Showing 135001 words to 138000 words out of 200647 words

Chapter 46 - Farkon-Ganin-Idona-Book-Compeletex

08 Sep 2026

46

*Shafi na talatin da takwas(38)*

*IDAN KINA DA BUKATAR TALLAH KI TUNTUBENI TA LAYINA KAMAR HAKA 93811618*

LABARI

Baba Hamza ya dubi su AL'WALID a tausashe ya ce" Bari in kai shi shago in dawo, ina zu

wa"

Aba ya wani sakar masa harara yana cewa" Ka yi zamanka makaho ne Ni yi?"

Baba Hamza ya masa banza da hannu ya nuna masa su tafi

Haka Aba ya juya ya kama hanya baba na bin bayansa suka nufi waje

Bayan fitarsu ne AL'WALID ya dubi Malan Ya'u d

a har yanzu hankalinsa bai gama dawowa jikinsa ba, du yayi wani sokoko, gaba daya ba a hayacinsa yake ba ya ce" Baba, tun yaushe kake cikin irin wannan halin tsakaninka da D'an uwanka?"

Malan Ya'u ya dago ya dubi AL'WALID, sannan ya dubi Muhammad da ka

nsa ke kasa saboda tsabar tsoron abinda zai biyo baya na budar bakin da yayi ya fadi gaskiyar abinda yake faruwa bayan ya san cewa mahaifinsa na iya yin komai a kan shiga tsakaninsa da d'an uwansa ama ya aikatan saboda shi dinma ya raina shi ya raina umarn

insa?

Murya a raunane ya ce" Mene Elhaji?"

AL'WALID ya dan goge hancinsa a tausashe ya ce " Ka yi hakuri, jinninka ne, baka da wani makusanci sama sama shi a nan gidan duniya, ama ina son Sannin tun yaushe ka yarda ka zama abin wasansa ? i mn abinda

zai iya wulakantawa ya dora maka dukkan abinda ya yi niya a lokacin da yayi niya koda kuwa wannan abin na daya daga cikin abinda Allah Ya haramta.........., ka yi hakuri ka yi hakuri ama karya ai Allah ne ya haramta mana yinta ko? shine zai saka ka sabawa

Allah saboda wani dalili?"

Hankalin malan Abdullahi ya tashi sosai, ya zubawa AL'WALID ido cike da tunanin kardai ace shi fa Elhaji AL'WALID Baima yarda da maganar rashin lafiyarta ba?

Murya a dan hargitse malan Abdullahi ya ce" Elhaji yaya zan yi?

a kulun ina kokarin gannin koda zumunci ne mun rike mun bi umarnin Allah koda sau daya ne, ta yiwu mu samu rabauta ta hanyar zumuncin...."

"BABA, ba komai bane zumunci, wani abin wulakanci ne saboda abinda zai ba mutun damar kowani motsi ya ringa tuna m

aka da wata yar taimako da ya taba yi maka, ko ya ringa saka ka aikata abinda kuke gannin karami ne dan cinma manufarsa kaskanci ne...."

Ya dan dakatar yana duban baba a tausashe ya ce" Mutuncinka fa? mutuncin y'ayanka da?, shi zumuncin ai ba haka aka b

ayyana siffarsa ba, kuma wannan da kake gani a zaune ba laifi yayi maka ba, Baba idan abu ya zama shirme a koyi cewa A'A a abin koda kuwa zai batawa mutun........"

Ya sake yin shiru yana jiyo tafiyar baba Hamza saboda a bude ya bar falon , haka kuma yan

a jiyo Muryar Mufeeda na amsa waya , ya dora da fadin" Ni ba kwallo bane, da za'a ce dole sai an ciyo Ni, ba Nine kadai namiji a duniya ba, nd ina cikin hayacina har yanzu , ka yi hakuri kana iya sanar da shi cewa a yanzu na gama gane an riga an dage sai

an kai ga matsaya ne saboda abinda idan na furta sai kunya ta kamani., inada lmt wanda idan aka kai shi karshe ba zan kyale ba, ......a bani lafiya shi nake da bukata, a daina saka iyayena a lamarin da bashi da wani importance, ban saka mata zobe ba, ban b

ada dabino ba, plz a barni da maganar nan tun ban yi aiki da hanyar da nake da ita dan dakatar da abin ba!......."

