Showing 195001 words to 198000 words out of 200647 words

Chapter 66 - Farkon-Ganin-Idona-Book-Compeletex

08 Sep 2026

66

da suka dauka zasu kula da ita sati biyu ne, bayan sati biyun zasu ga idan zasu karra wani lokacin ko zasu salameta daga haka, daga nan su kuwa suka shiga yawace yawacensu kasashen waje dan shakata

wa da yayada manufa ta sati biyu kacal saboda tuni sun cinye sati dayan a Saudiya

Sati biyun nan sun yi shi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, sati biyun da ya sa suka sake shakuwa da junna fiye da tunani, domin ko waya zata yi da gida ta whatsup da

lokacin da take yi, haka idan suka yi kiran gida suka yi fira da baba Hamza da su Hajiya , sannan ta tatauna da likitar da ta kawo da kanta wace ke kula da lafiyar Hajiya kafin ta dawo shima da lokacin da suke yin call din nan sunna gamawa suke kashe wayo

yin su koma ibada mai zaman kanta mai daraja wace ta ringa saukar mata da zazza

Ι“

i kala kala da sirfa iri iri wace ke karra tabbatar masa da zancen mama shareefat harma ya ji hankalinsa ya sake kwonciya cike da zumudin irgen kwanaki a zuciyarsa tare da Bint

a da addu'ar samun lafiya

A lokacin da wa'adin lokacin da suka diba ya cika na lafiyar mama Khadeeja Hajiya zainab ce ta zo ta dauketa suka juya saboda shi ogan basu gama nasu hutun ba, sai waya da yayi da likitar ta tabbatar masa cewa alhamdulilah jiki

da sauki, a hankali a hankali ana iya samun abinda ake so, dumumuwan nan babu yanzu, idan aka ci gaba da kiyaye dukkan abinda akace in sha Allah zata samu sauki sosai, magungunanta na tsayin wata uku ne, tana gama shanyewa a dawo da ita su karra dubata su

gani.... Hankalinsa ya karra kwonci a lokacin da suke yin waya da ita ya zamo bata ringa rigimar ya zo ya zo ba kamar yadda take yi da farko farkon baro ta da yayi ba.

Cikin ikon Allah duka gama hutunsu suka juyo gida, a nan kuma anmy ta shiga cikin

lamarin laulayi sosai da sosai wanda a dole aka bata hutu a makarantar saboda ita kam tana da laulayi har sai da kowa ya ringa tausaya mata , hatta yan uwanta da suke gidajensu bini bini sun lekota, Lubna ce kawai dake wani garin sai dai su yi VIDIO callll

A cikin wannan tsannin na watanni hudu kafin cikinta yayi kwari ta ga soyaya da kula daga wajen AL'WALED da danginsa baki daya dukkan lalurar laulayinta sunna tare da ita sunna nan nan da ita....., a kullum Aba zai miko mata kosai da koko da take sha

harda rubutun addu'a na samun lafiya, baba Hamza kuwa zai shigo mata da guzurin aya ne, da sauransu harda goro na tashin zuciya ......, mijinta kuwa hannayensa a bude suke har ya zamo ta rasa bakin magana sai dai kawai ta rungume shi a jikinta ta yi ta sa

uke ajiyar zuciya, Uwa uba kakaninsa da iyayensa kanana a zo kan mama Khadeeja wace bini bini zata leko ta ga jikin KHADEEJA saboda halin galabaita da take ciki ya Hanna mata zuwa ta leko su sai in ta gaji da dakunan ta

Ι—

ora masa rigimar ita zata je ne san

nan yake yarda ta lalaba su je ita da kurma wajen Hajiya Inna su zauna su yi mata fira daga nan su leka sauran da kuma mama Khadeeja, har yayi kwari ta fara samun Ζ™arfi, inda shekarar karatunta ya zamo sai dai wata shekarar ta sake saboda wata hudu cirrr t

a yi ba a aji ba, karatun likita kuwa ya fi karfin ka tsallake ranaku ka ce zaka ci gaba da ganewa........

