Showing 129001 words to 132000 words out of 200647 words

Chapter 44 - Farkon-Ganin-Idona-Book-Compeletex

08 Sep 2026

17

kamar yadda kika sani, ko wanene kuma wannan Sannin gaibu sai Allah sai kuma lokaci zai bamu damar Sannin halayarsa, ko kuwa idan a kagauce kike ki samu

mijinki ku yi bayani, ki yi hakuri carbi nake ja kafin yan kai Gara su taru a hau wani aikin kuma"

Daga haka Mama ta sake jan hijabinta da kyau ta ci gaba da jan carbinta a nutse

Kasa magana amarya ta yi zuciyarta na kunna sosai, kawai sai ta juya ta

fice a dakin tana ayana' ba zaka taba Sannin abinda ke cikin wannan munafukar ba, a gama taron nan ki gani zan je da kaina a min binciken da ya dace a kanki kuma zan dauki matakin da ya dace!, in kuwa wani cikin ne da ke shima sai ya bi dayan in dai ina r

aye'

Bayan ta fita Mama ta jima tana kallon kofar da ta bi ta fita kafin ta sauke ajiyar zuciya ta dan hada tagumi na tunani......, wato ita dai ba zata taba so ace ƴaƴanta sun biyo hanyar da ta bi ba, shi yasa tun jiya har zuwa yau cikin tunani da addu

'a take, tana yi musu fatan inma auren wata mijinsu zai yi kar a hade su, ita kam bata ji da dadi har ga Allah, bale wannan yarinyar so take yi karfi da yaji sai ta kaita inda za'a ce lah Usainar da kanta ce ta yi abu kaza?

Ajiyar zuciya ta sake saukewa

kawai ta mike gannin takwasss ce zata yi ta cenza hijab dinta ta feshe jikinta da turare ta nufi bangaren Elhaji saboda ta ji bayani a kan masu kai garar dan ta tabbata yanzu sa hadu a je a kai a gama, cen kasan zuciyarta kuwa da Anmy ta kwana, tana ta tu

nanin yaya yarinyar take? duba da bata da lafiya.

A nutse ta tura kofar bayan ta bude daga baya ta shigo, sai ta ja ta tsaya sakamakon muryarsa da take ji yana fadin" Yauwa Habu, irin kallon nan da ka yi a gidan cen shi zaka fara yi, ya zama wajibi

mu ci uban mutumen nan, uban budurwar mijin Anmy ai kishiyanmu ne, in an jima karfe hudu na yama ku hau shadojin nan ku sameni a shago mu shiga motar mu je, Ni da ALLAH ya bani zaradan samari, in sha Allah sai mun ci ubansa, ku tashi ku je ku fara shiri"

Sunna mikewa mama ta shigo da sauri tana dubansu ta ce" Kai, innalilahi wa inna ilaihi raj'une, kai ku dawo min nan ku dawo"

Zaratan samarin nasu biyar suka dawo kawunnansu a KASSSSS saboda sun gama hardace Muryar mamansu ta zaman lafiya da akasin hak

a

Aba ya dubeta ya ce" To Gimbiya lafiya da shigowar sasafe haka?"

Mama ta dube shi , eh lalle, haka fa, zai ce haka kam

A tausashe ta zauna tana dubansa ta ce" Yanzu babansu fisabililahi ka kyauta kennan? me kuma kake son koyawa yaran nan? kar ka

manta fa du abinda ka koya musu zasu zo su baka harda a gida ne ko ba dade ko ba jima"

Ran Aba ya fara

ɓ

aci yana dubanta ya ce" Kin ga gimbiya ki kiyayeni? kin ga ki kiyayeni? su bani harda kamar yaya? so suke su shiga wuta ne? na ga ai ubansu ne Ni Ko

?, to bari ki ji y'ayana sun san zafina, nan na zo jiya nace maki an min rankwashi an harbeni a tumbi kika yi biris da Ni, yanzu da Allah ya bani masu tsayawa a bayana in ja abinda ya dace in ja sai kuma ki ce a'a? mutumen nan har nan ya tardoni ya wulakan

tani a gaban yan anguwa, kin san irinsu kuwa idan suka sakoka a gaba ka kyale ka shiga uku?, to dai ki ji da kyau walahi gadin y'ata zan yi, kafarta kafata, yanzu zan shirya in fita saboda tsaro, kuma ki sani daidai nake da ke da duk wani wanda zai ce a'a,

aikin banza ma kennan a tardoni har nan in ce a'a? baki isa ba gimbiya, kin yi tsugul, kuma ya batun da muka yi da ke na kai karar uban Mudansir? ai mun ce in an gama bikin nan zamu ke ki samo mana wani mai ilimin munafukan yahudawan ya yi mana tsaye a ru

fe uban yan iska, yaya kina kan batun ki ko Ni zaki cuta ki min halayar masu jan kunne?"

