Showing 63001 words to 66000 words out of 200647 words

Chapter 22 - Farkon-Ganin-Idona-Book-Compeletex

08 Sep 2026

37

ta tafi ina? Duda ya san amsar tambayarsa ba zai.wuce yace Hajia ta tafi gida ta bar amarya ta yi jinyarsa? shi kam Yana girmama soyayar da Elhaji ke yiwa matarsa,

Aba ya dago yana

dubansa a hankali ya ce" Gidan Hajiar Larabawa ta tafi tunda safe"

Baba ya dube shi a dan zabure ya ce" Sakinta ka yi itama?"

"A'a, ban saketa ba, wai me yasa za'a ringa min wannan mugun alkaba'in? ban saketa ba, fushi ta yi ita da yaran suka tafi gi

dan Hajiar Larabawa tare"

Baba Hamza ya zuba masa ido, yana auna maganar da ya fada yana yiwa kowace fashin baki har ya gama fahimta sannan ya ce" Subahanallah, me ka yi mata da zafi haka? kana nufin ita ta tafi gidansu, sauran ya'yan kuwa duk sun je in

a?"

Aba ya fitar da huci ya ce" Ni babu abinda na yi mata, Ni ta wanke sumul sanan ta yi tafiyarta da yaran"

Baba ya dan buda ido abin mamaki, sannan ya sake kure Aba da kallo a tausashe ya ce" Ka fada min abinda yake faruwa mana, me ya faru?"

Aba

ya rasa inda zai kama, gaba daya sai ya dora laifi a kan amarya da ta je ta fadawa baba Hamza bashi da lafiya tsabar bata da hankali, yanzu idan ya ji wata fitinar ce ai shi da kansa zai iya cewa an fasa auren nan a masa bakin ciki a hadasa masa hawan jin

nin da zai kai shi kiyama

Gannin ya ki yin magana ya sa baba fadin" Shikenan bari in je inda take na san ita ta fada min abinda yake faruwa, Allah ya kyauta maka, kai ace baka da gwani a rayuwa? in kana rigima ka cireta a gefe, yarinyar nan kana gannint

a ka san Allah ne ya wanke ya baka, ama sai ka kure hakurinta?"

Aba ya ce" Ka zauna ka ji, babu abinda na yi mata fa, duk abinda yake faruwa laifinka ne fa ba na kowa ba"

Baba ya kalle shi shekeke jin abinda yake fada

Aba ya dora da fadin" Ka ga i

ta matsalarta boko, banzar bokon nan du ta cushe tunanin gimbiya, kana jin wani abu , a lamarin nan na ga abinda ya fi karfina sosai, sun nuna min sunne mata sun nunan iyakata, ama na gimbiya da bambanci da na uwar KARIMA "

Zuwa yanzu baba ya nutsu yana

sauraronsa, dan haka ya ce" Me yake faruwa ne ? wani abu aka yi?"

Aba ya zauna da kyau yana ajiye hannunsa mai karin ruwan a wajen da ya dace ya fuskanci Baba ya ce"Rigima ce da rashin fahimta ta sa ta yi gaba ta yi tafiyarta, ko ji take yi idan babu i

ta ba zan rayu ba ko menene? Ni dai abinda na sani shine ya'ya nawa ne zan yi iko da su ne yadda na ga dama, ita da kanta bata fi karfin ikona ba bale y'ar da na haifa, idanma a rigimar ba zan yiwa y'ayana aure bane ta tile gwara ta baje, dan na fahimci in

har ban yi musu aure ba tabas zasu bani ladan kiwo a hanuna , wai yanzu ace Ni gimbiya zata duba tace ba zan yiwa yarinya aure ba sai in tana so? wato an yi lalacewar da zamu yi tsaye yaya su mulke mu ? soyayar me, ita tsoronta kar aje a ba yarinya wanda

zata zo tana kukan an yi mata na dole, akoy abinda ya kai auren hadi dadi a duniya? du laifinka ne , da ka yarda ta san waye za'a aurawa y'arta da ta amince dan ta san gidan tarbiya za'a kai yarinyar ta........."

Sai kuma yayi shiru na dan lokaci kafin

ya ce" Koda yake, in dai gimbiya ce, ta ga damar cewa bata yarda ba, koda ta ji wanene din, Allah dai ya shirya matar nan, sam bata saka zaman lafiya a lamuranta "

Baba Hamza a tausashe ya ce" Da aka fasa da Karimar, khadija ce aka bamu?"