Kwonci tashi kayan Allah

Kwonci tashi mai cinye kwanaki....., an wayi gari Mama ta sauka lafiya a asibiti , ta samu baby boy dinta,

wanda suka yi tafiyar su asibiti asirinsu rufe ita da kanwarta ta haihu suka kunso abinsu suka dawo sannan ta yi kiran Aba ta sanar masa, domin nakudar bayan sallar asubahi ta sakota gaba, ta rufe bakinta Allah ya taimaketa har ya bar gidan bata nuna ba, s

ai kusan karfe daya na rana ta nuna , saima da ta kama hanya ta sanarwar mama fateema suka hade a asibitin.....komai ya kankama ta samu lafiya, harma ta yi awa hudu bisa kulawar likitoci sannan suka dawo gida ne ta sanar masa a lokacin kuwa yama ta yi sun

baza tabarmu a kofar shago sunna tattaunawa, aba na sauraron baba Hamza dake fadan ya dawo da matarsa sintirinta ita da iyayenta ya ishe shi hakanan, Gimbiya da kanta sau uku tana masa zancen, idan ma horo ne ya isa hakanan, shi kuwa ya wani dauke kai ya b

ashi keya yana kada kafa, a lokacin al Walid ya karaso majalisar ya zauna shima saboda har sun saba da zaman yamar nan, in dai sunna gari to kuwa da shi ake yinsa shima, shine kira ya shigo ya kuwa daga yana murmushi ya ce" Gimbiya sarautar mata, Gimbiya m

ai Ni , ya aka yi? Yanzu ubana ke batun in maki kishiya danma na bijire masa.....ya aka yi ko in zo?"

AL'WALED ya sunne kai kawai yana murmushi a lokacin da kukan jariri ya karade wajen saboda handsfree da ya maka

Ido ya zarro ya ciro wayar yana duba

wa ya ce" Ke yanzu asibitin kika je bayan su da kansu sun ce an baki juyin haihuwa? Haba Gimbiya wai menenene Ni kike so mu yi balaki iyeah? Kina jan kafa da kyar kika je amsar haihuwar wata idan ta daka maki kafa a rumbu kuma ace min me????"

Mama ta yi

murmushi a tausashe ta ce" Ka dai ga kawai idan ka tashi sai ka zo gida, na sauka fa"

Baba Hamza ya dan zarro ido, hakama Aba, AL'WALED kuwa ya dago da sauri , dan kuwa bayanin cikin Gimbiya ai aba ya gama sanar da suruki sala sala

Aba ya ce" Daga i

na kika sauko din? Innalilahi kar dai ace haihuwa kika yi Gimbiya? Na shiga uku wannan kukan ai na gardi ne, wai Gimbiya kin haihu? Namiji????"

Mama fateema na dariya ta karbi wayar saboda mama sai murmushi kawai take yi abinta ta karra a kunne ta ce"

😫

Yana mana bankwana ka dai yafe mana

😁😁😁😁

farkon gannin idona

😍😍😍😍

54.......

07/12/2024, 17:39 - samiraharounayacouba: Ta ce" Wallahi yaya ta sauka gamu a gida, gayanan boy yana ta tsala kuka wai wanka Hajiya iya ke ma

sa"

Aba ya yi wuuuuuu ya zabura yana fadin" La'ila ha ilalahu, kai Gimbiya an yi yar bakin ciki yanzu bata bari na Kaita ba?, hahaha Baba Hamza ta sama min? Allah ya miki albarka Gimbiya kin haifo min ubana, ganinan zuwa gidan dama na san abinda ke ciki

n nan dan ubansa namiji ne"

Baba Hamza baki har kunne faman fadin alhamdulilah yake yi shima yana kokarin tashi, AL'WALED kuma sai murmushi yake yi yana kallon su

Baba Hamza ya ce" Mun tafi sai yadda ta yiwu kuma"

AL'WALED yayi dariya yana girgiz

a kai ya furta" Allah ya raya mana, zan zo in dauke ka da dare ko?"

