Showing 168001 words to 171000 words out of 200647 words
nutse suka wuce
ɓ
angaren Baba hamzan tare
A dakin HAJIA Inna kuwa khadeeja bata saki hannunta ba, haka HAJIA Binta na zaune daf da ita bayan ta gama yi mata kuka da ra
ntsuwar sai ta amshi magani sannan a tausashe ta ce" In dai shi din kike so mu yiwa rikici ai ba da lafiyar ki zaki yi mana wasa ba, ki sha maganinki idan ta kama mu gudu mu buya wani wajen zamu gudu, na san me yake damun ki na san cewa dama akoy ranar da
zaki gaza kawar da kan da kika jima kina yi a kan gaskiyar ki, ki yi hakuri yar uwata"
Khadeeja ta yi mamaki matuka da gannin wannan lamari, dama wai akoy abokan zaman dake yiwa junna magana irin haka har ya zamo furucin bakinsu abin da
ɗ
in sauraro ne sa
boda fitar amonsa dake tafe da kauna da mutunta junna? Ikon Allah, to ai su a gidansu ko su ga ana gaba da junna ko kuwa su jiyo maganganun da suka saka suka gama yarda cewar kishiya masifa ce daga nan ba ragi ba kari, domin har fata suke yi a tsakaninsu c
ewar idan sun yi aure Allah ya sa mazansu ba irin mahaifinsu bane daga su kar ya karra musu wata wace zata fitine su ta hanna musu zaman lafiya a cikin gidan auren su
HAJIA Inna kam ajiyar zuciya take saukewa har doctor ya zo, ta kuwa amince din ya dub
ata sosai sannan ya bata magani bayan ya sake yin nasiha a tausashe wace zata saka hankalinta ya kwonta harma ya yarda ya danka magungunan a hannun khadeeja a lokacin da ya gane cewar likita ce , likitar ma mai baban mukami
Sunna nan tare da ita har ba
rci ya dauke ta bayan ta sha maganin saboda yana saka barci ne, sannan suka gyara mata komai suka fito
A nutse khadeeja ke biye da Mama b, har suka zo baban falon inda suka tardo mutanen gidan du a falon sun yi jigum jigum sunna jira
Murmushi ta yi b
ayan du sun hada baki kan masu tambayar yaya jikin sai masu tambayar ko ta yarda likita ya ganta?
A tausashe HAJIA Binta ta ce" Alhamdulilah, har ta samu barci, ku tashi ku je ku yi shirin sallar nagariba lokaci ya matso , SHAREEFA ke ki zauna min in je
in kimtso in dawo , sannan ki sake ba y'arki magani itama jikinta fa da zafi kuma Please idan na zo sai a rakata
ɓ
angaren ta huta, bai dace tun yau ta hadu da dagawar zuciya irin haka ba"
Du yan matan da samarin gidan suka wuce sunna yiwa HAJIA Inna f
atan samun lafiya aka bar aunty shareefat kadai da khadeeja, wa'inda suka dauro alwallar suma suka gabatar da sallar a nan aunty shareefat na jira HAJIA Binta na zuwa suka mike dan ta raka khadeeja bangaren ta saboda ta huta
A nutse suka koma bangaren n
ata, tana jin irin yadda kaf gidan ke kanshi, suka karasa falo sunna amsa sannu da zuwan da maman baby ke musu ana jere musu abin sha da na ci
A nutse aunty shareefat ta fuskanci khadeeja bayan sun zauna a falonta ta ce" Daughter, Ni in ba dan kin gaji
sosai ba da mun yi magana mai mahimmanci"
Khadeeja da har Muryarta ta yi laushi sosai ta ce" A'a Mama, muna iya yi ban gaji ba"
Aunty shareefat ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" ban san ko idan na fada maki abin nan zaki ga kamar abin bai shaf
e ki ba, ko kuwa ki yi tunanin a kan me zan fada maki? Ni da kaina zan fada maki abinda tunda baba Hamza yayi mana kashedin ko da wasa baya son zancen a gidansa muka haka rami muka birne maganar , wato a yau zan taka dokar nan saboda na fuskanci tabasss z
uwa gaba abin na iya neman fin karfin mu , dan ina tsoron fushin wanda baya fushi, haka kuma ina tsoron maganganun ta saboda gaskiya ta fada, zan sanar maki abinda yake faruwa tsakanin mijinki da mahaifiyarsa da kakansa.....ta yiwu ke ki iya yin wani abu a
kai domin ko ba komai kusancin mace da miji ya fi karfin wasa"
Khadeeja ta sauke ajiyar zuciya tana yiwa Allah godiya da ya sa zata ji abinda take son ji din nan cikin sauki ba tare da ta jigata da neman hanyar da ta dace ta fara bi ba, dan kuwa ta san
i in ba sani din ta yi ba bata da wani abinda zata iya yi, kuma ba'a yi sabon da zata budi baki ta ringa musu tambayoyin nan, shi din da kansa wuni ta yi tana tunanin shin idan har ta nemi shiga lamarin nan ba zai iya taka mata birki mai tsananin gaske ba?
