Showing 141001 words to 144000 words out of 200647 words

Chapter 48 - Farkon-Ganin-Idona-Book-Compeletex

08 Sep 2026

60

TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBE

R 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you

😍

*



LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA

Y'AR MAHAUKACIYA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA

BAK'A CE

KUTKALE

DUK NISAN JIFA

MAGE

IDAN KA RAINA INDA KAKE

DUTSE

NI ZAN LADABI

ZAKIN SARAKAI

WATA KOKOWAR

DA CIWO A ZUCIYATA

AURE YAƘIN MATA

AZAL

WATA TAFIYAR

*Shafi na arba'in (40)*

*IDAN KINA DA BUKATAR TALLAH KI TUNTUBENI

TA LAYINA KAMAR HAKA 93811618*

LABARI

Dakinsa ya wuce yayi wanka a gagauce saboda lokacin sallar azahar ne sannan ya fito ya saka jalabiya bak'a sidik doguwa sannan ya dauki karamar wayarsa kawai, wace ke dauke da layi

nsa na sirri ya fice a dakin ya sauka kasa

Ya tarar da aunty shareefat da kaka Z kadai, aunty shareefat na danna wayarta ta ki tashi ta tafi ne dan haka kawai irin yadda kaka Z ta nace a kirawo shi ya dan so daga mata hankali, ko dan ya zamo sunna da sh

akuwa sosai da AL'WALID ne, ko menene? haka kawai dai ta ga rashin dacewar haka din bale da yana hawa suka hada ido da sauran yan uwan suka saka dariya da ido suka yiwa alamun su tafi, sai gani suka yi mamansu Hajia z ta kasa mikewa karshema sai ta saka ku

rma ta kirawo AL'WALID din, ko da ta nuna a barshi mana zai tarda su idan da wata maganar sai kaka Z ta nuna a'a a je a kirawo AL'WALID din tana jiransa, shine fa har sun fita kawai ta dawo tana call ta ki tafiya

A nutse ya karaso yana duban agogo Ganni

n yanzu za'a kira sallah ya ce " Kaka Z, zan je masallaci in dawo, idan na zo sai mu yi maganar"

Hajia z dake bin sabuwar suturar da ya cenzo da kallo ta yi gagawar fadin" Aa big son dama lokacin sallar ne ya gabato nace bari dai a kirayeka kar aje ka r

asa jam'i"

Aunty shareefat ta kalleta da dan mamakin furucinta, sai kuma ta kawar da kai bata ce komai ba

Shi kuwa murmushi kawai yayi ya fice dan kar ya rasa sallah

Hajia z ta mike tana dan tabe baki tana jin kamar ta je saman ta gano abinda ke f

aruwa, sai dai ta san idan suka hau sama abu ne mai girman gaske zai kai su, dan tunda aka kawo amaryarma ita bata je saman ba, tun dai gyaran da aka yi rabonta da saman nan

Aunty shareefat na kallonta har ta fice kafin ta mike ta danna abin kiran mai a

iki tana ta tunanin me yake faruwa ne haka kuma da kaka Z?

Mai aikin na zuwa ta dubeta da kula ta ce" Maman baby a tabbatar da an gyara wajen nan sosai, sannan a kula kar kowa ya wuce falon nan, idan baki ne a ajiye su a falon baki kawai, in an jima za

n zo kafin mu je kai kaya, a barta ta huta bata da lafiya, ko baki suka zo kar a tashe ta plz,.idan tana da bukatar wani abu na gwada mata komai zata yi muku magana, kar a bari kanshi ya katse a ringa sakawa ana kula da wutar kin ji maman baby?"

Maman b

aby ta dan duka tana fadin" In sha Allah Hajia, a fito lafiya"

Aunty shareefat ta fice, ita kuma Maman baby ta yi kiran mutun biyu cikin ma'aikatan suka shiga sabon gyara da kwashe kaya , su fa tunda suka gane cewar ba wannan mai zuba musu wulakanci bac

e uban gidansu zai aura hankalinsu ya kwonta, dan kuwa cikinsu babu wace bata yiwa alkawarin kora ba idan an yi aurensu ita da Elhaji, su kuwa aikin nan shine rufin asirinsu nan gidan duniya

A bangaren Hajia inna suka ringa jera akwatunnan da zasu je

su kai gidan Aba, domin da farko sun so a ajiye mata abinta kawai a nan sai baba Hamza ya nuna a'a sai an je an kai idan yaso yadda iyayenta suka tsara mata za'a yi, wannan dalilin ya sa suka jere saitunnan akwatunnan da kamfanin dake hada musu harkar lefe

suka hada babar motarsu ta kawo, kuma yanzu haka motar na nan sai an kai kayan gidan Aba sannan zata tafi , saboda idan motocin gidan za'a saka za'a laya motoci ne dauke da kayan , motocin iya mutanen familly zata dauka kawai

Hankalin kaka Z sai da y

a tashi sosai da ta ga irin uban kayan da aka dankarawa KHADEEJA,

Na fa halayarta bane kyashi da bakin ciki, hasalima tsoro ne ya fi jagorantar zuciyarta da tunanin ana daf da raba su da yaron su mai kaunar su, ta dauki vidio sosai da sosai ta tura a way

ar maman karima tun kafin ta gani da idannuwanta sannan ta sanar mata cewa ta hau online ta ga kayan KHADEEJA.

