Showing 12001 words to 15000 words out of 200647 words

Chapter 5 - Farkon-Ganin-Idona-Book-Compeletex

08 Sep 2026

16

Ki yi hakuri mama, dan Allah ki yi hakuri ba zan kuma ba"

Hajia dake kallon yannayinta a tausashe ta ce" Zo nan"

Mikewa ta yi ta je ta zauna daf da ita sosai

Ta zuba mata ido, kalaman bakin Khadija tamkar ba

na shekarunta ba, lamarin nan na bata tsoro lokuta da dama, harta girman jikinta ba na shekarunta bane haka kalaman bakinta, tana da zafi Khadija, tana da fada, shi yasa take son zama a gefenta dan ta ganar da ita baki da fari ta kuma tabatar mata rayuwar

yau fa haka ta gada, koda Allah zai hadata da mai baudaden hali ta yi ibada da zuciya daya sai idan ya gagara ne zata dubeta, domin ita ta yiwa kanta alkawarin in sha Allah ba zata tafiyar da y'arta irin yadda Hajiar Larabawa ta tafiyar da ita ba, idan za

i yiwu a yi, in ba zai yiwu ba kuwa a hakura ne saboda rai daya ne jal, daga bakin lokacin da ba zai anfani mai shi ba bashi da wani anfani.

A tausashe ta yi mata nasihar da ta saba yi mata sannan ta umarceta da ta je ta shirya zuwa makaranta kar su yi la

ti, idan direba ya fito kuma wasu basu fito ba ba zai yi jiran kowa ba tafiya zai yi hakan kuma na nufin wani tashin hankalin a wajen Elhaji.

Sai da Yaren suka tafi kaf dinsu sannan ta koma dakinta a nutse ta kwonta, sai a lokacin zafin magangannunsa su

ka karra kona mata zuciya, ta tashi ta yi zaune abin na tukarta

Firgit ta mike ta fito, tana daf da nufar hanyar da zata kaita inda yake ya shigo dauke da jakar kudinsa , dama dakinta zai je ya karra gannin jikinta sannan ya wuce, bayansa kuwa jelar tasa

ke biye da shi

Tsayawa yayi yana kallon yannayinta , dan kuwa fuskarta a hade take sosai ta dube shi cikin idoda tarin balaki ta ce" Kana tunanin zaune da nake a gidanka saboda wani abin ne? soyaya ko kudin da kake gannin ka take su zaka take wanda ka

ga dama a lokacin da ka ga dama? Kana tunanin idan ka sakeni ba zan rayu ba? a yanzu da Ni nawa sawun ya kai inda ba zan moru ba ai ba namiji ke gabana ba ka san da haka, a haka har ake mangarina a waje? a haka har ake zagina da kalaman na malakeka kana ta

auri saki kafina, haka kuma bayana sai aurowa kake yi kana saki Ni ce ka ki saki dan na malakeka? Allah ka jarabi du wace ke burin shigowa gidan nan ta zo ta maye gurbina, ina kuma dakon ranar da zaka sakeni, dan walahi na saku har gaban abada! "

Ido y

a dan zarro yana kallonta kafin yace" to yanzu kuma me aka yi zaki min rashin kunya? sai kace kamar wace lafiyarki kalau walahi, ke da baki da lafiya kike fada kina dagawa aljanarki murya me aka yi ne gimbiya waye ya bata maki rai kuma?"

Takaici ya sha

ke mata wuya, so ta yi ya maimaita maganarsa ta dazu wa bilahilazi ta nuna masa itama danyan kai ce, rai bace ta ce" Ko me kake tunani a kai ka maida hankali, akoy ranar kin dilaci, idan kana abinka kuma ka guji idannuwan yaran ka dan ina mai tabbatar maka

idan girmanka da mutuncinka ya idasa zubewa a idannuwansu ka kade,, Wadinnan din da kake gannin ba komai bane sunne gatanka, walahi sunne gatanka dan ko Ni ban jin zan iya da kayan tsufa! idan kuwa ka yi wasa su zasu fitineka su fitini duniyar ka, babu ar

zikin da ya kai maka su a duniya, ka dage ka kakarya su daya bayan daya , anan zaka gane su ba gado bane da za'a kawo kafinta ya gyara ba, a nan kuma zaka gane madara suke idan fa suka zube walahi ba zasu kwasu da dadi ba, igiyar aurena kuma in yau kake

son tsinkewa ka bani dalilin da za'a bani damar yin zawarci a gidanmu ka ga in zan sake second daya a wannan bakin gidan!"

