Showing 99001 words to 102000 words out of 200647 words
ganninki a irin wannan yannayin, ga kudaden da Anmy ta je da su ranar da kuka yi yaji, Allah ya karra hakurin zama, a karra jurewa a ci gaba da biyaya, in
sha Allah mahakurci mawadaci ne Usaina, zaki tsinci abinki tun a duniya sannan ki tarda kyakkyawan sakamako gobe kiyama, Allah ya yi albarka, ya sakata dakinta lafiya, kar a manta wunin gobe ko kofa kar ta fito, sannan a kula da dukkan abubuwan tsari , a k
iyaye komai, Allah ya tsare"
Da amen suke amsawa gaba dayansu
A tausashe Mama ta ce" Hajia Ni ba zan amshi kudin kawarki ba, dama abinku naku ne ai"
Nanma suka yi dariya
Hajiar Larabawa ta yi murmushi ta ce" Su takwarraty sai na je gidant
a ma hade ko Usaina? ko kuwa sai na zo daurin auren? haka fa tace in na yarda aka yi mata auren dole zan iya rasata in shiga uku, gashi an hadu da Ni za'a ci amanar ta"
Mama ta sada kai tana murmushi, mama Fatima ta ce" Hajia ki yi zamanki ki huta muna
nan ai, ita da zata dauke abinta, ai kin ji cewa take yi in ta yi aure zata tara kudi ta maki ginin larabawa sai ta kai ki tana siyar da kosai tana siyo maki kayan shayi, Anmy kennan manyan gari"
Du suka saka dariya, sannan ya kamata suka tafi a hankal
i , su kuwa sunna tsaye sunna kallonsu har suka shige mota uncle Umar ya tayar, mai gadi Ya bude musu suka wuce
Ajiyar zuciya Mama Fatima ta sauke a hankali ta ce" Ki je wajen su Anmy, ki zauna a wajenta, dan Allah aunty banda fada da jan warning, ki yi
hakuri da ita ki kuma nusar da ita, bana son amaryar gidan nan ta fahimci komai, kin dai ga irin abinda suke yi ita da yan uwanta so suke yi a kula su, iya tsohuwa tace kar wanda ya kula su, ta fadawa matan anguwar nan kar ta ji kar ta gani, kin ga kuma s
un ji gasucen aikace aikacen su suke yi, sun ce zasu yi safiya su je kasuwa siyan kayan miya gobe "
Mama ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" To shikenan Fatima, ama a nan zaki kwana? malan fa?"
Mama fateema ta yi gaba tana fadin" Na ce masa sai
bayan sati biyu"
Mama ta zarro ido tana dariya ta ce" Kin isama, yarinya mu je dai in gama samun nutsuwa ki wuce ki je dakinki, zaki yi bayani ne na kusa fara maki irin na Hajiar Larabawa"
Haka suka shige sunna dan barkwancinsu
Mama fateema ta
yi wajen baki ita kuwa Mama ta shige bayan ta yafito iya tsohuwa dan kar su nemeta su ga bata nan, ta sanar mata zata je ta rarashi y'ar dakin nata , iya kuwa tana dariya ta ce" Je ki rarasheta, ai na ga ta tsorata kamar ba da ita muke koyar surfen tsakar
gida idan mai gida na nan kalarsa daban da wanda baya gida, sai kuka take rusawa yar ashata"
Mama ta kama baki kasa kasa ta ce" Iya, wai Anmyn ce take abin nan?"
Iya ta yi dariya ta ce" Ke dai hade min ta wajena tsaf mikata daki, sauran abubuwan ma
ji da shi innar ya'yan Ya'u"
Murmushi Mama ta yi ta nufi cikin, a ranta tana ayana' o, gidan nan ba iya ina son jin me suke aikatawa kuma yanzu ina tsoron kar in juyowa kaina fitina, harda wani surfen tsakar gida na gaban mai gida? Allah na tuba ya'yan
yanzu tafe suke da fitinu, Allah ya sa itama Anmyn ba tafiyarsu daya da Karimar ba , dan kuwa lamarin abin tsoro ne '
Dakin ta bude a lokacin da Khadija ta kwonce , kanta a saman cinyar Karima tana magana muryarta cen ciki ta ce" Ba zaku gane ba, Ni na
san mutuwa zan yi, ashe har haka babanmu ya tsane mu?, me yasa ba zai bamu lafiya mu yi rayuwarmu bane a gidansa ? aure ai yi zamu yi in lokaci yayi ko? ama ace dole sai an yi mana auren hadi? an daukowa Karima wanda bai yi mata ba ta bijire Ni yanzu ba'a
bani damar in ga wanda za'a banin Bama , Allah idan dai fitinar nan ta ki mutuwa Allah ka zabi daya ka dauka kawai, ko Ni din ko uban nawa dan ka fi kowa son'mu "
KARIMA ta dungure mata kai ta ce" Ke walahi in baki daina addu'ar nan ba zan ci ubanki!"