Maman karima na cikin dama fura zata sha ta ajiye ta kunna data hannunta har yana rawa ta shige whatsup din sannan ta shiga daukan vidion da

ke cikin wayar

Tun a vidion farko zufa ta keto mata, ta zuba ido tana kallo har ta gama kallo kawai ta ajiye ta hade kanta da gwuiwarta ta fashe da kuka mai tsananin gaske

Mahaifiyarta da ta shigo da kora dan jiran ta gama dama furrar ta zuba mata ne

ta karaso tana fadin" Ke kuwa ta yabuwa me yayi zafi da ba wuta ba wannan zafin zuciya haka? kukan me kike yi ke kadai a nan a zaune ? "

Maman karima ta dubi mahaifiyarta ta ce" Yanzu inna kiyayar Elhaji har ta kai nan? ya dauki miji irin wannan ya ba

KHADEEJA bayan ga karime a gabanta itace baba?, "

Inna ta zauna da kyar tana bismillah ta ce" To, to , to, wato ba zaki rabu da lamarin gidan Elhaji Ya'u ba ko? ba zaki taba dadara da shiga lamarin gidansa ba ko? salon ki janyo min mafisa ya zo har gida

n nan ya hade mu ya zane mu? kin ga ta yabuwa idan har kin gaji da zama da Ni ki maida Ni kauye in lalaba rayuwa har in koma ga ubangijina, inma ba mantuwa ba irin taki kin manta karime din ya fara zaba yace ya bata mijin ama a nan a filin gidan nan ta bug

o maki tace da ke miji ba kowa bane , kika yi tsalan albarka kika nuna ta bijire? ai ba wannan maganar a yanzu kice ba haka ba?"

"Inna" Ta fada da karfin da ya saka uwar zabura tana kallonta

A kausashe ta ce" Inna, walahi, walahi ba zan yarda ba, ko

naman jikina zai yanka gutsi gutsi ba zan yarda ba, sai Karima ta shiga gidan nan"

Da tsoro uwar ta ce" Ta shiga wani gida? ke kina cikin hayacinki kuwa?, Karima fa yar uwar Khadeeja ce uba guda, idan ba mutuwa ta yi ba mijinta ba zai taba halastawa Kar

ima ba!"

Mikewa ta yi ta dauki wayarta ta shiga aikawa Hajia z kira ta ce" Du wanda ya kama shi za'a yi, abinda na sani shine ya zama wajibi Karima ta shiga gidan nan, ko ana kare jini biri jini ne!"

Hajia zainab na daga wayar maman karima ta ce" Kaw

ata, idan an jima kar ki bi su kai kayan nan dan Allah, ganinan zuwa gidan dan ki min jagora Wajen Khadeeja"

Hajia z ta ce" A'a me zaki yi a wajenta ke kuwa? ki bi komai a hankali, Ni ina gannin gwara ki zama ta hannun damanta kin ga ko menene kya kwash

i rabonki"

Maman karima ta girgiza kai tana dafe kugu ta ce" Ga dukkan alamu baki yarda da abinda na fada maki ba, baki yarda cewa yarinyar nan da kika gani ba walahi sai ta yi sanadiyar da ko hanyar inda kuke zai daina kallo, kin ga magana tsakaninku d

a shi sai ta gagara, jinnin Usaina ce fa, jinnin asiri jinnin munafurci, sai ta sa ya manta kowa da komai sai ita sai uwarta da danginta da ta zaba,, fada maki ne nake yi , ke kin ga yaya nake da mijina kafin ta zo gidanmu, da ta zo masifa kala kala ta Kun

no Kai, a yanzu ko sunnana Elhaji ya ji sai ransa ya bace, an fada maki banza ta barni? tun daga lokacin da na bar gidan nake zubawa malamai kudadena dan a karya asirin da ta min ama har zuwa yanzu abu ya gagara, bari ki ji cikin kawayenmu a kulun kece abi

n mangari, ko taro in dai naki ne babu wanda ke jiran katin gayata kai kanmu muke yi, idan har wannan rayuwar ta farin ciki kike son zubarwa ki je ki kama wace bata daga tabas irin rawa, rayuwar kunci da bakin ciki, rayuuwar a jika kwaki a kora da ruwa kud

a na wawar nasa sauro na cizon rabonsa ba damuwa sai in tayaki addu'ar komawa zaman lungu da ƙatuwar budurwa a gabanki, dan kin sani ne babu mai rike maki y'arki a cikin gidan nan"