Rai bace ta juya ta shige dakinta ta mako kofar ta dana ky, dan kuwa ta sani ne ta gama ha

ษ—

a masa damuwar da zata hanna shi wuni

cikin dadin rai a yau, dan a duniya a yi du abinda za'a yi ama kar ta alakanta kanta da zawarci, cewa yake yi ina wane mutun shi ko mutuwa yayi babu mai aurar masa mata, kuma a kanta kadai yake wannan balakin dan kuwa sauran ai ya sake su sun je sun auri w

asu, yakan ce macen gado arzikin mai kudi ce gimbiya a nan ya dasa aya.

Ai kuwa balaki ya zuba yana huci har sai da amarya ta yi data Sannin biyo bayansa, domin a kanta abin ya kare ya mata tatas har yana fadin tana kallo gimbiya ke masa haka ko? ta yi

tsuru tsuru cike da jin haushin Hajia dan kuwa da bata yi ba da ba zai yi haka ba, kuma a yau ta karra yarda kwarai Hajia nada iko da mulki a fadarsa ta yadda shi din da kansa bai yarda ba ama kuma take gigita duniyarsa, a haka dai ya shige motarsa ya fice

a gidan ya nufi baban anguwar da tankamemen shagonsa yake, wato anguwar dake bayan gidansa, wace ake yiwa lakabi da jeune cadre, Anguwar masu ku

ษ—

i kennan

Da ya je tuni an jima da bude shago ana ta shigi da fice

Tun a kofar shagon yaran shagon suka gan

e yauma uban gidansu a hasale ya zo, har a lokacin da mai kosai ta karaso tana gaishe shi dan amsar kudin kosai da take yi masa sadaka kulun ta ce" Mijin kurma Barka da safiya"

Bai amsata ba ya bata kudin sadakar da ake yi ya shigewarsa shagon ya wuce fu

uuuuuuuuuuuuu bai ko dubi mutumen nasa ba, uban gidansa kuma abokin shawararsa ba wato Elhaji Hamza mai masalaci ya wuce cen office dinsa ya bude ya shiga ya mako kofar office din

Elhaji Hamza ya yi yar dariya bayan ya ga yannayin mutumen nasa, abokin

rikicinsa, abokin firarsa, wanda yake tsagawa gaskiya ya fadawa su yi sama su yi kasa sai dai bashi da bakin da zai ce da shi Ni mai kudi zaka wulakanta ? ko Ni mai kudi zaka kawowa raini? dan ya riga ya sani cewar a nan ne kudin ke magana, shi lalube yake

yi a inda aka samu, ya kuma gama yarda cewar GABA DA GABANTA

Mikewa yayi da kyar saboda jikin tsufa domin Elhaji Hamza ya ba shekara tamanin baya, danma tsufa ne na gata ana samun dukkan kulawar da ta dace, ya dubi samarin dake ta aiki a shagon bangare

n cafet da labulaye ya yafito Yusuf,

Yana zuwa a tausashe ya ce" Ka cewa mai kosai ta nadewa bebe direbanta zai zo ya kai mata makaranta tace yau shi zata ci a break"

Ya karra dan dukawa ya amsa sannan ya fice ya tafi dan isar da sakon,

Bebe jika

r jika ce a wajen Elhajin, y'a a wajen Baban d'an d'ansa da ya rasu , wace ya rike a wajensa tunda mahaifiyarta ta rasu itama, itace ake ce mata matar Elhaji mai komai dozin saboda takan zo ta zauna wajensa ta wuni baya korarta baya kyararta, yarinya ce so

sai dan ba zata wuce 9yrs ba , nakasunta ya sa take da wahalar sabo da mutane, ama kuma sai ta saba da wuri da Elhaji dan wasu tunani suke jikarsa ce idan suka zo siyaya shagon, irin yadda in yana filin shafin a zaune ita kuwa tana gefe zaune saman kujera

rike da ipad dinta tana buga game tana dagowa tana masa Yaren kurame yana bata amsa tana ci gaba da wasanta da wayarta dan itama tana da dan hasken fata kadan na mahaifinta

Kai tsaye ya bude office din ya shiga ya tarar da Elhaji ya bude katon litafi ya

na ta rubutu kamar wanda ya san me yake rubutawa irin bugagun yan bokon nan , bayan bai je boko

Karasawa yayi ya leka litafin , sai ya ga da larabci ne yake yin rubutun sai yayi yar dariya ya zauna yana fadin" Na zata ai da freinch kake rubutun Elhaji

da ince yau ko aljannu suka hayo kanka suke rubuta mana balakin da ba zamu gane ba?"

