Showing 108001 words to 111000 words out of 200647 words

Chapter 37 - Farkon-Ganin-Idona-Book-Compeletex

08 Sep 2026

58

zai san yadda yayi ya hadu da Elhaji Hamza, dan

kuwa shi kadai yake son gani, ya san idan ya sanar masa halin da y'arsa ke ciki tabas zai dube shi, zai sam masa mafita, bai wani nemi d'an uwansa ba dan ya san babu abinda zai iya yi masa!..........................

*Precius dy,

wato Babar rana, Rana mai daraja*

07/12/2024, 15:13 - samiraharounayacouba:

๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ

*FARKON GANIN IDONA*

๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ

*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช



*PAID BOOK*

*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numb

ana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you

๐Ÿ˜

*



LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA

Y'AR MAHAUKACIYA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

DAGA TAFIYA ฦŠAUKAR SOJA

BAK'A CE

KUTKALE

DUK NISAN JIFA

MAGE

IDAN KA RAINA INDA KAKE

DUTSE

NI ZAN L

ADABI

ZAKIN SARAKAI

WATA KOKOWAR

DA CIWO A ZUCIYATA

AURE YAฦ˜IN MATA

AZAL

WATA TAFIYAR

*Shafi na ashirin da tara (29)*

*TALLAH, TALLAH, TALLAH*

https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf

YAR UWAH SHIN KINADA LA

BARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE

KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*

๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ

๐Ÿ‘‰

0912 262 1080

LABARI

RANAR DAURIN AURE

Daurin aure ne da bai taba tunanin zuwansa nasa ba a kwana kusa kusa, sai gashi an fadi ranar da aka yanke za'a daura masa shi, da macen da ba zai nuna kamaninta ba, harma safiya ta yi aka tisa shi a gaba da shirin da ya jima bai yi ba, shiri irin na m

anyan kaya masu darajar gaske, dinki mai darajar gaske, wanda Baba Hamza ne da kansa yayi tsaye ya ciro kala uku ya da jikokinsa manya su hudu zaba , wa'inda a cikinsu du sa'anin AL'WALID din ne, domin girmarsu da yayi bai wuce da yawan shekaru biyu ko uku

ba, ya katse masa motsa jikin da ya je ya fara ya tiso shi a gaba ya sha shiga ta babar Gari da y'ar ciki harda kafa hula tamkar shine angon sai kanshi yake bazawa fuskarsa kuwa ya kwace da fara'a tamkar gonar auduga suka nufo baban falonsa nan ya samu b

rothers dinsa suma sun sha shiga ta alfarma sai fira suke cikin fara'a da farin ciki

Dubansa ya sauke a kan Jameel dake kashe masa hoto yana fadin" Elhaji karami, bari a fara ajiye maka hotunan da zamu hada befor daurin aure, hanyar daurin aure, lokacin

daurin aure da kuma after daurin aure"

Dariya Badamasi yayi ya ce" Wannan zane haka? Elhaji karami yau babar ranar sai ka motsa jiki? idan ka tadawa kanka gajiya fa?"

Al'walid ya sakar masa harara ya ce" Yaran nan ba zasu daina nemana da rigima ba,

sunna manta ฦดaฦดansu ne ni ko baba?"

Baba Hamza ya ce" Mu je dai, so kake sai na gaji dan in kasa katabus a wajen daurin auren bayan amarya zan gyalo sabuwa dal, mu je ka yi wankan"

Dubansa ya yi a tausashe ya ce" Inace mu Hausawa Bama zuwa daurin aur

en mu"

Baba ya yi masa kallon shekeke a nutse ya ce" Muna zuwa kam, mu je sai fa ka je daurin auren nan"

Murmushi yayi ya shige cikin dakinsa ya rufo ya karasa direct bayi

Wanka yayi cikin nutsuwa ya fito daure da tawul ya karasa wajen turarukansa

yana goge ruwan dake jikinsa yana hangen wayarsa dake saman gado tana haske tana daukewa

Karasawa yayi wajen wayar ya dauka ya duba domin numbar dake cikin wannan wayar numbarsa ce ta sirri

"Allah ya sanya albarka a aurenka, ina nan har yanzu ina ji

ran ranar da zan amsa sunnan wace ta fi kowa kusanci a duniyar ka, i love You so much gudaliya" Message din dake cikin wayar kennan bayan miss call guda biyu

A hankali ya lumshe idannuwansa kirjinsa na btng fiye da ka'ida

Idannuwan nasa ya bude saka

makon alamun bude dakin da ake ta gwadawa duda an gane a rufe daga ciki ba'a hakura ba, wannan kuwa ya san aikin baba Hamza ne