Da sauri Lubna ta ce" Ta sakamu gaba sai kuka take sakamu, kuma yanzu tana neman mu da fitina, Anmy salon mu taba lafiyarki jiki ya haye maki ko? ba laifi , dan so dama ai babanmu baya son'mu mun sani, ki daina kukan hakanan mana, kin san dai Mama zata t
ayamu yakarsa ko? zata tsaya mana, zamu kai makiyi kass tabass!"
Kan mama sai da ya fara sarawa, sun tsundumu a duniyar tashin hankali basu san ta jima a tsaye a kansu ba suke magangannun da suka san ba zata taba lamunce musu yi mata shi ba
Hankalint
a yayi kololuwar tashi da jin furucin bakin yan Ζ΄aΖ΄anta
A hankali ta karasa cikinsu ta yi zaman da bata shirya ba tana cire hijabin dake jikinta dan tsabar shiga wani hali na matsuwar zuciya
"Innalilahi mama yaushe kila shigo?"
Lubna ta fada tana z
abura zata matsa dan ta sani in dai Mama ta jiyo furucin bakinsu tabas dakan danyar kubewa zata musu a dakin nan ba ruwanta da amarya ko yayun amarya gaskiya
A zabure Anmy ta mike zaune tana bu
Ι
e idannuwanta ta ce" Ke dilla Mama kuma?".....
Ai kuwa sa
i gannin Maman ta yi a zaune tare da su, da sauri ta rika neman hijabinta ta ce" Mama, sannu da zuwa yaushe kika zo?, innalilahi Allah ga Anmy, Allah ka ji kaina ba dan na mutu ba..."
Mama dake kallonsu, murya a raunane sosai ta langwabar da kanta t
ana dubansu ta ce" waye yace muku baya son ku? waye yace muku zai muku zabin tumun dare?, kun san Allah a kusa kusan nan ban ga mai son yaya irin mahaifinku ba, kuma ba zai taba yi muku zabin tumun dare ba, ko waye yace muku ku je ku zauna da shi ku je, in
a da yakinin sai kun yi masa godiya....."
Ta ajiye maganar tana dubansu, idannuwanta na cika da kwallah ta ce" Ku barshi da fadansa, da dukansa, bayan wannan me yake muku? ya tsare muku ci, sha, sutura, ya muku ginni mai kyau ya kilace ku, ya tsaya kan
ilimin ku na addini da na boko, idan kana son gannin bacin ransa a tabo ku, me kuke nema da uba sama da haka?, Mahaifinku uba ne tsayaye , tsaurinsa ya samo asali daga irin yadda aka raine shi shima, yanzu haka kuke zama kunna zagin min shi?".........Sai k
awai hawayen nan suka bale mata, saboda bata da baban firgici sama da wannan, ita fa tana girmama yadda yake tafe da ya'yansa, wasu furucin nasa ne ke daga mata hankali wa'inda take addu'ar ya daina a kan ya'yansa saboda rayuwa, ama ace ya'yan nan su zasu
yiwa rashin mutunci har haka? fisabililahi me suka yi musu da zafi har haka?
(Uhum' Hajia mama kennan, ke dai Allah ya baki hakuri ama kam ai abubuwa kam mijinki na yi sai dai a yafe masa kawai
πΆπΏ
ββ
οΈ
πΆπΏ
ββ
οΈ
πΆπΏ
ββ
οΈ
)
*ALLAH, KA SA CIKIN YAN KUNG
IYAR BATI DA AKE FITARWA NOVEL DIN NAN A SAMU MASU SIYA YA RAB, AMEN AMEN AMEN KU TAYANI DA AMSAWA AMEN*
07/12/2024, 15:11 - samiraharounayacouba:
πΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊ
*FARKON GANIN IDONA*
πΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊ
*LABAR
I DA RUBUTAWA*
*SAJIDA NIJAR*
π³πͺ
*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER
0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you
π
*
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ΖAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAΖIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na ashirin da shida (26)*
*TALLAH, TALLAH, TALLAH*
h
ttps://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf
YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DA
DE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*
ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌ
π
0912 262 1080
LABARI
A tsorace du suka dubeta, dama kawunnansu a kasa tunda ta fara maganar, jin gargadar murya ya saka du suka dago a tsorace
Hannu Khadeeja ta
Ι
ora a kai ta ce" Innalilahi, kuka kuma?"