Elhaji ya tabe baki kamar ba zai amsa shi ba sai kuma ya dakata ya dago yana dubansa ya ce" dadin abin da yare mafi daraja nake yi wanda zai anfaneni har a kiyama ba na

yahudu ba, freinch ai takamar wa'inda suka ba yahudu gaskiya ne ba mu na Annabi ba (S.A.W)"

Baba tsoho ya kama baki ya dan zarro ido sai kuma yayi dariya yana tafa hannu ya ce" Hakane kuma walahi, dadin abin nima ina takama da shi, kuma ai neman ilimi

ba haramun bane, hasalima Allah baya son wanda baya zuwa neman ilimi"

Baba ya tabe baki yana kada kafa ya ki ce masa uffan

Sai da baba tsoho ya sake dan bubuga sandarsa ya ce" Magana da na zo mu yi kuma ka sani sarai kake basarwa"

Baba ya dago yan

a duban gefensa ya ce" Kai innalilahi, wai kai me muka hada da kai fisabililahi da zaka galabeni? gaskiya Ni an isheni"

Elhaji Hamza ya ce" Anguwa daya mana kakan kurma"

Baba yayi dan murmushi ya ce" Na fa hanna ana ce mata kurma ba kurma bace tana j

i mayarwa ne bata yi"

shima baba tsoho yayi dariyar yannayin Elhajin , kwarai ya sani gamon jini daga Allah ne, ko dan ya nunawa kurma ga kakanta nan ne ya sa itama ke masa kallon wajen da zata zo ta yi firarta kai tsaye? haka shima yake jin yarinyar ta

mkar jikarsa ta cikinsa?

Da kula Elhaji Hamza ya ce" to ai na ga yau ba mutunci ka ga gwara na idasa hasalaka in yaso yau ka daukeni ka wurgar ka huta "

Baba ya dafe haba ya ce" ka rufa min asiri in wurgaka in bi ina in gudu? kai dai kawai dai ka je d

a halinka ama sam baka da hali mai kyau ya zamo mutun sai neman fitina wa salihan bayi? in ka zagar min jika dadi zaka ji a ranka hala?"

Baba Hamza yayi dariya sosai sannan ya nutsu ya fuskanci Baba a tausashe cike da nunin kwarai maganar da yake da it

a tana taba zuciyarsa ya ce" Maganar da na fara yi maka ne, da gaske ina kanta kuma wannan zuwan nake so idan ya zo a yi a gama, shekara takwas ba kwana takwas bane, ka ga bai fi wata ya rage masa ya dawo ba, ina so da zarar ya dawo su fuskanci junna a yi,

dan ba zan taba so ya fara auren yarinyar nan da suke tare ba, inada baban dalilin da ba zan so ya fara aurenta a yanzu ba, idan yana so bayan an yi da wannan da kamar wata ya aurota"

Baba na kallonsa ya ce" Ama ka san ba'a matsawa namiji a kan maganar

aure ko? ka barshi ya dauki wace ya zaba , bale namiji mai dukiya irin wannan idan an matsa masa da maganar aure ai ka ga yana iya yi din ya jingine matar"

Elhaji Hamza ya fitar da numfashi a hankali ya ce" Na sani, sai dai Ni na san dalilina mai karfi

n da zan tirsasa a min biyaya ne, kuma ai ba mazaunin ketare bane, yana zuwa ya dawo ne, in dai da raina ba zai jingine auren daraja ba. ba zan hanna shi aurenta ba, ama kuma dole nima ya amshi nawa tayin , kai ka san idan har mace uwar gida aka samu ta ba

nza an kade, komai ba zai kuma yin albarka ba, matarsa uwar y'arsa ta rasu, tunda ta rasu nake cikin tsoron abinda ke iya zuwa ya dawo, ba dan ina zargin wani da wani abu ba, sai dan irin yadda a yanzu haka ake daukan ba dadi saboda dan abinda bai taka kar

a ya karya na dukiyarsa dake ฦ™arฦ™ashina ba, Elhaji ina gudun duniya ina gudun dukiya da mata, rayuwa kuwa rai akoy mutu akoy, zafin zuciyarsa ke bani tsoro, shi yasa nake yi masa wannan kwadayin"

Baba ya ce" Dukiya abar gudu abar nema, dan Allah ina mah

aifiyarsa ne shi?"

Elhaji Hamza ya dube shi, ya Basar ya ki bashi amsa, dan idan har zai irga ya masa tambayar mahaifiyar yaron nan ya fi a irga bai bashi amsa ba, ama dan fitina irin ta mutumen nan in dai sa yi maganarsa sai ya tambaye shi.