Jikin Hajia Z ya karra yin mugun sanyi, ita da yanzu ta gama fadin kalar

kayan da zasu saka su uku matan Elhaji Hamza idan zasu je kai kayan nan, dan Hajia inna ce da kanta tace da su tana rokon alfarmar su tafi su kai kayan jikansu su da kansu, yanzu yaya zata yi kennan?

Jiki ba karfi ta ce" Ki kasance cikin shiri da sun f

ara tafiya sai ki taho"

Maman karima ta saki murmushi a nutse ta ce" Ko ke fa"

Hajia z ta ce" To ama, wai yaya zaki yi hakan ya kasance Ni fa bana cikin abinda ya shafi allhakin rai fa? kuma yaya zaki yi ki shigo ba tare da wani ya ganki a cikin yara

n shago ko shi da kansa mai shagon? tunda kurma tana cen fa hakan na nufin bai tashi ba har yanzu bai koma gida ba"

Maman karima ta tabe baki ta ce" Kin ga, Ni nikaf dina kawai zan dauka in saka baban hijab ba zasu gane Ni ba, kuma maganar yadda zan yi

ta halastan kuwa wannan Ni na sani, sai dai ba boka babu malan zan bi da kirsa ne idan ta gagara in gwada karfina a kanta Ganinan zuwa jira zan yi a nesa kadan da an bude baban get din zan shigo!"

Bata tsaya ta ji daga gareta ba ta katse kiran ta shige

daki daya jal ta dauko hijabinta zumbulele da nikaf dinta

Mahaifiyarta da jikinta ke rawa ta ce" Ta yabuwa, ki guji muguwar kadara ko in kirayi hakan da janyowa kai jafa'i, ta yabuwa ke dai in ba Yaren kudi ba bakya gane komai? rayuwar da kike ciki ce k

ike zagi haka ta yabuwa? ai kuwa babu baban arzikin da ya wuce rai da lafiyar da kike da shi, ki kiyaye kar su kubce maki cikin garari ta yabuwa, meye a arzikin banda fitina da tashin hankali"

Bakin gyauton dake jikin uwar kawai ta kalla ta gyada kai ta

ce" Ba laifi, idan arzikin ya samu dama ke babu inda zaki je dan baki iya ci ba, gayanan ai da na je rabo ki daga kwonciyar tabarmar kaba a kauye da gudu kika biyoni kika zo koke cin dadi, da na rabu da gidan Elhaji kin fi Ni kuka dan jar miya ta kare, ya

nzu kuma da bakinki kike maganar wai kudi ba farin ciki bane? ama kuwa in ba dan uwata ce ke ba yau da ban san me zan gaya maki ba, hummm!" ta yi gaba da sauri ta barta nan tsaye tana kiran sunnanta ( Allah ka rufa mana asiri duniya da kiyama, Allah kar ka

jarabcemu da ya'yan da ba zasu ji kunyar harshensu a kanmu ba, Allah ka shirya mana zuri'a ka rufa mana asiri duniya da kiyama)

Hajia Z na gannin wayar ta mutu kawai ta yi kai kawonta sau biyu ta rasa madafa sai kawai ta cire dan kwalin kanta ta yi fla

shing din khalisat ta ajiye wayar a nan ta yi bayi da sauri ta rufo

ƙ

atuwar buta ta cika ta bude WC ta saurara, tana ji an shigo ta aniyar zubawa a cikin WC din tana kakari da karfinta dan ta jiyota

Khalisat ta karaso da sauri kusan bayin tana dan fa

din" Subahanallah, Mama? lafiya?"