Karasawa yayi ya kimtsa jikinsa ta hanyar saka tufafin da aka ciro masa, sai dai bai dora babar rigar ba, hular kawai ya kafa

bayan ya saka turarensa mai daraja da sanyi, sannan ya saka takalminsa kafa ciki ya riko rigar da agogonsa yana tafe yana sakawa hadi da soke wayarsa a aljihunsa

Yana fitowa falonsa ya ja da sauri ya tsaya zuciyarsa na wani irin amsawa sakamakon cikar d

a falon yayi da dangi, wa'inda zuwan wasu bangaren nasa a irin wannan lokacin saboda fitowar da aka yi da Hajia inna saman keken guragu

A hankali yake kallonta zuciyarsa na sake karyewa, a tsayen nan kuwa da yake sai ya kasa karasawa inda suke, domin y

a jima rabonsa da ya ga an fidota, ita da kanta ne da ya matsa cewar a ringa fito da ita ta nuna masa a'a bata so a barta kawai, a dole ya hakura dan bashi da damar takura mata

Ya Allah, wannan ita ya sani uwa, ita ya sani mama, saboda shi dama da aka

haife shi dan gidan kanani ne, kulun yana nan tun yana baby , bale a lokacin Hajia lafiyarta kalau

A kan Hajia ya tashi da zuciyar tara dukiya, tunda ta fara ciwo burinsa ya kaita asibiti da kudinsa, Duda Elhaji Hamza ba talaka bane, ama shakuwa da soy

ayya dake tsakaninsa da hajiarsa ya sa yake fadin shine zai kuma da lamuranta a nan duniya, shine zai riritata zai siya mata dukkan abinda take so

Sai dai kashhhh, bai taba yarda cewa ba komai kudin ke iya siyawa mutun ba sai da ya gama tarawa yayi yawo d

ukkan kasashen duniya da Hajia aka rasa injin da zai tashi hajiarsa, Hajia duka duka shekarunta nawa? ama gatanan ciwo ya gama karar da komai nata sai imani da ibadar da ya rage mata

A hankali ya sado dubansa inda aka kama hannunsa

Hakoranta a fili s

uke tana watsa masa dariyar da ta samu yan kwanakin nan na farin cikin da yake gani kamar fa kurma na son zarce gona da iri

Da sauri ta nuna masa time sai kuma ta yi gagawar rike ipad dinta wajen rubutun nan ta rubuta abu kamar haka" Tsohon mutun na ta

fada Aba, gayacen a kofa kar ya sake zuwa bamu je an bamu sabuwar maman nawa ba, mu je Aba mu je"

Bayan ya karanta dan murmushi kawai ya kakaro da hannayensa ya mata alamun ta yi kyau abinta, domin ta sha lesh ne dandatsetse wanda aunty sharifat ta zo m

ata da shi , dan Kurma bata da dinke dinke na kece raini, du kayanta yan waje ne da uban ke siyo mata ko Mufeeda, to waye zai yi mata dinke dinken, kowa yana abinda yake gabansa?

Shigowar Mama Binta ne ya sa bayan gaishe gaishen junna da ake yi ta dubi

AL'WALID tana murmushi ta ce" Ni kam wai ko ka fasa min kishiyar ne Elhaji karami? , ga Babanku cen zai fara cenza kamani, ka san amarya da shiga rai kar ka sa yayi tunanin za'a fasa bashi amarya ne mana"

Dariya aka yi, a lokacin da yayi murmushi ya kar

asa inda Hajia take ya duka a hankali yana taba kaffafuwanta da aka saka mata su cikin silifasss, a Hankali ya ce" Inama ace kulun zaki ringa yarda ana fitar da ke Hajia"

Hajia ta yi murmushi, an luluba mata sabon mayafinta masha ALLAH, ita da kanta da

aka fito sai da ta rufe idannuwanta saboda wani irin suka da suka yi mata na jimawa bata ga rana ba, Elhaji karami ba zai gane ba, ba fa bata son fitowa bane, bata son sakewa kowa wani nauyi ne, saboda rayuwa, bata so kuma a ringa yi mata dan dole, domin b

a zata taba so ace sun yi zaman kyautatawa junna dan dole ba, ba zata so su hidimta mata dan yaronta na jan ragamar kula da gidan nan ba, a'a, yau da gobe kuwa ta fi karfin wasa, idan ciwo ya zama abokin tafiya yana saka naci sosai, ya zo ya zauna daram ya

ki tafiya, sai ya gama daidaita bawa sannan ya hakura ya tafi da kai, to fa a dan lokacin da zaka yi shi in baka kama jikinka ba ana iya samun matsala da tarihi marar dadi