Baba ya d

ube shi da kyau yayi murmushin kyale shin da yayi a tausashe shima ya ce" Elhaji, wai dama da gaske kake ? walahi na zata kawai dai ka fada ne duba da su manyan mutanen nan ka ga ba'a musu haka ko?" ya sake yin tambayar kamar bai gane me ake nufi ba, kamar

baya gane yaran Elhaji Hamza, shi kuwa so yake yi sai ya tabbatar masa da shi ya nema, dan idan ya bashi ya gane ba zai iya kyale wanda ya wulakanta masa y'a ba komai kudinsa walahi

Elhaji ya dube shi da mamaki ya ce" Dama a maganar aure akoy wasa a ci

ki ne? manyan mutane to Ni ina ruwana da kasantuwarsa baban mutun a dukiya? du girmansa ta kai Ni da na haifi ubansa ne? tun yana zanin goyo ubansa ya bar duniya, maganar mahaifiyarsa kuma kai ka san me ake ciki ba sai na maimaita ba, idan yau zai dubeni y

a ki wannan maganar bayan a cikin

Musulunci ba kaka nake a gare shi ba ubansa nake sai yayi in gani, ba ruwana da maganar wai girmansa a duniya, Ni Nine ubansa!"

Baba ya gyada kai ya ce" Kuma hakane ya baba, cabdijan, Ni yanzu ai har tsoro ya fara kaman

i, to fisabililahi in y'ata ta aure shi sai a biyo dare a kasheni a yi tunanin na yi kudin nima"

Elhaji ya zuba masa ido yana kallonsa dan lamarin nasa fin karfinsa yake yi

Baba ya dora da fadin", hum koda yake ba komai yanzu a cikinsu Wacece kace El

haji? sai in sake zage dantse ta karra nutsuwa, koda yake ai Ni din akoy bada tarbiya " ya wani karashe yana murmushi irin ga baba din nan

Elhaji Hamza ya dafe goshi, kai takaici zai kunsa masa ne ? wai wani a bi dare a kashe shi, koda yake haka duniyar

ta koma yanzu Allah ya kyauta

Yana dubansa yace" Kar ka yiwa kowa komai, kana tunanin idan ina da shaka a lamarin iyalinka zan nemi hada iri ne? Ni na yarda da tarbiyyar iyalinka na kuma yarda da kowace aka bamu, kar ka tsaurarawa kowace, sai dai kamar

yadda na fada maka bana so a san shi din ne, ina so ita da kanta ta yarda har zuciyarta a yannayin da zai zo mata, idan ta amince shikenan na amince har zuciyata dan Allah ka min wannan alfarmar"

Baba ya gyada kai yana rufe littafinsa, a tausashe yace"

In sha Allah, za'a yi, ina fatan Allah ya sanya alkhairi, idan Allah ya kawo shi kuka gama maganar sai a fada min, in sha Allah sai a hada shi da Karima saboda ita shekarunta suka kai, ba dan sauran basu kai ba, a'a ta dai fi su girma ne da dan watani"

Elhaji Hamza ya ringa godiya har sai da baba ya dakatar da shi yana nuna masa ya bari mana haba dai, Allah dai ya tabbatar musu da alkhairi,a ransa kuwa yana tunanin eh lalle shi kam ya zo duniya a Sa'a, idan y'arsa ta auri Elhaji Al_Walid sun haye, hayew

a ta koluluwa ba ta wasan yaro ba, cabdijan.......

Da wannan dai suka yi zamansu su yi fada su shirya har lokacin sallah yayi, dama idan suka je masallaci daga nan Elhaji Hamza ke shigewa gida kuma sai da yama in ya fito sallar la'asar yake sake zuwa wa

jen Elhaji , amincin nan nasu na ba mutane mamaki, sosai mutane ke mamaki, domin kuwa lamarin Elhaji sai mai hakuri , kuma kowa ya san irin zaman nasu Yawancin lokuta ma Elhaji Hamza ke jansa da rigima su yi abinsu su gama da an jima ka ga daya ya leko nem

an daya, Duda nisan shekarunsu bai hanna su zumunci mai karfi kamar wasu abokai ba, kowane ya yi waje mai girma ya ajiye dan uwansa, shi Elhaji Hamza tunda ya rasa yaronsa bai ji shi da karfi ba sai da ya hadu da Elhaji, du kuma halayansa da ake kadawa bas

u hanna shi zumunci mai karfi da shi ba, tabas da d'ansa na raye da zasu kai shekaru daya da Elhaji, shi yasa idan ya kalle shi yake jin wani sanyi a zuciyarsa

07/12/2024, 14:40 - samiraharounayacouba:

๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ

*FARKON GANIN ID

ONA*

๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ

*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช

*PAID BOOK*

*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAG

ERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you

๐Ÿ˜

*



LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA

Y'AR MAHAUKACIYA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login