadda aka riko amarya
r ya birgeta sosai, yayunta dake duke da ita sun birgeta suma sosai hakan ya nuna mata akoy tarbiya a tare da yaran, a tausashe ta furta " Allah ya miki albarka kishiya, Allah ya sa kin shigo gidanki a Sa'a, Allah ya tsare ki daga dukkan abin ki, Allah ya
baku zuri'a dayiba"
Da amen ake amsawa, ita kuwa idannuwanta a rintse suke kawai kanta na sarawa
Mahaifiyar khalisat, wato Hajia z ta ce" Masha Allah, a bude mana amaryar mu gani mana? ko du kishin ne ya sa aka kunshe ki?"
Da sigar tsokana ta fada
a baibai, domin tun a nan ta so gannin amaryar, sai Hajia Binta ta yi gagawar hannawa tana yar dariya ta mike ta ce" Bismillah, mu je na yi maku jagora zuwa dakin Hajia inna"
Ita dai tun a nan ta ringa jin kaffafuwanta tamkar zasu gaza daukanta, a haka
dai ta rabawa yayunta nauyinta suka talabata suka nufi cikin baban falo da ita sannan suka dauki hanyar dakin Hajia Inna
Bayan Hajia Binta ta shiga ta basu damar shigowa
Baba Hamza na zaune saman kujera daf da gadon Hajia inna aka kawo Khadeeja ak
a dukar da ita kusa da su a tausashe Hajia Binta ta dan janye mata rufarta kadan ta ce" Wannan shine kakan mijinki, mahaifin mahaifinsa, wannan kuwa dake jingine itace Hajia inna, wato mahaifiyar mahaifin mijinki, Allah ya yiwa mahaifinsa rasuwa, sai su ,
sai mu, muna yi maki Barka da shigowa ahalin Elhaji AL'WALID ELHAJI BASHIR ELHAJI HAMZA"
Wata irin sarawa kanta yayi, ba dan komai ba sai dan jero elhajin da aka yi a jere, domin har yanzu bata gane a wani irin gida suke ba, bata gane a wani irin daula
suke ba, dan idannuwanta a lumshe suke, haka kuma kanta a sade, ga yannayin da take ciki ya hanna mata dagowarma bale ta tsare kowa da ido har ta gane abinda yake faruwa
A hankali baba Hamza bayan yayi murmushi ya ce" Allah ya miki albarka Anmy, Allah y
a kade duk wata fitina ya karro duk wani alkhairin dake tare da ke a ahalina, .....ku kaita ta huta in sha Allah ai ma hadu ko Hajia inna?"
Hajia inna ta yi murmushi a hankali ta furta" In sha Allah ma hadu y'ata, a kaita bangarenta Hajia, Allah ya saka
da mafificin alkhairi, sannunku da dawainiya...." Ta karashe tana duban Mama FATEEMA dake duke itama
Mama fateema a tausashe ta ce" Allah ya karra lafiya da nisan kwana, mun barku lafiya"
Daga nan suka mike aka fitar da ita yayunta suka sake riketa
bisa jagorancin Hajia Binta da aunty shareefat y'arta suka nufi bangaren AL'WALID
Bayan fitarsu da yan mintuna Hajia inna na kallon kasa a hankali ta ce" Kakan AL'WALID"
Baba Hamza dake jan carbi ya dago ya ce" Na'am ta cen cikin zucin kakan AL'WA
LID"
Murmushi ya kubce mata, wato duk girman mutun in dai yana cikin hayacinsa halayarsa na tare da shi, baba Hamza ba dai barkwonci da sakin fuska wa iyali ba
A tausashe sosai ta ce" Baka tunanin lokaci yayi da zaka yi hakuri?, baka tunanin girma da
daraja irin na uwa? kar ka manta aljanarsa tana karkashin kaffafuwanta, Allah fa babu ruwansa da ga laifin da ta yi tunda ba shi d'an nata ta yiwa ba, Duda abin ya shafe shi ama kai ka san Allah sai ya tambayeshi tsakaninsa da mahaifiyarsa...., Elhaji uwa
ce fa, dan Allah ka karashe nuna masa soyaya ta hanyar bashi damar gyara mu'amalarsa da mahaifiyarsa, tana raye, ta jima da fitowa daga gidan gyaran halin, abin yayi tsauri da yawa Elhaji , babu wani Abu tsakanin biyayar d'à da mahai........."