Zata yi magana baba ya dawo yana fadin" Kai, ku fito mana ku ku koma wajen bak

i, masu zuwa daurin aure kuwa motoci sun fara yin gaba, karfe takwas ta yi jama'a a gaggauta a gaggauta"

Da dan sauro Hajia ta mika masa hannun dan tana iya motsa hannayenta da kuma kanta, kaffafuwan ne suka shanye

A tausashe ta kama hannunsa ta ce"

Allah ya yiwa aurenka albarka Elhaji karami, ka je ka amshi daurin auren nan, na tabbata ka amso alkhairi kuma zaka rayu da alkhairi, a dawo lafiya, yau ai zan wuni a falo da baki in sha Allah "

Murmushi yayi yana jin karsashi na shigarsa, daidai Baba

ya dubi Hajia Binta ya ce" Wai ba zaki ja kanwarki ki mayar da ita bane? yau na bani zasu rikita Ni"

Da sauri ta karasa tana sake gyarawa Hajia inna rufarta ta ce" Kin ga mu je , mu je mutumen nan a kan amaryar nan tasa kar ya mana ba daidai ba"

Ta

ringa tura Hajia sunna dariyar rikicin da baba tsoho ya tashi da shi

Fitowar suka yi tare harda Kurma wace sunna tafe tana faman hade hannaye sai ihun kuramenta take yi tana rokon a je da ita, mahaifinta na kallonta dai, ama bai amsata ba har suka fito

ya ga irin yadda ake cika mota ana tafia, domin daga nan inda suke sunna hangen irin yadda baban get ya cika da baki da kuma yan tafiya daurin auren, masha ALLAH sai da abin ya bashi mamaki sosai, shi dai ya san ya dora gayatar daurin auren bisa umarnin Ba

ba Hamza jiya da magariba fa, daga nan Baima taba wayar ba ya shigewarsa ne ya dan zauna ya huta, daga bisani kuma suka zauna da baba kan maganar inda za'a ajiye yarinyar, shi ya zatama daura auren ne za'a yi a gaba ta tare? gannin ba'a yi maganar inda za'

a kaita ba, sai baban ke ce masa yana sane, yana so a fara kawota nan ne daga baya sai a kaita inda ake so, ama a yanzu yana so ta zo su rayu a gidan nan gaba daya......, kuma a jiyan ne ya fahimci wani abu, kamar fa baba ya shirya masa wani abu, domin a j

iyan ya dan nuna masa alamun bayan daurin auren da kwana ko biyu yana son yin tafiya, zai baban cewa yayi to to masha ALLAH, kafin nan an sama mata passport ko? dan ka ga ai kafarka kafarta ita amaryar tamu....., to abin nan dai ya dai tsaye masa a rai, da

n bai gama ganewa ba gaskiya

A nutse ya dubi Kurma dake karra rokon a je da ita, da yan yatsunsa ya mata nuni ta tafi bangaren su Hajia

Idannuwanta ta yiwa raurau zata fashe da kuka, nan take ya hade fuska hakan ya sa da sauri ta juya ta nufi bangare

n Hajiar tana sakin kukanta mai ha

ษ—

e da boda

Baba ya masa alamun su je yana fadin" Kai wannan kuka na kurma dan Allah saurara ka ji? Allah mun tuba kamar ana barzar shinkafa, kurma rigima ne da ita walahi yaya za'a je daurin auren babanki da ke?"

Dar

iar da bai shiryawa ba yayi yana duban babban da ya bude masa mota ya ce" A kalamanka babu abinda zan manta idan mun dawo in sha Allah, ka san yau na batawa Litle rai, ba laifi mun gode "

Baba ya yi dariyar shima yana kallonsa ya ce" Ka rufa min asiri s

o kake yi ta daina min magana ? dama fa tun a cen nace ta yi hakuri maza ne ke zuwa abinda maman nata zata zo, sai cewa ta yi sai ta je shine na kyaleta ai dan na dan uban nata daidai da ita ne, gayanan kai da yan yatsu ka kori baiwar Allah, ba ta ki raras

hi ba? mu je mu je ma dawo gidan da wahala ka ga hakoran kurma yau"