Aba ya dube

shi, sai kuma ya gyada kai yana fadin" Ita na so, ama in har uwar ta ki ba laifi, sai in bada Lubna "

Baba ya hararashe yana fadin" Kai, dan kawai ya zame maka wajibi hadin auren? na fada maka abinda zai yiwu zamu yi, Ni da kaina ba zan so a bani da ka

rfi ba, saboda maganar zaman aure ake yi ba wai zaman dan lokaci ba.....ama, zan je gidan ta Larabawan bayan sallar magariba in sha Allah, zamu zauna da su in har suka kiya shikenan sai a bar maganar kawai"

Takaici ya sa Aba hadiye maganarsa yana ta t

unani, bai san me zai kirayi ranakun nan ba, ama sunna cikin manyan ranakun da ba zai taba mantawa da su ba a rayuwa

Wani irin haushin amarya ya tsaye masa a kahon zuciya, da ta je ta kawo baba Hamza ita wawuya, idan har ya wargaza abin nan walahi daid

ai da rabuwar nata igiyoyin auren ne, ita kuwa gimbiya ta maida hankali idan har bata yarda aka aurawa khadija AL'WALID ba tana ji tana gani za'a aura mata wani , dan ya rantse ba zai bar dayansu ba nan da ranar daurin auren nan, gaba dayansu sai ya aurar

da kowace da manemi ko babu, ina ba zai tsaya ya ga abinda ke wayar Karima ya tabata a gidansa ba!

Firar sai ta dawo wata iri, dan kuwa baba kawai ke surutunsa yana ta nasiha mai kama da fada, nasihar da ya saba yi masa ce, nuni da yake yi masa da ray

uwa sai ana hakuri, ire iren haka dai har kiraye kirayen sallar magariba suka tashe shi ya shige ya dauro alwallah ya tarar ana cirewa aba karin ruwan dan haka ya fice ya nufi masalaci da masu gadi da direbansa suka bi sallar jam'i da nufin bayan sallar za

i wuce gidan su Usaina.

😍😍😍😍😍😍😍😍

07/12/2024, 14:53 - samiraharounayacouba:

🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺

*FARKON GANIN IDONA*

🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺

*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*

πŸ‡³

πŸ‡ͺ

*PAID BOOK*

*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a ban

i shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you

😍

*



LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA

Y'AR MAHAUKACIYA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA

BAK'A CE

KUTKALE

DUK NISAN JIFA

MAGE

IDAN KA RAINA INDA KAKE

DUTSE

NI ZAN LADABI

ZAKIN SARAKAI

WATA KOKOWAR

DA CIWO A ZUCIYATA

AURE YAƘIN MATA

AZAL

WATA TAFIYAR

*Shafi na sha bakwai (17)*

*TALLAH, TALLAH, TALLAH*

https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf

YAR UWAH SHI

N KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FOR

CE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*

πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ

πŸ‘‰

0912 262 1080

LABARI

Tund

a Hajiar Larabawa ta gama sallar magariba bata sauka daga saman dardumarta ba, tana zaune tana jan carbi har Baba Umaru karami ya shigo ya karasa ya duka yayi mata magana sannan ya tsaya har ta gama Jan carbin da ta masa alamun sai ta gama ta dube shi da k

ula ta ce" Kamani uncle din yara mu je"

Kama Hajia yayi ya mikar da ita sannan ya kamata suka nufi waje sunna tafe a hankali, Mama kuwa tana ciki ita da kanwarta sun kule tun dazu sunna tataunawa , sai yaran dake kai kawonsu, aikin gidan nan yau kaf su

suka yi, Hajia da kanta sai da ta girmama irin tarbiyyar su ta kuma karra ji a ranta eh lalle y'arta na zaune da zuciya daya da ya'yan mijinta

Har wajen da aka shinfidawa Hajia darduma ya kaita ya taimaka mata ta zauna bayan salamar da ta yi sannan da

kula sosai ta dan sada kanta tana sake gaisar da Baba Hamza

Da kula yake amsawa shima yana yi mata gaisuwa irin ta girmamawa da darajantawa sannan suka yi shiru na dan lokaci kafin a tausashe ya ce" Ya abinda yake faruwa tsakanin yaran nan? Allah dai

ya karra hakuri, Allah ya sanyaya"