"Ramatu,
ki yi hakuri ki bar maganar nan, Allah ya tashe mu lafiya" Baba hamza ya fada a kausashe sannan ya Mike ya juya ya yi tafiyarsa a hankali fuskarsa a daure sosai
A hankali hajia Inna ta ringa shafa gashin kurma dake kwonce tana barcin gajiya, domin yau
ta sha ciriniya sosai , domin biki ta yi da iyayen nata kananu wato y'ayan su aunty shareefat , kuma kowane yana nan nan da ita, ......ajiyar zuciya take saukewa a hankali zuciyar tata a matukar kuntace da wannan Lamari
Shine an taba yin Haka ne? Baba ham
za bashi da gaskiya domin Dukan tsaurin abinda ta yi ita da ubangijinta ne, kuma mijinta sai da ya ringa fadin ya yafe mata, Ama tunda Allah ya dauki ransa Baba hamza ya duka gaban gawarsa ya kifa Kai yayi kuka sosai , yana mikewa ya Mike da kiyayar baiwar
Allahn nan mai munin gaske, Kiri Kiri ya hadata da hukuma, kuma ya rabata da d'anta,
Tabas ta tafka kuskure mai tsaurin gaske, sai dai wannan Allah kadai ya san hukuncin da zai yi mata, Bama kamar idan ta tuna cewar shi marigayi da bakinsa da hankalinsa
ya ringa maimaita cewar ya yafe mata, ta yiwu bata da wani laifi a wajen Allah fa, kar aje idan an tashi a babar ranar da take tabasss Baba Hamza da AL'WALID su shiga uku a kan laifin da suke gannin su aka yiwa...., ita dai ta yi kuka ta yi kuka mai tsanan
in gaske na rashin tilon d'anta, a hankali kuma ta yi hakuri ta bar komai, daga bakin lokacin da aka karra yi mata karatun fari fari cewar Allah na amsar bayinsa a lokacin da ya so, sanadiyar tafiyarsa ce kawai ta biyo ta hanyarta sai ta yi ta astagfari ta
na karra kusanta kanta da Allah, ta rungume AL'WALID har Allah ya kawo su wannan lokaci
A hankali ta furta " Ya Allah, ka yi min maganin damuwata, idan har mijina da jikana zasu shiga wata fitina sanadiyar laifin da wanda aka yiwa ya yafe ka shirya su k
a sasauta fushin su ka sa su gyara kura kuransu "
A haka ta yi ta jan carbi, mutane da daidaya na yi mata salama ta yi musu fatan alkhairi sannan ta ba hajia zainab salamar yan kawo amarya da kanta saboda farin cikin wannan rana, kyauta ta musamman, ta
sanar mata ta sanar da uwar amaryar maganar lefe da dukkan wasu kyautuka a gobe ne za'a yi, dama haka suke su, sai kin kwana a dakin d'ansu kike samun wannan kyaututuka
Hajia Zainab na fita waje ta samu ta sake kiran maman Karima ta idasa fitar da ita a
hayacinta, bale da ta sanar mata tarin abin alkhairin dake jiran Amarya sai kawai ta yanke jiki ta fadi numfashinta na wani iri kuka na dane mata kirji, bale da ta daga kai ta ga rufar karan dake dakin sai ta ji kamar dakin zai rufu da ita, innalilahi wa
inna ilaihi raj'une gaskiya an ci amanar ta, ba'a fada mata ba da yanzu itace ke gaban lamarin nan? innalilahi wa inna ilaihi raj'une Elhaji AL'WALID din da kansa? lalle dole ta halastawa Karima shiga gidan nan ta kowace fuska!