Baba Hamza da ya shigo da salama yana tafe ne yana dariyar yadda suka kwashe da Aba, domin da suka fito Elhaji Maiga na jikin motarsa tsay

e da sigari a hannunsa wace yake zukawa, daga shi har shi sai da suka tsaya da mugun mamaki shine fa Aban yace ashe da d'an iska ake gardama?, to kuwa ba zasu bashi auren AL'WALID ba, shi kam baba tun nan ya ringa masa dariya yace da shi sai an bada, shine

fa aba yace kishiya za'a musu? ba'a isa ba, karshe da ELHAJI Maiga ya hango su sunna rikicin da sauri ya buya inda basu ankara na, domin har motar Aba ya leka bai ganshi ba yana fadin Ni fa kawai tumbina da ya harba zan rama, sai da baba Hamza ya ja shi s

uka fice ya raka shi har shago ya masa kwakwaran kashedi da fadin cewa gayanan dawowa ama kar ya ga ƙafarsa a gidan cen, shi ko kunya baya ji ne? a gaban sirikinsa yana fadin magangannun nan?, shine fa Aban yace shi kam Elhaji ai abokin zaman majalisarsa n

e, dan ya auri y'arsa ba shi zai cenza wannan alakar ba

Baba na neman zama a ransa yana ayana' Allah ya sa ba maganar suka tattauna ba, dan kuwa ba zan so su kaishi inda zai nuna hali ba, domin kuwa in har ya nuna hali akoy matsala, du hakurin nan da ya

ke yi sai ka raina shi saboda bai san a yi hakuri ba sai idan Allah ya sa shi yana kusa ne yake tsawatarwa a bari dan an isa da shi ba dan an kayar da shi ba

Fitowar Mufeeda ido yayi mata jajir ya saka su kallonta banda AL'WALID da ya yi mata kallo daya

ya dauke kansa

Murya a birkice ta ce" Wai me na muku na kiyaya ne a gidan nan baba?, babana yace ka hanna zamana a nan idan na zauna din me zan yi da zai cutar da wani a gidan ne?, dan me yasa kana yiwa kowa uzuri banda Ni? ka tambayi ra'ayinsa mana k

afin ka dauki mataki Baba"

Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, da ta san waye AL'WALID da bata yi tsaye a gabansa ta dagawa baba murya haka ba, domin hannayensa har rawa suke yi ya mike tsaye da hannunsa ya nuna mata hanyar fita ya ce" Mu je waje"

Bab

a yayi gagawar fadin" a'a fa, kana ji Elhaji karami zauna zauna, "

Mufeeda cike da dacin zuciya da bakin cikin halayar tsohon nan ta dauke kanta ta juya din ta nufi wajen saboda yace su je ne, idan kuwa su je ne haka din take so itama, dan tana son maga

na da shi, dama sai da ta fadawa babanta ya kyaleta da rigimar nan ita zata shawo kan abinta da kanta ama ya kiya, ta so yayi tafiyarsa , ta ci gaba da zuwa da komawa kamar yadda ta saba a da, domin a haka ne zata cimma matsaya ta kuma amshi AL'WALID dinta

, sai ya nuna ya fi so ace tana cikin gidan, gayanan mahaukacin brother din nan nasa da dan iskan dansa sun zo sun musu shirme a nan, ama ba komai ko kasheta AL'WALID zai yi a shirye take ya dawo mata irin na da, so ai ba karya bane, ita fa Bama ta kawo ma

ganar wata a zuciyarta, ta riga ta ajiye haka matsayin yayi ne dan ya horata, har akoy yarinyar da zata kaita wani abu ko ta fita matsayi a wajensa ne? shekara nawa suke tare ko ita ba dukkan abinda take so ta samu a wajensa ba, bale bakuwar yau yau? su zu

ba su gani.

Dan murmushi kawai ya yiwa Baba Hamza ya juya ya bi bayanta

Bai tsayar da ita ba sai da suka yi nisa kadan da bangaren su Hajia inna , a lokacin ne kuma Khadeeja da kurma suka fito daga bangarensa , khadeeja na rike da hannun kurma wace s

uka gama tsara zasu je su kwaso kayanta a dakinta su dawo da shi nan, domin tun dazu firarsu ne suke sha, harta docter da ta zo ta dubata ta tafi sai da suka birgeta, aunty shareefat kuwa wani farin ciki take ji a ranta da yarda cewar in sha Allah kurma ta

yi uwa, haka kuma da Khadeeja tafe su je haka kawai ta ji a ranta eh barima ta barta su je din ko Mufeeda ta ganta, dan ta tabata idan ta ganta ko y'ar faduwar gaba ce sai ta yi, saboda zata ga cewa ita Tata tsarin halittar ba komai bane a gaban ANMY!, ku

ma zata ga abinda suka gani gaba dayansu cewa ANMY fa zata samu abinda ke ba w

asu matan wahala cikin ruwan sanyi, koda yake dama ance idan ka ga ana gardamar kokowa babu kasa ne a wurin (





Allah ya sa haka karin maganar take)

"BAB" Mufeeda ta fada baya

n ta langwabar da kanta hawaye na bale mata

Idannuwansa da suka yi ja ya dora a saman fuskarta, lokaci daya yana jimke hannunsa ya dan dago mamakinta ya ce" A gabana?, Baba kike dagawa murya? ashe baki da tarbiya?"