Baba Hamza ya ce" In sha Allah, bari in je in ga takwara, ka sanar da yan gidan "

Shi dai yana kallo , ba ya Hanna aba tuka su ba yau aba ya fitar masa da lasisin tukinsa ya masa kar

atu sala sala, sai kawai ya bi su da adu'a ya ci gaba da jiran sallar magariba, yana burin ya shige ya sanar da tasa mai tsohuwar ajiyar itama dan ya ga murnarta, a yanzu take da wata bakwai Ama Tata ajiyar ma ta turo sosai ana nan ana ja sai fatan rabuwa

lafiya, yanzu haka sunna nan ita da y'ar sunna soye soyen yama ......, wani murmushin ya saki, idan ya tuna irin yadda yanzu litle ke farin cikin kasancewar Khadeeja mamanta farin ciki da kwanciyar hankali ke mamaye kirjinsa, ko watan da ya wuce sai da ta

kaita wajen kakarta ta wajen uwa ta sanar masa da sunna callll, sannan ta nuna normal ne ta yi haka a matsayinta na uwa a wajen kurma, tana da yancin daukan dΓ©cision din da ta dace da y'arta in har ba zata cutar da ita ba, sannan ta nuna cewa kwana biyu za

ta yi, zata je ta dauko abinta, sai kawai ya bita da kallo irin yadda ta wani daure fuska ta dauke kai........Anmy....... Khadeeja.......kwarai yana tare da mace daya tamkar dubu.................. Allah ya karra lafiya .

Bayan sallar magariba ya shigar

musu da wannan abin farin cikin wanda ya sa Khadeeja ta nemi daka tsalle abinta na murna sai da mama khadeeja ta yi gaggawar rikota tana dariya ta ce" ki rufa min asiri takwara ke yanzu ai idan murna ta wuce ta dariya daga zaune a yi hakuri a yafe maki it

a"

Hajiya Inna me zata yi banda dariya a hankali tana dan motsa kaffafuwanta da sandunnanta biyu, dama motsin ne suke yi na dole wanda idan ba'a yi ba Anmy bata bata lafiya shi yasa itama da ta ga lokacin a motsa jikin yayi sai ta yi iya yinta su shiga

motsawar kuma cikin ikon Allah kullum karra gannin sauki ake yi

AL'WALED ya zauna saman kujera yana murmushi , kurma ta zauna daf da shi tana sake tambayar a ina ne wai aka samu babyn? , yana murmushi ya kwatanta mata cewar ai kakarta mai kiranta kishiy

ale ce ta kawo baby....., ai kuwa yarinya ta wuce bangarensu tuni bayan ta sanar cewa ita kam zata hada kayanta sai gidan kakan kurma

Al' Walid ya mike yana fadin " Anmyn litle dauko hijabinki mu je mu dauko baba sannan mu gano baby, idan ya so kwa je

ku wuni gobe in sha Allah"

Sosai kurma ta

Ι—

ora musu rigimar ita fa sai ta je da kaya, da kyar suka mata wayo ta dauki kala biyu suka kama hanyar gidan Aba

Da suka karaso sun samu samarin gidan a kofar gida sunna firarsu da dariya sama sama

Saukow

ar kurma ya sa habubakar sakin murmushi ya mika mata hannu yana fadin" Ga y'ar Habu ta iso, zo nan yarinyana, "

Muhammad yayi dariya ya ce" wallahi Sadik sai son girman tsiya, idan ya ga amu ya ringa wani budewa shi mai y'a, Ni so nake yi a bamu ita, ka

ga fa yanzu gidan nan ba mace itama mama maimakun ta karro mana wace zata maye gurbin su Anmy sai ta karro mana gardi , mu KENNAN babu mai mana sangarta a gida du yah baba ya kawar da su? Allah ni ina son girl"