Da sauri Lu
bna ta sauka kasa daf da kafar maman ta mika hannu tana janyo sauran, du suka sauko suka duka kawunnansu a Ζasa
Murya a raunane Lubna ta ce" Mama, kuka kuma dan Allah kar ki mana kuka mu fada fushin Ubangiji, ki yi hakuri ba zamu kuma ba"
A hankali
Khadeeja ta sake dago idannuwanta ta dubi fuskar mama, zuciyarta ta shiga babalewa, a hankali ta mike ta fada jikin Maman muryarta na rawa sosai ta ce" Ko da wasa ba zamu so gannin hawayenki ba, bale da gaske, dan Allah ki yi hakuri, in sha Allah ba zamu k
uma ba "
Mama ta lumshe idannuwanta tana yiwa Allah godiya da ya yi mata arzikin da idan ta nuna bacin ranta ko menene sun barshi kennan
A tausashe bayan ta zaunar da Khadeeja ta kuma zaunar da yan uwanta ta dube su ta ce" Ku gane, dole a yi muku fad
a, dole a dake ku idan ta kama, wannan shine baban gatan da zamu yi maku, saboda rayuwa babu kwaba, babu hannawa ai ba rayuwa bace"
KARIMA na duban Mama, tunaninta na rabuwa waje waje, ba zata manta ba du idan suka yi laifi aka musu duka da fada mahaifi
yarta na fadin babu ubanda ta haifawa da za'a kashe mata, ta sha cewa idan ta dawo gidansu zata hanna mahaifinsu dukansu dan bai isa ya dakesu tana tsaye ba, takan ce na anfanin a saka yaro a gaba a yi ta zagi ana duka? me yasa za'a yi ta Dukansu? takan c
e du mai dukan ya'yansa baya sonsa, gwara a kyale yaro da kansa zai gane in laifi yake yi ya daina, takan ce da ita mamansu itace ke ziga babansu ya dake su, a gabansu ta nuna ba haka ba, ama itace ke hada su
Mama ta ce" Ku sani, Ni da kuke tunanin wai
zan yi muku yaki da shi ba abokin gabana bane, na fada muku ba abokin gabana bane, kuma ban fi karfin mijina ba, biyayya nake yi masa dan aljannata tana karkashin kaffafuwansa, Mahaifinku bashi da wata riba da zai ci dan kun lalace ko wani abin ya same ku
, shine wanda zai fi kowa shiga tashin hankali idan wani abu ya same ku a rayuwa, mahaifinku shi ya fi kowa son gannin kun zama wani abu na alfahari a duniya, a mizanin da kuka kai kuwa kun isa aure, auren da za'a yi muku shine baban rufin asirinku , daraj
ar ku, a gidan duniya dan ya samo muku mijin aure shine alkhairin da zai yi muku mafi girma a rayuwa......., ku sani walahi da ace Karima tunda farko ta nuna min bata son mijin da aka samo mata da ba'a samu matsalar da aka samu ba domin ko yayane zamu samu
mafitar da ta dacewa damuwar , muna zama da shi, muna shawarar abinda ya dace da ku, ba daba bane shi da kuke gani kuma zai fi kowa son ganninku cikin farin ciki, kun fahimta?"