Da irin abun kukan nan mai tafe da

yannayin rarashi wanda ya ba su Khadeeja damar jiyo muryarta ita, domin tunda suka gansu Kurma ta yi tsayuwar jin tsoron Mufeeda, ita kuwa Khadeeja ta samu kanta da zuba musu ido , Bama kamar mutumen da dazu ya fito daga dakinta, ta shaki numfashinsa ya sh

aki nata, ya hadasa kusancin da a yanzu a duniya idan bata da lafiya muguwar rashin lafiya ne kawai Mama, da yan uwanta yan mata ke kawo fuskarsu daf da Tata dan su ji abinda take fada, hakan ke sakawa har idan numfashinta ya fito ya shige hancinsu, itama

kuma har ta shaki nasu, ama shi a yau , ido bude kai sake cikin hayacinsa ya bata wannan abin , ya saka wannan baban kusancin da ya soki kirjinta har ya barta da wani irin tunani mai girman gaske, suturar dake jikinsa ta matukar haska shi ta yadda a yanzu

ma ya karra haska idannuwanta, a hankali ta bi kusancin dake tsakaninsu da ido kafin ta sake zuba masa idon shi, dan haka kawai wani baki da munin macen da suke tare yaa rufe mata ido., Mufeeda ta ce" Bab, ai ba zaginsa na yi ba, ba kuma magana na......."

"Ke har kin isa ki zage shi ne?, " Ya fada a kausashen da ya sakata dan ja baya tana rintse ido saboda fargaba, sai kuma ta bude idannuwanta tana fashe masa da kuka da sauri ta miko hannayenta zata kama nasa, ya janye yana sake yi mata wani kakausan ka

llo ya ce" Na fada maki, dabi'ar taba jikina itace babar dabi'ar da na tsana a tsakanina da ke saboda ina kokarin kiyaye hakkin adinina, Mufeeda bana son abinda zai sakani a yannayin bacin ran da zaki yi mamakina ama kina Kai ni wajen da zaki ga haka, kina

ji.......ki tafi gida , idan kin je ki wuce tare da su dady Niamey, zan neme ki."

Daga haka ya juyo da nufin yin tafiyarsa ne idannuwansa suka sauka a cikin na Khadeeja dake tsaye a inda take idannuwanta tsai cikin nasa

Idannuwan nata ta lumshe a ha

nkali ta cire daga cikin nasa ta kama hannun kurma a hankali ta ce" Mu je mu dauko kar yama ta yi litle am"

Kurma ta juyo dan ta ji Khadeeja ta dan matse hannunta ne ta dubi Khadeejar sai ta ga ba magana take yi ba dan haka ta sake juyawa inda babanta k

e kallonsu, Duda ba wai kallon kafewa da idon nan bane, ama ya dan kalle su ne, ya juya ya sake kallon su din nan

Mufeeda tunda ta ga irin kallon da yake musu, da kuma yannayin shigar Khadeeja, da kurma dake hannunta, da kuma alamun daga

ɓ

angaren da suk

a fito hankalinta yayi mugun tashi

Kallon Khadeeja take yi irin kallon nan na neman makusa a yan sekwani, kuma ta gani kam, kwarai ta ga makusar, haka kuma lokaci daya idannuwanta suka gama rufewa, kishi? kishi balaki ne, kuma idan ana so babu abinda ke y

in iyaka da abin so din nan sai kulawarsa , .....kwarai Mufeeda na cikin baban tashin hankali saboda abin yayi mata yawa ne da ya hadu da rashin mafada da kwaba, a irin wannan lokacin babu abinda ta fi buƙata irin rarashin uwa da kwaba da nuna gaskiya a ba

yane, shi kuwa uba ya zamo karma ya bada fuskar jin wannan lamari , domin idan har abu ya kai inda yake to kuwa a duniyar mu ta hausawa, idan kuwa ya kai inda yake tabas hukunci ne zai dauka mai tsananin da sai hankalin kowa ya tashi sai dai son zuciya da

kwadayin abin duniya ya saka ita uwar ta manta cewa Mufeeda fa sunnanta yarinya a duniyarsu, kuma koda akoy buri na son mallakar baban mutun da dukiyarsa da kyansa din nan, akoy soyaya mai tsananin gaske dake rike zuciya da dukkan wani tunani, basu sani ce

wa ba a halin da take ciki tunda har ta iya duban idannuwansu su iyayenta ta sanar musu cewar eh fa so din take yi mai tsanani ya dace su dawo hayacinsu su nemi mafitar tsira da mutuncinsu da na y'arsu ba, sai suka ga ai babar hujja ce da zasu tayata yakin

samun abinda take so, sai suka sake turata cikin ramin domin ai abinda take so din nan ba wai ita kadai ce ke so din ba, a'a, su din sun fita bukatar a yi abin saboda datin duniya mai hada uwa da uba fada ya riga ya lashi harshensu.