Duba da ko auren su ai na hadi ne bale tace son da yake yi mata ya isa ya sa ya saurareta koda baya so, abu daya ta sani ba gudu ba ja da baya dole sai ta dauki matakin da ya dace a kan lamarin
A tausashe sosai ta ce" Shekarun da suka shige, kusan shek
ara talatin da tara kennan a lokacin da ran baban yayanmu
ɗ
an gidan HAJIA Inna, wanda shine namiji daya tall a cikinmu, har yanzu kuwa da aka yi aura Khaleesat Allah bai kawo wani namijin ba, ........., Khadeeja kin san shakuwa kam dole za'a samu tsakanin
marigayi da baba Hamza, sun shaku sosai da sosai shakuwarsu a bayyane take khadeeja, akoy soyaya mai tsafta da biyayya a lamarin wanda ya sa Baba ke daraja duk wani abu da ya shafi yayanmu....."
A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Kin san jarabawar
bawa babu irin yadda bata zuwa, a lokacin da Allah ya bashi matar aure sai ya jarabeshi da mace mai tsananin kishi, kishin da ya kazanta, kishin da ya wuce gona da iri...saboda khadeeja a lokacin da baiwar Allahn nan ta shigo ahalinmu hatta shakuwar dake t
sakaninmu da shi sai da ta nuna bata san zancen ba, ina hadin mace da namiji duniya ta riga ta rikice kawai idan ya zo sanunsa in baya nan a yi hakuri banda kiraye kirayen waya da bin sawu da nufin ba'a ganshi ba an zo a ganshi ne......wannan lamari ya gig
itamu Daughter am, saboda a lokacin shi daya ne namiji a cikinmu, shine yayanmu kuma ya ja mu a jiki fiye da tunanin ki, Bama kamar Ni, saboda du irin yadda take korata idan na nufi inda suke bana iyawa sai na buya ya fito, idan ya ganni yayi ta masifa , d
an a kaina ya taba yi mata saki daya saboda wani lokaci da ta mareni ta zageni bata san tare da shi muka zo gidan ba ya ji komai ya ga komai"
Ta sake sauke ajiyar zuciya ta ce" shi yasa ake so, ko me bawa zai yi ya ringa sasautawa, domin duk abinda aka
ce za'a zazafa sai an ga ba daidai ba Khadeeja...."
Kwalar dake idannuwanta ta share Muryarta na rawa ta ce" Babu abinda bai tsare mata na zaman duniya ba, ci, sha, sutura , bukatun badangarci na yau da gobe wa'inda suka zamo gishirin zaman rayuwa domin y
ana son matarsa shima, duda irin yadda ta fita a ran iyayenmu mata harda mazan , karshe ta sa Baba ya zuba mata ido saboda fitintinun da ya budi baki wani lokaci yayi mata nunin ta kama kanta, idan aure d'ansa yayi niyar yi zai yi ne, ya zamo a hankali ta
fara yaki da baba ta hanyar kauce duk wani abu da zai hada su, ta dauke duk wani kokari dan girmamawa da samun zuciyar baba, ta sake ninka fitintinunta na tsananin kishinta, ya zamo ta yi da yan gida, ta yi da yan anguwa, ta yi da yan office, duk wani wand
a ya ratsa duniyar mijinta in ba HAJIA Inna bace sai ta nuna cewar mijinta za'a so.....sannu sannu karamin abu har ya giga ya zama katoton da lokaci ya kure har mai aukuwa ta auku....."
Aunty shareefat ta lumshe idannuwanta hawayenta ya tsananta , ta bu
de baki ta ce" Khadeeja, ki kiyayi mugwayen kawaye, ki guji duk wata hanya da za'a ce a bi da karfi a samu biyan bukata, kin ga idan kika rike Allah WALAHI sai dai a daka a bari babu yadda aka isa a yi da ke, kuma bukatunki a wajensa ne kawai zaki samu su
biya cikin salama....., khadeeja muna rayuwar lafiya lafiya yayanmu ya so wata yarinya a lokacin ya so aurenta ko Allah zai sa matarsa ta daina abinda take yi ta nutsu, saboda a lokacin AL'WALED fa shekarunsa shida , ama ta kasa dainawa kuma tun haihuwarsa
Allah bai kawo wani cikin ba, ko shi yasa ta daure ciki yake tafka ba dadin nan?, ke dai magana na fitowa fitina ta tashi, tashin hankali, wulakanci, rikici, duk wani nau'in balaki sai da ta sauke ko an janye maganar, ama aka ki janyewa, karshe sai ta afk
a tashin hankalin bin malamai dan a kade abin domin ita fa abinda ba zata taba yarda da shi ba kennan shine a yi mata kishiya!"