Mama ta yi tsuru tsuru, a zuciyarta fadi taken Innalilahi na shiga uku, ashe bai manta abin nan ba?, mu kai ƙarar baban Mudansir? na shiga uku Ni Usaina mutumen nan

sai ya kasheni hankalinsa zai kwonta?'

A bayane kuwa ta dubi yaran ta ce" Kai ku tashi maza ku je ku yi shirin makaranta, ku ajiye min kayan nan a nan!"

Sumui sumui suka mike suka yi waje, ta juyo inda Aba ya rike kugu tana kallonsa a tausashe ta ce

" Haba mana baban su Sidiku, jiya jiyan nan fa ka karra rike daraja a gari ka yi suruki, kuma sai a hangoka kana dambe fisabililahi ba zaka ji tsoron sirikin naka ya gani ba?"

Aba ya zabga mata harara ya ce" A'a!" sannan ya nufi ciki

Mama ta zarro i

do tana kallonsa ta bi bayansa a tausashe ta ce" Da kunya mana, haba mana, kaine fa sirikin AL'WALID guda"

Aba ya ja ya tsaya ya juyo ya nuna mata yatsa ya ce" Kin ga gimbiya ki rabani da jaraba? kin ga ko? in kin hanna y'ayanki bina ai Ni kadai na isa

in janyo maki fitinar, Allah kuwa sai na je, sai fa na hadu da mutumen man na masa jijigar da zai raba y'arsa da mijin y'ata dan karya ne a mana kishiya Allah kuwa!"

Ya shige dakinsa ya mako kofar ya bar Mama baki sake da hanci kamar ta yi summar tsaye

Ikon Allah, wanzan baka so a jikinka kennan, kishiya dai kishiya ce yake nufi ? lallema, lallema

Tana nan zaunen nan ya fito ya sha dakakiyar shada sabuwa dall, sai buga kanshi yake ya kafe hula a kansa ya harareta da gefen ido kasa kasa ya ce" Aiki

n banza da bata kishin mijinta, bari in je a ja gaban garar nan mu kai , in yi dukkan abinda ya dace , babu fa wanda zai dagawa y'ata hankali in kyale shi ko waye shi!"

Ya yi gaba ya bar Mama baki bude tana kallon sa

Da ya fito ya samu Mama Fateema

da Hajia iya sun zo sun sha shiga ta alfarma , sai kawai yace su tashi su tafi

Mama FATEEMA ta mike tana fadin" To yaya bari in sanar da Hajiar, bata dakinta ne"

Aba ya wani dauke kai ya ce" Wai wace wancan? Ni zata wulakanta ko FATEEMA? Ni zata hann

a fada ? kyaleta kawai mu yi tafiyarmu wancen bata kishin mu mu je, mu tafi"

Mama fateema a dole ta bi bayansa saboda guguwarsa ba zata iya ba, suka fita suka shiga babar motarsa ya shige gaba yana hararan ya'yan da hannu ya musu alamun zasu hade ya war

ci motarsa ya karra gaba, shi da yan uba sai dai hange!

_________________________________________

Barci mai cike da mafarkai irin wannan ta jima rabonta da irinsa, sai dai lokacin sallar asubahi na yi ta farka da kasala da ciwon mara na al'adar

da ta dan dawo mata kamar yadda ta saba yi mata

Wanka ta yi na kirki ta darji jikinta sannan ta fito ta bude akwatinta ta ciro fari kal din leshhh da Abansu ya musu tsarabarsa daga Dubai dandatsetse mai sanar da darajarsa da an kalle shi

A nutse ta

kimtsa domin ta san ko yayane a yau tana iya yin bakin fuskar da zasu dan kawai su kalli amarya domin amarya akoy farin jinnin wannan

Zama ta yi ta shiga hada allurar da zata yiwa cinyarta tsigar jikinta sai tashi take yi saboda ba son allurar take yi b

a, sai dai kuma rashin son nata ba zai bari ta bar kanta cikin ciwo ba tana ji tana ganni a irin wannan gidan kare kukan ka

Ta gama hada allurar ta ji dan kwankwasawa, tun bata bada damar a shigo ba aka murda aka shigo hakan ya sa ta yi tsaye tana ka

llon mai shigowar hadi da dan kashe girman idannuwanta

A nutse ya shigo, da salamar da ta fito daga makoshinsa kawai ya dan tsaya ya sauke dubansa a kanta