Hajia Z ta yi shiru ta karra abinda take yi har sai da ta ga sosai Khalisat ta rikice sannan ta wanke fuskarta hadi da dan jika gaban rigarta ta fito tana numfashi sama sama ta rike hannayen khalisat da ta miko ta rikot

a da kyau suka nufi bakin bed dinta ta zaunar da ita tana fadin" Mama lafiya? subahanallah yanzu fa na neme ki akace kin nufi daki"

Hajia Z ta make murya sosai ta ce" Bari khalisat cikina ne ya dan juya min fa sai na shigo na shiga bayi, tun dazu amai n

e nake yi da gudawa"

Hankalin khalisat ya tashi sosai domin nan da nan ta fita ta kirawo mama B suka dawo tare

Hajia Binta cike da tausayawa ta ce" Subahanallah Hajia wani abin kika ci ? bari a yi kiran docter subahanallah "

Hajia Z na nishi ta c

e" Nima ban sani ba, Ni dai kawai abin ya kece min, baki ji murdawar da cikina ke yi ba"

Mama B ta ce" Subahanallah bari in je in yi kiran docter in dawo"

Da sauri ta ce" A'a Hajia, haba Hajia daga ciwo sai a taso Docter? "

Kaka B ta ce" A'a fa Ha

jia amai da gudawa ai abin tsoro ne yanzu da yana iya fitar da ke a hayacinki?, ai shi matsalarsa akoy saurin karar da ruwan jiki"

Hajia Z ta ce" Duda haka a dan bari zuwa an jima idan bai tsaya ba sai a kirawota, Ni yanzu damuwatama bai wuce tafiya kai

kayan nan ba, kin ga kayana har na fitar fa, gashi har lokaci yayi ke har kin shirya, ban san yaya zan yi ba"

Hajia B ta ce" A'a haba dai, ciwo ai yana gaba da komai Hajia, ki huta bari in je mu tafi mu dawo, khalisat ta zauna a wajenki sai in ringa ki

ranta ina ji daga gareta jikin naki, kin ga Hajia inna ma masu aiki ne ke wajenta du tafiya zamu yi"

Kai ta gyada ba tare da ta so an Bara mata khalisat ba, dan ba zata taba son kowa ya san shirin su da kawarta ba, ama kuma ta san tunda aka riga aka ce

haka din idan ta kawo wata gardamar za'a iya fassarata ne

Haka Hajia Binta ta wuce ta sanar da sauran abinda yake faruwa, du suka lekota kafin su wuce, Hajia inna ce kawai basu sanarwa ba, ita kuwa dama in ba abu ya zama baba ba basu cika fada mata ba d

an kar a daga mata hankali, domin abu karami ke daga mata hankali

motocinsu na tafiya tun ba'a rufe get ba ta shige bayan an yi mata tambayar wace ita ta sanar cewa daga gidan su amarya aka aikota ta kawo sako, ta nuna musu leda dauke da abu, dan haka

suka bata dama ta shige

Tunda ta shigo ta sanar da Hajia Z, wace ta mike da sauri tana neman dan kwalinta da hijabinta

Da sauri khalisat ta mike tana kokarin kamata ta ce" Sannu mama, mu je in raka ki ya murda ko?"

Hajia Z ta dan dakata ta dubeta

ta ce" Au, a'a da sauki ai , kin ga yi zamanki ki yi game dinki ina zuwa, na yi bakuwa"

Yannayin da take da kuzari da magana da kuzari ya saka khalisat dubanta da dan mamaki ta ce" To ama mama ko Wacece ai sai a sanar da ita baki da lafiya sai ta dawo

ko?"

Da dan hasala ta ce" Ke Khalisat!, Ni Lafiyana kalau, nace kuma ki zauna ta yabuwa ce ta zo, ina zuwa!"

Daga nan ta saka hijab dinta ta fice a dakin ta bar khalisat tsaye da mamakin abinda ya faru, ta yabuwa? mahaifiyar Karima kennan sister din

amaryar AL'WALID, wace suka zo kwanaki wajen baba cewar babanta ya mata miji bata so?

Mikewa ta yi ta fito dan du sai take gannin kamar maman nata ba lafiyar gareta ba dan dai kawarta ta zo ne ta fito, domin khalisat akoy sarkafar uwa

"Rike min kwa

non nan da na dauko, maganin nan ne na sako a ciki saboda kar su hannani shiga su ja min tsayuwa a kofa, na ga Elhaji Ya'u tsaye da Elhaji Hamza da kurma sunna ta dagawa masu tafiya da kayan hannu kamar sunna tsaye bakin hanyar da shugaban kasa zai wuce"

Maman karima ta fada

da sauri Hajia Z ta amsa ta tura shi nan lungu ta ce" Magani kuma? na me? kin san sai da na yi karyar rashin lafiya sannan suka tafi suka barni? mu je bangaren nata Ni dai ko menene kar ki yi abinda zai ja min matsala a gidana da

mai gidan nan, saboda walahi kin ga yana kyale komai ya wuce banda abinda ya shafi yaron nan, sam baya yafe abinda ya shafe shi, kennan kin ga ko menene ya zamo wanda hankali zai dauka, kin dai ji na fada maki"

Ta yabuwa ta tabe baki ta ce" Ba dai kin

tabata babu abinda ya shiga tsakaninsu ba? domin a nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login