"Khadeeja, kin san irin yadda duniya ta rikice, bale a lokacin sosai yayanmu ke karra samun budi, dukiya kuwa kin san dama ta
na tafe ne hatsari kala kala, a cikin abokan nemansa aka samu wanda ya shiga rigar boka , ya san hanyar da ya bi ya samu yardarta har ya ringa bata karamar gubar da tunda ta fara sakawa yayanmu a abinci ciwo ya sako shi gaba, a hankali a hankali har aka k
wonta, abu ya ki ci, ya ki cinyewa sai karra gaba yake yi, ga wani irin amai da yake yi mai baki baki, hakan ya sa likitoci karkata binciken su kan guba duda baba Hamza ya ja ya tsaya cewar babu rami me ya kawo zancen rami? Domin shi baba din ya hanna yaya
nmu cin abinci a waje, idan ba na hannun matarsa ba to kuwa sai na hannun Hajiya Inna ko mama b, daga su ba'a bashi kowani abinci Daughter am....."
Aunty shareefat ta idasa tana sakin kuka a hankali ta ci gaba da fadin" ashe ba'a isa a zagaye abinda Al
lah ya kadartowa bawansa ba? Ashe shi yayanmu hannun da ake gannin ba zai taba ciyar da shi wani abin ba shine ke bashi guba?, a lokacin da aka tsare abinci in ba na asibiti ba sai wanda ita kadai ta yi ne aka gane, wai ace yana asibitin a kwoncema bata ha
kura da dan tsakura maganin mallakar da boka ya bata ba a zuwan ta malake mijinta sai ita sai duniyarta a duniyarsa?, ashe bata san cewa bokan nan Bama boka bane ba? Rana daya aka gane abinda ke boye, a lokacin ne kuma da aka titsiyeta hankali tashe ta fad
i abinda yake faruwa harma ta warci abincin ta ci tana fadin yaya za'a yi ta bashi guba? Sai dai ita nata karfin jinnin bai kai nasa domin a nan ta yanke jiki ta fadi har sai da ta sha karin ruwaye daban daban ta dawo hayacinta........."
"Khadeeja, tun
daga lokacin KHADEEJA ta fita hayacinta, tun daga wannan lokacin ta idasa firgicewa saboda tashin hankali, ta gaza yarda cewar guba ce take ba yayanmu ba, gashi inda tace take gannin bokan an je komai ba'a samu ba dake nunin an taba rayuwa a wajen, bincike
ake yi ba ji ba gani hakan ya sa ita dinma idannuwan hukuma ke kanta, ga tsangwama da tsana daga wajen mu baki dayanmu, ba'a maganar Baba hamza dan a lokacin da ace ba'a yi da gaske ba sai dai yayi kason ranta......, bamu tana shiga tashin hankali irin na
lokacin ba, KHADEEJA bata ta
ɓ
a shiga tsakanin mutuwa ko rayuwa irin na lokacin ba, kuma ina mai tabbatar maki daga lokacin bata kuma samun nutsuwar zuciya ba har zuwa yau, domin an hannata gannin d'anta, an hannata gannin wanda mu sheda ne so din nan fa t
ana yi masa mai tsananin gaske, ta rasa dama a wajen danginta, sai ya zamo ta shiga tsaka mai wuya mai wutar fasara"
Aunty shareefat ta fuskanci khadeeja da kyau ta ce" kin san me yasa na baki bayanin nan tun daga farkon sa?"