Sidik ya tabe baki ya mike yana rike da h

annun litle dake faman ihun wai an kawo baby? Ita fa ta kauro gidan nan tunda an kawo baby, ya ce" ai sai ka yi, abinda auren kawai dai sunnan an kai su ne, ita wannan bini bini an kawota, ita Karima dama ta auri mijin tace dan iskanci lokacin da ta yi niy

a zai kawota ta ga babarta, ita Ummi ai ta fi uban kowa kaniya saboda rainon cikin a nan take yi , Lubna kanta in ba dan aba ya bi su da gudu ba kai ka san da kullum tana kan hanyar Nijar to Nijeriya, shine zaka ce basa nan? Ni ai kallonsu nake yi ina shir

yawa saboda idan na yi aure babu y'ar da zata mayar da Ni mijin Hajiya!"

Wuce su Khadeeja ta yi da gaggawa ta fara shigewa falon zata wuce ciki tana tura tulun cikinta

Aba ya kalli baba Hamza da sauri ya kalli inda ta wuce din, kasa kasa ya ce" Ji y'

ar nan yadda take tafe da kadarar mutane, ya dace in ci ubanta yau"

Baba Hamza ya girgiza masa kai yana sake rungume jariri ya ce" ka ga, wallahi ka kiyayi matar AL'WALED, idan ya kyale mu furfurar karya ke habata, ka ga murmushin nan da yake yi? Na mu

nafurci ne kadan muka taba masa mata zai kai ya rufe a yi abinda za'a yi, ba kunya gare shi ba fa a kan matarsa, kana ganni ai idonka na gane maka, sai ka yi aniya ka taba masa mata harda ciki ka ga aiki da cikawa "

Aba yayi tsuru yana kallonsa lokacin

ne kuma AL'WALED ya karaso tare da su Sadik da ya dakatar suka gaisa da kurma wace ta nufi wajen baba Hamza direct tana bu

Ι—

e babyn farin ciki kamar ta yi me

Aba ya gyada kai kasa kasa ya ce" Ni abinda ke bani mamaki da suke kai mace gari wai su yi jiran

ta, sai kace wace ta shanyeka? Ta isama yo Ni an isa ma???"

AL'WALED yayi kiskirim yana sauraron su saboda irin yadda ake magana kasa kasa ya tabbata hali ake yi, wato gulmarsa

Baba Hamza ya ce" Kai ka ji tsoron Allah, kai da kake kwana a kofar asib

iti fa an gaya maka ban gane ka ba? Ko so kake yi a yi a bayyane kowa ya ji?"

Aba ya zarro ido harda zabura yana kallon baba Hamza kafin ya dauke kai yana mikewa ya kama hannun kurma ya dawo da ita daf da shi yana fadin" Zo, a nan ke kadai ce ta Allah,

meye a jakar in gani???"

AL'WALED na murmushi ya ce" Wai tufafi ta kwaso, tana jin ance an samu karuwar nan ta rikice mana da kyar ta yarda aka dauko biyu, banma san ta inda zan yi mata wayo mu juya ba"

Aba ya ce" Elhaji karami ku juya ina? Inace sun

shiga baban hutu kuma dama ba yau ba nake ce maka tunda ka kwace uwata ka bani jikata mana? In ba'a bani ita gaba daya ba a bani na dan lokaci mana dan Allah dan Annabi iyeah? Ni menenene ya sa ake son daga min hankali ne???"