Gaba daya yan uwa da aminan arziki suka rankaya gidan su Khadeeja daurin aure, kuma sun samu tarba mai daraja da mutunci, domin Elhaji Ya'u da ya'yansa da jama'arsa sun tarbe su da dara

ja da mutunta junna

Karfe yara na safe da yan mintuna aka daura auren Elhaji AL'WALID da NANA KHADEEJA a gaban duban shedu, Daurin Auren da ya saka jama'a da yawa mamaki, domin wasu tunaninsu a ina KHADEEJA ta gidan Elhaji Ya'u ta hadu da Elhaji AL'WALI

D na gidan tv da Radio? domin ba kowane ya sanshi ba, ama ana jinsa a tv da Radio sai wajajen da sakonsa ke zuwa a boye..., an dai san hamshaki mai kudi ne na bugawa a jarida, an san fitatacen mutun ne da yayi shura, daidaiku suka san ya taba aure, wasu ba

su san da haka ba sunna dai tunanin itace matarsa ta farko,

A cikin gida kuwa mata ne cike makil, tun daga kan dangi, da yan anguwa da abokan aikin Mama an cika sai kawo ake yi, inda amarya ke cen cikin dakan mama, mama FATEEMA zaune a bakin gado tana r

ungume da Khadeeja wace jikinta ya dauki zafi sosai na irin boyayan kukan da take yi, dan kuwa gaba daya abin ya zo mata wani iri, a yanzu nema da iya ta shigo da goro ta damkawa Mama FATEEMA a tausashe ta ce" Alhamdulilah, ta wajena ta zama mata a wajen E

lhaji AL'WALID" ta ji sunnan ainahin mijin da aka aura matan, sannan ta ji abinda ke hade da sunnan Elhaji, nan fa hankalinta ya karra tashi, a zuciyarta ayanawa take yi' Innalilahi wa inna ilaihi raj'une Allah ya Allah ka sa mahaifiyarsa ce ta je Saudiya

da shi aka haife shi aka kamo su aka koro su ta dawo gida take siyar da kunu da kosai dan su samu abinda zasu ci su yi rayuwa, ya Allah ka sa sunnan Elhajin da aka hada da sunnansa ba yana nufin abinda nake gudu bane, ya Allah kar ka sa ace mutumen nan mai

kudi ne, ya Allah na tuba ka rufa min asiri...' Sai kawai ta sake saka musu kuka , suka ci gaba da aikin rarashi, abin takaicin yan uwanta yau ita suka yiwa tawaye ko? ko sunna gidan uban wama?

A kofar gida

Idan ka ga Aba a wannan rana zak

a karanci tsantsar farin cikin da yake ciki a bayane a saman fuskarsa, Hakama baba Hamza, an gama daurin aure, wasu har sun juya gida ama baba Hamza sai sake gaisawa yake yi da mutane cikin farin ciki ya ki motsawa daga saman kujerar da aka fito musu na al

farma

AL'WALID dake bin mutane da kallo, yannayin fuskarsa a sake saboda tarin mutanen dake zuwa sunna gaisawa da yi masa Barka, sai dai yannayin jikinsa a sake yake sosai da wannan rana....., tabas wata daraja ta sake hawa kansa a karro na biyu, daraja

ce, domin aure sunnar ma'aiki ne, babar daraja ma kuwa mai wuyar sha'ani......, gashi dai ya ji sunnan matar da aka zaba masa, sunnan da sai da ya dan zabura a lokacin da aka fada domin wannan sunna dai da baba Hamza ya zaba ya aura masa sunna ne mafi dar

aja a cikin zuciyarsa, boyayan sunnan mafi daraja mafi soyuwa kuma wanda ya fi wahalar da zuciyarsa a duniya, Bai san yaya aka yi daga Karima da baba ya taba fada, sunnan ya koma Khadeeja ba, abinda ya Sanni shine sunnan nan in har ba sosai shakuwarsu ta z

arce misali da baba Hamza ba, ba zai taba zabarsa ba, domin shine sunnan matar da ta saka shi kuka da girmansa da komai sannan yayi alฦ™awarin ba zai taba yafe mata ba, yayi alฦ™awarin a duniya zasu yi gaba kuma a lahira su tsaya a gaban Allah, yayi tirrr da

ita kuma ya koreta, ya saka katanga mai tsaurin gaske ta karfe a tsakaninsu, yayi rantsuwar ba zata ji dadin haihuwar da ta samu da babansa ba, yayi rantsuwar AL'WALID nasa ne babu ita babu shi, yace idan ba dan sunnan da take da shi sunna ne mai daraja a

duniyar masu daraja ba da harta sunnanta sai ya la'anta, sai ga wani abin mamaki sunnan da baya kamawa yau ya aura masa?......., sunnan MAHAIFIYARSA ne take dauke da shi, wato NANA KHADEEJA....., Uhum

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login