Khadeeja ta girgiza kai
tana duban aunty
Aunty shareefat ta ce" saboda ki fahimceni da kyau, domin saura kwanaki biyar yayanmu ya bar duniya Allah ya bashi sauki irin sauƙin da yawanci masu jinya ke samu idan lokacin tafiyar ya matso, domin har zaunar da shi aka yi, ya sha ma
darar da baba ke bashi da kansa, a lokacin gana dayanmu muna dakin nan, a gabanmu ya nemi izinin baba ya bashi dama ya ga matarsa, da baba ya kiya ne yayi furucin da ya sa Baba dubansa ya kasa magana, har HAJIA Inna ta je da kanta ta janyo hannun Khadeeja
ta kawo ta dakin, a gabanmu bayan ta duka gabansa tana kuka ta sanar masa komai da yanayin mutumen nan ya lumshe idannuwansa a sanyaye yayi mata nasiha sosai da sosai , khadeeja a gabanmu ya mika mata hannu ta je inda yake ya rike hannayen ta ya janyota ji
kinsa , a gabanmu ya furta mata kalmar yafiya, shima ya nemi tata yafiyar, khadeeja ya yafe mata laifin da aka bi ta kanta aka aikata, kuma ya fadi sunan mutumen wanda har yanzu yake rufe a gidan kaso, khadeeja tun daga lokacin matarsa ke gefen sa, du irin
fushin da baba ke ciki bai iya hannawa ba, saboda a hankali jikin ya karra rikicewa lokaci ya tafi har mai aukuwa ta auku....., yayanmu ya rasu..., rasuwar da ta kasa fita daga ran Baba, saboda a lokacin da aka kai yayanmu gida bayan matarsa ta farfa
ɗ
o ka
mar zata yi hauka tana kuka kamar ranta zai fita, a lokacin ne kuma baba Hamza ya yi mata iyaka da gawar mijinta, tana ji tana ganni aka tafi da mijinta gidan gaskiya, bayan an yi kwana uku tana zaune a falo zata ba AL'WALED abinci baba ya shigo falon ya k
wabe abincin, a lokacin ne ya yanke mata hukuncin da ya shiga tsakaninta da d'anta"
"Daughter am, a lokacin ne baba ya sanar da ita ba ita ba abinda ta haifa da cikinta, a lokacin ne ya raba hannayensu, ya nuna mata kofa bayan ya kwashi takardun dukiy
ar mijinta kaf ya watsa mata , ya sanar da ita bata da wani muhalli a duniyarsa da ta jikansa, A ranar ne kuma aka kamata , aka saka mata ankwa aka kai aka garkame, bayan doguwar Shari'a aka yanke mata hukuncin kaso na shekara goma sha takwassss da diyar
dukiya , shi kuwa wanda ya bata abin aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai..........."
Aunty shareefat ta dubi khadeeja da hawaye ke bin kumatunta a sanyaye ta ce" KHADEEJA, tabbas maganar HAJIA Inna gaskiya ce, idan aka yi wasa wace ake yiwa jifan
mai laifi na iya tsira mararsa laifin su fada halaka HAKANE....., mu yi aiki da ilimin mu da addininmu, hukuncin baba a tsakanin uwa da d'an nan yayi tsaurin gaske...., an san cewa ita ta raba shi da nasa d'an, an san cewa nasa d'an itace silar barinsa dun
iya, ama kuma daga wannan sai wane?, ita nata d'an yana raye kuma Allah ya umarce shi da ya yi mata biyayya, shin idan wai aka rasu a haka me za'a cewa Allah?"
Khadeeja ta sada kanta, shikenan gaba daya zuciyarta ta idasa fita a nutsuwarta...., kuka t
ake yi sosai domin du lamarin nan ya gama firgitata
A hankali aunty shareefat ta ce" ki yi hakuri Daughter am dan Allah ki yi hakuri kin ji?, na fada maki ne saboda ki taya mu, ta yiwu ke ki iya, walahi ba zan so mutun mai daraja irin tasa da tarin alk
hairai ya afka tasku sanadiyar fushin kakansa ba, lokaci kuwa ba shi yake jira ba, ba kakansa yake jira ba"
A sanyaye khadeeja ta ce" Mama, ta yaya zan iya taimakawar? Mama kuma da kuke tare da shi tun yana yaro baku iya cenza wani abin ba Ni da na sh
igo rayuwarsa kwana uku kawai anya zan iya yin wani abu?"
Aunty shareefat zata yi magana aka bude kofar baban falon ya dano kai a nutse da waya a kunnensa yana amsa kira , sannan ya dakata ganninsu a falo ya juya ya amshi sakon da aka riko masa da hannu
nsa ya yi alamun a juya sannan ya karaso lokacin da suka mike daga auntyn har ita a nutse ta furta" Barka da shigowa, "
Sai kuma ta kalli aunty ta ce" A huta gajiya Mama, sai na shigo"
Daga haka ta juya a nutse ta shiga haurawa
Rakata yayi da ido
a hankali ya kalli aunty shareefat wace ke kallonsa kasa kasa ya ce" inaga ko tsawa ce na yi mata dazun nan? Fushi dai ne Hajiya karama ke yi da ni maman AL'WALED "
Aunty shareefat ta yi murmushi ta ce" Amaryar ake yiwa tsawa yaron shareefat? Ka yi gag
gawar neman kanka big son"
Murmushi ya yi yana shafa kansa ya ce" Dama yanzu na ajiye kakan kurma, ya Salam kakan kurma gidan rigima, da kyar suka hakura shi da baban nasa kamar an musu laifi, kuma muna zuwa gidan muka tarar da wani saurayi ya zo , sai
da ya bani tausayi ya duka yana kuka yana bashi hakuri wai yana son yarinyar wajensa, kakan kurma cewa yayi ina shi ina ba mai jan ido y'a? Hum nadai yiwa yaron alkawarin idan na yi bincike na ga nagartarsa zan bashi ita"
Aunty shareefat ta saka dariya
tana tafa hannu ta ce" wai baka san waye