07/12/2024, 15:14 - samirah
arounayacouba: *FARKON GANIN IDONA*
PAGE 33
TALLAH TALLAH TALLAH TALLAH
*Zumar 3in1 zumace ingantacciya mekyau megyara jiki sosai zatasaka kayi bulbul breast sugyaru hips yafito kiyi yar duma duma hajiya bazakigane abundanake f
adaba dai kinshata zakigane*
*08030861857*
*Zumar breast Zumar hips duk munadasu masu inganci sosai da sosai*
*Akwai pills na 3in1 shima aikinsu Daya da zumar 3in1 gawayanda basashan zumane mukayi daminsu*
*08030861857*
*Infection flusher Ingant
acce maganine mai magance dukwata matsalar mara Kai harda rashin haihuwa yanayi banahaufi akai don angwada angani mace indai rashin niima ne na cutar sanyi yararaketa kuraje kaikayi dattin mara zonabaki infection flusher kisha mamaki yar uwa Insha Allah za
kigodemin*
*Kayanmu guarantee ne sai angwada akansan nakwarai location gombe munaturawa koinah Insha Allah* *08030861857* Kira KO WhatsApp Insha Allah
LABARI
Da kyar Mama FATEEMA ta iya raba Khadeeja da yayunt
a a bakin baban falon Gidanta da zasu shigar da ita domin dama sun baro sauran baƙin yan rakiyar amaryar tun a wajen su Hajia, Hajia Binta da aunty shareefat da Mama FATEEMA da su Sidik ne suka yi mata rakiya har nan, su dinma bakin baban falonta suka ja
suka tsaya, du yadda Mama FATEEMA ta so su kaita har ciki suka nuna zasu dawo , idan mai gidan na nan zasu shiga in ya musu izini, su kuwa Aba ne da kansa yace da su bakinsu kofar falonta kar su shiga ciki, yayu suke kar su yi abin rashin hankali
Kukan
da take yi ya saka Muhammad juyawa da sauri hawaye na bale masa, yaya Sidik kuwa ya sauke ajiyar zuciya ya ringa kai kawo dan jiran Mama FATEEMA su tafi tare
Murya biyun nan kawai take ji na mama Binta da aunty shareefat har lokacin da suke hawa da it
a matatakalar gidan kanta na sake sarawa har suka karasa da ita bakin gadon da Mama fateema ta saka ta yi addu'a kafin su zaunar da ita.
A nutse Aunty shareefat ta yaye mata mayafin nan da aka luluba mata ta janyo kujera ta zauna tana fadin" Masha Allah
, masha ALLAH, Big son dina ya dauko tauraruwa a cikin taurari, yadda fatarki take da haske Allah ya sa hakama zuciyarki take, bismillah dan kwonta ki huta" A lokacin ne ta kama hannayen Khadeeja dan ta kwontar da ita, nan ta ji zafin jikinta
Da yannayi
n damuwa ta furta" Subahanallah, jikinta zafi sosai Hajia , zazabi take yi ba?"
Mama FATEEMA ta yi dan murmushi ta ce" Eh tana dan jin jiki ne da tunanin rabuwa da gida, ama alhamdulilah zata ware ne ai"
Hajia Binta ta ce" Aya subahanallah, kaikai ha
ba dai kishiyaty kar mu yi haka mana, Nanma ai gida kika zo, kin ga shareefat tashi je ki gani ki sama mata shayi mai zafi, bari Ni kuwa in je in samu wayata in yi kiran likita, ina na ga ta zama kishiyaty ba lafiya "
Mama FATEEMA dai tana murmushi har
suka fice kafin ta zauna tana duban Khadeeja da ta rufe ido ruff kamar wata tsohuwar makauniya ta ce" Ai sai ki bude idon, dan na kula kamar gam kika mana masa?"
KHADEEJA sai ta zo budewa sai ta mayar ruf ta rufe, murya a raunane ta ce" Mama FATEEMA, id
an na bude ne wani abu da bana son gani nake gani, sai sanyin raba nake ji ko dai ruwan nunar mangwaro muka samu ya daki zanar dakin nawa?"
Mama FATEEMA ta zuba mata ido, sai kuma ta dubi dakin , ta sake kallonta lokaci daya tana tuna cewa Khadeeja fa b
ata da ra'ayin auren mai rufin asiri ma, ta fi son wanda zasu nema a ci tare, A nutse ta ce" A'a a irin wannan lokacin? sanyin ac ne ai"
KHADEEJA ta langwabar da kai a hankali ta ce" Kalu innalilahi , Uhum, Lalalala, Allah innalilahi, to me ya ha
ɗ
a inda
za'a kaini da sanyin ac? Allah ya Allah Safa Safa fa na roka"
Mama FATEEMA ta saka hannu kusan idannuwan na Khadeeja ta dan buga kumatunta, hakan ya sa ta bude ido da suka rine mata tana kallon Mama FATEEMA, lokaci daya kuma ta mike daga zaunen da take
tana kallon dakin , sai kawai ta sakawa Mama fateema kuka tana fadin" Innalilahi shin da na yi addu'ar ban yita a daidai bane ko me yake faruwa? wannan gadon da shirin dakin nan ai na mai karfi ne, mama FATEEMA walahi bana son mai kudi, ina Ni ina auren m
ai kudi?oh shine na ji sun ja sunnansa da layin Elhaji ? kennan su yan zuwa sallah su dawo ne ba yan zuwa Saudiya neman kudi ba? innalilahi wa inna ilaihi raj'une sai da nace Allah ya sa d'an angula ne, mama tashi sahunmu a likafa mu gudu in sanar da baban
gidanmu sai dai ya yi dakan kullin dije da Ni ya matse mai a siyar, ba fa zan zauna a gidan nan ba!"