A hargitse ta dawo

gabansa ta bangaren da yake kallon su Khadeeja zuciyarsa cike da tunanin ina zasu je suka fito? me yasa suka tsaya suke kallonsu? lafiya?, me yake faruwa? me yasa da ta yi musu kallo daya ta dauke dubanta? me yasa bata tsayar da idannuwanta a kansa ya zamo

du motsinsa sai ya ga shi take kallo ba? me yasa bata fashe da kuka dan ta ganshi da wata ba? me yasa hankalinta bai tashi ba? eh ya san Yaushema aka hada su, ya san basu ma san junna ba da har haka zai iya faruwa ba, ama darajar aure ai ta isa ta sa a nu

na an damu da shi harma a yi masa kuka dan an ganshi da wata ko? ya dace a nuna masa mahaukaciyar damuwa da haka din saboda shi dai a iya haka da ta fito da mayafi filin gidan nan bayan hijab yace ta saka da zai fito sai ya ji wani abu a cen cikin ransa ir

in na kare hakkin addininsa ya dane masa kahon zuka

"Itace?" Mufeeda ta tambaye shi a hankali tana nuno inda su Khadeeja suke

Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, shi kam yau ya ga jaraba, wai da bata tafi ba?, .....shine kallon da ya sauke a kanta da

wani mamakin nata da tunanin wannan anya ba sai ya aikata mata halin da mata ke kiran an wulakantansu ba kuwa ko ta bashi lafiya?

Sai dai bai sani ba, bai san har inda mace mai so da kuma ta gaza dane zuciyarta da tsananin kishin abin sonta ke iya zuwa b

a, har sai da ya ga Mufeeda ta cire hijabin da ta sako har ake mamakinta da shi ta nufi inda su Khadeeja ke kokarin tafiyarsu dan ta gaza hakurin ci gaba da tsayuwar nan ta juyo kurma ta mata alamun su tafi

fa.........., sai ji ta yi da karfi an..........

.... fizgo hannunta dake rike da kurma an juyota sannan aka miko hannu da nufin za'a shake mata wuya

Cikin hanzari ya nufo su, dan babu abinda ya ayana sai zata karya y'ar mutane, sai dai yana daf da karasawa inda suke din ya ja ya tsaya yana zaro ido c

ike da matsanancin mamakin gannin lokaci daya Khadeeja ta tare hannunta ta damki tsintsiyar hannun ta dantse da karfe da faratunanta ta mika dayan hannunta ta riko wuyan Mufeeda, ba wai rigarta ba, a'a wuyanta ta rike taf, hakan ya sa mayafinta itama zamew

a, ama bata bi ta kansa ba saima sakin hannun da ta yi ta nemi kai Mufeeda kasss lebenta kuwa a dantse yake, idannuwanta ta zarro mata su sosai kamar zaka yiwa d'anka hukuncin nan dan ya tsorata din nan, a kausashe ta ce" In sha Allah daga yau kin daina ka

i hannunki jikin wata da nufin neman fada ko Wacece!"

Kakarin Mufeeda ya ankarar da shi daga summan tsayen da yayi, da kuma karasowar babanta da gudu gudu tumbinsa sai motsi yake dan a tsaye yake jikin motarsa yana haangensu yana jiran Mufeedan, ya wuce

su da nufin kama Khadeeja ya bambareta daga jikin Mufeeda yana fadin" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une ke saketa, Mufeeda me ya aike ki fada da y'ar mahaukaci? saketa saketa sakar min y'ata!"

Da sauri AL'WALID ya rike hannunsa yana jan baya da shi had

i da aika masa kallon da tunda suke bai taba yi masa irinsa ba, lokaci daya ya karasa inda suke din ya saka hannayensa biyu ya kama na Khadeeja ya cirata daga ita har hannayen nata ya dawo da ita jikinsa lokaci daya ya dago habarta ya.......

🥹🥹🥹🥹🥹🥹

🚶🏿

‍♀



🚶🏿

‍♀



🚶🏿

‍♀



🚶🏿

‍♀



🚶🏿

‍♀



🚶🏿

‍♀



🚶🏿

‍♀



🚶🏿

‍♀



🚶🏿

‍♀



🚶🏿

‍♀



07/12/2024, 15:16 - samiraharounayacouba:

🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺

*FARKON GANIN IDONA*

🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺

*LABARI DA RUBUTA

WA*

*SAJIDA NIJAR*

🇳🇪

*PAID BOOK*

*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login