Hajiar Larabawa ta murmusa da carbinta a hannunta tana girmama zumunci irin na mutumen nan, kuma sarai ta san harta dangin Elhaji ba wani shiri yake yi da su ba, ama wannan mutumen har yanzu bata hado su rigima ko wula

kanci ba, tabas a ciki akoy wanda ke hakuri da daya, Allah ya sa su dore a haka

A tausashe , cike da datako ta ce" A yanzu anya an kirayi yaranka da yarinta? rashin hakuri ne kawai, kuma laifin du na Usaina ne, yaya za'a ce ki dage mutun ba zai yi iko d

a ya'yansa ba a kan rigima irin taki? hujarta bata da Ζ™arfi ai Elhaji, aure akace ba wani abun ba, sai ki ce dole sai ya sanar maki wanda zai aurawa yara kafin a yi? Allah ya shiryi ya'yan zamanin nan da har suke musu da mazansu"

Aba yayi murmushi shima

ya ce" A'a fa Hajia, shima da kika ganshi Elhaji Ya'un ba dadi bane, ai bai dace ya boyewa uwar ba koda zai boyewa yarinyar, rabon dai a yi wannan rikicin ne, ama yanzu in sha Allah komai ya wuce an bar maganar auren, a kirawo min ita su wuce mu je , idan

aka zama daya ai ba'a yaji a bar gida, a gida ake yi, ina baba karamin, kirawo min maman yara maza su wuce mu tafi"

Uncle Umaru ya shigo ya wuce dan a kusa yake dama , waje dai ya basu

Jim kadan suka shigo, a lokacin da Hajia ke fadin" Elhaji me za'

a fasa? to ai Usaina haihuwarta aka yi, kuma magana ake yi ta mijinta wanda yake rike da gidansa ba wai ta isarta ba,wace Usaina kuwa da har mune zamu yi mata biyaya? sai ki karaso ki zauna marar kunyar banza marar kunyar wofi, kyale ki na yi, ban so ace s

un zo gidan nan da wuri ba da da kafarki zaki gudu da y'ayanki, Usaina ashe zan ga haka da raina? ki fito daga dakinki a kan maganar gaskiya ba ta cutarwa ba? ke mai y'a ko? usaina ke mai y'a ko?"

Sai kawai Hajia ta kama gefen hijabi ta ringa murza ido

kamar kuka take yi

Hankalin Mama ya tashi sosai

da sauri ta karasa ta duka gaban Hajia tana kama hijabinta tana fadin" Innalilahi Hajia kuka kuma? walahi walahi Hajia ba wai rashin kunya ko son y'ar nan ne yasa na yi haka ba, baba dan Allah ku gafarc

eni, walahi da ko a kan Karima in har bata ce min ta amince ba haka din zan yi,saboda Ni abu daya na roke shi ya sanar min waye zai aura mata, sannan ya bada dama su hadu su daidaita kansu, sai kawai yake zagayewa, Hajia walahi kin ji na rantse ba abinda k

ike tunani kennan ba"

Aba dai na kallonsu, abinda yake son fahimta yake so a kai wajen, dan haka bai hanna gumurzun Hajia ba, ya zuba ido yana kallo dan sarai ya gane bori ne take yi dan y'ar ta rikice

Hajia ta ture hannun Mama tana fadin" Kar ki da

ne min kafa Ni, meye in ba haka din ba? kina fadan wai an yiwa mijinki rashin kunya Karima ta gudu wai da wanda take so bata son wanda aka hada su, wai ko dan izala ne? kafuri ne? nace kafuri ne? akoy wanda ya kai dan sunna rike mace ne? kin manta waye uba

nki ko?, ko dai mai kudi kuke hange ya'yan nan? innalilahi wa inna ilaihi raj'une, ta yiwu so kuke yi ku aurar da yayan a hannun masu ku

Ι—

i shi yasa kuke neman sakawa marayan Allah ciwo kunna bijere masa, wai ke harda su yaji"

Mama ta yi dirshan kamar ka

ramar yarinya, ta karasa gaban Baba Hamza ta hade hannayenta hawaye na bale mata a tausashe ta ce" Baba, ka yarda da Ni, ban yi wannan abin dan in bijirewa babansu ba, sai dan na san maganata ko fushina babu abinda zai hanna, Baba shin laifi ne dan na nemo

Sannin asalin wanda za'a aurawa yaran nan? ko dan ina mace ne bani da wannan darajar da za'a sanar da Ni? baba dan Allah ka ba hajia hakuri in sha Allah ko wanene a aura mata, ba zan sake cewa komai ba, zan rakata da addu'ar Allah ya bata zaman lafiya a d

uk inda zata je, dan Allah baba ku yafe min gaba dayanku, in sha Allah na binne zancen ba zan kuma taso shi ba"