Su kawai suke ganewa, Karima gaba daya kwakwaluwarta ta cushe, Maman take k
allo tana sauraron kalamanta, ta shiga cikin yannayin fashin baki da don lalle a yannayin Mama da kalaman Mama sai ta tono munafurcin da mahaifiyarta ke fadar tana yi musu a rayuwa, hakan ya gagara
A hankali Mama ta ce" Ku yi masa biyaya shine kawai ab
inda zaku yi dan ku birge shi, ku yi mana biyaya shine abinda Allah ya umarce ku da shi muddin ba abinda ya sabawa Allah muka zo muku da shi ba, yana da niyar aurar da kowace a wannan shekarar dan haka ku shirya, a wajena baku da wata mafaka da ta wuce mu
yi masa biyaya, in sha Allah zamu ci riba baki daya kun fahimta? maza ku biyu da kuke sallah ku tashi ku dauro alwallah ku yi, ke kuwa Lubna ke da Karima ku gyara muku wajen kwonciya, bari in je in gyara muku abinda zaku ci in zo"
Mikewa mama ta yi ta f
ita, khadija kuwa ta nufi bayi, ita kuwa y'ar uwar tasu wato Ummu ta nufi dakinta dan a bude ta barshi da nufin dauko dardumarta sannan ta rufo
KARIMA jikinta a mugun mace yake, ta dubi Lubna a hankali ta ce" Lubna, ina cikin wani hali, Lubna ina cikin
wasu tunanika da suka cinkushe min kwakwaluwa, Lubna anya kuwa zan ga da kyau? idan ina gaban Mama zuciyata na cika da kaunarta, da tausayinta, da begen ta tamkar wace ta haifeni, saboda a tare da ita bana gannin wani bakin hali ko bakin ciki a kaina, idan
kuma na bar inda take na je gidan su Mama sai a ringa ganar da Ni wani abin daban..........gaba daya an hade min lissafin rayuwa"
Lubna na dubanta, a hankali ta ce" Ban san me ake fada maki ba, ban san girman zugar mahaifi a kan ya'yansa ba, dan Ni taw
a mahaifiyar a kulun nuna min take yi tunda Mama ta ci kashina da fitsarina uwata ce har a gaban Allah, idan na saba mata Allah ne zai saka mata, Karima ke ba mahaukaciya bace, zan so ki yiwa kanki adalci, ki yiwa Mama, abu daya na sani Mama haihuwarmu ce
kawai bata yi, walahi du wanda yayi mata butulci sai Allah ya saka mata.., kina kallon iri........"
Shiru ta yi saboda tahowar Khadeeja, domin idan Khadeeja ta ji yanzu wasan zai watse, koda wasa ka fadi wani abu a kan mama ta rikeka kennan, in babu yad
da zata yi da kai zata kai karar ka wajen Allah ne, idan kuwa tana iya dira ta rike maka kwalar riga an gama, wasan ya tashi dan walahi sai inda karfinta ya kare, dan sun sha fito na fito da Karima idan ta ga Mama ta yi musu fada Karima ta yi gaba tana tur
o baki, takan ce mata ke kam kamar y'ar iska, Mama ai uwarki ce, shikenan ta kirkiro hanyar da zasu daku da KARIMA, kuma yawancin lokuta Karima na kuka ake amsarta dan idan ta daneta sai an kwaceta
Sallar ta kabbarta , ta yi isha'i sannan ta yi shafa'i
da wutir, ta je ta kwonta a shinfidar Mama ta lumshe idannuwanta, ta afka duniyar tunani mai girman gaske....., gaba daya gani take yi ne an gama dukanta sannaan an hannata kuka, gani take yi an gama kashe mata rayuwa ita kam sai ceton Ubangiji, a irin maz
an da Aba ke zabowa mutun fa harda wanda baya ra'ayin a yi karatu?, idannuwanta ta rintse a cen kasan zuciyarta ta ayana' Ya Allah, baki da mafaka, bani da matsera sai wajenka, gashi maganar aure ake yi sunnan mafi soyuwa a wajenka, ya Ubangiji Ni din ban
isa in take ko in ki yiwa iyayena biyaya ba domin ina fatan samun rabauta a wajenka, ya Allah ka sa ko wanene alkhairina ne, ya Ubangiji ka sa ba'a bani mai kudi ba, domin na riga na sarewa auren mai kudi a rayuwa, ya Allah ka bani wanda zamu fahimci junna
, zamu yi wasa da dariya, idan ta kama sai na toya kosai dan mu samu abin ci in dai da kwonciyar hankali zan toya, ya Allah ka sa mijin da babana ya bani mai sanyin hali ne, Allah ka bani ikon yiwa iyayena biyayya.......
Tana jin lokacin da ake ta yi ma
ta magana dan ta tashi su ci abinci ta yi likimo ta ki tashin , Mama tace su kyaleta su ci su kwonta , tana yi tana duba lokaci, gidan an ragu sosai sai iya su da Mama fateema da kuma kannen amarya domin a lokacin da suka so tafiya da suka fuskanci Mama fa
teema a nan zata kwana shine suma suka ce ai a gidan zasu kwana, ita dai Mama fateema bata shige dakin Khadeeja da nufin kwonciya ba sai da ta gama aikace aikacen da ya dace tasss sannan ta shige ta rufe ta yi kwonciyarta, dan a lokacin karfe takwas ta wuc
e na