Walwalin da leshin ke yi kadai ya isa ya dauki hankalin mai kallo, ga wani dauri da ta kashe da

ya saka shi sake binta da kallo kafin ya dan kalli wajen kaffafuwanta sai kuma ya dauke dubansa ya karasa inda ta mike tana dan kallon gefe da gefe zuciyarta na kwasar barin nan irin na dazu

Allurar dake hannunta ya bi da kallo, kafin ya sake kallon

gashinta dake sake a bayanta

Kadara ce mai zafin gaske, subahanallah rikakiyar kadara ce mai zafin gaske yarinyar

A hankali ta bude bakinta kasa kasa ta furta" Barka da safiya"

Murya ce a sanyaye, murya ce mai zakin gaske, murya ce mai nutsuwa....

....Ya Salam.

Kasa amsawa yayi, ya dan dubi agogo ya ga karfe tara ce ta yi, dama ya shigo cikin dare ya ji jikin da zafi, ya jima ma a zaune kafin ya tafi dakinsa dan kar ya katse mata barcin, da asubahi kuwa da zai je masallaci sai da ya nufo dakin n

ata ya ga fitila a kunne sai kawai ya wuce dan an fara tayar da Sallah ,sai yanzu ya dawo bayan ya ga baba Hamza da Hajia inna sun yi fira sosai, a bangaren Nasa ma ya samu litle da aunty shareefat, sunna falon kasa yanzu haka, shine ya hayo ya shigo dan

ya ga jikin nata ya kuma sanar da ita bakinta dan ya ga kamar abin kari ne suka kawo

A hankali ya mika hannu ya amshi allurar , yana kallonta da kula sosai ya ce" Mu je asibiti"

Khadeeja ta lumshe idannuwanta, ba zata iya ba, bafa zata iya da bugu

n zuciyar nan ba, du idan ya budi baki sai kirjinta ya doka......................... innalilahi wa inna ilaihi raj'une

A hankali ta ce" Allurar ce zan yi "

Sauke seringin yayi daga saman allurar a nutse ya dan sake kallonta sai kuma ya girgiza kan

sa kawai bai sake ce mata komai ba ya nufi inda kayanta suke ya dan tsaya cike da tunanin abinda ya dace ya yi?, sai kawai ya dauki abinda yake kyautata zaton hijab dinta ne, ya juyo inda take din nan ya karaso

Yakan samu nauyin harshe dan bai san sunna

n da zai yi kiranta da shi ba, a lokacin da ya budi baki zai yi magana wayarsa ta ringa neman agaji

A nutse ya ciro ya karra a kunnensa a hankali ya furta" Babah"

Kanta ta daga tana kallon sajen fuskarsa , da amon muryarsa, a hankali ta

ɗ

ora dubanta

a jajayen lubanansa a lokacin da ya furta" Gara kuma?"

Baba Hamza ya ce" Eh walahi ka ga manyan motoci biyu sun shigo shake da abinci , gayanan shi uban yan rigimar ya min tsaye sai shasheka yake wai ya gaji da loda buhunnan shinkafar a bashi ruwa ya sh

a, Ni kam ya raina min wayo Allah kuwa, wai Gara, bayan nace masa kar a yi"

Karbar wayar kawai Aba yayi yana sakin murmushi ya ce" Asalamu alaikum wa rahamatulah wa barakatuhu "

AL'WALID ya dan yi kasa da dubansa, irin yadda ta zuba masa fararan idan

nuwanta masu

ɗ

auke da kwali sai da tsigar jikinsa ta tashi, haka kuma ya samu kansa da dan riko hannunta lokaci daya ya dan sado ta yadda zata ji Muryar a tausashe ya ce" Wa alaika Salam wa rahamatulah, Barka da safiya Aba"

Aba ya wani saki murmushi ya

ce" Fatan an tashi lafiya , ya gajiya, ya taro? ina Hajia ƙaramar fatan tana nan tana biyaya sau da kafa ko in ci ubanta?"