Baba Hamza ya yi murmushi yana kallon Mama, a tausashe ya ce" Ya isa haka kukan y'ata, tashi zauna da kyau kusa da mamanki mu yi magana"

M

ama tan goge hawaye ta koma kusa da Hajia ta zauna, Hajia kuwa ta wani kawar da kai sai kumburin take yi

Elhaji Hamza ya ce" Da farko dai ina neman afuwar wannan kai da kawo da aka yi ta yi da rikici kala kala, saboda ba kowa ya janyo haka ba Nine nan n

a hadasa haka"

Ya dan numfasa sannan ya dora da fadin" Nine na yi wannan abin da ya sa ya boye wanda za'a aurawa daya daga cikin yayanku, ba dan komai ba sai dan kwadayin na samawa yaron nan wace zuciyata zata aminta da halayarta , wato dai Hajia burina

shine in yi irin abinda muka yi in san da na bar baya mai kyau, dan ke kin san da ace bamu yi dacen uwar gida ta gari ba, da yanzu muna cikin gararin rayuwa "

Ya ajiye maganar yanzun ma a hankali kafin ya dora da fadin" Ba zan boye maku komai ba, sabod

a magana ake yi ta aure ba wai zaman kankanin lokaci ba, shi yaron nan dai shine daya cilo a wajen babansa wanda shima daya cilo Allah ya bani namiji da mahaifiyarsa har Allah ya amshi abinsa zuwa yanzu kuwa ban kara samun wani namijin ba sai shi jikan nan

nawa jal da ya Bara min"

Ya dubi su Hajia da suke dubansa a tausashe ya ce" Hajia, kin san doke za'a samu shakuwa mai karfi a tsakaninmu, akoy shakuwa sosai wace komai nake yi a rayuwa ina aunawa da tunanin halin dake iya zuwa ya dawo, duda na san ta y

iwu shi dinma ya rigayeni gidan gaskiyar? dan Allah keda komai , sai dai na fi raja'a a irgen yannayi da lokaci, a yanzu da na ba tamanin baya na san cewa a tare da ni take , a yanzu a nan tana iya daukana, wannan dalilin ya sa nake fama da abinda na riga

na san bani da iko da shi, sai dai addu'a da rokon ALLAH ya amince min, ya zamo abinda ke cikin ruhina ya tabbata, in samawa AL'WALID mace ta gari, wace zata zamo bango majinginar duk wani kai kawonsa, domin tun bayan rasuwar matarsa mahaifiyarsa y'arsa ba

n kuma samun gamsuwa da wa'inda ake nuna min matsayin matar aurensa ba, har sai da na gama dogon nazari na kawowa shi yaron nan Maganar bukatar ya bani daya a cikin yayanku na ba AL'WALID "

Ya dubi Mama dake kallonsa a tausashe ya ce" Y'ata, zaki yi tun

anin na so kaina da yawa ko? ko ko yi tunanin yaushe rabon duniya da irin haka, bale idan aka yi duba da gidana gidan yawa ne....., Ni da kaina na san na saka son rai a ciki, ama ki yarda da Ni har cikin zuciyata in dai ina numfashi ba zan yarda a cutar da

yarinyar nan ba, kuma ban nemi wannan hadi dan in mayar da ita abar tausayi ba"

Ya dubi Hajia da uncle Umar ya ce" Umaru, ta yiwu kai ka san kadan daga cikin abinda na yarda duniya ta sani a kan yaron nan da irin girman abinda Allah ya mallaka masa a r

ayuwa ko?, wannan fitinar da datin duniyar sun fi gigitani musamman da yarinyar wajena auta ke nuna min vidion yarinyar da suke tare yar gidan Kwamishina Maiga wace suke

Ι—

orawa a Tiktok, sai kawai in ji cewar a'a ba dai ita ba, wata, ba dan zan hanna a yi

da ita din ba, a'a, za'a yi da ita, idan Allah ya hukunta, ....uwar kurma nake nema, matar AL'WALID nake nema........, idan har Allah ya sa zaku amince ku fara bincike daga nan zuwa lokacin da kuka dauka in har kun gamsu da tarbiyarsa sai a yi, .."

Du

girman shekarun baba, da tsufa irin nasa ya hade hannayensa yana dubansu a tausashe ya ce" Ban shigo nan da isa ko takama ba, ban iso nan dan in boye wani abin ba, na zo ne dan neman iri, saboda na yarda da tarbiya da kuma nagarta, Nine na umarci yarona ya

boyewa jikkata wanda zai aureta saboda burina ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login