Mama FATEEMA baki da hanci a bude ta saki tana kallon wace ke lange musu kamar zata summa, wace yanzu haka jikinta zafin tsiya ne da shi, itace ta budi
baki take kora mata hadisin abin mamaki sala sala
Mayafin da ta yane a jikinta ta kar
ɓ
e ta yi mata zama irin na dangwararwar nan, ta dan duko ta nuna mata yatsa a kausashe ta ce" Na rantse zan cire sunnanki gefe, in yafo halin gidan Larabawa in ari na
ubanki in daka ki a dakin nan, Au ni zaki wulakanta, Ni zaki rainawa wayo? ai du balakin ubanki ba zai rabaki da gidan nan ba bale ke biyu biyar!, saurareni da kyau tunda kina cikin hayacinki, ELHAJI AL'WALID na gidan tv ne aka aura maki kuma zama daram,
kina jina Anmy nace zama daram, ki ji da kyau ki kuma bude idannuwanki ki hankalta da kowa a gidan nan, kin san me ake nufi da gidan yawa ai, to ki iya takunki ki rike addu'a, ki girmama na gaba da ke , sannan ki ja mutuncin kanki da darajar kanki, ba a ga
ban kowa zaki saki jiki ki yi fira ba, haka kuma kar wanda ya ringa tsallake falon kasa ana tardoki nan, ki kama girkin mijinki a hannunki, ki kama kula da mijinki, ai ke ba shashasha bace kina gannin yadda mahaifiyarku ke tsaye a kan komai na Babanku, wan
nan kadai ta rike ta ciri tuta ba boka ba malan, biyaya, kula da kai , kula da mijinta kawai ya sa du tsiya mijinta yana ta tata, Anmy zan ringa zuwa, eh dole zan ringa leko ki saboda jinnin Ya'u dake jikinki jinni ne mai karfin gaske dake iya hadasa maki
irin ciwon masu iskokai bayan kalau kike, ga kat nan kin langwabe mana kamar zaki mutu? , ki nutsu kin zo dakinki kennan!"
Ta karashe tana mikewa ta warci mayafinta
Har ta juya ta sake juyowa ta nunota da yatsa ta ce" Ga magungunnanki da alurai, wand
a ya zama lalle ko yi zaki yi, kar ki sha magani da yawa, ga cake dinki a jakar ki, ba kowa zai baki abinci ki ci ba, ki bari ki yarda da mutanen gidan kafin ki ci abin hannun mutane....., zan zo da mai kitso da kunshi gobe in sha Allah saura in tardo ki
da wannan bak'ar rigar da kika ce ita zaki saka da za'a kawo ki dakinki sai kace mai takaba!"
Ta karashe tana sakar mata harara ta yi waje
Ido Anmy ta zarro har Mama FATEEMA ta rufo mata kofar tana ji sunna magana da Hajia Binta, Hajia Binta na tam
bayar jikin nata, sannan ta ce Aunty shareefat tana hado abinci ita zata je ta salami baki sannan ta samu Elhaji karamin saboda likitan da suka samu namiji ne kawai macen wayarta a kashe, idan yace ya shigo ya duba marar lafiyar sai ya shigo kawai
Baki
ta turo a zaunen da take ta rasa wani tunani zata yi
Innalilahi, haka aka yi da ita? Mutumen da ake ƙiyasta kudinsa ba na nema bane na yanka ne? to na yanka mana shi da kansa ya san me ya mallaka kuwa? ita za'a yiwa auren in an tuna da ke a maki trensfer
din gigitatun kudin da zasu hannaki fita daga gidan duk tsiya? ita za'a yiwa auren rufa rufa auren rike daraja dan ace kana da auren? ita Anmy itace Aban Hajia yar ta Larabawa ya yiwa haka?? to kuwa zata yi jiransa ko waye ya bata takarda, ita fa ba da it
a ba auren rikitatun masu kudin nan su hadasa maka hawan jinni da kannanun shekarunka, ita bata ce tana yi ba, bata yi, babu wanda zai yi mata wannan balakin ana zaman kalau. ba'a isa ba!
Jakar da akace Tata ce ta dauka tana dubawa,