Daga shi har itan ido suka zarro, da sauri ta hade hannayenta idannuwanta waje har hancinta ba gogar nasa kasa kasa sosai ta ce"

07/12/2024, 15:15 - samiraharounayacouba:

🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺

*FARKON GANIN IDONA*

🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺

*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*

🇳🇪

*PAID BOOK*

*Y'AN NIJAR ZAKU T

URO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Ni

jar thank you

😍

*



LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA

Y'AR MAHAUKACIYA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA

BAK'A CE

KUTKALE

DUK NISAN JIFA

MAGE

IDAN KA RAINA INDA KAKE

DUTSE

NI ZAN LADABI

ZAKIN SARAKAI

WATA KOKOWAR

DA CIWO A ZUCIYATA

AURE YAƘIN MATA

AZAL

WATA TAFIYAR

*Shafi na talatin da biyar (35)*

*TALLAH, TALLAH, TALLAH*

https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf

YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN K

AWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN

HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*

💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼

👉

0912 262 1080

LABARI

"Dan Allah kace eh ina yi, Abanmu zai iya zane

ni da safiyar nan, gashi zazabi nake yi" Ta furta kasa kasa sosai, furucinta na dukan fuskarsa,

A hankali ya samu kansa da lumshe idannuwansa, a hankali yana dan sake dubanta kasa kasa ya ce" Alhamdulilah Aba, ama ka ga ai irin haka ke sakamu yin addu'

ar kary....."

Da wani irin sauri ta zarro ido ta saka hannunta ta rufe bakinsa tana girgiza masa kai

Ido ya tsura cikin idannuwanta har sai da ta sada dubanta ba shiri

A tausashe bayan ya yi aiki da hannun nata ya dan ciji yatsar ta saki bakin na

sa ya ce" Ganinan fitowa dan Allah kan maganar garar nan, yaya za'a bamu mutun kuma a bamu abinci?"

Aba ya wani cira kai ya ce" Kai haba dai, ai abinda yake faruwa ka ga an riga an gigitamu da harkar garar nan, ka kuwa san har saki ake yi saboda garah?

Shine dai aka dan kokarta karba zaku yi kar ka biyewa tsohon nan "

AL'WALID ya katse kiran saboda gaba daya yarinyar nan so take yi ta shiga jikinsa dan ta ji me Aba ke fadi, gaba daya yarinyar nan ta gama hadewa da shi sai faman mane kunnayensu da ju

nna take yi dan ta ji da kyau abinda ake fadi a ta dayan barin

A hankali ta dago da ta ji shirun yayi yawa ba amon Muryar Aba, shima kuma yayi shiru

Dan baya ta ja tana fadin" A'uzubulahi" haka kuma tana dan kikifta ido da janyewa daga jikinsa

Du

banta yake yi dai bai iya cewa komai ba,

A hankali ta ce" Walahi ban san har ka manemin ba, ina jin Muryar Aba, subahanallah ya zaka mane min?"

Ido kawai ya dan fitar yana dubanta, sai kuma ya yi murmushi ya dan nuna kansa, har zai yi tambayar da ta

ke harshensa sai kuma ya juya da dan hanzari saboda ba fa zai yiwu a bashi garah ba, yaya za'a yi wai a baka y'a sukutum kuma a hada maka da abinci? kennan ance ka ci ka koshi ka kirta mata rashin mutunci ko?

Har ya kama kofar ya dakata ya juyo , a hank

ali ya ce" Hajia karama, ki saka hijab din ki sauko mu je asibitin....., ba shawara na nema ba fa..........."

Daga haka ya sakar mata kofar ya fice

Khadeeja ta saki bakinta harda karkata kai bayan ya bar dakin

Gaba daya jikinta kanshin turarensa y

ake yi, innalilahi idannuwanta kuwa har gizo suke yi mata

A hankali ta dauki hijabin tana kallo, lokaci daya kuma ta saka, ta dauki jakar hannunta ta rataye ta rataya ta juyo a hankali ta nufi hanyar matakala tana ayana magana kamar haka' Inama ya'yan g

idanmu su ganni da jakar nan a haka ina saukowa? hahahaha su ga matan aure na saukowa daga dakinsu"

Hango iya da ta yi da mama fateema ya sakata saka dariyar farin ciki da gudu gudu ta karaso tana fadin" Wayo Allahna dadi, iya? mama? wuni kuka zo min ha

la?""

Iya ta zuba mata ido tana sake jan mayafinta ta dan leka inda su aunty shareefat suka nufa sunna kokarin kawo abincin kari kasa kasa ta ce" Zan ga Annabi idan na yi hali na gari, to wai ko irin yadda kudi ya rasa daraja hakama budurci? y'ar nan mu

ai sai mu yi sati a karkace ama ya'yan yanzu sai ki ga daram abinsu sunna da wata wakar yan soyayya"

Mama fateema ta kawar da kai tana yin kamar bata ji ba, Khadeejama ta yi kamar zata nutse kasa, haba dan Allah, wani budurcin kuma? wai ita iya bata ga

nnin babar mutun a zaune ne?

Iya ta sake dubanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login