AL'WALED ya dan zarro ido

sai kuma ya kalli baba Hamza wanda ya dage kafadu yana sake taba hancin Hamza karami

AL'WALED ya yi murmushi ya ce" Shikenan Aba in Allah ya yarda gobe sai maman nata ta zo mata da wasu kayan sai ta yi hutu "

Aba ya saki murmushi ya ce" Allah dai ya

maka albarka ya karra daukaka da dukiya masu yawa yadda zaka kara aure ka yi ta zubo min su, yauwa batun zuwa ka ga ka iya ce mata a'a fa, kar a fi karfin ka a gidanka, idan tace abu kace ke an ki ba'a yi gidana ne ko na waye, kana iya tsayawa ka hade fus

ka ka ce sai ka zane mutun ka zane banza, ko kuwa ka samu ka zane din ai Anmy kanwarka ce ka girme ta idan ka zaneta babu abinda za'a yi human right din sun ci ubansu "

Habubakar ya furta" La'ila ha ilalahu " yana zarro ido hadi da kame baki

Aba ya D

ube shi ya ce" Kaima ka ci ubanka , to me kake nufi? Ba za'a

Ι—

ora mutun a hanyar da ta dace ba? Kai ji karma ku turon matanku gidan nan ku rike abinku ranar sunnaa hade , duda Gimbiya tace ba'a taro ama sai na yi tunda ba shege bane , ita ke kunya to Ni Al

lah na tuba ai babu wanda zai ce min ya haka wai wani ta aurar da su anmy ace tana yi sunna yi? To sai me? In dai da lafiya badi ma in sha Allah ina fatan Gimbiya ta haihu ko baba??"

Da AL'WALED din, da Sadik din sai suka mike a tare har sunna kallon ju

nna kafin su kama hanyar waje, Aba ya kame haba ya ce" Ni suka bari ina zuba kamar mai sakin danyan magana?"

Baba Hamza ya Dube shi da harare ya ce" Kai dai Allah ya shirye ka, baka jin magana sam, wato idan kana tsoron dakar masa mata kar a rufe ka shi

ne zaka koya masa ya daka shi ko? Ai shima rufe shin za'a yi, wato kai kana lalaba taka a daki a waje kana hargagin karya kake so a ringa musu? Ba ruwana du Wanda ya janyo rigimarsa Ni yanzu sai dai in ce Allah ya kyauta dan in ya yarda ya daga mata hankal

i ta masa fushi ba zan bata hakuri ba, Ni yanzu abinda ya fi damuna ma takwara, kar aje ka ringa masa ihu ka gigita shi wallahi "

Aba ya Dube su daga shi har takwran kafin ya mike yana kama hannun litle ya ce" Mu je, tashi mu yi tafiyarmu mu barsu da ba

kin halinsu, in ba dan ba dan ba ai da sai ka je da takwaran naka ku karata, matsalar shayarwa ne kawai zai hanna, Ama gardi kam ai ya fado da kafar dama ubansa zai ci wallahi!"

Yayi tafiyarsa abinda, baba Hamza kuwa na dariya kawai yana girgiza kai

A dakin mama kuwa tunda yan matan suka hade ta hade fuska tana tambayar me suka zo yi yau kuma? Sai suka ki cewa komai saboda lamarin mama sai ita, karshema sai ta ja warning tana fadin" Bana son shashanci har an ce mun saka muku ido kowani motsi kunna gi

da, kar na kuma gannin kaffafuwanku a gidan nan sai na neme ku, kun dai ji na fada muku"

Karima ta shagwabe fuska ta ce" Mama Ama ai yanzu dalili ne ko mama, kuma ai dole ma zo mu yi shirye shiryen biki da ranar bikin"

Mama ta sakar mata harare ta

ce" Karima ki kiyayeni ban saka ku ba, Ni babu bikin da zan yi , ku tashi maza ku je ku yi abinda ya dace dare na sake yi kun wani zo kun sakani a gaba!"

Ai kuwa bata wani sauraresu ba ta Kore su sai fada take yi da famar fadin Bari babansu ya shigo bab

u mai mata taron sunna haba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login